Showing 63001 words to 66000 words out of 144575 words

Chapter 22 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

32176

na gefensa tare da nuna wasu maza su biyu,wannan sune wanda za a tafi dasu yau ko,jinjina masa kai mutumin yayi kafun ya komar da kallan sa kan sauran mazan guda uku daya ya sunkuyar da kansa. Cikin daga murya ya furta  wadannan kuna tunanin zasuyi mana aikin kamar yadda ya kamata  duk tsayawa sukai daga maganar da suke kafun su zubawa mazan idanu, wata matace ta furta ku daga mun waccan yaran cikin cika umarni daya daga cikin samudawan nan ya dago da fuskar Wanda akace din,fuskarsa duk tayi duhu ga idanuwansa da suke a kulle ,sosai matar ta kallesa kafun ta furta wannan shine Wanda abar kauna ta sa a killace sa kafun a yi aiki dashi ko, cikin jinjina kai suka amsa mata, cikin daka tsawa matar tace ya bude idanuwansa , cikin galabaita ya bude idanuwansa da suka kankance. Cikin san tabbatarwa na kurawa Wanda aka daka wa tsawan ido, take a wajan zuciyata ta buga tsabar firgici, bakowa bane face TAHEER duk jikinsa taban duka.

>???>???>???>???>???>???>???
?'?'?'?'?'?'?'?'?'?'

A kwana a tashi ba wuya wajan Allah,yau kwana biyar kenan da tahee tayi loosing memory dinta, acikin dan lokacin nan ne kuma tahee ta gama period dinta batare da kowa ya gane ba sai king amma shi kansa yana mamakin yadda take gyara jikinta,idan ya tanbayeta kuma sai ta daga masa hannu alamar itama bata wani ba, da yawan lokuta tana nanike da dadynta,tun yana shareta har ya fara dan sakar mata fuska. A ban garan mutanan gidan kuwa har yanxu tahee taki sake musu, dama dama dada da take yawan janta a jiki bayan ita babu wajan wanda take zuwa sai zoya da take zuwa part din dadan. A dan lokacin nan kuwa sosai tahee ta gane amrah,sau da dama tana yawan kokarin cutar da ita amma cikin amincin Allah har yanxu batayi nasara ba.
A na cikin wannan yanayin abeey ya bada damar a fara hadawa tahee lefenta da duk wani abu da ake yiwa ya mace na auranta.

Sanye yake cikin wasu fararan kananan kaya ko fuskarsa ba a iya gani sosai sakamakon p-cap din dake kansa black colour ,dukda fuskarsa bata fito wa sosai bakaramun kyau kayan sukai masa ba , gefensa tahee ce a tsaye sai faman turo masa dan karamun bakin ta take , ni de zan bika dafe goshinsa yayi yana kallanta, banasan nana ta magana , langwabar masa da kai tayi tana niyar sakar masa kuka, girgiza mata kai yayi yana lumshe mata idanuwa , a hankali ya dan ware mata hannunsa , da sauri kuwa ta fada jikinsa tana kudun dunesa&

Masu comment ina Godiya

SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN DA YAKE SHIGOWA DAKIN AMRAH!?.

WU WANNE MUTANAN YOLA !?

ME YA KAWO TAHEER HANNUN MUGAYAN MUTANAN NAN!?

WACECE ABAR KAUNA DA AKE YAWAN AMBATARTA!?.

=ؖ?=ؖ?=ؖ?



=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?=ؖ?
Duk karfin izzata(star lady )

Gidan aunty(mss Lee )

Sarki sameer( xeenat love)

Dara taci gida ( maman sayyid )

Baby( mhiz innocent )

Jini daya ( mrs bbk)

Ubanane ko kishiyarta ( meemarh)

Mss LEE=ؖ?>? ?.

=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY=ؖ?=ؖ?
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee =ؖ?


=ؖ?=ؖ?THE TALENT TROUPE WRITERS =ؖ?=ؖ?

PAID BOOK

MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581.


BOOK 1=???

Page 37-38 =ؖ?

