Showing 117001 words to 120000 words out of 144575 words

Chapter 40 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

32164

ya tayar dashi, kan gadon ya karasa har yanxu bacci take peacefully abinta, goshinta ya danyi pecking kafun ya bar dakin.

Mintuna 15 da futarsa ta fara motsa idanuwanta kafun ta budesu gabaki d aya, mamakine ya kama ganin ta kwance akan gado, wayar da akayi mada da text message ne kawai ya fado kanta, duk yanda zata tuna zuwan ta kan gadon ta kasa, sakkowa tayi daga kan gadon bakinta dauke da addua, agogon dakin ta duba, 4 ta wuce da sauri tashiga toilet kafun ta fito ta kabbara sallah , tana Idarwa azkar dinta tayi kafun ta mike , kara kallan agogo tayi mamakinta har yanxu be dauke ba ganin be dawo gida ba, dan karamun bakinta ta turo waje kafun ta bar dakin, shima falon shiru alamar ba kowa a ciki,3rd floor ta hau nan ma shiru sai ac da kamshin turaran da ke buso dakin,dacin da bakinta ya somane yasata nufar fridge din data gani, tana budewa kuwa idanuwanta ya sauka kan kayayyakin ciye ciye dake shake a ciki, fiye da saurin fridge din, wani abun ma bata taba ganin saba, strawberry ice cream din data ganine yafi daukar hankali, janyoshi tayi tana sakin wani murmushin jin dadi, waje ta samu akan gado tana shan ice cream din, tana sha tana sakin dariya sabida yanda dadin ke ratsa mata kwakwalwa, idanuwanta ne suka sauka kan wata yar karamar roba dake kan bedside dinsa, ajje Ice creams din tayi tana janyo robar  ANTI DEPRESSANT shine abunda aka rubuta jikin robar, har zata mayar sai kuma ta fara karanta abunda ke jikin robar, da wani irin shock ta mike tsaye, tana karanta abunda ke jikin robar, wasu hawayene suka fara sakko mata kawai ta fada kan gadon ta fashe da kuka , saida tayi me isarta kafun ta mike dauke da robar a hannunta, zata bar dakin kenan shikuma yana shigowa da sallama a bakinsa kasa kasa, cikin zuciyarta ta amsa sallamar tasa fuskarta kwata kwata ba fara a, kallan yanda fuskarta ta dan tashi yayi kafun cikin sauri yayi yunkurun nufar inda take what s wrong with my baby , hannunta d aya ta nuna masa alamar ya dakata karo na farko a rayuwarta, da wani irin expression yake kallanta, be gama tunani ba ta dago robar drugs din dake hannunta,  Menene wannan , ta fada tana zuba masa idanuwanta da suka kara haske sabida kukan da tayi,wani irin harbawa zuciyarsa yayi sam ya manta daya sha drugs din ya barshi a fili , cikin dan daga murya kamar ba ita ba ta furta  maganin Menene wannan kakesha  , kokarin matsota yake ta kara dakatar dashi please calm down, am sorry I will explain , bata san lokacin da ta buga robar a  kasaba maganin ciki ya zube me yasa , me yasa , I thought Dagaske kake da kace kana sona, i though da gaske kake da kace kai dady nane, kana shan wancan pills din dukda kasan illar su, u re a doctor, I thought ka d auke ni a matsayin matarka, Aushe nayi kuskure ba haka bane, you re taking this drugs to& . to&  , ta kasa karasa zancan nata sabida wani saban kukan da yake kokarin zuwan mata tana dannewa, wani irin shock ne ya dake shi, jin kukanta yake kamar ana kara cakarshi da maki a zuciya gabaki d aya ya rikice , cikin sanyin murya ya furta  please don t be angry, I will explain  , manyan eyes dinta ta zuba masa hawaye na sauka akan idon nata bana bukata kawai ta furta tare da barin dakin, wani irin jirine yaji yana neman kayan dashi yayi saurin samun waje ya zauna , ga baki daya hannayensa ya tusa cikin gashin kansa yana ya mutsasu  I m in a big mess , she s more angry than ever , ya rasa Wana irin tunani zaiyi , bayaso koka d an tayi fushi dashi dan bazan iya daukan fushinta ba, da sauri ya mike ya nufi bayanta, yana shiga ya tarar da bata cikin bedroom dinta, ragowar bedroom din second floor ya duba , shima duk bata ciki, muryar da ya fara ji sama sama a falon kasane yasashi nufar falon kai tsaye, TAHEE ce a falon tare da su sumayya da suka zo falon, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo , adaidai lokacin da ta daga idanuwanta itama, tana ganinshi ta d auke idanuwanta fuskarta a dan hade kadan ta yanda su Ihsan bazasu gane ba. Oh my god  ya furta cikin zuciyarsa har yanxu ya masa dauke idanuwansa akanta, su firdausi na ganinshi suka kara gaishe ganin yanxu yana amsa musu gaisuwarsu bakamar daba, kanshi ya dan daga musu alamar amsawa dan kwata kwata ba shi yake bukata ba,so yake ya rungumeta, ya lallasheta ko zata dena fushi dashi, he want to feel her warm , he can t take it , satar kallansa ihsan tayi ganin yanda ya tsaya gabaki d aya hankalinsa na kan tahee dake dannawa waya,murmushi ta saki kafun ta kalli tahee, sister yau dai bari na cika miki alkawarin Pam cake din ki , bata jira amsar tahee ba ta mike ta nufi kitchen, firdausi da sumayya ma duk sun ankara dashi dan haka da sauri suma suka mike  muma bari mu tayaki dukansu basu jira jin amsar taba sukayi saurin guduwa , bece komai dan Hakan yake bukata, ganin ta tashi zata bi bayansu yayi saurin shan gabanta, hannunsa biyu yayi hade alamun pleading, dauke kanta tayi daga kansa zata wuce yayi saurin riko hannunta, fisge hannun tayi kafin ta furta  don t touch me again  , tana gama maganarta tayi upstairs, waje ya samu ya zauna kansa na sara masa, gabaki d aya launin idanuwansa ya canza Sabida yanda yaji xuciyarsa na masa zafi, ya dau tsawan lokaci zaune a kan kujera kamar ya bita amma yana tsoro karta kara wani fushin, ganin lokacin sallah yayi ne yasashi barin part gabaki d aya .

