Showing 57001 words to 60000 words out of 144575 words

Chapter 20 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28457

ta dakko wata doguwar riga baka sai digo digon ja dake jikinta, kara kallan jakan tayi,kafun ta sa hannu ta dauki wata jaka a ciki, bude cikin jakar tayi inners ne a cikin jakar sai pad shima,pant da bra ta dauka har zata kulle jakar sai kuma ta dauki pad din guda d aya ,tare da Mayar da trolley din ta rufe kamar yadda ta ganta, a nutse ta saka pad dinta da pant, a wannan lokacin har bra dinta ta saka kafun ta kalli rigar dake gefenta,murmushi ta saki da har dimples dinta na dama da hagu na lobawa kafun ta saka rigar, bakaramun kyau rigar tayi wa jikinta ba musamman da ta kasance fara sai kayan suka haskata kasan tuwar kalan kayan ne ja da baki, hips dinta sosai ya fito cikin rigar jikinta ,yalwataccen gashin kanta da ya sakko har gadon bayanta me shegen cikowa ta kama da niyar tufkewa amma ta kasa,sosai ta fara kiciniyar yadda zata kamashi,ganin ta kasane yasa ta dakko gyalan kayanta daniyar barin dakin, taku d aya biyu tayi kanta ya sara mata,tsayawa tayi tana bin inda take da kallo , tunani ta shigayi kafun ta turo dan karamin bakinta to ni ya naganni a nan ba nashiga can ba ta karasa zan can nata tana nuna kofar toilet ,sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan jikin ta , wayo manyan idanuwanta tayi tana bun jikinta da kallo, kafun ta kai hannu ta shafa kamar me tsoran shafawa, cikin Sauri ta dauke hannunta, ko dady ne yamun wayo ,yasamun kayannan  tunanin hakan yasa ta saki murmushi, cikin sauri ta karasa kofar fita daga dakin gashin kanta duk ya rufe mata fuska, bude komar datai ba wuya ta hango dadin nata na kokarin kai wani kyakkyawan cup bakinsa ,a guje ta nufi inda yake tana sakin gyalan hannunta,Daidai zai kai cup din bakinsa ta saki kara  dady ,dan juyo da idanuwansa yayi yana kokarin Shan coffee dinsa ta daka tsalle tare da bare kofin hannunsa,hawaye duk ya bata fuskarta cikin rawar murya ta furta  dady karkasha ,ansa guba  & ..

(Tofa=?3?).

>???>???>???>???>???
?'?'?'?'?'?'?'?'

AMRAH

Karfe 4:30 ta farka tana ya mutse fuskarta , dafe goshinta tayi tana ware yan mitsi mitsin idanuwanta kafun ta waresu gabaki d aya ,bin dakin ta farayi da kallo kafun ta motsa jikinta da niyar tashi, zafin da taji a kasantane yasata koma tare da bin jikinta da kallo,da kyar ta tashi zaune tana faman damshe bakinta sabida zafin da take ji a kasan ta, kallan yadda take babu kaya tayi kafun taja dogon tsaki tana mikewa tsaye ,kofar dakin ta sawa key kafun ta koma ta zauna,tana danasanin kiransa da tayi a waya , amma in kasan wata ai bata san wata ba ta furta tare da nufar wardrobe dinta, wata fincinar riga ta dauka tare da sawa a jikin ta sai faman wale kafa take, kwalbar magungunan da tasha ta dauka tare da mayar dasu ma ajiyarsu data boyesu,tunanin yadda zata kawar da tahee ta fara,ko tunanin gari be gama waye ba ,batayi ba ta dauki wayar ta tare da danna wata number ,kusan missed called uku har yanxu ba a daga ba ,wani dogon tsaki taja kafun ta kara kiran wayar, ringing biyu aka daga wayar,nishin da ta fara jiyowa cikin wayar ne yasata sakin tsaki dakashe wayar tata tana jefata kan gado duk tsikar jikinta ya tashi,sosai ta fara juyi saman gadon jarabarta na tashi, ga wani tsanan tahee dake kara ruruwa a cikin zuciyarta a wannan karan da kaina zanje wajan boka ,bana bukatar te makon kowa a haka ta cigaba da tunanin yadda Zata cika burinta batare da kowa ya farga da ita ba .

