Showing 21001 words to 24000 words out of 144575 words

Chapter 8 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28443

cewar tahee harta kammala cin abincin, kuskure bakinta tayi tare da watsa ruwa , sannan ta hau kan lapiyayyan gadon dakin ,lilliba tayi jin sanyi na ratsata ta ko ina , bata dade da kwanciya ba bacci ya dauke ta .

?'?'?'?'
A gajiye ya dawo gidan bayan zaki ya ajjesa, ko part din ammi be Jeba, Wanka kawai yayi tare da nufar down stairs , Kai tsaye kitchen din dake falon ya nufa, banban kitchen ne da ya gaji da haduwa komai na anfanin kitchen akwai shi a ciki,kitchen din sai faman daukan kyalli yake, coffee ya hada cikin coffee maker din kitchen din, kan daya daga cikin kujerun dining din kitchen din ya zauna, a hankali yake sipping coffee din dake hannunsa,bayan ya shanyene ya kara hada wani tare da barin kitchen din, stair case ya dau tare da nufar kofar hagunsa, taku kadan ya kai shi wasu kofofi guda uku, kofar tsakiya ya shiga , ya dau dogon lokaci a ciki kafun ya fito, stair case din da zai kaishi second floor ya hau, a hankali yake taka stairs din har ya karasa hawa saman, kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da fara operating din system dinsa, ya dade yana anfani da ita kafun ya kashe ta gaba daya , toilet ya nufa be dade ba ya fito tare da nufar faffadan gadonshi, remotes din fitulun part din ya kashe kafun ya kwanta cikin lallausan gadonsa, be dade da kwanciya ba bacci ya daukesa.

Wutace sosai take ci, da anzuba mata ruwa Sai ta kara tashi kamar wacce ake hurata , ga hayaki da ya gauraye ko ina, daga cikin wutar kuwa hannu ake miko masa cikin azaba  Akhee habeeby!!Akhee habeeby!! hannunsa ya Mika da niyar ya kamo Wanda yake cikin wutar& farkawa king yayi sai faman hada gumi yake bayan sanyin Acn da ya cika dakin, adduoi ya fara karantawa a hankali wata nutsuwa tazo masa ,wayarsa dake side din gadan sa ya kunna,4:30shine abunda agogon ya nuna masa, mikewa yayi tare da nufar toilet, wanka ya fara yi kafun yayo Alwala, ya dade yana nafila kafun ai kirin sallah, direct kasa ya nufa bayan ya idar da sallahn , sanye yake cikin white jallabiya , sosai farar jallabiyar tayiwa surar jikinsa kyau,gashin kansa sanye yke cikin bakin rawanin larabawa, sosai kyawun fuskarsa ya fito, musamman idanuwansa da suka kara haske sai kyalli suke duk da kasancewar fuskarsa a hade yake,a hanyar zuwa Masallaci suka hadu da abeey shima zasu tafi masallacin,a haka motocin su suk fita , a dawo wa ma tare suka dawo gidan,Kai tsaye part din dada suka nufa dukansu, ganin babu kowa a falon yasa su samun waje ko wannan su ya zauna. Mintuna kadan sai gashi ta fita sanye da hijabi a jikinta , ko wannansu gaishe da ita yayi , yayinda take amsawa fuskarta washe da fara a, kankance ido king yayi dada yau naga sai fara a kike ko an miki albishir da zuwa umarace a hankali yayi maganar amma duk da haka sai da ta jisa, hararar sa dada tayi A ah gorin daurin aurenka aka kawomun kara hade fuska king yayi tare da dauke idanuwansa daga kanta,tabule baki dada tayi  Kai dai Kasani mutum kullum cikin daure fuska ,kamar audiga ina dalili , be tanka mata ba sai ma lumshe ida nuwansa da yayi, abeey kam murmushi kawai yayi, hira suka dada ta fara tare da su uncle musaddiq , abeey na sa musu baki lokaci zuwa lokaci na yana kallan king, ganin hirar tasu bame karewa bace yayi musu sallama tare da nufar part dinsa. Gym room dinsa ya nufa , tare da sa kayn motsa jiki , ya dade yana motsa jiki kafun ya futo duk ya hada zufa ,kwantaccen gashin kansa ya zubo masa har wajan idanuwansa,Wanka yayi tare da shirya cikin wani hadadden suit red colour, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina , gashin kansa ya sha gyada yayin da gefe guda na fuskar sa gashin ya futo harwajan idanuwansa,pink lips dinsa ya turo sosai , yayinda fuskarsa take a daure,sosai yayi kyau cikin shigarsa , sai ta kara futo da ainahin kalarsa ta larabawa,cikin takun sa ya bar part din , direct part din ummey ya nufa, har lokacin zoya bacci take , be dad e ba ya bar part din tare da nufar part din ammi.