Aban garan su ihsan kuwa suna shiga cikin kitchen din suka kulle kofar, kwai kwayar yanda suka ga king na kallan tahee suka fara,  wayaga Romeo and juliet  cewar ihsan , dariya suka saki gabaki d ayansu, kan kujerun dake kitchen suka zauna suna dasa saban hira , daman space suka basu kar king ya koresu, sun dade suna hira abunsu kafun su fito falo, ganin babu kowa ne yasasu sakin ajiyar zuciya , da Sauri ihsan tayi hanyar kofa ,kallanta sumayya tayi alamun karin bayani kun manta pan cake mukace zamuyi mata, tana fitowa kara zaunar da mu zatayi , ni kuma ban shirya shan masga ba Wajan yaya ,ga baki daya basu yi wannan tunanin ba, gudun karta fito tazo ta samesu sukayi saurin barin part din.

Tahee kuwa tana shiga daki wani saban kukan tayi kafun ta shiga ban daki, Wanka tayi ganin ana kiran sallah tayi alwalarta, ta kabbara sallah bata bar daddumar ta ba sai da akayi isha i, wasu English wears ta saka masu daukar hankali blue colour , cikakken gashin kanta ya sakko har bayanta duk da hular da ta saka, wani irin masifaffen kyau tayi na musamman amma fuskarta har yanxu a cin kushe take, Fararan hannunta da yan yatsunta sun fito fes da masu musamman da kunshin hannunta ya kara fito da farinsu,Daddadan kamshin turaran princess ne ke tashi a cikin dakin ta ko ina, message din data gani akan wayarta ne ya sata sakin baki  sorry sis karkizo kiga bamanan ummey ce ta kiramu , ba kowa bane ya tura mata text din face ihsan, hararar wayar tayi kamar suna gabanta,kafin ta fito daga dakinta, karo suka ci da king da gaba daya yanayinsa ya canza, kallo daya tayi masa kafun ta d auke kanta  sannu da zuwa  ta furta zata bar wajan, ya rungumota ta baya yana sakin ajiyar zuciya, cikin disashewar murya kamar mara lapiya ya furta  I can t take it any more , please am so sorry, bayanda Kike tunani bane, raba jikinta tayi da nashi kafun ta furta  your dinner is ready , am not hungry, ya furta yana binta da kallo, bata kuma ce masa komai ba tayi wucewarta kan dining, apple ta dauka guda daya ita ma, ta wuce dakinta, zuciyar ta na raya mata ta kallesa amma ta danne, tana barin Wajan ya dafe kansa dake sara masa, tayi masa kyau sosai yau , and he don t like her frowning face, cikin sanyin jiki ya nufa dakin shima , yana kallan yanda take shan apple dinta cikin kwanciyar hankali, bece mata komai ba yace toilet,ya dade a ciki bayan ruwan sanyin da ya sakar wa kansa, ganin zazzabin nasa na kara yawa ne yasashi kashe ruwan, shima wasu kayan bacci ya dauka white colour masu kauri sabida yanda yake jin sanyi, turare kawai ya fesa ya fito, yana fitowa yatarar da fitula aka she sai lamp din da aka dan kunna, sai tun zuciyarsa ya rike yana cije lips ,sallar da ya saba yake so yayi amma ya kasa sabida ynda yake jin jikinsa, a tunaninsa tayi bacci ne shiyasa ya na hawa bed din ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya,kara rungumeta yayi kamar wacce za a kwace masa ita, tun lokacin da ya rungumeta ta bude idanuwanta ga zafin jikinsa dake ratsa nata jikin,tausayi ya bata kamar tayi magana sai kuma tayi shiru har bacci ya dauketa,  am so very sorry  yake fada a cikin zuciyar sa& .

