Showing 24001 words to 27000 words out of 144575 words

Chapter 9 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28439

mune abun bautawanku, saura Kiris komai yazo karshe, tabbas aikin ku ya fara zuwa gangara  , kallan daya daga cikin mutanan falon tayi,  abar kauna shine sunan da ta kira , wacce aka kira da abin kaunace ta fito tsakiya,  tuba nake me sharemun hawaye , tuba nake shugaban dudduniya , shafa kanta wannan bakar matar tayi ,  tabbas kaso mafi yawa na aikin nan yana hannunki,dole ki tabbatar jinin da kika dade kika kiwo ya kwaranya ga dodon tsafi , muna bukatar jinin kafun nan da mako biyu kara sun kuyar da Kai Wadda aka kira da abar kauna tayi  Godiya muke abun bautarmu tabbas babu me share mana hawaye seke kara hade fuskarta tayi tare da bin abar Kaunar ta da mayataccen kallo,Tashi tsaye abar kauna tayi , tare da rungumar bakar matar nan, matseta sosai matar tayi ajikinta tana shinshinar wuyan ta kafun lokaci daya su bace a falon ,sun kuyar dakai ragowar mutanan falon sukayi kafun ko wannansu ya buga cinyarsa sau uku,suna gama bugawa wani bakin hayaki ya cika falon, lokaci d aya hayakin ya dauke, sabanin dazu, yanxu ba kowa a falon.

*************
LAGOS

zaune ammi take kan daya daga cikin sofa din falo, sosai taci ado cin ash din material sai faman walwali take , ga sanyanyan kamshi dake Tashi a jikinta, iya haduwa ammi ta hadu , har yanxu fuskarta dauke da murmushi akai kamar kullum, lokaci zuwa lokaci takan duba agogon wayarta , ganin 9:00 ta kusa yasa ta mike wa , hart fara taku zata bar Wanjan, daddadan kamshin turaran king ya cika falon, jiyowa tayi tana sakar masa murmushi, shima narkakkun ida nuwansa ya zuba mata yana binta da kallo, har ya karaso wajan, hannunsa guda daya yasa tare da kamo na ammi ya zaunar da ita, har lokacin be ce komai ba , kusan mintuna daya kafun ya ce mata kinyi kyau sosai hakwaranta ya fito waje jin abinda yace  kaima kayi kyau son , kamar Wanda ya dawo daga zance , dan tabile bakinsa yayi tare da kawar da zancen, coffee ammi har ta bude baki da niyar bashi amsa wayar hannunta ta soma ringing, tana zaunan ta daga kusan mintuna biyu kafun ta kashe ,mikewa tayi tare da nufar kitchen , a tsaye ta tarar da tahee da asabe suna aiki, kallan asabe ammi tayi a hada coffee a kaiwa son , kinsan baya san jira , tana gama fadar hakan ta bar kitchen din, hannu asabe ta dora a ka  na shiga uku na lalace sai kuma ta shafa kumatunta, tuni jikinta ya hau rawa, ita tahee dariya ma abun ya bata daga cewa takai coffee har da yar kwalla , bata ce Mata komai ba sai binta da kallo da take,girgiza kai kawai tayi atunanin tayi coffee din ne bata iya hadawa ba shiyasa duk ta zure haka  kawo kayan na hada miki , sosai asabe ta shiga yi mata Godiya kamar zata zugunnata mata, kayan coffee din kuwa ta dakko mata , tare da nuna mata coffee maker din, bata san yadda ake anfani dashi ba, da temakon asabe ta hada coffee din da ko a ido sai ya burgeka, neman hanya guduwa asabe , tana ganin tahee ta kammala hadawa, tace mata bari taje ta dawo, TAHEE bata gane ba sai jinjina mata kai da tayi , kusan yan mintuna ganin coffee din na kokarin jin sanyi yasa ta dauka hankali kwance tare da nufar falon, agaban idan asabe dake bayan kofa sai faman hada zufa take, da sallamarta t shigo falon, Sam ta manta coffee ne a hannunta sabida dandanan kamshin da ya cika mata hanci, kanta a kasa sai faman murmushi take, jin tana kara kusanto kamshin da takejine yasata lumshe idanuwanta,sosai yanayin falon yayi mata dadi, da bugawa kadan kadan da zuciyarta ke mata, bata ankaraba taji ta taka abu, a firgice ta bude idanuwanta, tsabar firgita bata san lokacin da kofin coffee din ya subuce mata ba ,baya b???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aya tayi zata fadi, sosai ta rintse idanuwanta dan ta sadakar faduwa zatai& .


Comment and share =??
Daga alkalamin Mss Lee =ؖ?

=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?

=ؖ?DUK KARFIN IZZATA (star lady)=ؖ?

=ؖ?GIDAN AUNTY( mss Lee )=ؖ?

=ؖ?YA FITA ZAKKA( maman sayyid )=ؖ?

=ؖ?JINI DAYA (mrs bbk)=ؖ?

=ؖ?SARKI SAMEER( xeenat love )=ؖ?
 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA


=ؖ?=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?=ؖ?
( a heart touching love story )

Story &written
By
Mss Lee =ؖ?

