Showing 42001 words to 45000 words out of 81012 words

Chapter 15 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

192

son Mahaifinsu na mamaye zuciyarta
kuka mara sauti ya taso mata ta silale a gurin tanayi tana jin tausayin Hammanta wanda ya rasa uwa da uba dan ita kam shine uwa da ubanta.

Sayyid ne ya shigo dakin gabaki daya gidan a sanyaye kowa yake ba walwala sbd Ummitah gaba daya ta sauy kwana biyun bata cikin walwala musamman da tafiyar Hamman gobe ce sai gaba daya yau ta rikice bata jin dadin komai hakama suma duk sun shiga damuwa.

Ko kadan a daren Ummitah bata rintsa ba hakama ABDULAZIZ din kwana yayi yana mata adduar Allah ya saukar da ita lafiya.

Da asuba koda ya dawo sallah wanka kawai yayi ya shirya ya fito dan 7 jirginsa zai tashi,

Sanye da Black UGG knit top da Straight jeans ya fito sai fcap ta balenciaga yana qamshi me sanyi ya fito Sayyid tini yakai kayansa mota ya dawo.

Fuskansa tayi wani irin fresh yayi fayau sbd rashin rintsawar da baiyiba da damuwar datake cin ransa dayake ganin tafiyar da zaiyi ne yabar Ummitah a wannan halin.

Cikin dauriya da danne damuwar ta harma da ciwon datakeji ta fito itama fuskanta tayi fayau ta qarasa har gabansa ta miqa masa hannu tana sakin murmushi me kyau dan kwantar masa da hankali.

Ajiyar zuciya a fili ya sake ahankali yana mata kallan tsafta ya miqa hannu ya kama hannunta data basa sukai musabaha ta sauke ajiyar zuciya tana sake qanqame hannunsa cikin nata tace

"ALLAH ya baka nasara akan abinda zakaje ya baka nasara a duk abinda zaka nema a duniya ya kuma dafa maka ya hanaka damuwa kowace iri ce...

Shiru ta dan yi kafin tace

"Allah kuma ya dawo da kai lafiya Hammah"

"Amin ya furta ahankali yana kallan cikin idanuwanta da ita shi take kalla tana murmushi me kyau da nutsuwa.

Mama ya kalla da sayyid yace

"Idan akwai abinda ya taso a kula sosai a tafi asibiti akirani,a kula"

Addua mama tai masa itama tana masa fatan dawowa lfy.

Hoton daya bata jiyan Ummitah ta fidda?? a cikin dayan hannunta ta saka masa shima a hannunsa tana cewa

"Nagode Hammah"

Murmushin karfin hali shima yayi mata yana shafa fuskanta ya matso kaman yanda ya saba ya karanta mata adduar dayake mata tin tana yarinya ta neman tsarin ubangijin a kunnenta ya share mata hawayen da suka gangaro mata tana murmushi ya juya ya shige mota yana daga musu hannu.

Sayyid ne ya shiga motar sbd tareda shi zasu Airport din da drivern gidan Alh Saad.

Motarsu na barin gidan gidan ta sauke ajiyan zuciya me karfi tana jin wani abu kamar yabar jikinta dan haka mama ta jata suka koma cikin gida.

Koda Sayyid ya dawo daga Airport bai dameta ba kyaleta kowa yayi sbd ta samu ta warware da kanta sedai hakan bai yiyiba dan kuwa zazzabi me qarfine ya kamata wanda ya sakasu damuwa.

Haka suka wuni da ita har dare batajin dadi sedai tace ba buqatan zuwa asibitin dan haka sai baa takurataba.

Washe gari ma haka ta wuni cikin yanayi na rashin lafiyar datake cinta a hankali,

Fama su mama suka fara da ita sbd gabaki daya lafiyar tana neman gagaranta sbd wani irin silent ciwo take fama dashi wanda ta rasa menene yake damunta itama hakama da kanta ta hana a sanar da Hamman sbd kada ya shiga damuwa tace zata iya daurewa har lokacin haihuwanta ya qara yi tinda ta kusa.