Mss Lee =ؖ?

GIDAN AUNTY
07041879581

BOOK 1

Page 62

Kallan fuskarta dake bacci peacefully yayi kafun ya mayar dashi kan dan karamin bakin ta, lips din ta da sukai jajawur ya zubawa eyes dinsa kafun ya lumshe ido, kara rungumota yayi a jikinsa sabida sanyin da yaji yana ratsa shi, ya dau tsawan lokaci idanuwansa biyu ko alamun bacci bashi da niyar yi, har 2:30 idanuwansa biyu sai da bacci barawo yazo ya daukesa.

Farkon kiran sallahr asuba ne ya tayar da ita, jinta rungume a jikinshine yasa ta dan motsa a hankali tare da zare jikinta cikin nasa. Kyakkyawar fuskarsa ta zuba wa ido, kafun ta saka tafun hannunta akan goshinsa, tazo zata dauke taji ya rike hannun nata yana bude idanuwansa, da Sauri ta kwace hannunta tashiga cikin toilet, kanshi ya dan girgiza kafun ya bar dakin shima.

Tahee na fitowa simple doguwar jiya ta saka me warwar ash colour sosai kayn sukai mata kyau, tana idar da sallah gashin ta da ya ta kura mata ta soma tajewa bayan ta zauna kan stool din gaban mirror din,ta ciki taga shigowarsa dakin, a hankali ta amsa sallamarsa kafin ta jigaba da gyara kan nata, gaban stool din ya karaso shima, zata mike ya Mayar da ita tare da karbar Kum din hannunta batare da yace mata komai ba,a hankali ya gama taje mata kan nata kafun ya daureshi da ash ban din da yagani , ina kwana , yaji saukar muryarta har cikin kunnansa, wani irin dadi ne ya zuyarcesa amaimakon ya amsa mata gaisuwar da tayi hannunta d aya ya tare da juyo da stool din da take zaune akai, binsa kawai tahee take da kallo ganin kamar bashi da lapiya yau,bata Ankara sai ji tayi king yayi kneeling a gabanta, da wani irin mugun sauri ta sauka daga kan stool din itama zatayi kneeling ya hanata tare da mayar da ita kan stool din, kanshi kawai ya dora a cinyar tahee batare da yace mata komai ba, tunda ya dora kansa take jin zafin kansa na ratsa mata cinyoyi a hankali ta zura hannunta daya cikin gashin kanta , dady jikinka da zafi har yanxu, bari na hada maka breakfasts sai kasha magani, shiru be amsa mata ba ,sannan be dauke kanshi daga kan cinyartaba, sosai ta damu da hakan taga zazzabine a jikinsa ga sanyin Acn dakin da yawa kara mura ya kamasa, dady please ka koma kan gado sai na kashe mata Acn karya saka mura yanxu ma be amsa mata ba, gaban tane ya fadi tayi sauri saka hannunta a wajan hancinshi  da..dy,dady ta kira sunansa murya a harde cikin rawa rawa , a hankali ya bude bakinsa kafun ya furta  am sorry please  , hawayenta da suka sauka akan tashi fuskarne yasashi saurin bude idanuwan, bata Ankara ba taji saukar bakinsa akan kumatunta, eyes dinta ta ware masa , cikin sanyi da rauni ta furta  karka karashan maganin nan dady , kansa ya daga mata na dena tun da princess dina ta fushi dani, ya furta mata a hankali har yanxu muryarsa bata gama daidaitaba, hannunta me zobe ta mika masa,tare da mike wa tsaye, toh ka tashi mana , ta fada tana dan turo masa bakin ta, hannun nashi ya mika mata ita a dole zata mikar dashi, tana rike hannun nasa ya janyota jikinsa suka kwanta kan lallausan cafet din wajan me shegen laushi,bakinsa ta tura masa yayi sauri kuwa ya cafkesu ya fara tsotsa, ganin hakan be masa ba ya juyata ta koma kasan sa bakinsa cikin nata, bakin take kokarin kwacewa amma ya ki bata damar Hakan saida ya tsotsa iya yinsa kafun ya janye bakinsa cikin nata da yake ji kamar karya dena shansu, bakin ta kara turowa tana kauda kai, bata ankaraba ta karaji ya bata wani passionate kiss a wajan,  nifa Allah ka bari ta fada a shagwabe,  you re making me to add more  , girgiza masa kanta tayi  Nima kamun nauyi , hanjin cikina zasu iya fitowa fa , hannunsa daya ya dora kan cikin nata yana shafawa batare da yace mata komai ba ya dauketa ya kwantar kan gado, zai sauka tayi saurin jiki hannunsa  dady baka da lapiya fa, yanxu zan maka abinci sabida kasha magani , lumshe mata ido yayi  dont worry dear, I have important meeting, am sorry please  , kanta kawai ta daga masa tana sun kuyar da kanta common ni bana san wannan kalan face din, murmushi ta dan sakar masa tana boye fuskarta , oya let s go , ya kamata matata ta dunga yi mun wanka fa , ya karasa cikin zolaya, karamin pillow din dake hannunta ta buga masa  ni kana sani jin kunya  , murmushi ya saki kawai tare da shiga dressing room.

