Showing 15001 words to 18000 words out of 81012 words

Chapter 6 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

183

nauyi kaman zai haukace shima yakeji ya fasa kukan da babu me jinsa bayan Allah dayake fatan ya kawo masa dauki da sassauci a wannan rayuwar.

Tsakar dare sosai ya dago jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumbura ya kalli ummita datake a sake jikinsa ya miqe ya koma gefen da babu sanyi a adakin ya gyara gurin kwanciyarsu ya kakkabe duk da baya ganin komai ya sauya mata kaya sbd na jikinta akwai sanyi ya kwamtar da ita.
#MAMUH
#BESTSTORY
#BESTLOVE
#BROTHERS LOVE
#LIMBAS
#ZADEENS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
9
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


********
Tashi yayi ya fito cikin duhun ya sauya kayansa yaje toilet ya fito yayi alwala ya dawo dakin
A gefen ummita yayi sallah yafara sabon kuka yana fadawa Allah ummansa kadai yake fatan Allah yabata kyakkyan kariya tareda fatan dawowa garesa.

Har akai asuba yana fadawa Allah ummansa tareda neman jariya da yadda da duk kaddarar da zata tinkarosa a rayuwa ya basa ikon inganta rayuwar Ummitah har mutuwarsa.

A gida yayi sallar asuba bai fita ba kaman yanda yakeyi a baya,

Yana gamawa ruwan zafi yai dubara ya dora yazo ya gasa ummita dasu sosai ya mayar mata da kayanta ya fita yaje ya samo mata koko da kosai ya dawo ya bata kaman ma dura mata yayi.

Bai gama bata ba tayo masa amansa a jikinsa ya tashi yaje ya gyara mata jikinta ya sakeyi wanka shima ya sauya kaya ya sake bata kokon amma wannan karan batai masa amansa ba dan haka ya kwantar da ita tayi bacci har lokacin jikinta akwai zazzabi.

Basuda wasu kayan dan haka ya wanke musu wainda duka lalace sbd kada su fita dana jikinsu su dawo babu wasu na sakawar dan haka yana gama shanyawa ya dauketa suka fice.

Local government ya nufa acan yakaita wani chemist aka dubata akai mata allura aka basu magani ya siya mata bread sa freshYo na roba shikenan kudin hannunsa suka qare suka zagaya sosai nan ma ya bincika ummansa amma ba labari sai yamma sosai suka dawo gida.

Kwantar da ita yayi ya gyare gidan fes kafin yayi sallan magrib suka shige dakinsu ya rufe.

Yana yin sallan ishai kadan yaci bread din data rage da ruwa ya kwanta gefenta tareda rufesu sai a lokacin wani baccin azaba shima ya daukesa.

Seda aka fito sallah ya farka yayi sallah yayita addua har gari ya waye sosai ya fito baida ko sisin siya mata abinci dan haka ruwan wanka kawai ya samar musu sukai wanka ya dauketa suka fice zuwa gurin aikinsa.

Koda ya isa sbd rashin zuwansa kwana biyu tini aka saka wani a maimakonsa dan haka sedai ya tayasu suka dan hada masa dan abinda ya samu ya siyawa Ummitan Wainar gero taci yabata magani daganan ya nufi shagon dayake aiki a baya ko zai samu a karbesa suma.

Yama xuwa shima ya riga ya samu wani amma dai yace ya tsaya ko miqa abu ne idan an siya ya taya wanda yake shagon yanzu a dan ringa basa wani abin.

Haka ya zauna a bakin shagon da ummita wadda take lafe jikinsa har dare suka kai kafin ya basa 200 ya dawo gida.

Suna dawowa tuwo ya siya mata da 200 din taci kadan tasha magani ya cinye sauran yasha ruwa yai sallah ya kwanta.

Washe gari ma haka ya tafi ya ringa yawo garari da ummita yana dan kama aiki ana basa abinda zai siya mata abinda zataci saita rage yaci wani lokacin kuma ruwa kawai yakesha ya dawo su kwanta.


****rayuwa tai masa tsananin gaske dan kuwa daga shi sai ummita suke rayuwa yayi yawon neman umma har inda bai kamata suje ba sunje ba labari dan haka ya maida hankali sosai gurin tattalin Ummita wadda ita kadaice hope dinsa na rayuwa a yanxu,sbd ita ya dage yafara gwagwarmaya da rayuwa,

Tin dafe idan suka fita da ita yake yawon aikin wahalar dayake fama dashi se dare suke dawowa su shige su rufe gari na wayewa suke fita sai kuka wani dare.