******ciwon kwana daya kwana biyu zai qara gaba yakeyi cikin tsananin azabar da bata taba saniba take a yanzu hakama batasan me zatace yana damunta ba ga damuwar datake damun zuciyarta da kwata kwata bata mata dadi,

Wata irin rama me muni ta fara da wani irin haske dayake bawa mama da sayyid tsoro sosai hankalinsu ya tashi sosai kuma har lokacin sun kasa fadawa ABDULAZIZ din.

Zuwansu asibiti biyu dr yana dubat yana ce musu lafiyarta kalau kawai yanayi ne na haihuwan daya matso.

Dawowa sukai gida suna cigaba da kulawa da ita sedai tashin hankalinsu da tsoronsu tsananta yakeyi sbd qarewa takeyi kamar wadda mayu suka kama takai komai tafara gaza yiwa kanta jinya takeyi sosai wanda ya fara taba lafiyar cikinta.

Dole suka tattara suka sake komawa asibiti gashi anty maryam bata nan su kadai suketa Fama sai drivern da aka samar musu sbd fitarsu.


********Dzad ne a zaune a lafiyayyar office dinsa dayake cikim mansion dinsu ya zare farin glass dinsa yana kallan Ammar wanda Maheer ma shi yake kalla.

Numfashi Ammar din ya sauke cikin samun nutsuwar biyan buqatan shekara da shekaru yace

"Komai na matar da aka samu zuciyarta ya kammala magani ya gama aiki akanta wanda kowane time a wannan stage din datake shine daidai lokacin da zataiwa Jannah donor,
Anyi bincike akanta ba kowa bace daga kauye suka taho suna zama gidan wani relative dinsu ne wanda baima cika zamaba so bandai tsaya nasan sunansa ba kokuma buqatan hotonsa sbd ba buqatan hakan,

Abu daya ne shine lokaci yayi zuwa jibi zaayi aikin wanda muke fatan wannan shine na karshe sbd baa taba samun matching din da ake tinanin yayi 99% ba kuma gashi cikin ya riga yazo lokacin haihuwa so the right and perfect time has come"

Maheer jin yayi wani nauyi da sanyi na cike zuciyarsa lokaci daya

Dad ma jin yayi bayajin komai baya buqatan komai kawai ayi aikin su samu abinda suke so shine burinsu.

Nutsuwa da nauyin daya danne musu zuciya shekara da shekaru ne sukaji dukkaninsu yana fada musu.

Washe gari ranar da zaayi aikin Anny ce ta bawa Jannah maganin data yanke jiki aka kwasheta zuwa asibitin sbd suna buqatan ta kasance a asibitin koda zaa shigo da Fatima Abdulaziz Ayoub din
Wannan shine sunan dayake jikin katinta.

Ummitah kuwa a daren ranar gabaki daya jikinta ya rikice jini ne yake mata zuba ba kakkautawan daya saka a cikin daren mama da sayyid suka kwasheta zuwa asibiti hankali tashe.

Dr ken yana asibitin daman yana jiran zuwansu sbd yasan hakan zata faru,

Dayake ansan shine dr dinta kiransa akai da gaggawa

A rikice cikeda kulawa da tashin hankali yayi kanta yana kiran nurses.

Naquda ce ya tayar mata tareda mata allurar da zata hanata iya haihuwa da kanta dan haka hankalin nurses ya tashi gashi bleeding takeyi sosai gashi tayi wani irin ciwon data jima acikinsa ya bayyana sosai a jikinta.

A cikin daren ganin an kasa shawo kan matsalar take yayi mata transfer zuwa ZADEEN HEALTH CEN.

Su mama da sayyid tinda suka gwada kiran Hamman baa samesa ba sai suka maida hankali kan Jikin Ummitan da aka tabbatar musu ba sauki gashi private hospital ce babu mutane sosai sbd tsadarta da tsarinta.

