Showing 30001 words to 33000 words out of 144575 words

Chapter 11 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28441

riko hannunta yayi tare da kallanta  coffee shine kadai abunda yace mata , jinjina masa kai tayi tare da nufar kitchen din, a tsaye ta samu tahee da asabe na aiki a kitchen , sosai tahee take jin dadin hakan sabida tana Kaunar taga ta iya abinci hala hala , ba tare da ta kalla taheen ba ta soma magana,  tahee hadawa son coffee kafun na kammala dafa masa abinci , suman tsaye tahee tayi , zuciyar ta sai bugawa take gashi bata da dalilin musawa, kamar wacce zata saki kuka haka ta hada coffee din tare da fita falo , ko ina na falon mayataccen kamshin turaran da ke mata dadi ne ya cika wajan, Zuciyarta sai faman zillo take sabida tsoro, a hankali ta karasa inda yake bayan tayi sallama , cikin in ina ta soma magana  ina.. kwana , kamar wacce tai da gunki ko motsi beba sai ma sarrafa wayarsa da yake cikin nutsuwa , kamar wacce zata saka kuka ta kara cewa  ina.. kwana , yanxu ma be motsaba balantana tasa ran amsawar, siraran hawayene suka dan zubo mata kadan tare da sun kuyar da kai, kamar daga sama tayi saukar muryarsa  fine , wani murmushi ne ya subuce mata, sosai taji dadin amsawar dayayi, a hankali ya sa fararan dogon yatsunsa tare da dauka cup din, a hankali ya fara sipping, zuyawa tahee tayi da niyar komawa tazo daf da kitchen din ta tsinkayi muryarsa  who permit you to leave , sun kuyar da kai tayi tare da dawo wa ciki  bakowa  ta bashi amsa , tsawan mintuna goma tana a tsayen , kofin hannunsa ya ajje tare da kyara zama, another cup, Tom  kawai tace masa tare da nufar kitchen din, har lokacin ammi na tsaye tana masa abinci da kanta, kallanta ammi tayi sai yanxu, sauke ajiyar zuciya tayi  wani cup din yace na hada masa kallanta ammi tayi sai dai bata ce mata komai ba sai jinjina mata kai da tayi, wani cup din ta kara hadawa tare da nufar inda yake har yanxu zuciyarta bata bar bugawa ba, sallama tayi a falan kamar bazai amsa ba , sai ya amsa a hankali, batare da wani dalili ba lokaci daya taji kanta ya sara mata Daidai lokacin da zata mika masa coffee din, a maimakon ya sauka a hannunsa sai ya subuce ya zube a jikin hadaddan suit dinsa & & .

(=?3?=?3?Tahee )& &

Manage plx & .

Masu comment ina Godiya sosai da sosai

MASU BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 .

MASU BUKATAR A TALLATA MUSU KASUWANCINSU SU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581 AKAN NAIRA 500 KACAL.

=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?

DUK KARFIN IZZATA ( star lady )

GIDAN AUNTY (mss Lee )

JINI DAYA (mrs bbk)

YA FITA ZAKKA( maman sayyid)

BABY (mhiz innocent)



=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?Mss Lee
'?.
 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4

=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?

PAID BOOK

LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDI NE AKAN NAIRA 300KACAL , MAI SAN CIGABA DA KARANTAWA HAR KARSHE ZAI BIYA KUDINSA TA WANNAN ASUSUN :
7041879581 OPAY
AYSHATOU GALADIMA , sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

BOOK 1 =???
(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE d'?d'?&
Free page 16 >؋?

Sosai tazaro idanuwanta waje tana faman girgiza kai,bata san lokacin da ta karasa kusa dashi tana kokarin goge masa ba , gigitacciyar tsawar da ya daka mata a lokaci daya da lafiyayyen marin da ya sauke mata ne yasata kara firgita, ga kanta da yake tsananin sara mata, lokaci d aya taji juwa na dibarta  Dan Allah kayi hakuri shine abunda bakinta ya iya furtawa, be kuma cewa komai ba sai mikewa da yayi kwasan wayoyinsa,Daidai lokacin da tahee take kokarin fadawa kan wani designer dake gefenta , taku daya yayi ya riko damtsen hannunta tare da Jefata kan daya daga cikin kujerun tare da sakin siririn tsaki, cikin bacin rai ya bar part din azahiri Kuma fuskarsa tananan a yadda take, baka isa fassara yanayinsaba  me ya Hana ban karyataba  ya fada a cikin zuciyarsa ransa na kara baci , dogon tsaki yaja iya kasan makoshi, hatta zaki daya bude masa kofa yayi mamakin ganin sa haka amma bashi da hurumin magana a haka har suka koma part dinsa.