>???>???>???>???>???>???>???

KANO

 Assalamu alaikum  zahra ta shigo dakin tana dukar da kai,amsa mata oumma tayi tana sakin mata murmushi,itama zahra murmushin ta saki tana kallan oumma, oumma daman breakfast aka gama ke kadai muke jira yanxu  , kallanta oumma tayi kamar bazata ce komai ba sai ta mike ,daman sanye take cikin hijab dinta, zahra na ganin hakan ta saki a jiyar zujiya , ta dauka oumma bazata biyo taba kamar yadda Khaleed ya fada mata,da sauri ta bude kofar dakin tana nunawa oumma hanya har suka karaso babban falon, Khaleed na ganinta shima ya mike,kwalo zahra ta sakar masa tana mika masa hannu  yaya my gift ,dan hararar ta Khaleed yayi kije kafun ya soma magana  kije dakina ki dauka tsalle ta daka har da juyi tana dariya,kallan oumma Khaleed yayi tare da hararar zahra kin tsaya shiririta kirbar mana oumma a tsaye  da Sauri zahra ta juya Wajan oumma  kiyi hakuri oumma , shima Khaleed kallanta yayi ,tare da nuna mata hanyar dining  oumma kiyi hakuri mun barki a tsaye  murmushi kawai ta sakar masa itama tana tuno su taheern dinta , basu kara cewa komai ba suka nufi dinning din gabaki d aya ,har yar rigan rigan Wanda zaiyi serving din oumma ake ,saida suka gama cika mata gabanta da kayan abinci har saida ta dakatar dasu , a hankali zahra tayi serving din Khaleed shima kafin su fara cin abincin, har sun kusa kammalawa breakfast Dinsu sai ga dady yafito, da sauri zahra ta zaro ido tana mike wa  dadyy  ta furta da niyar nufar inda yake ,nuni yayi mata data koma ta zauna kafun ya karaso wajan shima ,cikin zoyala ya soma magana  wato har kun fara mantawa dani dariya suka saki banda oumma data kura wa abincin gabanta ido, a hankali ta bude bakinta tare da gaishesa, kallo daya yayi mata tare da amsawa shima zama yayi zahra tayi serving dinsa,shine ya soma tashi tare da musu sallama , mikewa Khaleed yayi shima dady ya komar dashi ku kammala cin abin cinki, akwai meeting din da zani, auta me kikeso na taho miki dashi girgiza masa kai zahra tayi  any dady gyada mata kai kawai yayi tare da barin wajan ,yana jiyo yadda take faman furta  Allah ya tsare dady,love you more  girgiza kai yayi yana sakin murmushi kafun ya bar falon. Suma suna kammala cin abincin falo suka dawo, suka fara hira da oumma wannan karan sunki barinta ta koma har saida ta fara sake musu suna hira,sallah ne kawai ke tayar dasu da oumma ta idar dasu kara zuwa su dakko ta , ko gajiya da hiran basayi.

>???>???>???>???>???
?'?'?'?'?'?'?'

BUNKURE

zaune Dije suke a daki ita da bintalo sai faman irgan kudi suke ,kallan Dije bintalo tayi cikin ya tsine, wai ke dije wace Irin mutum ce me shegen san kudi,yanxu kudin ma bazaki barni na irgaba Haba ki canza Hali da wannan shegen san kudin naki batare da dije ta damu da bakar maganar da bintalo ta saba fada mata ba ta wangale bakinta Haba yar albarka ta ,Kema kinsan da kudin nan nake so ki koma gidan gayunnan  dan ta bile baki bintalo tayi kafun ta kammala irga kudinta tana mikewa, ni yanxu bani da wannan lokaci,ki jira nagama cin duniyata sai ayi wannan maganar ta karashe zancan ta tana jefawa Dije dubu biyar  ga wannan  da Sauri Dije ta wawuri kudin tare da zurasu cikin zaninta,tsaki bintalo taja tana daukar wayar ta da ake kira,ganin me kiran ne yasa ta sakin murmushi  hajjaju barka da dare daga daya ban garan banji me aka ceba sai dariyar da bintalo ta saki tana furta  baki da matsala hajjaju ganinan tafe tana kammala zancanta ta kashe wayar tare da wawurar mayafinta tana barin dakin,ko damuwa da fadawa Dije inda zata bayi ba ta Sakai ta bar gidan.