Wahalar rayuwa yakesha sosai ga kulawa da ummita wadda ya kasa barwa ko mama sakina sbd tsoron bazai iya rayuwa ba ummitan a tareda shi ba dan haka yake gwagwarmayarsa da ita a gefensa duk da tafara qara wayo sosai kuma itama bata iya rabuwa dashi ko nan da can dan hakama sbd bata tsaro da kariya ya aske mata kanta daman batada yan kunne ya siya mata kayan gwanjo na maza ya maidata namiji sunanta kuwa kwata kwata baya fada cikin mutane kaman yanda ya hanata magana a cikin mutane sbd muryanta.


Ana cikin ya fara examsa dinsa dan haka tare suke zuwa makaranta ya zaunar da ita bakin window dayake ganinta har a gama ya fito ya jata su tafiyarsu gurin yawon nema.

Rayuwa tayi musu nauyin da duk kansa yafara neman kuncewa amma ya riqe sbd Ummitah dayayiwa kansa alkawarin inganta rayuwarta bazai bari insha Allah ta taso cikin qunci da azabar daya taso a cikinta ba,
Shine uwa kuma ubanta dan haka ko rayuwarsa zai iya siyarwa dan inganta tata.

***Ummita a tata rayuwar batada wani hasken data sani bayan BAABAH dinta wanda shi kadai ya isheta rayuwa, ya isheta jin nutsuwa da ganin haske arayuwar ba duhu ba,
Shine uwa kuma ubanta wanda take ganin indai gashi bata buqatan komai hakama shi kadai ne abinda take buqata a rayuwarta.


Daqyar ya kammala exams dinsa sbd babu lokacin zuwa aiki dan haka abincin dazai bawa ummita bama kansa ba yake musu wuya dan haka koda aka gama exams din yayi wani irin ra??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ma daga shi har ummitan sun bushe dan haka yana gamawa ya duqufa aikin kamfanin daya sake samu da tsaron shago yana hadawa biyu sai suka fara daidaituwa.

Ahankali abinci yafara wadatarsu kullum sunaci su koshi ya siya mata abubuwan buqata da nasa ma.

Ya siya musu katuwar fitila basa cikin duhu ko kadan yanxu,
Ya siyawa kansa waya yar qarama sbd jamb daya rubuta da kuma jiran kiran fitowar jarabarsu.

Rayuwarsu tafara daidaituwa shine malamin Ummita na karatun addini harma dana bokon dan haka tafara koyan karatu a gunsa kuma tana ganewa sbd yanada qwaqwalwa sosai dan duk tsananin rayuwar da suke ya tsaya ya samarwa kansa ilimi sbd burin dayake dashi akanta.

Mama sakina na cikin tsanani a gidan aurenta sbd baba ila daya tsaneta gaba daya tinda ta kasa cire su abdul a ranta duk ta rame ta qare akan tinaninsu da rayuwar da suke wadda bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kwata kwata sbd Abdul rayuwarsa ta qare ne akan kulawa da ummita hakama bazai tabbata boyeta a amtsayin namiji na sbd girmanta idan yazo zai nuna hakama tayaya zaici gaba da iya kulawa da ita shi kadai dan haka take cikin damuwa me tsananin gaske da kuma batan Fatima daya tabata itama ta rasa kwanciyar hankali kwata kwata.

Baba ila gaba daya ficewa tai a ransa sbd babu dadin zama da ita tinda ta saka ranta a qunci sbd yayan da ba ita ta haifa ba,uwarsu ta tsallakesu ta gudu sai itace zata kawo masa qunci gidansa sbd su duk tabi ta bushe babu komai a jikinta hatta gatanta jin yayi ya bushe masa dan haka ta fice masa kwata kwata a rai ko abincin ma seya dena bata azaba kawai take sha a gidan da baqin ciki tareda hantara da tsana da gori.

Abdul bai taba zuwa ko sake barin hanyama ta hadasa da yan uwan babansu ba sbd babu abinda yake buqatan dayafi kada Allah ya hadasa dasu harsu bar kauye dan haka kwata kwata baya hulda da mutane ko shiga mutane sosai kaman iyayensa ya killace kansa daga shi sai kanwarsa wadda itace tafi masa duk wani abu dayake duniyar nan.