Yana shiga falan ya tarar da ba kowa a ciki sai yan aikin dake gyara dinning , suna ganinsa ko wanne jikinsa ya dau rawa, cikin rawar murya suka gaishe shi,da hannu kawai yayi musu alama , suna ganin haka sukai saurin barin wajan, kan daya daga cikin 2 sitter din kujerun ya zauna tare da crossing legs dinsa. Cikin shigar material ammi ta fito daga kitchen , hannunta dauke da tray din abinci, cikin na tsuwarsa ya mike tare da nufar inda take da nufin sauke mata tray din, girgiza masa kai tayi  no son,abincin daughter ne , kallan ta yayi na yan sakanni kafun ya bude bakinsa me ya kawo su part dinnan da sassafe ,hararar sa ammi tayi  Kai me ya kawo ka da sassafe, Kai tsaye ya bata amsa  to see my happiness  murmushi ammi ta sakar masa tana kara jin kaunarsa a ranta , ba abincin su amrah bane, wannan na sister dinka ce , you will see her soon bai ce mata komai ba sai lumshe mata ido da yayi, itama Kai tsaye dakin da tahee take ciki ta nufa, akan dadduma ta tarar da ita , mikewa tayi tare da karban tray din hannun Amin ta ajje mata a gefe ina kwana aunty kallanta sosai Ammon tayi  from today ki kirani da ammi not aunty jinjina mata kai tahee tayi sai kuma ta bude baki insha Allah ammi dariyar jin dadi ammi tayi  kin tashi lapiya, hope ciwan kan ya sauka ,  eh ya dena ammi cewar tahee,  toh Allah ya kara sauki, ga breakfast nan in kin gama sai ki fito falo karkiyi ta zama a daki ke kadai , jin jina mata kai tahee tayi  toh ammi na gode  , fita ammi tayi daga cikin dakin, TAHEE kuma waje ta Samu ta zauna  ya Allahu har na fara kewar ku oumma na da taheer dina  .
A falo kuwa har yanxu king na zaune ya lumshe idanuwansa  if not for ammi, who dare to keep him waiting ,lips dinsa na kasa ya fara tsotsa kwata kwata bazaka gane yanayinsaba, shafa gefan fuskarsa da akaine yasashi bude idanuwansa,ammi ya tarar a tsaye sai faman murmushi take saki, dauke kansa yayi daga kallanta, sorry my son , dago da idanuwansa yayi tare da kallanta  it s okay , ammi am hungry  ,am coming kawai tace tare da komawa kitchen , hadadden breakfast dinsa da tayi masa shida tahee takawo masa , tsabar sarauta a baki take bashi,kadan yaci tare da Shan kunun ayan da yake matukar kauna,bayan ya kammala cin abincinsa ammi ta kallesa  son Yaushe zaka dawo gida Kai tsaye ya bata amsa it can be possible da yamma , kina bukatar wani abune  girgiza masa kai tayi  no son na tanbaya ne kawai ,mikewa yayi tare da pecking din goshinta  am going now , take care shine abunda ammi tace masa , jinjina mata kai yayi tare da barin part din.

A daki Kuwa tahee wanka tayi bayan ta kammala cin abincin da ammi ta kawo mata, hijab dinta ta saka tare da kwashe kwanukan ta fito falo, Daidai lokacin da yan matan gidan ke shigowa, kallan tara saura kwata amrah ta bita dashi ke kuma daga ina ,murmushin yake tahee ta saki ina kwananku  wani hararan amrah ta bita dashi  bashi na tanbayeki ba .ihsan ce ta katse mata zancen ta easy amrah , ki bita a hankali mana , kallanta ihsan tayi cikin sake fuska yan mata ya sunan ki , amsa mata tayi da  TAHEERA  tana sun kuyar dakai, lokaci d aya zuciyar firdausi da amrah ya buga,  wow gaskiya kina da suna me dadi gaki kyakkyawa ,Shigowar ammi ne ya katse ihsan,  ah ah yan matana yana ganku a tsaye  , sumayyace tai saurin bata amsa  bakomai ammi mun shigone sai mukaga bakuwarki shine muke dan gaisawa murmushi ammi tayi  kun kyauta kuwa , ku samu waje ku zazzauna , Kema tahee zo ki zauna , kallan ammi tahee tayi  dama ina san wanke wadan nan kayan ne girgiza mata kai ammi tayi  basai kin wahalar da kankiba , wani dan button ta danna sai ga yan aiki guda biyu sun fito, kallan daya daga cikinsu ammi tayi  asabe ga kwanukwanan a hannun tahee su zaki kai kitchen , toh hajiya cewar wadda aka kira da asabe,kwanukan hannun tahee asabe ta karba  nagode  murmushi asabe ta sakar mata , oya zo ki zauna  cewar ammi, waje ta samu daga kasa zata zauna ammi ta dakatar da ita,  ga waje zauna akan kujera ,batai musu ba ta hau daya daga cikin kujerun,  toh yan matana wannan sunan ta taheera ana ce mata tahee, Kema tahee wadaddan yayyunkine, wannan ta farkon ta nuna sumayya, sunanta sumayya,sai ihsan a kusa da ita , sai amrah da kuma firdausi yawu firdausi ta hadiye ammi ko itace wacce Kikace zaki kawo mana  , gyada mata kai ammi tayi,  tahee zata cigaba da zama tare damu, Inaso ku zauna kamar yadda nasan ku, hope zaku karbeta , murmushin yake amrah ta saki  insha Allahu ammi a haka suka dan taba hira kuwa da abunda yake sa kawa a ransa, TAHEE ma duk a takure take ganin irin kallan da amrah take binta dashi,dama dama ihsan da ke janta da hira, sumayya da firdausi ko kallanta basa yi.

