Showing 99001 words to 102000 words out of 144575 words

Chapter 34 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28404

tsaki ta saki a fili ta furta  Allah ya shiryeni  tana daukar paper har zata saka a trash bin dan karami dake wajan sai ta fasa tare da bude ta , Rubutun da tagani ne yasata jefar da takardar zuciyrta na tsananin bugu, kara kallan paper din tayi da kyau tana karanta ta , bata gasgata abunda yake ciki ba ta dan goge idanuwanta , d same kallarce a jiki KILL YOUR HUSBAND shine dai still a jikin paper din sai wani dan karamin zare ja da ya fado, a matukar rude taja baya in bata manta ba ta taba ganin zaren wata mata ta jefo mata tana dariya a cikin baccinta,yanxu ma kuma ta sake ganin zaren, Bismillah tayi ta dauke zaren tare da paper harzata yardar sai kuma ta fasa ,cikin dakinta ta koma , wani dan karamin locker da ba kowane zai kula da itaba tasaka paper da zaran a cikin tare da kullewa , har yanxu bata dena mamakin paper data gani ba musamman Rubutun ciki  KILL YOUR HUSBAND ta kara nanata kalmar, tunani take so tayi Akan paper amma komai ya tsaya mata, ganin kanta na kokarin ciwo ne yasata ajje tunanin a gefe daya ta sakko down stairs din adai adai lokacin dasu zoya suke shigowa parlorn ita da su ihsan.da gudu zoya ta rungumeta ,itama rungumetan tayi ajikinta tana sakin mata dariya , kallan su ihsan tayi da suke shigo da trays a hannunsu,  bismalla  ta furta musu binta da kallo sumayya tayi dan batayi tsammanin jin haka daga gareta ba, zama kowannansu yayi kafun ta gaishesu tana sakin murmushi, suma gaishe tan sukai dan kwata kwata basu kawo tana da saukin kai hakaba , tunanin me zata kawo musu tayi kai tsaye tanufi kitchen , wasu manya robobine masu shen kyau da girma a gefe, dan bubbudesu tayi taga garane cike a ciki, Baban trays ta dakko ta zuzzuba musu aciki tundaga kan dublan, cincin , har abunda bata sani ba saida ta zuba musu ta kawo musu, still saidata koma ta dakko musu lemo da ruwa data gani shake a fridge, binta kawai suke da kallan, tana zama ta sakar ta sakar musu murmushinta da baya boyuwa bismilla ku , suma martanin murmushin suka mayar mata ,
sumayyace ta furta  mungode  , yaya fa firdausi ta dan tanbaya,cikin dan jin nauyinsu ta furta  ya dan fita , daga nan babu Wanda ya kara cewa komai sai zoya dake faman hira da tahee cikin wasa itama taheen tana bata amsa , su ihsan sai binsu da kallo suke dan sosai suke mamakin shakuwarsu,basu dade ba suka tashi zasu tafi kamar zatayi kuka,dan ko bakomai sun debe mata kyewa,kitchen ta koma tadakko wasu designers back masu kyau ta juye musu garan da ta zubo musu,kallan zoya tayi  amma zaki zauna ko , zaro funny eyes dinta zoya tayi ,ummey nace karna zauna akwai islamiyya yau ,amma zan dawo gobe muyi game , Tom shikenan kizo da wuri kinji,Jini jina mata kai tayi har bakin kofar falon ta rakosu tare da mika musu bags kin,suma cikin girmamawa suka karba ko ba komai ta karramasu, ku gaishe da mutanan gidan  ta fada tana sakin musu murmushi, suma martanin murmushi sukai mata kafun su bar part din, ganin ana kiran sallah yasa ta koma sama tayi sallanta, bataci abincin da aka kawo ba sai gyara su da tayi a dinning har lokacin king be dawo ba.

>???>???>???>???>???>???