Dr ken kallansu yayi cikin nuna damuwa da kokarinsa yace

"Haihuwace tazo mata gadan gadan gashi lokacin bai qarasa yiba sbd bata bude ba gashi kuma babyn ruwan dayake rayuwa a cikinsa cikin cikinnata ya tsiyaye dole Aiki zaa mata a cire babyn idan ba hakanba komai zai iya faruwa da ita har babyn dan haka aikin Gaggawa zaa shiga da ita a acikin daren nan anan likitocinmu duka basa nan Nayi muku transfer zuwa qwararriyar asibitin da muke da ita Kusa yanzu can zaa tafi da ita.

Babu abinda mama da sayyid ke nanatawa bayan sunan Allah cikin matsanancin tashin hankali dan haka basuda zabin daya wuce aminta da hakan.

Cikin ambulance da gaggawa akai Asibitin da ita koda suka isa tafara nisa dan haka Hannu kawai sayyid ya saka a takardun komai aka shige tiyata da ita suna kallonta kowannensu idanuwansa na cikowa da hawayen dake zana radadi a zukatansu har aka shige da ita aka rufo kofar wadda ta saka kirjin mama bugawa da wani irin ciwon daya sakata dafa bango tana silalewa qasa ta zauna har lokacin kirjinta na qara ciwo.

Sayyid kuwa sunkuyar da kansa yayi yanajin kaman kunnuwansa da kansa iska na musu yawa.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALB???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?IM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
23
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


*************
Wayar hannun sayyid da yayiwa wani irin riqon dayake gap da saka screen din lalacewa batareda ya saniba sbd damketa yayi zuciyarsa najin kamar zata baro kirjinsa sbd abinda yakeji,

Ummitah bayan mahaifinsa a duniya itace abinda yakeso fiyeda komai da kansa sbd baida mahaifiya shima ta rasu,
Ummitah itace wadda baya kaunar gani ko yanayinta kadai ya sauya dako ciwon kai bare damuwa ko wani babban abin,

Ayau gata a gabansu anshiga aiki da ita yankata zaayi a ciro abinda yake cikin amma basuda abin yi sbd Allah yin Allah ne da ikonsa.

Hawaye ne sika cika idanuwansa da sukai jajir amma sun kasa saukowa,

Wayarsa ya kurawa ido yana sake saka kiran Hamman a karo na babu adadi ayau din amma har lokacin bata shiga.

Cigaba yayi da kiransa idanuwansa ko gani basayi sosai hakama hankalinsa da zuciyarsa duk basa aiki daidai kawai hamman yakeson ji dan haka ya kasa dena kira kaman mara hankali hannuwansa har rawa sukeyi.

Mama kuwa kanta yana qasa soke cikin qafafunta tana jin kirjinta na tsananta nauyi dan haka ta daure cikin karfin hali tana tsananta adduarta akan ayi aikin lafiya su samu daga uwar har yar lfy.

Shiru tsit gurin ya dauka kwata kwata babu motsi ko hayaniyar mutane a bangaren da ake aikin wanda guri ne na musamman a asibitin ba kowa yake zuwa ba sbd bangaren masu asibitin ne da babu wanda aka taba kawowa gurin sai wanda zaa illata.

Yanda hannun sayyid ke rawa cikin tashin hankali da fita hayyaci ya kasa dena kiran Hamma kaman zararre ya saka wayar faduwa daga hannunsa ta fadi tana fashewa gurin yana kallo screen yafara wani kyaftawa yana rawa a fashe haryayi duhu gaba daya ya mutu.

Rintse idanuwansa yayi yana silalewa a gurin ya zauna a qasa shima duk da akwai kujera a gurin baya buqata.

Adduar mama ce datake yi cikin dagewa da rashin sanya sautinta yake fita ahankali batareda ta san da hakan ba,

Rintse idanuwansa yayi dake masa radadi yana adduar shima a zuciyarsa.

Babu wanda suka gani babu wanda ya fito ko yazo wucewa ya gansu zaman azabar jira kawai sike tsawon awanni ba labari.