Maso da fuskarsa yayi Daidai kunnanta kafun ya furta  banda rashin ji da sauri ta gyada masa kai ,dago da ita yayi daga jikinsa kafun yayi mata kallo d aya ya dauke kansa,Jan hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujera kafun ya dakko magungunan ta, tana ganin magungunan ta fara kunkuni duk yana kallanta,Ballan magungunan yayi ya bata, kamar zatai kuka haka ta sha magungunan Sabida kallan da yayi mata, allura ya fara hadawa ,tana ganin alluran ta fara bunburi idanuwanta duk sun cika da kwalla, kallanta yayi kafin yayi magana tayi saurin cewa  ni bana san Allura ,be ce mata komai ya rike hannunta , da sauri ta mike zata gudu ya rike hannun nata kafun ya hade ransa , narai narai tayi masa da ido har kwallar data tara sun fara sauka, ce mata komai ba har yanxu ya dakko allurar,kuka kawai tahee ta fashe masa dashi, duk da Hakan be kyaleta ba sai da yayi mata allurar.Ta dade tana kuka be ce mata komai ba har sai da tagaji dan kanta ta fara ajiyar zuciya a hankali ,kofa ya nuna mata kafun ya furta  jeki wanke fuskanki , cikin turo baki ta mike tare da barin wajan , ba a dau dogon lokaci ba ta dawo idanuwanta har sun fara canzawa zuwa red colour . Har yanxu be kulataba sai ma nufar kofar fita da yayi,itama cikin sauri ta biyo bayansa sai faman kunburi take.
Direct part din dada suka nufa ,koda suka shiga ba kowa a falon sai su ihsan da basu dade da shigowa ba, ko wannan su shiga taitayinsu yayi musamman su amrah da ke binsa da mayataccen kallo kamar su hadi yeshi,har yar rige rigen gaishesa suke ,ba gaisuwar Wanda ya amsa acikinsu sai ma tanbayar da ya jefo musu cikin hade rai  ina da dada har saurin hada baki suke wajan furta  sunje gaisuwa ne , be kara cewa komai ba sai tahee da ya dan kalla ta kasan ido, har yanxu sai faman kunbure kunbure take , Taki yadda ta kalli kowa na cikin falon  I will be back  ya fada cikin kasa kasa da murya ,ko su da ke cikin falon babu Wanda ya jisa sai tahee data kara cuno baki, be kalli kowa na cikin falon ba ya fita ,ihsan ce ta kalli tahee tare da sakar mata murmushi, kin tsaya a tsaye ,toh kizo ki zauna mana  ko kallanta tahee batayi ba bare ta sa ran amsawa,kara maimaita maganar ihsan tayi, yanxun ma tahee bata kalleta ba sannan bata amsa mata maganar ba, cikin tsakanin jin haushi da tsantsan kishi amrah ta ja tsaki aikin banza , kece ma kika tsaya kula wannan kaskantarciyar da bata da maraba da kazamar bola, ni naso ace ba iya kwakwalwar ce ta juyeba naso ace ta haukace shegiya dan gin mayu da alama ba haka kika bar muba,kuma wallahi ko ina so ko ba kyaso sea kin rabu da king danshi mallakinane,bata kammala zancan nata ba sumayya ta kalleta cikin jin haushin karshen zan centa wai malla kinta,dogon tsaki sumayya taja kafun ta furta  iska na wahalar da me kayan kara tana kammala zancan ta tabar part din tana bin tahee da kallan tsana,ita dai har yanxu tahee tana tsaye kamar wacce aka dasa ,itama firdausi tashi tayi tabar part din batare da tace da kowa Uffan ba, falon yayi saura daga ihsan sai amrah da tahee ,tabe baki ihsan tayi kafun ta soma magana  ni bansan me ke damun ku ba wallahi tunda aure dai anriga an daura ai.. bata kammala zancan nata ba amrah ta zabura tana katseta cikin sauri, tsaya tsaya, idan bazaki goyan mana baya ba ,bama bukatar bakinki a ciki bude baki ihsan tayi da niyar yin magana taji wayarta na ringing , sunan mamy ne ya fito cikin wayar ,daga wa tayi tare da kara wayar a kunnanta,toh kawai tace kafun ta mike tsaye  zan dawo mamy na kira na  tana gama fadar hakan ta bar wajan. Sosai wani farin ciki ya lullube amrah, ganin daga ita sai tahee, dogon tsaki taja tare da mikewa tana bin tahee da wani matsiyacin kallo,kafun ta fara zagayeta tana tafa hannaye,TAHEE kuwa na tsayen ta har yanxu bata zauna ba sannan batayi wa kowa magana ba, bata ankaraba sai jin saukan mari tayi a fuskarta , da sauri ta dafe wajan da aka mare tan tare da dago fuskarta,amrah ce ta mare tan ,ta daga hannu da niyar kara marin nata tahee ta daddage ta tsinka mata marin itama, kara amrah ta saki sabida sosai taji zafin marin ni kika Mara ,shareta tahee tayi tare da juyawa da niyar barin wajan , saurin fincuko tahee tayi baya,sosai kafarta daya ta bugu, itama taheen karar azaba ta saki cikin fitar hayyaci ta shake amrah,tare da gantsara mata cizo,sosai suka fara fada musamman tahee da idanuwanta suka rine,sosai take jibgar amrah kamar wacce aka aiko,suna cikin wannan rigimar king ya shigo falon ,da sauri ya daka musu tsawa,rabuwa sukai ko wannansu yana sauke nunfashi sabanin amrah dake sauke nunfashin wahala, me ya faru ya tanbayesu cikin daka tsawa, mari na tayi tahee ta furta tana nuna ban garan fuskar da amrah ta mareta ,cikin rawar murya amrah ta furta  karya take mun,rashin kunya ta zo tana mun dan nace ta zauna , ganin irin kallan da king ya jefa mata,bude baki tahee ta yi da niyar magana ya daka mata tsawa, bata hakuri da sauri ta dago idanuwanta ,cikin rawan murya ta furta mari na tayi fa , Kallan da ya jefa mata ne yasa tayi shiru tana sauke idanuwanta,  kiyi hakuri ta furta kawai tare da juyawa , hawayen da suka zubo mata ta share tare da soma tafiya cikin din gishi, dan kallanta yayi ganin tana dingishi har ta fice da ga falan kafun ya mayar da kallan sa yayi kan amrah dake faman sakin murmushin jin dadi,tana cikin dogon tunanin da ta fada taji saukar mari a fuskarta , sosai marin ya shigeta ,bata gama dawowa ba ya shako wuyan ta ,ganin hakan be masa ba yasa ya murde mata hannu da karfin gaske kamar me shirin karya hannun kafun ,kara amrah ta saki cikin azaba ta soma bashi hakuri,guntun tsaki yaja kafun yayi wulli da ita yana binta da kallan tsana kafun ya soma magana cikin kausashshiyar murya  daga yau ,idan kika kuskura hannunki ya kara taba ko gashinta ne ,hmm ya karasa tare da jinjina kai kadan yana taunar lips, ko inda take be kalla ba yayi hanyar barin falon, amrah kuwa sabida azabar da takeji da bakin ciki yasa kukan da take ma ya dauke duka sai kukan zuciya da ta fara tana faman tsinewa tahee .