Karfe 4:30na yamma ta koma sama da niyar yin wani Wankan gani tayi kamar ana binta da sauri ta juya amma wayam babu kowa awajan , sharewa tayi tare da cigaba da tafiyar tata , tana shiga dakin Daidai zata nufi toilet ta karajin mutsu mutsu kamar na taku, da sauri ta kara juyawa Dan yanxu abun ya fara bata tsoro, bin bakin kofar ta farayi da kallo ko zata mebinta, wuff taci abu ya wuce ta gefen kunnanta, addua take so tayi amma bakin nata ya kasa motsi , karabi ta kunnan ta akai ta saki wata iriyar kara, launikan idanuwanta ne suka canza zuwa launin ja sosai mutsun nan yazo zai kara giftata, taku ta d aya tayi ta shako wuyan abun ,take a wajan wata bakar kuliya ta bayyana bakakirin da ita hatta idanuwan Magen baki ne babu ko digon fari a ciki, mutsu mutsun kwace kanta tasoma yi amma ta kasa ,sai wani irin gurnani da take saki, sai ayanxu bakin tahee ya bude ta soma karanta adduoin da oumma ta koya mata,kara Magen ta somayi da karfi ,itama taheen kara sautin karatunta tayi tana makurewa Magen wuya,tana karatun tana lumshe idanuwa Sabida wata iriyar juwace take neman kada ita, daddagewa tayi tanaka Magen da kasa ,aikuwa tana buguwa ta saka wata iriyar kara kafun ta bace battt a dakin, tsugunnawa tayi tare da dafe kanta dake neman cirewa daga jikinta, wani irin kuka ta fashe dashi jin yanda kanta ke sarawa da karfi,ta dade a tsugunne dafe da kanta sai faman kuka take kamar wacce tasoma fita daga hayyacinta, turo kofar dakin yayi a hankali kafun yayi sallama , yanda ya ganta a tsugunne ne yashi karasawa wajan ta da dan sauri sauri, yana dagota ta fada jikinsa tare da fashewa da wani saban kukan har yanxu hannunta rike da kanta, kallanta yayi kafun ya furta  meke damunki kasa yi mishi magana tayi sai kanta da take nuna masa, kallanta yayi kafun ya taba kan ,sosai yayi wani irin zafi na ban mamaki,cikin sarkewa ta furta  Kayi mun addua , da sauri ya dauketa be zauna ako ina ba sai akan gadon , jingina yayi da jikin gadon tare ta dora ta akan cinyarsa yana kama kan,addu oi ya fara tofa mata , ya dau kusan 20minutes yana tofa mata adduar , wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke jin kan yadena yi mata ciwon kwata kwata,lafewa tayi ajikinsa tana shakar kamshin jikinsa me sanyaya zuciya ,kafun a hankali ya furta  me yafaru , amaimakon ta bashi amsa sai cewa da tayi  ni yunwa nakeji kallanta yayi da mamaki bakici abincin da aka kawo miki ba kanta ta daga masa alamun eh, dan Jim kadan yayi kafun ya dauketa gabaki d aya ya sauko kasa da ita dakansa yayi serving dinta kafun ya bata a baki, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta ya kamata ki dunga cin abinci sosai sabida duk lokacin da ajiyata ta sauka bazan lamunta ba , bata gane me yake nufi ba ta dai daga masa kanta kawai, wani irin murmushi ya saki yana lumshe mata idanuwa. Janyota jikinsa yayi kafun ya soma shinshinar wuyanta, da sauri tayi kokarin janjikinta amma ya hanata hakan, Yaushe zaki bani abunda nake so kallo na irin ban gane din nan ba tayi masa ,sarai yagane bata gane ba ,sai kara janyota dayayi jikinsa, I want you here with you , kasa motsi tayi jin yanda kamshin bakin sa na strawberry ke shiga cikin hancinta, zanyi wanka, come and help your dad, daman kin taba mun alkawari zakiyi mun wanka ,to lokaci yayi zomuje oya , waro masa idanuwanta tayi tama kasa magana ,hura mata iskar bakinsa yayi da Sauri ta lumshe tana sakin ajiyar zuciya, kayi hakuri&  be bari ta karasa zancan ta ba ya hade bakinsu,sai da ya tsotse mata baki tas kafun ya janye bakinsa,kallan yanda ta soma hawaye yayi kafun ya dauke kansa, it s ok  ya furta be kuma cewa komai ba ya haye sama,ganin yanda ya wuce din sai taji bataji dadin abunda tace masan ba, tsawan lokaci tana zauna tunani ta fara ta bishi ko karta bishi, daga karshe zabin zuciyarta tabi ta hau saman, tana shiga dakin taga wayam bayanan atunanin ta yana sauran dakin,d aya bayn d aya ta duba duk baya ciki,sai yanxu white room ya fado mata,da Sauri ta nufa saman tana bude kofa yana kokarin shiga dressing room dinsa da bathrobe a jikinsa blue colour , idanuwanta ta kulle ganin ba Kaya a jikinsa a hankali ta furta kayi hakuri  bece mata uffan ba ya shige warsa, zubewa kasa tayi tare da fashewa da kuka ganin be kulataba, bude kofar da yayine yasata dagowa , hannu d aya kawai ya mika mata bata san lokacin da ta karasa wajan sa ba , daga ta yayi gabaki dayanta be tsaya ya nufi toilet hanyar toilet da ita, da mugun sauri ta fara mutsu mutsun kwace kanta  bana so yace mata a hankali be kara bata wani damar ba ya shige toilet da ita tare da turo kofa , kusan mintuna 30 kafun ya bude kofar yanxun ma dakko ta yayi amma ko sau daya bata dago da idanuwanta ta kallesa ba, sai ma kara Boye fuskar data keyi,dauke kansa yayi kamar be ga me take yi ba, yanxun ma duk mutsu mutsunta shine ya shiryata da kansa kafun ya nufi masallaci, yana fita tunanin abunda ya faru take kokarin tunawa ganin kanta na kokarin ciwo yasa ta kawar da zancen tare da kabbara sallah.

