Showing 81001 words to 84000 words out of 144575 words

Chapter 28 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28458

a haka bacci ya dauke sa me cike da mafarkai kala kala  .

>???>???>???>???>???>???
>???>???>???>???>???>???>???>???

Damshin kirjinsa da ya taba tane yasa ta kara sakin wata karar, a tsorace ta rufe idanuwanta zata bar wajan ya rike hannunta,a kausashe ya furta bude idanuwanki, ba musu kuwa ta bude idanuwan batare da ta kalle saba  me yasa zaki mun ihu a kunne , ba komai ta amsa masa,guntun tsaki ya saki iya mako gwaro  kalleni ki bani amsa kafun ranki ya baci , a hankali ta dago da kanta kafun tayi saurin kulle wa sabida arba da kakkarfan jikinsa da tayi,cikin rawar murya ta furta  bazan iya ba , gira ya dage guda daya kafun ya furta me yasa , da sauri ta furta  ba..babu kaya ajikinka  ,murmushine yake kokarin subuce masa a fuska amma ya dake batare da yyi murmushin ba, naji bude idanuwanki  , kara girgiza masa kai tayi  Allah bazan iya ba , jinjina mata kai yayi  okay tunda bazaki iya ba, amma kin iya ganin abinda ke cikin towel ko , bata san lokacin da tayi saurin toshe masa baki ba ,wani masifaffen kunyarsa na kara kamata tuno abunda bata mafarki kara gani ,kamar zatayi kuka ta furta  dan Allah kayi hakuri ,hannunta da ta dora akan bakin ya sumbata, da Sauri ta janye hannunta tana kokarin barin wajan, janyo ta jikinsa yayi kafun ya soma kokarin cire mata rigar jikinsa , hannun nasa tayi saurin rikewa tana zaro ido waje wasu kwalla ne yasoma taruwa a idanuwanta,kallanta yayi alamun menene, sun kuyar da kanta tayi kasa ganin taki maganane yasa ya kwace hannunsa da zai mayar kan rigarta, ringing din da wayarsa tayi ne yasa ya jiyo slowly kafin ya nufi d aya daga ciki, kamar yanda yayi zato abeey ne yake kiransa ganin tana kokarin tsinkewa ne yasa yadaga wayan, a hankali yayi sallama , shima a bangaran abeey amsa masa sallamar tasa yayi yana kallan ammey da sai faman sakin murmushi take tun lokacin da taji warkewar tahee dukda taji zafin abunda basma tayi sai bata nuna ba,tasa abeey da yace king ya saki yarinyar tunda wacce aka jiwa raunin ta samu sauki,tanbayar me jiki abeey yayi,kallan bayanta yayi lokacin da take kokarin shigewa cikin kofar dressing room dinsa yayi ,kafun ya masa da  Alhmdllh  a takaice, TAHNOON  abeey ya kira sunan sa kai tsaye, dan waro eyes dinsa yayi jin yadda abeey ya kira ainahin sunansa yau , na am abeey ya amsa masa cikin yar kasalar da ya faraji  inaso ka saki yarinyarsan, hukuncin da kayi mata ma ya isa haka ba sai ka kulle taba , da mamaki king yace  wace yarinya abeey ,basma  abeey ya kara furtawa , shi sam ya manta ma da ya kulle wata ma , tuno abunda tayi dazun yasa ransa soma bashi abeey  dakatar dashi abeey yayi,  umarni na baka  yana kammala zancansa ya kashe wayar, bin wayar king yayi da kallo kafun y zura hannunsa guda daya akan sumar kansa yana ya mutsata . Dakin dressing dinsa ya shiga ,ganin bata ciki ya gane ta shiga toilet ne , a nutse ya shirya cikin white din kaya me shegen laushi, sumar kansa kawai ya taje da ta kara yawa kafun ya feshe ilahirin jikinsa da daddadan turaransa me sanyaya zuciya , yana gama shiryawa ya fito daga dakin, dakin da ya kulle ta a ciki ya nufa bayan yasaka turn print dinsa,
Ba a ganin komai na dakin sabida yan da wajan yayi duhu sosai , light din dakin ya kunna,kwance ya hangota a sume kan carpet din dake cikin dakin , babu komai a ciki sai wasu cushions da aka kawata dakin sai ya zama kamar na hutawa , a hankali ya tako inda take ganin bata motsine yasashi nufar fridge din dakin, wani ruwa ya dauka me shegen sanyi da ya fara kankara yana zuwa inda take ya bude ruwan tare da zazzaga maga shi, a matukar firgice ta farka daga suman da tayi tana faman zare ido, ganin har yanxu ruwan be dena zuba bane yasata sakin kara cikin firgita, tsawar da ya daka matane yasata shiga taitayinta,a mugun tsorace take kallansa da bakinta daya kunbura, nuni da yayi mata tayi mishi shirune yasa tayi saurin kame bakinta hawaye na tsiyaya da sauri sauri a fuskarta,dan ran kwafowa yayi kallo daya yayi wa fuskarta ya dauke kansa, a kausashe ya soma magana  Daga yau, ko me kama dake na kara gani a kusa da matata, sai na la antasa ballantana ke da ko matsayin dan kwalin kanta baki taka ba yana kai karshen zan cansa ya nuna kofa da hannunsa , kafun na irga uku ki bace mun anan idan ba haka ba sai dai a sauki kasusuwanki  be rufe bakinsa ba ta arta a guje dukda yadda kafarta da fuskarta tane zugi, ba ciwon da yaji matane ya fi bakanta mata ba, matarsa da ya kira shine ya fi komai tsaya mata a rai,koda ya Fito daga dakin,lifter ya hau direct ta kaishi hawa saman sa, koda yashiga ne shiga daki ba, dakin da ya taba shiga nan ya shiga ,me aku a ciki kallan sararin samaniya yayi ganin yadda stars suka fiffito ga duhu da Garin yayi, sosai yanayin yayi masa dadi, kan wasu chairs ya samu ya zauna yana kara bin stars din da kallo har wajan karshe shabiyu kafun ya sakko down stairs , dakin da take ya nufa, koda yashi a cikin bargo ya sameta duk ta takure jikinta, sanyin Ac din ya rage sosai kafin ya taba goshinta, temperature dinta ya fara dawowa normal, dan goshinta da akai wa dressing ya bi da kallo kafun ya gyara mata abun lullubar tata,alwala yayi tare da kabbara sallah kamar yadda ya saba, bayan ya idarma karatun alkurani me girma yayi kafin ya kashe light din dakin gabaki d aya yana janyota jikinsa.