Yana fita daga part din yaci karo dasu dadan suna kokarin shiga part din,TAHEE na rike da hannunta,sai hawayen da take sharewa, ganin king ya fito daga part dinta yasa tayi saurin kallansa  Yawwa kwanda da Allah yasa na ganka,ga tanan sai faman kuka take mun na mata tanbayar duniya tace mun faduwa tayi sai ka lallashi kayarka,dan bazan iya ba ,ka dauketa ku tafi , ta kasan ido ya dan kalli taheen gefen fuskarta har ya danyi ja,kafun yace komai tahee tayi saurin cewa  ni zan zauna a wajan ki ba dada ba hatta king sai da ya dago idanuwansa ya kalleta ganin yadda ta hade ranta lokaci d aya, kikace me dada ta tanbaya cikin mamaki ,sau da dama in dada tace tazauna bata zama shiyasa abun yayi mugun bata mamaki zan zauna a wajanki ta kara fada har yanxu bata kalli inda dadyn nata yake ba,washe baki dada tayi cikin farin ciki oh Allah na ,yau de tahura zata yini dani ,Allah na gode ma  ,ta karasa tana kamo hannun tahee sai faman zabga mata murmushi take, dan tabe baki king yayi ba tare da ya ce musu komai ba ya soma tafiya,kallansa dada tayi  Kai de bakin halinka yayi yawa,yanxu matar taka ma bazaka ce mata ka tafi ba tunda ni ka rainani  , dan tabe bakinsa yayi kadan kafun ya kalli yadda taheen take danyin dingishin kadan kadan,harta shige part din dada,har yanxu kuma bata kalli dadyn nata ba, mai da kallansa king yayi kan dada kafun yace  toh matata sai na dawo  ya na kammala zancan nasa ya bar wajan, rike baki dada tayi tana bin bayansa da kallo kafun ta furta shi wannan Auran dan iska ma ya Mayar dashi ,wacece matar tasa ganin ba me bata amsa yasa tabi bayan tahuran itama.