Kiran asuba ake farawa tinda daman a tsakar daren suka iso asibitin,

Kiran farko da aka kwada yayi daidai da bude kofar dakin tiyatar wanda ya saka mama da sayyid din miqewa a tare suna zubawa kofar jajayen idanuwansu zuciyoyinsu na wani irin sanyin da basu iya taku ko daya ba.

Dr Abraham sanye da kayan tiyata da hula ne a gaba sai dr finn a bayansa da wata Nurse wadda ba kowa bace Anny ce wadda take sanyeda face mask fari da kayanta na Nurses.

Ammar ne ya fito karshe shima sanyeda facemask din na likitoci da wularsu ta tiyata akansa baiko kalli inda su maman da Sayyid sukeba ya wuce yana jin jiri da nauyi a kirjinsa na fata da tsoron dacewa a aikin da zasu shiga yanzu na jannah.

Anny ma bata tsaya kallan nasu ba tabi bayan Ammar suka bar gurin zuwa wata kofar dake gurin.

Wata Nurse ce ta sake fitowa dauketa baby nade a cikin farin showel me tsananin taushi da tsadar dasuka taho dashi aka karba tin acan asibitin dr ken.


Tinkarosu Nurse din tayi da babyn wadda take lafe idanuwanta a rufe.

Dr Abraham da dr fin sai wani likitan daya fito baqi ne bahaushe musulmi ma yana zare hular kansa ya wuto gaba yana kallansu suma akansa suka maida kallansu suna kallansu da imaninsu sbd ganin shine nasu tinda su dr Abraham turawa ne bama gane musu zasuyiba.

Nurse ya kalla tana miqawa Sayyid din baby ya miqa hannuwansa cikin wani irin farin ciki dayake saka jikinsa rawa yana kokarin karba Muryan dr ismail wadda take tafe da bayayyanarda radadi da alhinin kai tsaye ta sauka a kunnuwansa....


"Anyi nasarar cire mata abinda yake cikinta cikin koshin lafiya sedai ALLAH YA KARBI RAN UWAR bawa baya wuce lokacinsa ayi haku........

Sakin jaririyar hannunsa Sayyid yayi cikin mummunan shock din dabai masan yayi hakanba.

Nurse dince tayi saurin zubewa qasa ta tare babyn a hannuwanta cikin ihu.

Wani mugun busashiyar yawu mama take kokarin hadiyewa amma ya kasa wucewa yankar mata maqoshi tanaji yanayi kaman da wuqa dan haka ta kyafta idanuwanta da suka qanqance tana kallansu daya dayan daya kafin ta tsayar da idanuwanta akan dr ismail din da qyar ta tina bakinta zata bude ba hannuwanta datake budewa ba muryanta na yankewa tace

"Kace an sauka lafiya ko?
Ita Ummitan fa?

Numfashi me zafin gaske ya sauke yana kallan Sayyid da yayi mutuwar tsaye yana wani vibrating amma tambayar maman ta sakasa dago jajayen idanuwansa da suke neman fashewa ya kallesa yana son jin amsar tamyar maman dan shima abinda yakeson tambaya amma ya manta yaya ake bude baki ayi magana gaba daya..

Sunkuyar da kai dr ismail din yayi yana kasa kallan idanuwansu da suka zuba masa ya bude baki yana tausasa harshensa yace

"Babu yanda zamu iya dukkaninmu akan hukuncin ubangiji,
Hakuri zamuyi dukkaninmu,
AN RIGA AN RASATA,TA RASU ABINDA TA HAIFA KAWAI AKA SAMU....."


Mama bakinsa take kalla kalaman na fitowa daga bakinsa kafin ta juya ta zubawa kofar dakin idanuwanta kafin ta sake wani yunqurin wani bugu kirjinta yayi so daya ta yanke jiki a gurin ta zube idanuwanta na juyewa gabaki daya.

Sayyid kuwa baya yayi kafafunsa na kasa daukansa ya durqushe a gurin yana fasa wani irin irin ihun daya saka gabaki daya rabin asibin daukan qarar kafin ya fasa wani irin kukan daya saka su dr Abraham yin baya cikin firgita sbd kukane daya zo masa kansa na zarewa gabaki daya yana wata irin jijjigar data saka dr Ismail kasa riqe abinda yakeji ya rungumesa yana jin idanuwansa shima cikowa da hawaye sbd radadin abinda sukai dayake ji a zuciyarsa wanda yayi a bisa rashin zabin dayake dashi.