ASUBA TA GARI & .

>???>???>???>???
>???>???>???>???>???>???>???

ABUJA

CEDARCREST HOSPITAL LTD

Karfe 8:30am ta shigo dakin da yake , ganin ya rakube ne yasa jikinta yin sanyi, yana ganinta yayi saurin kokarin tashi, dakatar dashi tayi tare da karasowa inda yake,kallan abubuwan da tasa akawo masa tayi ganin babu abunda ya taba,  me yasa bakaci abunda nasa a kawo mata ba , jiki a sanyaye ya furta na dauka bazaki dawo bane ,kwallar dataji tana kokarin zuwar mata tayi saurin hadiye kafun ta ja plate daya serving dinshi me yasa kake tunanin zan tafi in barka, as I promise bazan tafi na barka ba , da zaran na dawo daga tafiya na zan zo na d auke mubar musu ganin gabaki d aya kaji  girgiza mata kai yayi tare da saurin bude bakinsa ta saka masa chicken din daga debo, da kanta ta dunga serving dinta, bayan ta gama shima ya karba ya bata,wata irin kaunarsa yaron ne taji ya shigar mata zuciya farat daya. A asibitin ta zauna har yamma tana tare dashi,sosai ya bata labarin su oumma da tahee har ta soma kwadayin san ganin su, taji dadin hirar tasu ko ba komai ya debe mata kewa , wata kafceciyar waya ta dakko a cikin Jakarta kafun ta mika masa, idan na tafi zamu dinga yin waya da kai kaji , zaro idanuwansa yayi hawaye na zubar masa  dagaske zamu dunga yin waya  gyada masa kai tayi  kwarai ma kuwa ,kara mika masa wayar tayi ganin yayi shiru be karba bane ta kallesa me yasa bazaka karba ba oumma zata mun fada ita da taheer ,kallansa tayi tana nazarin kalamansa tabbas mahaifiyarsa ta bashi tarbiya  bakaso ka dunga gaisawa dani kenan girgiza mata kai yayi  inaso ok karba , hannu bibbiyu yasaka ya karba, hawaye na zubo masa ya dunga yi mata addua har saida ta tsayar dashi kafun ta nuna masa yanda ake anfani da wayar bayan ta fito masa da games da yawa a ciki. Ba ita tabar hospital din ba sai 9 bayan ta masa alkawarin dawowa gobe da safe suyi sallama.


?'?'?'?'?'?'
?'?'?'?'?'?'?'?'