Zuciyarta tafarfasa take ba abunda take nanatawa sai  bazai yuba, it s impossible  tare da mikewa & ..


Comment and share =ؖ?
Alkalamin Mss Lee
'?

=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?

LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA

=?G?=?G?=?G?=?G?=?G?
DUK KARFIN IZZATA (star lady )

GIDAN AUNTY ( mss Lee)

JINI DAYA ( mrs bbk)

YA FITA ZAKKA( maman sayyid )

SARKI SAMEER( xeenat love)


Alkalamin Mss LEE
'?
'?
'?
'?
Ina Godiya masu commenting , I heart you all=ؖ?=ؖ?.
 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY=ؖ?=ؖ?
(A heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?

PAID BOOK
MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1 =???

Free page 12 >؋?

Zuciyarta tafarfasa take babu abunda take nana tawa sai  bazai yiwu ba , it s impossible  tare da mikewa , kallanta ammi tayi  ah ah amrah ina zaki cikin dan rawar murya ta amsa mata  dama ina da lectures naga lokaci yana tafiya inaso na shirya jinjina kai ammi tayi alamar gamsuwa  All the best daughter , murmushin yake amrah ta sakar mata  thank you ammi , tana gama fadar hakan ta bar part din, cikin sauri ta nufi part din auntyn ta, cikin sauri take tafiya ko kula da auntyn ta dake falon batai tai shigewa dakinta, ganin hakan yasa hajiya ameena bin bayanta , a tsaye ta tarar da ita sai faman safa da marwa take ,  lapiyar ki kuwa amrah kika shigo duk a rude ko har kingansa  , jijjiga mata kai amrah tayi sai faman zagaye take , kallanta hajiya amena tayi , kiyi mun ba yani mana ,aunty akwai matsala  cewar amrah  kinsan jiya ammi tayi tafiya , yanxu baki gani ba da wata yarinya ta dawo , itama wai anan zata zauna  ta be baki hajiya Amina tayi  to sai me dan ta kawo wata yar kauye girgiza mata kai amrah tayi  ah ah aunty bazaki gane bane , kinsan sharadin da boka ya sa mana , baki ga yarinyar bane , kyakkyawace sosai , gata a cike ta ko ina kamar wata babba, koni da na ganta sai da naji sha awata ta motsa, balantana king da yake namiji, dole yaji wani abu aka ta, banasan kwata kwata king ya ganta , Kema kinsan dalilin da yasa nake zuwa part din ammi sabida kawai acan zan iya ganinsa bata bari hajiya Amina tayi magana ba ta dora  aunty ya kamata kiyi wani abu,dan wallahi duk Wanda yayi kokarin rabani dashi sai nayi azalinsa, hakuri ya fara kare wa duk lokacin da na gansa sai sha awata ta motsa , jin maganganun amrah ba karamun jijjiga hajiya Amina yayi ba  dole na kaiwa boka ziyara dan bazan taba bari dukiya ahalin nahyan ta su bucemun ba, yanxu ki kwantar da hankalin ki karyi abunda zai sa a zargeki, dan Nima ko zanyi yawo tsirara sai dukiyar nan ta dawo waje na  tana gama fadar hakan ta har dakin, waya amrah ta dakko tare da kiran wata number, ringing 2 aka daga wayar , bata jira cewarsava ta soma magana  Ina bukatar ka kashe mun kishirwar data tasomun, zan fada maka inda zamu hadu , tana gama fadar haka ta kashe wayarta, sai faman lumshe ido take tana Cizan yatsa.