Tana ganin shigarsa tayi saurin sakkowa kasa , tunanin abunda zata hada masa me sauki ta fara, omelets ne ya fado ranta , cikin sauri ta soya masa shi, tare da coffee me zafi da ta hada masa daga saban abun coffeee dinta, bread ma tayi Toasting din shi, kafun ta koma dakin, a gaban Mirror ta tarar dashi yana taje gashin kansa da ya fara tsaho, wani blue din suit ne a jikinsa me kalar sararin samaniya, fadar irin kyau da haduwar da yayi bata baki ne ga wani irin daddadan kamshin turaran sa dake cika mata hanci, hakanan kawai sai taji wani kishi ya kamata , kenan yarda taga kyansa haka wasu zasu gani, har bata san lokacin daya karaso Wajan ba , sai tray din hannunta da taji ya dauka , a jiyar zuciya ta sauke tana bin bayansa  kayi kyau sosai fa, kuma ni .. kallanta yayi alamun ta karasa , itama kan kujerar ta zauna  kuma ke Menene  , kanta ta langwasar to ka gama breakfast dinka kasha magani, sir maa, your wishes is my command my stubborn wife  , bakinta ta turo ganin coffe kawai ya ke sha , fuskantar hakan ysashi fara cikin omelet s din ganin bata cine yasa shi kallanta ni bazan sha coffe ba, kuma bazanci kwai ba,sabida ni bazanyi kiba ba , kallanta yayi kafun ya furta  you re looking for my trouble ko , dariya ta saki bata kuma ce masa komai ba har ya kammala cin abinci, thank you, I enjoyed the food , but karki dafa komai , I don t want you to stressed your self , sakin baki tayi tana kallansa ganin yana kokarin saka suit din saman yasa ta temaka masa , bata san lokacin da ta furta  suma mata haka zasu ga kyankya in ka fita , ni Allah ban yardaba , sai kuma tayi saurin rufe bakin ta jin bara baraman da tayi, forehead dinta ya sumbata  duk Wanda ya kalleni zan ce a harbeshi matata tace kar a kalleni , murmushinta me kayatarwa ta sakar masa kafun tayi hugging dinsa  Allah ya baka abunda kaje nema, Allah ya kare ka da kare warsa, Allah ya tsareka daga Sharrin ma sharrata ya dawo dakai lapiya , so tie ya rungumeta  thank you, take care of your self, love you dariya ta saki kafin ta ce  me too , hancinta ya dan dan gwale mata  you will explain me too din nan, kinsa na makara ko , gwalo ta danyi masa tare da rakashi har falon kasa, zataje wajan kofa ya hanata, take care  ya furta tare da barin part din, ji tayi kamar an cire mata wani abu me nauyi Akan zuciyarta, shaf shaf ta gyara masa ban garansa , tare da naga ban gwaran, kulu na zuwa down stairs kawai ta gyara, ganin babu wani aikin tahee ta sallameta, taliya da manja take sha awa shiyasa tayi taliyanta da yaji pepper sosai tana gama ci ta dauki wayarta dagata tayi haske alamar message ya shigo  I LOVE YOU Angel  , murmushi tayi kafun ta bashi amsa da  LOVE YOU TOO , wani irin dadi ne taji ya kara kamata, cikin kan kanin lokaci tayi wani wankan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login