Riqe sayyid din yayi a cikin jikinsa sbd irin jijjigar dayake zata iya sakasa samun collapse wanda zai iya qin tashi idan hakan ta samesa.

Jijjiga me karfin gaske yakeyi yana wani irin kuka me gunjin daya saka nurses dake kusa tahowa sun kallansa cikeda wani irin tausayi me cikeda tsoro sbd ganin namiji kamarsa yana irin wannan kukan me tada hankali.

Mama kuwa dr Ken ne yace nurses suyi saurin daukanta akaita emergency sbd ita kam kamar raima ya fita a jikinta.

Sayyid ma rikicewa yanayinsa yayi dole cikin tsananin gaggawa dr ismail yasa akai emergency dashi sbd wani irin kumfane ma yake fita bakinsa kaman yana kokarin samun wata matsalar ne suna buqatan gaggawar dawo dashi daidai.

Nurse Latifat aka bari da babynsu a hannunta tana yawo da ita sbd tashin hankali da firgicin ganin su dukan suna neman mutuwa a asibitin tasu.

Dr Abraham da dr finn kuwa Bayansu Dr Ammar suka bi sbd shiga tiyatar Jannah wadda Allah yayi sun samu abinda suke zo ba matsala fatarsu daya yanzu ana sakawa tayi saurin matching da vessels na jikinta batareda tasha wahalar kafin gama sabawa ko binding na komai daga zuciyar zuwa jikinta da jininta.


Duk yanda Su dr ismail da wasu likitocin suka shawo kan Sayyid kasawa sukai gashi sai muni jikinsa yakeyi dole sikai rendering nasa unconscious.

Mama kuwa kaman qaramar coma ta shiga sbd komai nata dena aiki yayi.

Tsit bangaren yayi babu mafitar komai har rana tai daga mama har sayyid babu wanda aka samu kansa bare asan yanda zaayi dasu ga baby ma tafara kuka sosai ga gawar Ummitah a ciki an rasa ya zaayi dasu.

A wannan halin ne Baba alhassan ya iso abuja sbd tin a jiyan Sayyid ya sanar dashi jikin Ummitan aiki zaa mata dan haka jinsu shiru ya iso.

Asibitin dr ken ya isa kai tsaye sbd acan ya taba zuwa dubo Ummitah wani zuwan da yayi kwanaki.

Acan ana kiran dr ken da kansa yaje ya dauko Baban ya kawo Asibitin nan sbd daman neman yan uwansu suke kai tsaye.

Ana kawo baba alhassan kallo daya yayiwa Sayyid yaji tasa zuciyar na neman bugawa sedai ya dauka zai iya riqewa da jarumta seda aka miqa masa baby aka sanar dashi Ummitah ta zama babu ya zube a gurin shima yana qanqame yar a jikinsa yana hada zufa me tsananin yawa da tashin hankalin dabai taba tsammanin samun kansa a ciki ba.

Dr ken da dr ismail ne sukaita kokarin basa hakuri da hanasa shiga wani mummunan halin kamansu Sayyid sbd kada arasa wanda zai karbesu.

Addua yayita yi yana hada zufa harya dawo hayyacinsa yana jan numfashi daqyar sbd take ciwon zuciya me qarfi ya kamasa amma ahakan ya daure yana danne azabar dayake ji a kirjinsa.

Mama da sayyid din kusan a lokaci daya suka farka,

Babu me karfin iya magana ko wani abu,

Idanuwa kadai suke bin baba alhassan dashi wanda yake kokarin hanasu ganin halinda yake ciki ya bude baki daqyar cikin karfin hali ya ringa musu nasiha da adduar data saka Sayyid zuba masa idanuwansa suna rinewa.

Mama kuwa haka suka lallaba bata iya tsayuwa da kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login