>???>???>???>???>???>???

Tun bayan data Barar masa da coffee din hannunsa bai motsaba,kafun ya dago da idanuwansa a zuciye yana kallanta  how dare you , kura masa ido tahee tayi tana kallansa har yanxu da sauran hawaye a fuskarta da gashin kanta ya rufe fuskar,daga hannu yayi da niyar tsinka mata mari a bazata yaji ta rungumesa tana sakin saban kuka,kasa motsi king yayi ba  a jin karar komai sai karar sautin kukan ta dake tashi,a hankali ta soma magana cikin shashsheka  dady karkasha kaji, suna so sukashe mu ni banaso ka mutu kaji ,yanxun kam ko kwakkwaran motsi king be yi ba ,tunani ya fara  Anya buguwar da yarinyar nan tayi be taba mata hankali ba , ban bareta yayi daga jikinsa yana hade ransa,langwabar masa dakai tahee tayi tana tuna dan karamin bakinta, bin wajan da ta zubar da coffee din yayi kafin ya maida hankalinsa kanta, me ke damunki  ,girgiza masa kai Kawai tayi alamun itama bata sani ba ,sai alokacin idanuwansa ya sauka kan kayan jikinta, sosai kayan sukai mata kyau musamman dogon gashin da ya gani a kanta,duk da ne gama yadda da gashin kanta bane ,a hankali ya fara taku tare matso ta,ganin yanda ya hade fuskarsa yasa ta tsorata,tare da cuno bakinta, itama baya ta fara ja kamar yadda taga yana matsowa ,bata san lokacin da suka jingida da jikin bango ba,hannunsa daya king ya sa tare da dafe jikin bango ,sosai yayi mata runfa ko ganinta ba a yi sosai,dan sunkuyo da fuskarsa yayi dai dai kan tata& .


Mss Lee =ؖ?
07041879581

=ؖ?=ؖ?The talent troupe writers =ؖ?=ؖ?
=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY=ؖ?=ؖ?
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?


PAID BOOK

Mai bukatar complete din gidan aunty yayi mun magana ta wannan number 07041879581.


MASOYIYA WANNAN PAGE DINKI NE =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?I heart you so much =ؖ?.

BARKAN KU DA SALLAH , hope anyi sallah lapiya, ina mika sakon jinjinawa ga al ummar musulmai baki daya .

=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?

Kuma ban barku a baya ba &
=ؖ?=ؖ?masoyiya ta (duk karfin izzata )
Aunty sadiya (Jini daya )
Maman sayyid (ya fita zakka )
Auta( baby)
Maman twins (sarki sameer )
Memerh (ubana ne ko kishiyata)

Dukan ku ina Kaunar ku lodi lodi =ؖ?>???,Allah ya kara hada kawunanmu (Ameen)


BOOK 1 =???

& & .=ؖ?=ؖ?(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Page 33 _34=ؖ?