Tunda ya jefata kan kujerar da ya tashi har yanxu bata bar wajan ba , sosai taji kanta na sara mata, ta dau kusan minti biyar zaune a wajan tana addua, kafin lokaci daya ta nemi ciwan kan ta rasa gabaki daya, ajiyar zuciya ta sauke sai a lokacin kumatunta ke mata zafin marin dayayi mata , dafe wajan tayi tana sosawa  Mugu kawai ta fada a zuciyarta tana turo dan karamin bakinta, amaimakon ta koma kitchen kai tsaye dakin ta ta nufa tare da fadawa kan gado tana sauke a jiyar zuciya har yanxu hannunta na kan kuma tunta.

*******Ta dade kwance a ban dakin a sume, bugun ban dakin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da ake da karfine ya farfado da ita, tayi mamakin ganinta kwance a kasa ga tsami da jikinta ke mata,kara bugun kofar da akaine yasata mikewa cikin din gishi, towel dinta dake Yashe a kasa ta dauka tare da daurawa, da Kyar take taka kafarta dake mata tsami, sai bin ko ina da kallo take, da kyar ta karasa jikin kofar, a tsaye ta sami aunty duk ta rude, tana ganinta ta saki ajiyar zuciya me kikeyi acikin ban daki tun dazu, kinsan irin neman ki da nayi , batasan lokacin da bakinta ya furta  bacci ne ya daukeni  ,kallan ta aunty tayi tana sakin baki  bacci fa Kikace amrah  , gyada mata kai amrah tayi tana turo bakinta tare da rabata tawuce , binta kawai aunty tayi da kallo batare da tace komai ba tabar dakin. Samun waje amrah tayi kan gadonta tare da dakko wayarta dake ajje saman gadan, dogon tsaki ta saki sai a lokacin take tuno abunda tahee tayi mata,azabure ta mike tsaye  ni amrah , nice yau nake bawa wata yar iska hakuri, ni amrah hmmm girgiza kai tashigayi  yau nice na kaskantar dakai na bawa wata shegiya hakuri, wallahi ko zanyi yawo tsirara sai na wulakanta ta sai na musgunawa rayuwarta sai tasan dani take magana  ta kare zancen tana sakin kwallar bakin ciki&

******* Director part dinsa ya nufa sai faman taunar lips dinsa yake, be bi steps ba ta elevator ya hau , a second floor dinshi ya tsaya ko ina sai faman tashin kamshi yake da sanyin Ac musamman kamshin turaransa da ya kama ko ina na part din, rigar jikinsa ya cire kai tsaye faffadan zurar jikinsa ta fita fari tass dashi,sosai muscles dinsa da 6 spacks dinsa ya fito kallo daya zaka masa kasan ba karamin motsa jiki yake ba,kofar da take facing dinsa ya nufa, ya dau kusan mintuna 30 aciki kafun daddadan kamshi ya karade ko ina , sosai yayi kyau , a maimakon suit yanxu kananan kayane a jikinsa ,tun daga kan bakar jigar jikinsa tare da bakin wanda jikinsa , sosai yayi kyau cikin kayan , sumammiyar gashin kansa ya fito sosai yau ma kadan daga cikin yalwataccen gashin kansa ya fito har wajan idanunsa, sabida tsananin bacin rai pink lips dinsa ba karamin turuwa yayi ba sai faman tsuke fuskar yake, cikin takunsa na kasaita ya hau elevator tare da nufar 3rd floor, a maimakon hanyar da ya saba bi yanxu wata daban yabi,babban waje ne nashakatawa gata iska me dadin gaske dake huro wajan,kayataccen wajan shakatawa ne a wajan sosai wajan ya hadu,ga gefe d aya dayake abude ko ruwan sama akai yana dan shigowa kadan kadan , akan daya daga cikin kujerun shakatawan yazauna ne kama da sararin samaniya, sosai yanayin wajan yasakashi cikin nutsuwa sai faman lumshe ido yake, daga gefensa ma wani cup ne me shegen kyau cikin sa wani lemone kamana da sararin samaniya shima.sai faman lumshe idanuwansa yake yana budewa, wayarsa dake ringing a hankali ya dauka batare da bata lokaci ba, Ahankali yake magana ko nakusa dashi ba Lalle yaji me yake cewa ba,sai lumshe kyawawan idanuwansa da yake faman yi.