*****Apart din ammi duk yan matan sun koma part Dinsu, part din dada ammi ta nufa da tahee, sai faman bin ginin gidan take da kallo musamman wani dogon building din glass da ya burgeta , da wasu irin flowers me hade da pink colour , sosai flower din sukai mata kyau, falon dada suka shiga komai yana nan kamar yadda yake sai faman tashin kamshi yake kamar ba a amfani dashi, Assalamu alaikum cewar su ammi, itama dadan amsa wa tayi tana gyara farin glass din idanta, zama ammi tayi kan daya daga cikin kujerun falon, tahee kuwa samun waje tayi daga kasa kan carfet ta zauna, hakan da tayi ba karamun burge dada tayi ba amma bata ce komai ba.  Sannu da hutawa dada , murmushi dada ta saki  Yauwa maman yara, a ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar , murmushi ammi ta saki, ina wuni  cewar tahee, amsawa dada tayi taba bin tahee da kallo, nutsuwar yarinyar ya birgeta, dada wannan Itace yarinyar da nace miki inaso ta dawo waje na, na kawo miki itane ta gaisheki ,murmushin jin dadi dada ta saki  kin kyauta kuwa, yan mata ya sunanki dada ta fada na mayar da hankali kan tahee, sun kuyar da Kai tahee tayi sunana Taheera , zaro ido dada tayi sai kuma ta tabe baki, yaran zamani kowa dai da irin nasa sunan , shi wancan bod ararran ansa masa tahanuni (tahnoon), ke kuma ga naki salan sunan wai tahura (taheera), sun kuyar da Kai ammi tayi jin yadda ta kira sunan su, gashi ba halin dariya , dada kuwa bilhakki da gaske take ko dariya a fuskarta, kara kallan tahee tayi, nikin ganni nan , wallahi iyayena sunan kwarai suka samun, ina dalili ai ku sunayan ku sai ku wallahi ,itama tahee dariya dada ta bata amma sai tai saurin gimshe kayarta amma murmushin yaki buya a fuskarta. sannan ki saki jikinki nan ma gidan kune , ko me sikeso ki tanbaya za a miki kinji tahura  ,sosai murmushin da take boyewa ya fito har dan gaf din hakorin ta fitowa  nagode sosai hajiya dada bata bari ta karasa ba ta dakatar da ita yau naji wani batu, dada zaki dunga cemun kamar sauran ,jinjina mata kai tahee tayi  nagode dada sosai tayi wa dada adduar da har yar kwalla saida ta share  Allah yayi miki albarka  kasa kasa tahee ta amsa  ameen ita de ammi sai binsu take da kallo tana sakin murmushi, kallanta dada tahee maman yara , gasky wannan  ya a kwai hankali, nasan a gajiye kuke , idan ta huta sai a gabatar mata da kowa na cikin a halin ta san yan uwanta, cikin girmamawa ammi ta amsa mata mun gode sosai dada, Allah ya huta gajiya , ameen aka wai dada tace mata kafin su kama hanyar fita da ga part din, bin bayansu da kallo dada tayi kafun ta saki wani murmushi akan fuskarta .

************
ILORIN
babban waje ne katafaran gaske , me dauke da abubuwa mabanbanta a cikinsa , ba karamun makudan kudi aka kashe ba wajan gina falon, komai na cikin falon red colour ne tundaga kan carfet har zuwa kan labulayen dakin, hatta mutanan dake tsats tsaye ko wanne fuskarsa a rufe , matan sanye suke cikin jajayen kyalle iya gwiwa , yayinda mazan suka sanya dan karamun jan kyalle da ya bude al aurarsu, magana suka fara cikin wani irin yare Mara dadin saturate, kasancewar falon babbane hakan yabasu daman Jan layi kowannansa dauke da glass cup ne Jan abu acikinsa, Yaren suka cigaba dayi , sunayi suna sunkiyar da kansu, wani hayakine ya cika falon , yayinda wata murya Mara dadin ji ta farara babbaka dariya, sannu a hankali ta koma ta jarirai, a haka karuwar muryar nan ta kuma karade ko ina da dariya , data gama sai kukan jarirai suma, an dau lokaci ana haka kafun hayakin ya dauke.
Wata katuwar matace ta bayyana a falon , baka kirin da ita fuskarta dauke da wasu kananan kuraje ba kyan gani, durkusawa sukai baki dayansu tare da yi mata sujjada(wa iyazubillah), sosai suka shiga yi mata kirari shugaba me share mana hawayen mu, kece farin cikin kowa ne halitta , kece maganin kukanmu, kamar yadda kika saba share mana hawaye  , dariya Matar nan ta fara kafun lokaci daya ta hade ranta kamar ba yanxu ta gama dariya ba, cikin kakkausan murya ta soma magana  lokaci yayi, lokaci yayi da zaku mallaki duniya, duniya takuce , mu kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login