A gurin aikinsa ahankali yafara zamowa abin kaunar kowa sbd nutsuwa da kamun kansa da kuma maida hankali kawai akan aikin daya kawosa.

Tamkar yanda mahaifinsa yake da farin jini da kwarjini haka yafara cika idanuwan mutane duk da shine qaraminsu a kaf ma'aikatan gurin hakama sbd rufin asiri daya fara samu da cimar safe rana dare sai yafara zamowa lafiyayyan saurayinsa wanda haskensa na bafulatin asali suka fara fitowa sosai.


****examsa dinsu ce ta fito wadda tayi kyau sosai kusan fiyeda ta kowa a makarantarsu dan haka yake cikin farin ciki.

Rayuwarsa ta qara zamowa akan tsari ne a lokacinda ya samu admission dinsa a university of lagos wadda acan ya cika sbd yanason koyan gwagwarmayan nema,

A daidai wannan lokacin ne baba Ahmed ya kawo musu ziyara sbd rasuwar da me gidansu yayi dan yazo ya tafi dasu da takardar da akai ta kudinsu da zai basu zuwa abuja.

Sam Abdul bai nuna ummita mace bace a haka suka tafi har abuja bayan tafiya me tsayi suna isa aka saukar dasu gidan wani dan uwan baba Ahmed wanda yake gadin wani gida da babu kowa a cikinsa.

Sai washe gari suka isa gidan alh kabeer inda babu wahala bayan sunyi gaisuwa daman ansan da zuwansu babban dan Alhajin ne ya nema Baba Ahmed sbd takardar da dad dinsa ya basa a hannunsa tasu Abdul din dan haka ba wani wahala aka basu dukiya me yawan gaske.

Kafin su tafi kwanansu shida a abuja Alhaji Sa'ad 'dan Alhaji kabir din yaji kaunar Abdul kaman yanda dad dinsa yaji yana kaunar Ayouba a can bayan dan haka bae bari sun tafi ba yai masa tambayoyi yaji yana shaawar sakasa a business dinsu sbd Alhaji Kabir ya rasu bayan doguwar jinya wadda sanadin businesses dinsu ne da sukai qasa sun karye sosai dan haka ciwon zuciya ne da Diabetes ya kwantar da Alhaji wanda sukaita yawon kasashe sauran dukiyar duk ta qare daga qarshe koda ya rasu basuda wani abin daya dage musu bayan gidan da suke ciki a yanzu.

Amma sbd sauke nauyi da biyan haqqi ya sakasu saida duka motocin gidan suka hada kudin da dad dinsu yayi alkawarin bawa su Abdul wanda yake ganin haqqinsu ne dole ya basu suka nemesu dan basu,

Amma ganin nutsuwar Abdul din wanda idan suka basa duka kudin zasu koma ko abinda zasu juya basuda shi gashi shima Saad shi kadaine namiji a gidan sauran kannensa duka mata ne sai mahaifiyarsu dan haka ya gabatarwa Abdul kalar business dinsu na companies din shigowa da manyan qarafunan manyan motoci daga kasar waje da kuma kamfanin Qera nasu da suke dashi tareda bayyana masa komai na business da kuma yanda ake tafiyar da huldodin duka a gaban baba Ahmed da lawyer dinsu.

Abdul daman bai saka kudin a ransa ba bare saka lissafinsu a ransa dan haka yace ya bar musu amma a saka baba Ahmed a cikin huldan ya basa kaso daya a bisa uku na dukiyar shima ayi dashi.

Gabaki daya familyn gidan jin farin ciki da tsananin kaunar ABDULAZIZ sukai musamman Alhaji Saad dayaji ABDULAZIZ ya zama kaman wani savior dinsu.

Baba Ahmed ma jin yayi yana zubarda hawayen farin ciki sbd yana cikin gararin rashin aikin yi shima sai wahalar rayuwa yake sha shiyasa kunyar su Abdul din ta hana ya fito ya taimakawa rayuwarsu.
#MAMUH
#LIMBAS
#ZADEENS
#BESTLOVE

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
10
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci? cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA? NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


*******
Lawyer ne a gaban kowa yayi drafting komai da yawan adadin kudin da date da cikakken sunansa ABDULAZIZ AYOUB LIMBA sai sunan Saad din da baba Ahmed kowa ya saka hannu.