>???>???>???>???>???>???>???
Futowar da ammi zatayi a kitchen ne taga babu king babu tahee, tsayawa bin falon tayi da kallo kamar anan ne zata gansu,a tunaninta tahee ta koma daki ne shiyasa bata bita ba ta dauki wayar ta da niyar kiran king, tana kara wayan a kunnenta ta haye stair case din din falon..

A dan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci ya dauketaba, wasu matasan yara tagani da akalla befi su bata shekaru uku ba, kyawawa dasu sai faman kuka suke , daga gefensu wani farin macijine shima tass dashi, kallan tahee dake gefe sukai sai suka kara fashewa da kuka , suna kuka suna biyota , cikin tsorata tahee ta fara jan baya, girgiza mata kai suka shigayi, cikin daddadan muryarsu  sun kashe mana farin cikin mu , sun cutar damu, bamuyi musu komai ba, laifin me mukai musu, nace laifin me mukai musu suka karasa cikin data tsawa , firgita tahee tayi da yanayinsu, ganin sun tsaye ne yasa itama tsayawa,cikin rawar murya tahee ta fara magana  su..suwane ku, me nayi muku , dariya suka saki tare da kara sakin wani saban kukan,  SIF,LOLA, sai kuma farar magan ciki ta shafa can macijin nan SUSAN , tana gama fadar haka suka kara sakin kuka tare da bace bat kamar basu taba wanzuwa ba. A firgice tahee ta farka daga baccin da ya dauketa bakin ta dauke da addua , shafa wuyanta da ya dan rike tayi me yasa nake yawan mafarkin masu sunannan,su wanene su ganin babu me bata amsa yasata mikewa , kayan jikinta ta cire tare da shiga wanka , mintuna kadan tafito daga nan dakin, daya daga cikin abayoyin da ammi ta bata ta saka , gaban mudubin dake shake da kaya ta nufa,kurawa fuskarta ido tayi ganin irin sahirtaccen kyan da tayi a cikin kwanaki uku da tayi a cikin gidan , sanye take cikin red Egyptian abaya sai faman walwali stone din jiki ke dauka,asalin farin fatarta ta buzaye ta fito tass a jikinta, yayinda cikakken yalwataccen gashin kanta ya sauko har wajan kugunta, sosai bakin kwantaccen gashin goshinta ya kara kwantawa tare da dogon siririn hancinta , ba make up ne a fuskarta ba amma fadin haduwarta bata lokaci ne musamman dan karamin lips dinta da ya fito tass dashi kamar wacce ta saka janbaki,bakin kwalli ta saka da ya fito da farin kyawawan idanuwanta, sosai kwallin ya fito da asalin kwayar idanunta,cikakkiyar gashin girarta da dogayen eye lashes din idanuwanta su suka kara fito da ainahin kyawun fuskarta , ba ma a bociyar lip gloss bace shiyasa tabar dan karamun lebenta a haka, ribbon dinta ta dauka shima red colour tana kichiniyar daurashi, sosai ta jigata kafun ta daureshi sabida cikowarsa,mayafin abayarta ta dauka tare da yafashi saman kanta, red din takalmin ta ta saka , gaban mudubin ta kara komawa tare da karewa kanta kallo , murmushi ta sakar wa kanta tare da rufe fuska ,  ke din me kyau ce  kalmar da kullum taheer ke fada mata, murmushi kawai ta kara saki , tayi kewarsu sosai, hanyar fita daga dakin ta nufa bayan ta gama feshe jikinta da turaruka, Daidai lokacin da yan matan ke shigowa part din,amrah sai faman dingishi take haryanxu jikinta be dena tsami ba, sakin baki tayi ganin irin kyawun da tahee tayi, bama ita kadai ba hatta su ihsan duk sakin baki sukai suna binta da kallo, gaishe da su tayi babu Wanda ya amsa mata sai ihsan dake faman sakin murmushi,  tubarkallah Masha Allah , gaskiya ke kyakkyawa ce tahee ,sun kuyar da kai kawai tahee tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, binta da kallo su sumayya sukai kowa yana hadiye abunda ke ransa, dogon tsaki amrah taja tare da karasa kan daya daga cikin kujerun falon, sosai take bakinci, dama ace Itace take da wannan kyawun, wani dogon tsaki ta kuma ja tare da daukar wayarta suma duk yan matan waje suka samu tare da zama ,ihsan ce ke kokarin magana ,jin sallamar zoya ne ya katse mata zancenta, inda Ihsan take ta nufa  aunty ihsan rungumeta ihsan tayi  na am my baby kallan yarinyar da aka kira da baby tahee tayi , Itace dai yarinyar da ta gani tana bacci, aunty ihsan wai ina da wata aunty tana ina  murmushi ihsan ta saki,  toh daman bazuwan kowa kikai ba sai na auntyn taki ko dariya zoya tayi tana rufe fuskarta , itama murmushi ihsan din ta saki  oya kinganta juya wa zoya tayi tare da kallan Wanda aka nuna mata, zaro fararan idanuwanta irin na king tayi,  aunty ihsan tana kyau, harta fini ma, amma yaya king dina ya fita dariya ihsan ta saki kawai , sai alokacin tahee taga tsananin kamanninta da Wanda yake zuwa part Dinsu,murmushi kawai tahee ta sakar mata, itama murmushi zoyan ta saki  Aunt ya sunanki taheera shine kadai abinda tahee tace,kara zaro ido zoya tayi  sunanki me dadi , ni kuma zoya yanxu Kema kinzama aunt dina kinji girgiza mata kai tahee tayi sosai yarinyar tashiga ranta, duk wannan abun su sumayya na zaune suna kallan ikon Allah musamman amrah dake jin kamar ta samu wuka ta caccakawa tahee..shigowar ammi ne ya katsemata tunanin da ta shiga, yaude yan mata na sai yanxu nake ganinku ko wannansu murmushi ya saki sabanin sumayya da amrah da suka saki na yake  Aah ammi kinsan akwai school shiyasa  gyada musu kai ammi alamun gamsuwa kafin ta mike , yanxu dai ku Tashi ku kaiwa son abinci sai a dawo a yi hirar , cikin firgita kowannansu ya zaro idanuwansa tare da furta YAYA KING& ..