Kawar da fuska tahee tayi tana faman turo dan mitsitsin baki, bin bakin nata da ta turo yayi da kallo kafun ya dauki karamin finger dinsa ya bige mata bakin,saurin Mayar da bakin tayi tare da saka tafukan hannunta idanuwanta har sun fara tara kwalla, kara kallanta yayi na yan sakanni kafin ya daga hannunsa kan fuskarta,a tunanin ta marin ta zai yi tayi saurin rintse idanuwanta,yana kai hannun nasa fuskarta, gashin kanta ya ke kokarin rufe mata ido ya bude tare da mayar dashi baya, batai aune ba sai ji tayi ya rige gashin gagam, karamar kara ta saki batare da ta sani ba ta rike hannunsa,kwallar da ta tarar mata na zubo mata ,kara rike kan nata yayi gam ,cikin sheshshekar kuka take furta  da.. da zafi , sakin mata kan nata yayi yana hararar ta ,kamar Wanda aka sa dole ya furta  wayace ki barar mun da abu , kwalla na zuba ta turo dan karamin bakin ta, Nima ban sani ba  , kallan daya yayi mata ya jinjina kansa, be kara cewa komai ba ya bar wajan, saurin biyo shi tayi tana rike masa hannu,cikin narai da ido ta ke miko masa ribbon din ta,guntun tsaki ya ja kafun ya karbi ribbon din ,hannunsa yasa cikin lallausan gashin kanta,amaimakon ya Tufke mata gashin sai ya shiga ya mutsawa,sosai laushin gashin ya burgeshi, tsawan lokaci suna a hakan ,motsi tahee tayi tare da kallansa  ka fata dauke kansa yayi daga kanta kamun ya kamar kan sumar kanta har yanxu yana mamakin yawan cikin gashin kanta,tattare gashin yayi waje daya kafun ya sa mata ribbon din, kallan jikinta yayi kafun ya mayar da kallansa kan kyakkyawar innocent face dinta, a hankali ya furta a ina Kika dakko kayan nan girgiza masa kai tayi  Nima ban sani ba ,dady nayi kyau  girgiza mata kai yayi alamun a ah,shagwabe masa fuskata tayi kamar wata karamar yarinya dady"shareta yayi ganin tana ko karin bata masa lokaci kafun ya nuna mata veil dinta,shima mika masa tayi ,kamar Wanda ya kware kuwa haka ya nada mata shi ko wata macen albarka,dan siririn dantsen hannunta ya kama batare da yace komai ba yaja ta suka bar dakin, futar su ba dadewa wannan shayin da tahee ta zubar ya koma ba ka kirin dashi.

*****har suka fito falo hannun sa na ruke da nata Daidai saitin one sitter yasaki hannun nata batare da ya kara kallan gefen inda take ba, waje ya samu kan daya daga cikin kujerun yana crossing legs din,karasowa wajan sa tayi tana shagwabe fuskarta, dady yunwa nake ji ta furta a hankali sabida yunwar da ta fara ji,kallan agogo yayi kafun ya mike tsaye Daidai lokacin da idanuwansa suka sauka kan babban tray din dake wajan dinning, karasa wa yayi hannu daya yasa tare da bude wani dan dogon plate ,lafiyayyen charcuterie,scratch pastas,and bread ne akai ,dan guntun murmushi yasaki sabida yasan babu me gigin aiko da abu part din sai ita,alama yayi wa tahee ta da karaso,da saurin ta kuwa ta karaso wajan ,nuna mata plate din yayi da hannu kawai batare da yace komai ba, kallan abincin tayi kafun fa kallesa shima,waje ya samu ya sauka kan kujerar dinning table din,ganin Hakan yasa itama ta zauna da sauri tana binsa da idanu,abincin da ya nuna mata ta tsaya kalla,kafin ta kallesa ganin hakan yasa ya dauki fork daya dare da saka abincin dan kadan abakinsa yana taunawa, itama taheen kamar yadda taga yayi hakan itama tayi,nuna mata yayi da ta karasa cin abincin yana ajje fork din, binshi tayi da kallo tana ajiye fork din itama kamar yadda taga yayi,kallan ta kawai yayi ba tare ya yace komai ba ya koma falon, turo dan mitsitsin bakin ta tayi tare da daukan plate din tana binsa da kallo,Daidai inda ya zauna kusa dashi ta zauna har tana gugan jikinsa,yanxun ma langwabar masa da kai tayi ,kin kulata yayi take a wajan ta fara hawaye tare da mikewa da niyar Mayar da abincin,hannunsa daya yasa ya dauki plate din tare da daukan scratch pasta din yayi tare da kai mata bakinta da sauri ta bude bakin yasaka mata,kara daukan wani spoon din yayi ta rufe bakinta tana kallansa,ya gane me take nufi a hankali ya kai spoon din bakinsa shima,murmushi ta sakar masa bin dimples dinsa sake lotsawa a hankali, finger dinta saka a wajan ,a bazata ya kalleta,wani murmushin ta kara sakar masa  dady na kafi kowa yau , ta bude baki da niyar kara magana yasa mata abincin dake fork din abaki, be kara bari sunyi wata maganar ba har suka kammala cin abincin a tare ,duk Wanda yansu a lokacin sai yayi tunanin masoyaye da suka dade da fadawa soyayya, suna kammala ciki,magungunanta ya bata nan ma sai da suka sha daru kafun Tasha maganin.

