Showing 126001 words to 129000 words out of 144575 words

Chapter 43 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

28450

hankali, ganin yanayin da ta shiga ne yasa ya ajje mata naman da take ci ya gara shafa mata bayanta hartaji nunfashinta na daidaita, kallansa tayi murna sosai d auke a fuskarta  finally my son will be a father , and I will be a grandma , oh my god, congratulations son dina  ta fada tana rungumeshi, shima rungumetan yayi yana kara jin wani irin farinciki na mamaye ransa, tanbayarsa wata nawa cikin ammey tayi, be damuba ya fada mata, wani irin farinciki yagani a fuskarta sosai harya so Bashi mamaki, har Ammeey ta fara lissafin siyayyar da za saka yi wa baby, shidai nasa murmushine , ya dan jima a part din ammey kafun ya bar part din, yana barin part din wani irin ball abbey tayi da plate din Kazan ta da ya sata bare wa, bata zauna a falon ba tanufi dakin ta cikin sauri.

Yana fita ya hadu da kabeer da haroon, cikin ladabi suka gaishe da king, abunda ya basu mamaki ganin yanda ya amsa musu cikin sakewa ba tare da ya dauke fuska kamar yanda ya saba ba. Be kara wani minute din ba ya nufi part dinsa. Bin bayansa da kallo su haroon sukai,  bro kaga kuwa abunda nagani, yau yaya king ne ke amsa mana gaisuwa babu hade rai,  cewar haroon,  Nima dai abunda ya bani mamaki , amma in tayi tsami ai zamuji, Yaushe zamuje ganin amarya  , kallan baka da hankali haroon ya bishi dashi,  da alama jikinka tsami yake , ka kwana biyu baka sha mari ba  , dariyar iskanci kabeer ya sakin kafun ya cewa haroon  Yaushe zamuje part din ammey , yau tun safe ban ganta ba , banza haroon yayi dashi yayi wucewarsa , shima kabeer din bin bayan haroon yayi suka cigaba da tafiya daman part din ummey zasu .

>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???
ABUJA

MAITAMA

Babban gida ne katan gaske da ya gaji da haduwa, babban gate din gidan aka bude lokacin da wata mota fara ta shiga cikin gidan ,Daidai parking space mamallakin motar yayi parting kafun ya bude motar, ba kowa bane ya fito face Khaleed dake sanye da bakin suit a jikinsa, wayace kare a fuskarsa da alama waya yake , direct inda entrance din gidan yake ya nufa , knocking biyu aka bude masa komar, karo yaci da zahra lokacin da take bude masa kofar, wayo idanuwa tayi kafun ta saki kara tana rungumeshi  yaya Khaleed oyoyo, nayi missing dinka  Daidai lokacin da yake gama wayar , banbareta yayi a jikinsa kafun ya dungure mata kanta  ke har yanxu wai bazaki girma ba , daddy da oumma zance su aurar dake ko na fadawa Hajiya kin isa aure duk kin cika mana gida  , sakar baki zarah tayi tana kallansa , kafun tayi magana wata hamshakiyar mata ta fito daka wata kofa jikinta sanye da purple din material , sosai kayan suka haska kyakkyawar fatarta duk da ashekaru bazata wuce shakara 43 zuwa 44 ba , da sauri Khaleed ya karasa wajan ta kafun ya rungumeta,  nayi kewarki oumma ,kullum sai nayi mafarkin abincin ki, da sauri na juya dan ganin wacce yake kira da oumma , sosai nayi mamakin ganin oumma ganin yanda hutu ya kwanta a jikinta ga wani irin masifaffen kyau da ta karayi sak buzuwa abunta, cikin nutsuwa ta sakar masa murmushin da dimple dinta sak irin na tahee lo bawa  Nima nayi kewar ka son, yanxu dai kaje kayi wanka kafun kaci abinci  , toh oumma ya fada tare da kallan zahra, da Sauri ta matso wajan  oumma kinga ko , yaya Khaleed ya dawo yanxu kin dena sona daman yanxu dady kawai ke sona , hajiya ma ta dena sona  , hancinta oumma taja  waya isa ya taba mun Autaras dina Kema kinsan wasa nake masa sabida ya dawo ne  , dariyar jin dadi kuwa zahra ta saki kafun su shiga kitchen ita da oumma, dakansu suka hada musu lunch, zahra ta nufi dinning tana shirya musu abincin, ita kuma oumma wani tray ta dauka ta nufi wata kofa , knocking din kofar tayi kafun a bata izinin shigowa , wata matace zaune akan wani lallausan carfet duk da manyanta ya gama fito wa a jikinta, murmushi ta sakar wa oumma  sannu maryama , Allah yayi miki albarka , bakya gajiya da d a wai niya  , murmushi oumma ta saki ba tare da tace mata komai, akan lallausan carfet din ta ajje mata abincin Daidai lokacin da Khaleed yake shigowa madaidaicin falo urn bakin shi d auke da sallama,  hajiya me rankarfe , kiyi aure mu huta da kuwa wacce yakira da hajiya tayi masa ,  saidai kaine zakayi Auran dan jakar uba, aika dawo zamu dora , bari uban naka ya dawo da kai da waccen ya galalalliyar yazo yayi muku aure , Kai invaka da mata akwai wata yarinyar Dije yar kawar kawata ce da mukayi mutumci amma san yarinyar kamar zararriya, nasan Itace maganinka, ita kuma waccan yaga lalliyar a bata shu aibu me wanki , kamar mutumin arziki khaleed ya karaso inda take kafarta da ta mike ta fara yiwa tausa cikin kashe murya ya soma mata dadin baki  Haba hajiyar mu me yayi zafi haka ,kinsan ba a shiga tsakanin mu dake ko, Indai mata ce zankawo miki ba da dadewa ba , kisha kuruminki , ta bile baki tayi  oho maka  , kallan oumma dake faman sakin murmushi yayi, oumma kisa baki mana  dariya oumma ta saka tana mikewa  kunfi kusa Nidea ba ruwana , hajiya a huta lapiya  , itama hajiya murmushi ta sakar mata  ala huta gajiya maryama,nagode  , kafun oumma ta fita daga parlourn.