Comment and share .

=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?
Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Ya fita zakka
Jini daya
Sarki sameer
Baby .


MSS LEE=ؖ?..
 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4

=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?

PAID BOOK
littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581.

BOOK 1 =???

Free page 17>؋?

Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace  zani ammi jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta, mtswww na tsani shishshigi Wallahi  , kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi,  zaki hanani taka ko ina na gidan mune , dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu  malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita,  Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi  ammi zan bita murmushi ammi ta sakar mata  toh daughter  kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka.

Zaune dada take kasan lallausan carfet din falon ta, kamshin farfesun kayan cikin da akai mata sai faman tashin kamshi yake, cikin sallah tahee ta shigo falon tare da zoya,amsa sallamar dada tayi tana sakar masu murmushi sai yanxu kika tuna dani tahura, ai nayi fushi  ,sun kuyar da Kai tahee tayi cikin jin kunya kiyi hakuri dada ba haka bane , dan ta bile baki dada tayi  gaskiya kam ki gyara, ko d an hirar nan ki dunga zuwa kina tayani tunda su wadancan bankadaddun ba zuwa suke ba, sarakine kawai shima kullum cikin fada muke , kallan ta zoya tayi dada nifa , kinsan dai ina zuwa ko ,sakin baki dada tayi tana kallanta kiji tsoran Allah, ni nayi mamakin ganin ki ma yau, ba dai kyau karya kinsani , dariya zoya tayi tana rufe dan karamin bakinta, sakon da Ammi tabayar abata tahee ta mika mata  Allah sarki,kilishi ba dai mutunci ba ,duk gidan nan ita da hajiya suhaima ne masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login