A kofar shiga taci karo da amrah, tana ganin ta ,ta kara hade ranta ,tare da shigewa cikin falon,itama amrah binta tayi da kallan tsana kafun ta wuce tana cizon yasa.kan doguwar 3sitter tahee ta kwanta tana buye fuskar tata kafun ta fashe da kuka kasa kasa, a haka dada ta shigo ta sameta, ganin yadda ta rufe fuskar tata yasa dada tayi tunanin bacci ne ya dauke ta ke kuma tahura haka ake ai da kin wuce daki kinyi baccinki tana kammala zan can ta tayi hanyar zuwa dakinta. Har yanxun tana kwancan tana kukanta har bacci ya dauketa a hakan .

>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???

YOLA
Sosai ya jigata in ba kallan kurinla kayi masa ba ,ba Lalle ne ka gane saba, jikinsa duk ya saki sabida azabar wahalar da yasha, tsaki daya daga cikin mutanan ya saki kafun ya kalli Wanda ya dago da fuskar taheen,fatan dai kullum kuna basu hotan da ya kamata, cikin wata murmuya Mara dadi ya amsa mata,jinjina kai sukayi alamar gamsuwa kafun daya daga cikinsu ta furta ,a kara ninka musu hotan kamar yadda aka saba, ka tabbatar kana da ido a kansu ,duk Wanda yayi kokarin guduwa kuma ka harbe mun kansa ka ciro mun kwakwalwarsa,sosai matasan suka firgita da jin kalamanta, ko karfin motsa jikin su basu dashi balantana su rokesu,saukar bulala suka fara ji ,tun basa kokwarin guda har suka mike cikin a baza ,kafun a mayar dasu cikin kurkukun, kyalkyalewa da dariya mutanan sukai daya daga cikin mutanan ce ta furta  amma ni yarancan ya tayar mu da jikina ,dole na biya biyan bukatata kafun ya bar nan wajan,kara sakin wata yar iskar dariya sukai gaba ki dayan su , ta kusa da Itace ta kalleta , ni kuma ya zakiyi dani ,kinsan ke tawa ce ko shafa mata fuska tayi kafun ta sakar mata kiss agaban mutanan,saurin rungume juna sukai kafun su bar wajan, haka ko wannan su ya rike hannun partner dinsa suka bar wajan.

Cikin dakin da aka maidasu,cike yake da maza sosai aciki kowa ka kallesa a galabaice yake ,gashi ba daman yiwa juna magana, shima taheer yana rabe daga can gefe duk an tuttureshi,a boye yake share hawayan da yake zubo masa ,zuciyar sa fal tunanin oumman sa da tahee,kullum tunanin sa a Wana hali suke ciki yanxu..

?'?'?'?'?'?'?'?'?'