Tana fitowa ta tarar da dady da zarah,jakar da ya ajje ya dauka kafin tayi masa Sannu da zuwa , zarah na ganin oumma ta nufi part din hajiya itama , kallanta dady yayi,  Amarsu wannan kyau haka kamar yau ce aka shafa lapiya , kullum sai wani kara kyau kike kamar ba yarinya ba, kunya kalaman dady suka bata , bata san lokacin da ta dara ba kafun tayi wuce warta part Dinsu, shima bin bayan nata yayi lokacin har ta hada masa ruwa tana kokarin fitowa  Ah ah me kike nufi , yau fa amaryace zatayi mun wanka gaskiya inasan jin dumin matata nifa ba gwauro bane  Innalillahi oumma ta fara nanatawa aranta , yau taga abunda ya fi karfinta, dady kuwa ko ajikinsa yazo zai rike oumma kuwa tayi saurin Zillewa sai da taje bakin kofa kafun ta sakar masa wani murmushi da ya kusa kifar dashi  kiyi wanka , bari naje na hada maka lunch dinka  bata bari ya kuma cewa komai ba tayi ficewarta, dariyar dattako Alhaji kabeer yayi  maryam badai kunya ba  , yana gama maganar zucin sa ya shige bandaki.

FLASH BACK

Abunda ya faru, tun lokacin da dady da su zarah suka nema alfarmar oumma ta zauna , gabaki d aya tundaga lokacin wani irin shakuwa ce ta ban mamaki ta shiga tsakanin ta dasu zarah , duk da a yawancin lokuta gaisuwace take hada ta da dady, sati daya da faruwar haka dady ya yanko musu ticker zuwa abuja , inda yake rayuwa da mamansa, koda hajiya fatima taji labarin maryam itama sosai oumma tashiga ranta musamman yanda taga su zarah na kaunarta har hakan ya so bata mamaki.itama oumma gabaki d aya ta fawwala lawa Allah lamuranta, a kullum ba ta gajiya wajan yiwa ya yanta addua, har yanxu bata fidda Saran watarana zata gansu ba. Kwasam wata ranar litinin dady ya bijurowa hajiya cewar yanasan ya auri maryam sai su cigaba da kula dasu zarah kafun aga tahee da ya bata duk da haryanxu ana kan dubosa,itama hajiya sosai taji dadin maganar dakanta ta kira oumma akan auranta da dady yakeso yayi, rasa abun cewa oumma tayi ganin yanda dady yake satar kallanta yana jiran amsarta, a gefe guda ma hajiya na Rokan Allah kar maryam tace ah ah , wata iriyar kunyace ta kama oumma ganin yanda suke binta da kallo, a hankali ta furta  Allah ya tabbatar da Alkairi , ba hajiya ba hatta dady saida ya saki ajiyar zuciya, bakaramun dadi hajiya tajiba harda dan kukanta Aushe da raban zata kara ganin auren kabeerunta. A bangaran oumma kuwa har kuka sai da tayi ranar ganin yanda zarah da Khaleed suka nuna farincikinsu.wata iriyar soyayya dady yake nunawa oumma ko kunyar su Khaleed da hajiya bayayi, tun tana jin nauyin yadda yake nuna mata soyayya har ta soma bashi martani, sati biyu da hajiya taga abun nasa na musamman ne tasa aka daura musu aure da oumma .