****karfe tara da rabi yashigo dakin ganin ta a kwance kamar me bacci yashi kashe mata light, shaf shaf yayi wanka ya kwanta a gefenshi duk tana jin motsinsa,ya gani yau shiyasa kawai ya janyota jikinsa ya rungume wani irin bugawa kirjinta ya somayi da sauri sauri,jin hakan yasashi sakin murmushi me dan sauri a bazata ya rada mata  don t worry babu abunda zan miki ,inasan jin dumin matatane  ,wani ajiyar zuciya ta sauke duk da ba yaune ta fara kwana dashiba amma wani irin tsoranshine ya shigeta a haka har bacci ya dauketa, shima gyara mata kwanciyar akan chest dinsa kafun wani bacci ya d auke shi shima.


>???>???>???>???>???>???

WASHE GARI yau ma ana kiran sallar asuba ya farka yayi alwala batare da ya tayar da ita ba,itama ba dadewa ta farka ganin bayanan yasata sakin ajiyar zuciya ,shaf shaf tayi wanka tayi sallah ,tana idar wa ta fara gyaran gidan kamar me aljanu shaf shaf ta gyara floor 3 din duka sai wajan 8 ta dakko ganin ko ina kal kal yasa ta mamaki, down stairs ta sakko ta tarar da kulolin abinci , ajiyar zuciya ta sauke tare da dan kikkim tsa abunda beyi mata ba. Da sallama a bakinshi ya shigo part din, amsawa tayi tana binsa da kallo har ya karaso inda take ina kwana ta furta , dauke kansa yayi daga kanta ,ganin be amsa mata ba ysa ta kara furta  ina kwana dady , yanxu ma be kulataba yayi kokarin wucewa ,batasan lokacin da ta kamo hannunsa ba , da karfi ta lumshe idanuwanta ta sumbaci kumatun ta, murmushin gefan fuska ya saki kafun ya furta  lapiya Lou  , dan karamin ajiyar zuciya ta sauke , shima kama hannunta yayi Kai tsaye suka nufi dinning, serving Dinsu tayi kowa a plate dinshi amma ya matsar da nashi plate din ya matso da natan,dan bude bakinsa yayi kadan kamar lokacin da bata da lapiya da tayi masa, abincin ta dakko a spoon zata bashi ya cire spoon din ya sa hannunta ganin hakan yasa ta fara bashi a baki da hannunta da ke wanke tas dasu kadan ya ci ya kawar da kansa kafun ya fara bata itama a baki , dan dole kuwa ta amsa , suna gama ci falo suka nufa be bata damar zama a ko ina ba sai akan cinyarsa da ya dorata,itama batayi musun hakan ba , gabaki dayan su shiru Sukai ba me magana a hankali ta furta  naga angyara 2nd floor and kasn nan kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya furta  su ihsan ne suke gyara anjima za a kawo miki me tayaki aiki  yana gama zancan ta furta amma zan dungayin abinci ba sai na wahalar dasu ba kallanta yayi da sign din Dagaske kike kafin ya dan harareta  you are not allowed to cooked sai kinyi 7 days dinki kamar kowa bata kuma cewa komai ba kuma ,shima be sake ce mata komai ba .