8:30am tsaye tahee take gaban mirrorn dakin tana faman taje uban tulun gashinta ,gaban goshinta duk ya jike da ruwa har ya fara taba dressing din da akai mata,dan guntun tsaki ta saki lokacin da take kokarin tufke kan, kamar ta saki kuka haka take ji,ganin ta kasa sakawan ne yasa cikin haushi ta jefar da ribbon din, yana tsaye jingine jikin kofa , tun lokacin da ta fara taje kan ta ya shigo cikin dakin,ribbon din data yar dar ya je ya dauka haryanxu bata Ankara dashi ba saida taji ana ta ba mata gashin kai,baki ta bude daniyar kwala ihu , if you dare  ya furta kalmar a fusge, kallansa tayi sosai ta mirror ganin shidin ne da gaske yasa ta sakin ajiyar zuciya da harshi dake kusa da ita sai da yaji, gashin kan nata ya tufke kafun ya kalli dressing din da yayi mata  wa yace ki sawa ciwan naki ruwa , in ina ta soma ganin ya zuba mata rikitattun idanuwansa kwata kwata fuskarsa ba fara, sun kuyar da Kai kawai tayi tare da furta  ina wanka ne ya dan jike , be ce mata komai ba ya juya da niyar barin wajan yaji saukar muryarta  ina kwana , dan waiwayo da fuskarsa yayi kadan ya kalleta batare da ya amsa gaisuwar tata ba karki bata mun lokaci am waiting for u now , yana kai karshen zancenta ya fice a dakin,hararar kofar da ya fita tayi cikin kwaikwayar muryarsa ta furta , karki bata mun lokaci am waiting for u now  , sai kace wani baba na , cikin sauri kuma ta dauki hijab dinta gudun karya zo ya sameta a dakin, a tsaye yya tarar dashi har ta fito be kalli inda take ba sai ma kofar fita da ya nufa,ganin hakan yasa itama ta tabe bakinta tare da nufar kofar,yana fitowa zaki ya sara masa har ya bude masa kofa king ya dan girgiza masa kai tare da miko masa hannu,tsaya wa tunanin me ze basa yayi sai ji yayi king yace masa  the key waro idanuwa zaki yayi cikin suman tsaye jin ya anbaci key,idan zea iya ranshewa karshen ganin king ya tuka mota da kansa tun lokacin da yake zuwa hutu ne, the key" ya kara anbata, da sauri kuwa zaki ya bashi key din cikin girmamawa,wani dan karamin file king ya mikawa zaki , ba tare da yace komai ba ,shima zaki jinjina masa kai kawai yayi tare da barin wajan, motar da aka fito da ita , shiga ciki yayi tare da tayar da ita,kallansa tayi ganin be ce mata komai ba ta rasa ya zatayi,batare da ya jiyo ba ya furta  kika kuskura na kara cewa wani abu rankine zai baci , be kara kalmar tasaba tai shahada Kawai tare da shiga front seat din motar,Kai tsaye part din dada ya nufa yana gama tana binsa a baya kamar wata jaka,dada da su abeey kawai ya tarar a falon , tana ganin tahee ta soma washe baki  oh ni yau Allah ya kawo ni lokacin da zanga tahura batare da ta buya ba sun kuyar da kai tayi kasa tare da gaishe ta , amsawa dada tayi tana godewa Allah, su abeey ta gaisar yanxu kafun ta gaishe da su uncle Saleem da suke mata ya jiki,Shigowar mahma falon ne yasa ta gaishe da ita tama , cikin kulawa take tanbayar ta ya jikinta ,king ma gaishe da iyayan nasa yayi daga nan be kara cewa uffan ba ,shi dai abeey lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi musamman kunyar yarinyar tana burgeshi. Ganin taki sakewa ne yasa mahma janta da hira , mikewa king yayi , kallansa abeey yayi  ina zakaje son  ammey ya furta wa abeey kallan tahee abeey yayi  daughter tashi ki bishi kuje ,Allah yayi muku albarka baki daya  Ameen kowa ya ansa masa kafun subar part din, sosai take zumudin ganin aunty ta yanayin parking ta fito da Sauri ta manta ma tare da wa take, tsaye ammey take tana duba abincin kan dinning sai ji kawai tayi an rungumeta ,da Sauri ta juyo dan ganin wanene, ammey nayi kewar ki , tahee ta fada tana fashew da kuka,itama Ammeey hawayene ya fara zubo mata a tare suka kara rungume junansu suna yin kukan , ganin kukan nasu ba me karewa bane yasashi karasowa Inda suke hannu yasaka ya sharewa ammey hawayen nata, tare da kallan tahee ,rikitattun idanuwansa ya sa mata be ce komai ba ya kama hannun ammey suka zauna a falo, yayi farincikin ganin wannan murmushin na ammey da ya dawo, abinci ta saka musu su duka ta hada tana bawa a baki , TAHEE kam kadan taci tace ta koshi kasantuwar king a wajan. Sun dade a part din ta kafun su nufi part din ummey, itama sosai tayi farin cikin zuwansu, zoya ma tana ganin tahee ta nufeta wai suje suyi wasa,cikin jin kunya ta saki murmushi tuno lokacin da suke wajan , hira sosai zoya ta dunga bata har saida king ya dakatar da ita, lumshe idanuwa tahee ta fara , tun shigowarta falon ta fara jin jiri jiri da wani abu kamar yana kiran sunan ta , daurewa kawai take , ynxu ma jirin da take ji ne yasa ta yin shiru, sun kara kusan mintuna 5 a part din kafun suyi mata sallama itama , tana fitowa daga part din taji wani d irin juwa ta kamata kamar wacca aka bangaja zata fadi kenan king ya rikota,itama cikin tsora ta rike hannunsa sosai kamata yayi suka shiga mota, ganin yadda take sauke ajiyar zuciya ne yasa shi taba goshinta,normal temperature dinta yake , part din mahma ya mayar da ita , zata fita ya rike hannunta , are you ok  amsa masa tayi da ka kafun tace masa  eh tana shiga ta tarar da sha aban zai fita ,cikin girmamawa ta gaishewa, shima amsa mata yayi kafun yayi mata ya jiki , ganin kiran king yasa shi saurin yi musu sallama tare da barin part din. Hira suka fara duk da tahee tana nonnoke mata ,amma sai da tasa ta sake da ita, wani boil babba mahma ta miko mata tare da umartarta ta cinye komai da ke ci, ba musu ta karba kuwa ,loma daya tahee tayi kamar me shirin yin amai, cikin narai narai da ido ta kalli mahma, fahimtar haka yasa mahma hade ranta batare da ta bata damar yin korafi ba.