BACK TO STORY

A dinning oumma tayi serving Dinsu abinci gabaki dayan su, ko wanne da annashuwa a kan fuskarsa, yy khaleed har yanxu baka bani tsarabar bafa sai jamun rai kake , kallanta yayi kafin ya kai wainar masa bakinsa, saida ya tabbatar ya cinye kafun ya soma magana ,  Na fasa , kin bi kin adda Beni kamar kin aikeni , kamar zatayi kuka ta furta  shikenan  ta mike da niyar tafiya, daga dady har oumma babu Wanda ya tanka musu, saida yagama cin abincin sa tsaf kafun ya zuba wani a plate , kallanshi oumma tayi alamun karin bayani zan kaiwa autane, in tayi fushi dani ai babu zaman lapiya , yanxu sai tasa dady ya koreni ,gabaki d aya dariya suka saki jin kalaman sa , yana barin wajan shima dady ya kalli oumma ,  yanxu saura aikin lada , kin bawa kowa abinci a baki ban dani , da Sauri oumma ta mike , dady yayi saurin rike hannunta , waigawa oumma tayi gudun kar wani ya gansu  dan Allah kasakar mun hannuna kar wani yashigo , shikenan zauna ki baki a baki , ba musu kuwa oumma ta fara bashi, befi spoon biyar ba ta gudu falourn hajiya .

( Soyayya bata tsufa, dady ka bani kunya =??=??).


>???>???>???>???>???>???>???>???>???
>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???>???

A tsaye ya tarar da ita tana gyara dakinsa , da Sauri ya karasa ya karbi towel dinta  banaso ki bari sakin baki tayi tana kallansa yau taga ikon Allah  ka bani gyara fa nake  a maimakon ya bata kamata yayi ya zaunar da ita kafun ya taba cikinta,  karna kara gani kinyi wani aikin , okay  lapiya ta fa kalau, shima amsa ya bata  eh na sani ai , common me zakici bata dade da Shan complex ba  na koshi me kika ci!? , itama amsa ta bashi da complex, girgiza mata kai yayi  it s not a food, zo muje kici wani abincin , zanyi amai idan naci kabari anjima kaji, be kuma ce mata komai ba sai cikinta da yake shafawa a hankali har yanxu jinsa yake kamar a mafarki, itama lafewa tayi a jikinsa sabida yanda take jin dadin yanda yake shafa mata cikin.

Yinin ranar gabaki d aya tare da tahee yayi shi, hatta abinci da kansa yake bata,ita kuma sai faman narke masa take. Da daddare ma lokacin da zasu kwanta sai faman shagwaba take masa hakan da take kuwa ba karamun zautar dashi yake ba musamman breast dinta da suka cika masa ido ga wani girma da yaga sun karayi masa, be san lokacin da ya fincike rigar jikinta ba ta ynda zai ga breast din da kyau. Ga baki d aya ta birki ta masa tunanin, hatta lokacin da zai kusanceta jiyayi ta canza masa, kara susucewa king yayi gudun karya ji mata ciwo ne yasa yake binta a hankali sai faman surutai yake yi.
GIDAN AUNTY

MSS LEE
07041879581


BOOK 1

Page 65_66=ؖ?