?'?'?'?'?'?'?'?'

Zazzaune mutanan gidan suke a babban falon dada,tundaga kan abeey har zuwa kan su ihsan, zoyace kadai bata falan,da yawa daga cikin mutanan gidan babu Wanda ya karya kowa so yake yaji karin bayani akan zan tukan abeey musamman dayawa daga cikin zuciyoyin mutanan falon da take bugawa ,ummey da ammi na gefe suma a kan kujera ,sosai ammi ta fada sabida yar damuwar data sawa kanta akan rashin lapiyan tahee da kuma batan su oumma,gyaran murya abeey yayi  kamar yadda na fada zan sake maimaitawa taheera matar king ce yanxu,kowa yasan rashin lapiyar da ya jarabceta, duk da haka kuma bazamu tauye mata hakkinta ba,kamar yadda ake yiwa ko wace amarya lefe itama haka za  ai mata ,sannan daga rana irin tayau taheera zata koma ban garan mijinta,shine me alhakin kula da rashin lapiyarta, ba shawarar kowa nake nemaba wannan umarni ne na zartar  , jinjina kai dada tayi cikin gamsuwa itama kayi abun kai zayedu ,hakan ne ya kamata  sai kuma ta maida hankalinta kansu ummey  kuna da abun cewa ne  girgiza mata kai sukai kafun su hada baki  duk yadda kika yanke daidai ne dada ,suman zaune amrah da sumayya sukai jin zancen Auran na kara zama gaskiya , hatta su ihsan saida abun yazo musu a bazata,aunty kuwa kamar ta hadiyi zuciya haka take jinta.
A hankali daddad an kamshin turaran sa ya cika ko ina na falon, har yar Riga rigan dagowa ake, cikin takunsa da ke kara masa kyau ya soma takowa cikin falon,sosai shigarsa ta kara fito da ainahin kalarsa ,babu Wanda ya kalla cikin mutanan falon sai ma hade ransa da yayi duk da be dago ya kallesuba yasan shi suke kalla,tahee na bayansa tun Shigowar su falon ta  buya a bayansa sabida mutanan da ta gani,be hanataba har suka karaso cikin falon,kan daya daga cikin 2sitter din falon ya zauna ,itama tahee da sauri ta zauna kusa dashi tana buye fuskarta a jikinsa,abeey king ya gaisar tare da su dada,ta kasan ido yake bin amminsa da kallo ganin cikin kankanin lokaci ta rame,ga baki daya manyan falon ya gaishe dasu amma ba Wanda ya bari suka hada ido dashi musamman abeey, duk yan falon zuba musu ido sukai ganin kusan Anko sukayi,duk Wanda ya kallesu sai ya kara sabida irin haduwar da sukai musamman Jan colour din da yayi matching din shigarsu,mikewa dada tayi tana nufo su tahura ta zonan kinji yar albarka , girgiza kai tahee ta shiga yi,sosai ta damke hannun king, tana juya kai,zata saki kuka tsayawa kallonta dada tayi tana tabe baki dan kin samu ma zan kulaki aikuwa sai kinzo, kara nufota dada,aikuwa azabure tahee ta mike da niyar guduwa, cikin sauri king ya rike hannunta,kafin ya kalli dada ,cikin rawar murya ta furta  banaso  gyada Mata kai yayi kafun ya zaunar da ita,itama dada ganin kallan da king yayi matane yasa ta tabe baki da komawa wajan zamanta, ba kin cikin kamar ya kashe su amrah musamman da take tunanin wasan kwaikwayone kawai yarinyar take shiryawa,maganganun salma ne suka fado Mata arai,tabbas da wannan damar zatayi amfani wajan kawar da tahee,tunanin da take ne ya tsaya mata tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login