>???

=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?




Mss Lee =ؖ?
=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY=ؖ?=ؖ?
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?

=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?

PAID BOOK
MAIBUKAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE =ؖ?

BOOK 1=???

PAGE 47_48=ؖ?

Har kusan 3 na yamma tahee tana bangaran mahma kafun ta nufi bangaran ammeeyn ta acan ta yini sosai ammey take kula da ita, har tsawan wannan lokacin kuma bata ga yan matan gidan ba har ynxu kuma ba ayi magana akan warkewarta ba. Yan zuma kunun ayar da ammey ta hada ta bata sai faman tashin kamshi yake, tana kammala sha dakinta ta nufa wanda tuni an gyara mata,bin dakin tayi da kallo ,dan murmushi kawai ta saki kafun ta dakko wani material purple me simple style, Wanka kawai tayi tare da kwantawa jin kanta ya dan fara sara mata,ribbon din kanta daya takura mata tacire, take a wajan dogon gashin kanta ya sakko har wajan kwankwasanta, shima mayafin material din jefar dashi tayi a kasa ta kwanta, ba dadewa kuwa bacci ya dauketa.

7:01 pm ammey ta shigo dakin sanye da hijab a jikinta, kan gadon da tahee take ta nufa ganin tana baccinta cikin kwanciyar hankali, shafa gefan fuskarta tayi kafun ta kira sunan ta a hankali  Tahee , bata amsa ba sai da ammey ta kara kiran ta har sau biyu kafun ta motsa, a hankali ta fara ware idanuwanta kafun ta bude su gabaki d aya ta sauke kan ammey, murmushi ta sakar mata, itama ammey martanin murmushin ta Mayar mata oya a tashi a yi sallah, yanxu zan sa asabe ta kawo miki abinci,and idan an idar da sallahr isha i zamuje part din abeey yana nemanmu ,a sanyaye ta amsa mata da toh ammey. Ammey na fita itama ta mike ganin lokaci na tafiya ,alwala tayi tare da kabbara sallah, ta idar kenan ta soma kukan da ya rike mata makoshi, sosai take kukan ,oummanta da taheer take yiwa addua da kyar ta tsayar da kukan da take tana sauke a jiyar zuciya, idanuwanta har sunji jajawur da su, tana zaune kan sallayar asabe ta kwan kwasa kofa , bata izinin shigowa tahee tayi , bayan tayi mata ya jiki sannan itama ta fita,bataci abincin da aka kawo mata ba sai da ta idar da sallar isha i , shima dan tsakura kawai tayi sabida yanda ranta yake ba dadi, gudun kar ammey tai ta jiranta, ribbon dinta kawai ta saka tare da rolling din mayafin kayanta,turaren ta, ta saka dan kadan bame hawa kai ba tare da fitowa falo, kamar kuwa ta sani itama Ammeeyn ta shirya cikin ado na musamman cikin wata golden din Abaya ,tana ganin tahee ta sakar mata murmushi tare da furta  tabarakalla,daughter wannan kyau haka ko sarauniyar kyau albarka murmushi kawai tahee tayi ,kama hannunta ammey tayi kasan tuwar basu da nisa da part din abeey yasa cikin dan kankanin lokaci suka karaso.

Gabaki d aya family din suna zaune a babban falon abeeey tun daga kan dada har zuwa kan zoya da tana ganin tahee taje ta rungumeta. Gabaki d aya mutanan falon maida hankalinsu sukai kan tahee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login