12pm ya shirya ya fita ,kafun ya fitan sai da ya kira ihsan a waya akan suzo part dinsa ,da muryar su kuwa ta kashe wayar, dan kallanta yayi ganin yanda farinciki ya bayyana a fuskarta, dan dungure mata kai yayi kafun ya bar part din. Su ihsan ma ba dadewa sai gasu a part din su uku, ihsan ,sumayya, da firdausi,sai yar aikin da aka kawo mata me suna KULU,duk abunda tahee take so ta dunga yi ta fada mata,KULU sai washe baki take , babu wani aiki da zatayi yasa tahee sallamar ta, kafun ta tafi sai da ta zuba mata kayn Gara itama sai faman murna da adduoi take mata.da murna ta Tarbi su ihsan ,yauma sai da ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye , sabanin jiya yau har da hira ta dunga Jansu ganin ynda suka sake mata, cikin kan kanin lokaci kuwa suka soma hirar su harda tafa hannu kamar basu ba , sun dade a part din dan kin barinsu su tafi tayi sai da sukayi sallar azahar, nan ma da kyar ta barsu har saida sukayi mata alkawarin dawowa gobe.
Suna barin part din tazo wuce wa ta tarar da irin paper jiya da Sauri ta nufe ta, tana bude wa kalmar jiya ce a ciki  KILLED YOUR HUSBAND  , waigawa tayi ganin bamowa a wajan yasa ta nufi sama da sauri ta Adana ta da ta jiya,  Zan nemo ko ma wanene ta furta a bayyane kafun tashiga toilets.


****** 10:30 suna kwance kan gado yana rungume da ita, zagaye hannunsa ya farayi a jikinta da Sauri ta rike hannusa tana girgiza masa kai,be kulataba ya cigaba da abunda yake,ganin mutsu mutsun nata yayi yawa yashashi rungumeta ajikinsa yana shinshinar wuyanta kafun ya saki wani ajiyar zuciya, tsoro da firgicine ya kamata ganin yanda yake faman sakin ajiyar zuciya , rigar jikinta yake kokarin cirewa tasaka masa kuka , ina jin tsoro, ka bari please  ta fada murya a shake , shima cikin yanayi da muryarsa ta fara canzawa ya furta  ba abunda zan miki kara girgiza masa kai tayi tana kokarin tashi I promise  , daga nan be kara bata damar cewa komai ba ya hade bakinsu waje daya, kusan dogon lokaci ya dauka a haka kafun ya fara sakin wani ajiyar zuciya, gabaki dayanta ya daga ya shige toilets da ita , basu dau dogon lokaci Ba ya kara fito da ita a hannunsa sanye da wasu kayan, kwantar da ita yayi akan gadon kafin ya fita ya bar dakin, kusan Mintuna biyar da fitansa bacci ya dauketa,dawowa yayi hannunsa d auke da wani medium din ruwan roba, wasu magani ya sha kafun. Ya kwanta a gefenta sai faman sakin ajiyar zuciya yakeyi, sai da ya bari baccinta yayi nisa kafun ya janyota jikinsa ya dade a haka kafun bacci ya daukeshi.