=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?

PAID BOOK

Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart d'? you Lodi Lodi.

Book 1 =ؖ?

Free page 13>؋?

Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata, ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata  are you mad taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa  are you mute takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara  kayi hakuri dan Allah  , ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi , clean this mess, and bring my coffee , ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki  toh tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali Wa alaykumussalm  , ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace  gashi kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske  coffee daga nan be kara cewa komai ba. Innalillahi  shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa  wait ,ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa  coffee , kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa  is she mad  ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din.

A Daidai gaban dressing mirror din dakin ta tsaya sai faman haki take, ita kadai ta san karfin halin da tayi kafun ta rugo a guje , sosai zuciyarta take harbawa ga wani irin kasala da take ji,  amma kyakkyawa ne ta fada a ranta sai kuma ta ja dan tsaki, tare da hade rai  coffee , coffee ,coffee ,ko wanne shi oho, bata gama tunaninta ba fuskarta ta hango mata yadda fuskarsa yake a hade, yawun bakinta ta hadiye nide nashiga uku sai kuma ta tsaya kamar me tunani  wata kila bakone shima , naga bayajin Hausa gashi dan balarabe dashi da wannan tunanin ta kwantar da hankalinta, watsa ruwa tayi tare da kwantawa, lokaci zuwa lokaci tunanin mutumin na fado mata a rai musamman yadda dan karamin bakinsa ke cewa  coffee .

*******
WASHE GARI
Tahee na zaune kan lallausan medium carfet din dakin tana karanta azkar din ta aka kwankwasa kofa , bada izinin shiga tayi, a hankali asabe ta turo kofar bakinta Dauke da sallama sai faman kawar da Kai take gefe , TAHEE na kula da yanayin ta amma batace mata komai tunda itama Allah ya tseratar da ita .gaishe da asabe tayi, duk sai asabe ta tsargu ta kasa cewa komai har tazo fita sai ta Waiwayo kanta a kasa, uhm dama hajiya ce tace idan kin kammala cin abincin ki same ta a falo , toh kawai tahee tace mata kafun asabe ta bar dakin. Tana kammala cin abincin da aka kawo mata kamar yadda ammi ta umarcetan falo ta nufa, anan ta tarar da ammi na kallo a tv, ammi na ganin ta tamike  Yawwa daman ke nake jira , nasan kowa yana falan dada , da karfi zuciyar tahee ta buga , tuno fuskarsa da tayi  nashiga uku , yanxu ya zanyi idan naganshi acan , ammi ce ta katse Mata tunanin da ta fara , muje ko murmushin yake tahee ta saki har ynxu zuciyarta bata dena bugawa ba ,a haka suka nufi part din dada kasancewar hijabi ne a jikinta.

Zazzaune suke a falon dada , sai faman hiransu suke gwanin burgewa , shigowar su ammi ne yasa ko wannansu maida hankali kan har yar shigowa, amrah na ganin tahee take a wajan wani tsanarta ya darsu a ranta, ji take da za ta kashe mutum babu wannan da zata kashe face wannan maiyar. Cikin sanyin jiki ta gaishe da kowa na falon , ganin irin kallan da kowannansu ke binta dashi, sabanin ummey da abeey da fuskarsu ne dauke da murmushi, sai kuma dada dake faman washe hakwaranta.  Zonan kizauna kusa dani cewar dada , a hankali tahee ta koma kusa da ita , nuna abeey dada tayi  kinga wannan , toh shine babban dana , kuma shine baban yaran gidan, daga yanxu Kema zaki dinga kiransa da abeey kamar sauran , sai musaddiq da uncle Saleem da ta nuna,  wannan kuma Itace babbar maman ku, ana kiranta da ummey, ga kuma matan kawunki musaddiq , ana kiran wannan ta farko mamy sai kuma momy gatanan, sai kuma ta karshen su da ake kira da aunty , ita matar kawunci salim ce, ga yan matan gidan kuma ,duk da nasan zuwanki zaki iya saninsu tunda kullum suna wajan maman yara, bayansu akwai babbar yayarsu dake aure a saudiya sunanta samareena (samreen=??) ana ce mata ukuti( ukhti)zaki ganta wataran,akwai maza guda biyu suna karatu a turai, sai sadauki tana ambatar kalmar sadauki gaban tahee ya fadi , jitai dada na cewa  zaki ganshi shima wata ran amma kiyi taka tsantsan , ah too in fada miki gaskiya, ga autar gidan kuma can ta nuna zoya dake kwance kan cinyar ammi tana bacci,kadan tahee ta dago ta kalleta  amma kyakkyawace sosai  ta fada a zuciyarta Nima akwai yar autata da ban fada miki ba sunanta  zarmeen sai danta kwallin kwal wato mijina sha aban  .kallan abeey da ummeey tayi  nasan ku ai duk kunsan da zuwan ta ko eh dada duk suka bata amsa , har yanxu da Sauran guntun murmushi akan kumatun ummey, toh sunan ta tahura yalwataccen murmushi abeey ya saki  taheera dai ko dada , gyada masa kai dada tayi  au kai da kasan da sunan ma amma sai ka wahalar dani , wani murmushi abeey ya kara saki batare da ya ce komai ba , kallan ta hajiya ameena tayi cikin sakin fuska gata kuwa kyakkyawa da ita kamar ka sace , sosai ran amrah ya baci da Jin kalaman auntyn tata, ranta ya baci sosai da irin yadda kowa ke karbarta,  Shegiya in ma asiri kikai musu nice zan karyashi  ta karasa tare da binta da kallan tsana bata re da kowa ya lura da ita ba .