KANO
A cikin dan lokacin nan da tayi da mutanan gidan sosai suka saba musamman Khaleed da zahra, alhaji kabeer ne kawai bata haduwa dashi,har mamakin yadda su zahra suka sake da oumman yake amma har yanxu be ce mata komai ba akanta ko yayanta da suka bata .

Bayan idar da sallanta sosai take yiwa yayanta addua musamman taheer da batasan halin da yake ciki ba , tana adduar tana share hawayen da suke zubo mata,sosai tunanin taheer dinta yake mata yawo a zuci ko a Wana hali d anta yake ciki, ya zama dole ta koma bunkure ko ya dawo yana nemanta itama , wannan tunanin yasa ta mike sanye da hijab dinta duk da kasancewar bata da kudin motar da zata koma haka tafito falan , da sauri zahra ta mike tare da nufota  oumma sannu da fitowa, yanxu nake shirin zuwa wajanki, ga waje ki zauna kinji dan girgiza Mata kai oumma tayi  zan koma bunkure ko zanga taheer  da Sauri zahra ta rike hannunta  To zan biki oumma  girgiza mata kai oumma tayi , hawayene suka fara taruwa a idanuwan zahra  toh oumma ki zauna tare da mu dan Allah , share mata hawayen da ta fara oumma tayi kafun ta furta  kiyi hakuri zahra sosai zahra ta fashe mata da kuka gwanin ban tausayi dan ganin oumma take tamkar oummanta data rasa ,ganin yadda zahran take kuka yasa oumma kwata kwata bataji dadin abunda tace matan ba, suna tsaye a wajan shima Khaleed ya shigo falon, ganin yadda zahra tke kuka yasa ya karaso wajan ta yana tanbayarta ,fadawa jikinsa tayi sosai ta kara fashewa da kuka  yaya!! zata tafi ta barmu kace ta tafi dani kaji ta karashe zancen nata da fashewa da wani saban kukan.shima kallonta Khaleed yayi oumma dan Allah ki zauna damu, muna jinki kamar momma din mu da muka rasa ga baki d ayan su sun sakar wa oumma lakar jikinta,sosai tausayinsu ya kamata amma tasan ya zaman mata dole tunda ba a halinsu bace. Assalamu Alaikum  sallamar alhaji kabeer ta karade kunnuwansu, da gudu kuwa zahra ta nufeshi tana sakar masa kuka shima ,cikin matsanan damuwa ya kalleta , auta me akai miki abunda ta fadawa Khaleed shi ta fadawa dadyn nata, share mata hawayen fuskarta yayi  shikenan dena kuka auta ,zomu karasa ciki , murmushin jin dadi ta saki jin abinda yace mata,kama hannunta yayi suka shigo falan kafun ya kalli oumma shima, oumma dan Allah ki zauna damu ya furta yana kallan fuskarta ,ba zahra ba hatta Khaleed sai da ya murmusa ganin yadda dadyn nasu yayi,suma hade hannayensu sukayi kamar yadda dadyn nasu yayi, sun kuyar da Kai oumma tayi duk tana jinta a takure , fahimtar hakan yasa dady yace duk su zauna, samun waje sukai gabaki dayan su, cikin serous Tone dady ya soma magana, na da anbincika mun garin naku kamar yadda kika bamu labari, har yanxu ba a ga taheer ba amma jami ai suna kan bincikensu har yanxu cikin sauri oumma ta share kwallar dataji tana kokarin zubo mata, cigaba da magana dady yayi ko wana dan Adam da tashi kaddarar, sannan kisani Allah yana jarabtan salihan bayinsane domin ya duba imaninsu, tabbas duk musulmin Kwarai anaso ya yarda da kaddarar sa me kyau da mara kyau sosai dady yayi musu Nasiha gabaki dayan su ,har yanxu kan oumma a sunkuye taye, kafun daga karshe ya dora da  muna neman Alfarmar ki zauna damu nida yarana kafun abinciko inda taheer yake ,gamu da kokan baranmu ,saurin buda baki zahra tayi harda tsugunnawa Dan Allah kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login