Yau ya kama Monday, Tahee tana idar da Sallah ta d an yi gyara gyare kafun king ya dawo, Tana kammalawa tashiga wanka ganin lokaci na tafiya, sosai tayi shirinta na zuwa makaranta Bayan uban Noddles din dataci duk da haka saidata dauki wasu chocolate da yawa a jakarta, kallan lokaci tayi yau ta kusa makara gashi be dawo ba.Mikewa tayi ta nufi dakinta wani wafer ta dakko guda biyu da chewing gum shima,tana sakko wa kasa shikuma yana shigowa falourn, Tsayawa kallanta yayi from head to toe kafun ya tanbayeta inda zata je da shigar uniform haka, sakin baki tahee tayi tana kallansa  kaman ta yau Monday? , girgiza mata kai yayi alamun ah ah , Lokacin school fa yayi har na fara latti ,dauke kansa yayi kafun ya furta  Babu inda zakije , you re not feeling fine  da Sauri ta karaso gabanta har yana saurin rikota  Muna da text fa yau honey, please nifa lafiya ta kalau babu abunda yake damuna  ta karasa zancanta cikin narai narai da ido, kallanta yayi kafun ya sakar mata peck a goshi  you won t go anyway banaso ki wahalar mun da Baby na , ji tayi kamar ta saka ihu, tun ba aje ko ina ba ya fara fifita Babynsa akanta, Bata kuma kallansa ba ta juya zata tafi, Ina zaki , shiru tayi masa kafun a hankali ta furta  zan cire kayana , jakar hannunta ce ta fadi duk chocolate dinta suka fado kasa, kallan uban chocolate d in ta dake cikin jakar yayi, wani hau shin ne ya kara kamata cikin Sauri ta fara kwashe ku ko kallan inda yake bata yi, da mamaki yake kallan yanda mood dinta ya canza , yazo zai yi mata magana tayi saurin hawa steps din dakinta. Oh God  king ya furta kafun ya nufi dakinta,akan gado yasameta tayi rubdaciki da Sauri ya karasa Wajan ta  What s wrong with you my Baby , ya fada yana dago da ita, kwace jikinta tayi wani saban hawaye na kara zuwar mata zata kara komawa ya rikota a rikice  No please! Meke damun ki ? , Cikin kine ?,Baby nane? Duk shi kadai ya kara jefo mata tanbayoyin, wani karin ba kin ciki ne ya kara kamata wato shi ta Babyn sa yake bata ita ba,cikin dan karfi karfi ta kara fusge hannunta zata koma kwance ya kara rikota , gabaki d aya ya birkice ganin yaki sakin tane yasa ta saka masa wani saban kukan, runtse idanuwansa king yayi da tasan yanda yake jin kukanta a cikin zuciyar sa da bata soma ba , ji yake kamar ana Caka masa wutar karfe a cikin zuciyarsa, ganin ta ki dena kukan ne yasa yayi hugging dinta stop crying ,nayi lefi ko to am sorry , a  kulle ta furta  Ni babu wani sorry! Yanxu ka dena sano komai Baby Baby Baby, Babynka kake so bani ba , Sabida Babyn ka hanani zuwa nayi text dina ni babu ruwana da kai  , ta karasa zata fashe masa da wani saban kukan , murmushi ne ya su buce masa kafun a hankali ya d ago face dinta yana share mata hawaye , taki kallansa sai faman kunbure kunbure take  Shikenan nayi laifi! Am sorry! A dena wannan kukan , and kidena kishi da Babyn mu, ke kadai ce Baby na , shi kadan zamu san mushi kinji , ka fada ta d age masa alamun bata hakura ba, kunnensa biyu ya kama  ohk tell me , me kikeso ! I promise zanyi but ki share wannan hawayen kafun na shanye kayana , saurin goge hawayen tayi  Muna da test a school  ta karasa a marairaice, shiyasaki kuka? ,Bakinta Tadan turo masa  ok jeki gyara face d inki da Sauri ta run kura zata tashi ya riketa  please be careful  , kanta kawai ta daga masa , cikin kankanin lokaci ta gyara face dinta , ki kula please cikin ki be yi kwari ba and banasan kisha sweet da yawa , and your lunch kici on time , take care of your self , a bazata yaji saukar kiss akan Le b bensa, You re my hero ! I always cherish you  , ganin tana letti ne Yasa shi yin shiru yaga alama yau rigima take ji amma shi kadai yasan ya yake ji, yace zai yi driving dinta ta lallashi ya hakura ganin yana aiki tun dazu shima  , da kyar ta samu ya hakura shima still sai da ya kara mata motar sojoji guda daya , duk da ta hana su shiga cikin makarantar iya bakin kofa suke tsayawa , motar da take cike kawai suke shiga da ita,Mss Stella na gaba ita da driver, Allah ya temaketa tana shiga Teacher din da zai sauke su Civic education ya shigo, kafun ya fito wani Malamin ya shigo shima, a period na ukune suka test dinsu na Biology, saida aka fita break ne Husna ta kalleta  yau basa ban ba kinyi letti , ai na dauka bazaki zo ba  , murmushi Tahee ta sakar mata  Wallahi ba haka bane Husna ,Dan abune ya sha mun kai shiyasa  , itama murmushin Husna ta sakar mata  Daman ke ai kullum ina da amsar maganar mutum, Ni kinga yanxu i m hungry ! Let s go and it some food kafin lokacin dawowa yayi  , gyada mata kai Tahee tayi kafun su fito daga class din , yawanci student basa compound, daddai kune zaki gansu a waje, da sauri stella ta fito daga mota zata nifo su, Tahee tayi saurin dakatar da ita batare da ta bari husna ta luraba, suna shiga cikin cafeteria aka kara binsu da kallo musamman Tahee dake sanye da facemask, Daga gefen su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login