*********
**************
Zaune take kan daya daga cikin daddiyar kujerar falon mahaifiyarta, tunda suka dawo daga falon dada take zaune a wajan hannun ta dauke da juice yayin da Dayan hannun nata ke dauke da wayarta sai faman latsawa take , sam hankalinta na kan abunda take a wayarta, jin taku a falon yasa ta saurin fita daga abunda take tare da sassaita nutsuwarta, hajiya hauwace ta shigo falan, tun zuwansu falon dada sai yanxu ne take dawo wa , cikin izza take taku har ta karaso kan daya daga cikin kujerun dake fuskanta sumayya. Murmushi sumayya ta saki, mamy daman ke ce ,  nice mana akwai Wanda kike jiran zuwan sane  , tabe baki sumayya tayi , toh mamy daga tanbaya, tun dazu nake jiranki fa , amma daga zuwanki kina so ki bata mun fai  , washe baki hajiya hauwa tayi  Haba summy ta ne yayi zafi kinsa Nima wasa nake miki , jinjina kai sumayya tayi mamy baki kula da yar iskar yarinyar da aka kawo gidan nan ba , ki duba ki gani fa yanda kowa ke kaffa kaffa da ita ko mu da muke jininsu ba ai mana wannan abun ma , musamman dada da ke faman nanike mata, wallahi in bamuyi wasa ba sai dai mu zama yan kallo a gidan nan , se abunda yar iskar yarinyarcan ta fada sannan za ai , kina kallanta kinsan ba haka taxo ba , akwia wata kullalliya a kasa , ni tsorona kartaje ta asircemun king, sabida kinga yawanci king acan yake wuni kuma mu ba mu isa shigaba in yana nan, gaskiya mamy ya kamata ki dauki matakin gaggawa, bazan taba bari cikar burina ya tafi a banza ba , inaso nayi suna, inasan duniya ta san da za mana , inasan mallakar king ko ta halin yayane mamy kin Hana na nuna alamun ina san sa a fili har waccan banzar take tunanin auransa, dole mamy na mallakesa sannan dukiyar gidan nan mu ya kamata muji dadin ta ba wasu ba , ta karashe maganar tare da kurawa mahaifiyar tata idanu, sauke nunfashi hajiya hauwau tayi kafun ta soma magana  tabbas Kinyi gaskiya Nima na dade ina halkanta da hakan , a sannu zanyi maganin kowa dan bazan taba bari dukiyar da na kwallafawa Raina zubucewa ba , aure kuwa kamar anyi shine  . Sallamar ihsan ce ta katse musu zancensu , bin ko wannensu tayi da kallo tare da girgiza kai, tasan halinsu Sarai , fatan ta Allah ya shirya mata su, ganin yadda take bunsu da kallo ne yasa mamy mikewa tare da hararar ta sama sama ,bata jira cewar ihsan din ba tai wuce warts daki, itama sumayyan tashi tayi tare da nufar nata dakin,ganin duk sun watse ne yasata kiran number wayar da tayi saving da my yaya, bugu biyu ya dauka..

>???>???>???>???>???>???
Tunda ta dawo daga part din dada take safa da marwa , ita kadai tasan radadin bakin cikin da takeji, ta tsani yarinyar tsana mafi muni, ko ita lokacin da tazo ba a nuna mata kauna haka ba kamar yadda aka nuna wa waccan ,  tabbas sai na lahantaki, lahanin da ko kyawun da akace kina dashi ze gushe, da kanki zaki bar gidan nan , duk wannan zan tuttukan ita kadai amrah take yinxu kamar wata zautacciya, tunani ta fara me zatayi mata da zai kunsasa mata , ta dade tana tsaye a falon kafun ta saki wani shu umin murmushi, kitchen Dinsu ta nufa, ba a dau dogon lokaci ba ta fito sai faman sakin murmushi take , direct part din ammi ta nufa dan tasan har yanxu su ammi Suna part din dada, ilaikuwa tana shiga bata tarar da kowa ba sai kamshin turare da sanyin Ac dake tashi, jin motsi a kitchen yasa ta kara sakin wani shi umin murmushin, ta dau kusan mintuna biyu tsaye a wajan, jin alamun taku kamar za a fito daga kitchen din yasata zuba mangyadan da debo a kan hanyar da ta san dole koma wanene ta nan zai wuce . Taheee ce ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bottle water tana sha dan ishirwane ya kaita kitchen din, bata san da mutum a falon ba , sai ji tayi an tura ta da karfin gaske, kafarta ta sulleba a cikin man da amrah ta zube, sosai ta saki gigitacciyar kara tare da tafiya Gadan gadan zata fada , ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login