Anan aka saukesu suka baro gidan dan uwan baba Ahmed akai musu Kyakkyawan sauka wanda anan gidan ne aka gane Ummita mace ce dan haka umman gidan taiwa ABDULAZIZ din karfin halin rabasa da Ummitah ta dawo da ita cikin gida gurinsu.

Sosai suka ringa kulawa da Ummitah da tattalinta babu qyama tareda siya mata yan kayan sakawa aka gyara mata hujin kunnanta da harya rufe.

Satinsu hudu a abuja suka tattara suka dawo duk yanda Saad yaso ABDULAZIZ ya zauna anan abuja cewa yayi aa sbd makaranta da zai tafi bazai iya barin ummita anan dinba ya tafi karatu yabarta a gurin wainda bai saniba.

Bayan tafiyarsu suna dawowa gida da kwana biyu yaje ya sanarwa mama sakina karatu zai tafi.

Tashi hankalinta yayi mummunan yi sbd batasan tayaya ABDULAZIZ din zaiyi tinanin tafiya da Ummitah karatu ba har nesa dan ita batama san lagos din ba a baki suke jinta.

Shi kansa ABDULAZIZ din yana cikin tsananin damuwa da tashin hankalin yanda zaiyi sbd shi kansa bazai iya zuwa da ita inda yasan ba tsaro ba gwagwarmaya me kalubalen gaske.

Damuwar hakan ce ta sakosa gaba ya koma kalar tausayi damuwa me karfin gaske ta shigesa,
Daga karshe yafara tinanin fasa tafiya karatun sbd Ummitah sbd ta fi masa karatun zai zauna ya reneta.

Wannan shawaran daya yanke ta fasa karatun ya hakura dashi ya saka mama sakina shiga damuwa me tsananin data sake dagula dan zaman datake a gidan baba ila tsangwamar dayake mata tai yawan data saka ciwo kwantar da ita sedai ta kasa samun Sassaucin damuwar datake ciki na fasa karatun ABDULAZIZ din dan haka dataga babu sauyi ABDULAZIZ din ya hakura da karatunsa harya fara aikinsa kwana tayi tana kukan data kasa riqewa tana tina fatima da gatan da aka haifi a Abdul din a cikinsa har safe tana kukan daya sakata qarasa ficewa hayyacinta karshe ta hakura ta sadaukar da aurenta tayiwa baba ila maganar zata karbo Ummitah ta dawo da ita hannunta ABDULAZIZ zai tafi karatu.

Sadaukarwar datai da shahadar masa magana tasan ta tashin hankalin da zata fuskantace tareda Ummitan a gidan dan ko abincin da zasuci ta sani sedai ta fara nemar musu shi da kuma kaurace mata da kila baba ilan zaiyi gaba daya daman ya dade da kaurace mata kumata shirya hakan dan haka tai sadaukarwartai masa magana sedai babban abinda bata zata ba shine kai tsaye tana kai karshen zancenta yace ya saketa saki uku ta tafi can gaba tayi riqon Ummitan.

Dagowa tayi da jajayen idanuwanta na kukan data kwana yi ta zuba masa tsawon mintina tana kallansa harya wuce daga kofar dakinta ya fice daga gidan.

Wasu hawaye ne masu tsananin zafi da ciwo suka gangaro mata ta rintse idanuwanta tana kasa dagowa saiga wani irin kuka me ciwo ya kufce mata zube a gurin tanayinsa ba sauti.

Ta jima a gurin kafin ta miqe ta shiga dakinta ta tattaro yan kayanta da duka buhu daya ne zai dauke mata su sbd ko katifa batada ta siyar tin gurin taimakawa su fatima dan haka tabarmace kawai tsohuwa sai sanin shimfida daya da kayan sawarta da basu fi kala uku ba sai kwanonin da tini suka mutu tin na aurenta shekaru kusan ashirin harma da dori dan haka tana hada kayanta a buhu ta fito taje kuryan gidan tayiwa yan gidan bankwana ta fito suna gulmanta ta fice.

Kai tsaye gidansu ABDULAZIZ din ta nufa.

Basa nan dan haka tinda gidan ba kofane dashi ba ta shiga ta ajiye kayanta ta nemi guri ta zauna.

Sai yamma sosai suka dawo Ummitah na ganinta tazo gurinta da gudu ta rungumeta tana cewa

"Maama"

ABDULAZIZ kayanta ya kalla ya kalli fuskanta take ya fahimci abinda yake faruwa dan haka baice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login