Washe gari ma hakance ta faru su ihsan sun kara dawowa har lokacin babu kafar amrah ko basma, sosai sukai farincikin ganin juna ,hira sukai sosai wannan karan sumayyace ta roki alfarma KULU ta tafi su sai suyi aikin ,Sabida suna san zaga part din yayansu tun da basu taba shiga ba , haka kuwa akayi gabaki dayansu , su hudun suka gyara second floor da down stairs , 3rd floor ne kawai bata kaisu ba, sosai ko wannansu ya yaba tsaruwar part din sa, da kansu suka gyara part din suna yi suna hira sun dade a part din dan wannan karan kin barinsu su tafi tayi har saida mahma ta kira su awaya, gabaki daya wayar firdausi ta mikawa tahee tana dariya , gaishe da mahma tahee tayi acan ban garan ma cikin farin ciki mahma ta amsa mata tare da tanbayarta lafiyar ta , cikin jin nauyi ta ta amsa mata, janta da dan hira mahma tayi kafun ta umarci su sumayya su dawo, gabaki d aya dariya suka sa mata ganin ynda tayi da face dinta, har bakin falon ta rakasu, abun mamaki tana shigowa palorn ta kara tarar da paper nan still Rubutun da ta saba gani a jiki ci ta gani  KILLED YOUR HUSBAND ,duk tunanin da zatayi ta kasa shiyasa yanxu ma ta kara adana paper kamar sauran. Da daddare ma hakan ce ta faru sam ta ki bari king ya tabata balantana yayi mata wani abun, sai da ya kara mata alkawarin bazea mata komai ba sannan ta barshi yaba ta.

>???>???>???>???
?'?'?'?'?'?'

Akwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT yau kwanan tahee biyar da kaita dakin mijinta, acikin kwanakin nan sosai wata iriyar shakuwa taban mamaki ta shiga tsakanin king da tahee , duk lokacin da zasuji abinci baya bari suci plate daban daban sai plate daya, komai tare sukeyi , hatta wanka wani lokaci sai yace tare zasuyi ,Da taji hakan take samunta gudu tabarshi saidai kawai ya girgiza kai yai wuce warsa, a cikin kwana kinnan KULU ta fara zuwa aikin, harsun fara sabawa da tahee, su ihsan ma kullum sea sunzo sun debe mata kewa sosai suka saba , amrah da basma ne har yau Ba sa zuwa part din, hatta su ammey suna waya a wayar su ihsan wani lokaci kuma awayar daya bata take kiransu.har zuwa wannan lokacin kuma ba abunda ya shiga tsakanin ta da king sai dan rage zafi da yake , ganin hakan yasa tun bata sakar masa jiki harta fara.

Yanzuma tsaye take a gaban mudubi haka kawai tayi sha awar saka kananun kaya yau, wani top din Riga ce ajikin ta blue colour sai wando da yar karamar rigar ciki white ita ma, tunanin turaren da zata saka tayi hakanan ta dakko wani turare da amzy ta bata tace ta kwada sawa yana da dadi, tana bude kwalbar gabaki d aya dakin ya bade da kamshin turaran, a kokarin zuba wa a hannun turaren ya zubo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login