Showing 18001 words to 21000 words out of 81012 words

Chapter 7 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

181

komaiba sannu da zuwa yai mata yana fada mata abinda suka tsaya yi sukai yamma.

Ummita kallan Maman tayi tana cewa

"Mamah anan zaki kwana??

Murmushin karfin hali da boye damuwa mamah tayi tana cewa

"Eh yanzu na dawo dake zan ringa kwana kullum muna rayuwa sbd Baabanki ya tafi karatunsa,
Ai zaki yadda ya tafi ko??

Juyawa tayi ta kallesa yana alwala a natse kafin ta dawo da kallanta akan maman tace

"Eh zan yadda sbd BAABAH na son karatu ya fada a waya naji"

Ajiyar zuciya maman ta sauke sbd tasani idan Ummitah tace bata yaddaba to har abada yabar karatun.

Yana gama Alwala masallaci ya wuce sbd maman na tareda Ummitah.

Baa cika ganinsa masallaci ba sbd acan gurin aiki yake wuni dan haka a masallacin can suke sallah magriba kuma koda yake isowa gida anyi wani lokacin kuma jam'in waje yakebi sbd Ummitah sallar asuba kuma a gida yake binta sbd ba tsaro ya fita yabar Ummitah sbd akwai bata gari ko barayi.

Ayau ganinsa masallaci ya saka kawunninsa mamaki sedai ko alaman ganinsu baiyiba sbd bayama gane kamanninsu sbd rabonsa da ganinsu yama manta tin yana karaminsa.

Saida yayi ishai ya dawo gida sbd saida yayi karatun qur'ani.

Koda ya dawo maman ta dafa musu shinkafa da mai da yaji dan haka ya zauna a tsakar gidan sukaci suna gamawa yayi kwanciyarsa a kofar dakin da tabarman maman datazo da ita ya kunna maganin sauro guda biyu ya zagaye kansa dashi yabar musu dakin sbd gidan dakin daya ne tini ya rage sauran sun zube.

Washe gari gurin aiki ya tafi yabarsu gida ummita nata murna sbd mama zata zauna dasu.

Se dare ya dawo sbd baya tareda ummita daman sbd ita yake dawowa da wuri.

Tuwo ya samu anyi sbd yanada abinci a gidan sukaci suka koshi a daren ne sukai magana tace ya tafi karatunsa ita kuma zata koma gida gurin innarta da Ummitah sbd idan ma sun zauna anan zaaita tsangwamarsu ne hakama tinda an rena gidan ba kofa a bude yake idan bayanan zaaita musu sata ko wani abin ma dan haka zata koma can garin gashi a hade yake da local government.

Naam yayi da hakan shika tareda samun nutsuwa da zancenta dan haka ya amince sbd yasan kaunar da ummansu zataiwa Ummitah dama wadda batai mataba maman tanai mata dan haka zai tafi yayi karatu da nema dan inganta rayuwarsu su biyun da Ummitah da maman wadda a yanxi itama ta zama tasu nauyinta ya hau kansa kaman yanda na uwar data haifesa zai hau kansa.


Washe gari yafara shirin tafiya makaranta wanda ba wani shiri bane kudadensa dayake tarawane kawai da wanda ya bawa me gidansa na baya ya zuba a shago yaje ya karba ya dan yiwa su Ummitan siyayyar omo da sabulun wanki da mai se panties da vest da brush da macleans daya siya musu sai kuma abimci daya shiya musu me dan dama dama.

Kwana biyu suka gama shirin komai suka nufi garin mahaifiyarsa wanda shine garin mama sakinar.

A gidansu sakina koda suka iso baba ila tini ya kawo zancen tareda duka munanan illoli akan sakina wanda ya saka yam gidansu dayake gidan taro tsanarta tin kafin ta iso ita da 'yartata wanda kowa ya sani ba wanda ya isa ya rabata da ita tinda ansan irin yanda take da fatima dan haka ba wanda ma zaice zai rabata da jinin fatima sedai kuma kwata kwata basuyi maraba da dawowanta ba.

Innarta kuwa da tsufa ya kama sosai kusan batada karfin komai amma ita kam tayi maraba da 'yayan fatima sbd kaunar dake tsakanin fatima da sakina tasan daga Allah ne hakama Allah ne kadai yasan dalilinsa na hanawa sakina haihuwa yabar mata yayan fatima.

Koda suka iso kai tsaye bayan angama gaisawa da jamaa bangaren inna dayake dauke dauke da dan qaramin tsakar gida da daki daya sai bandaki da rumfar girki sai dakin kiwon kaji da yar tinkiyarta suka shige.

Dakin ba tarkace sosai dan haka suka zauna anan suka dawo da zancen komai baya suka tattauna kafin mama tai masa nasihar riqe gaskia da kaucewa haram komai kankantarta idan ya tafi can.

Ummitah tinda suka taho tana jikinsa ta lafe tanajin anfara maganar tafiyarsa tafara hawaye tana qanqamesa.

Jajir idanuwansa sukai shima sbd tinda aka haifeta baitaba rabuwa da ita ba sai yanzu.

Rarrashinta aka fara amma sai hakan yafara tayar mata da hankali tafara rikice musu tana fasa kuka me karfi tana sake riqesa da karfi.

Kasa banbareta daga jikinsa yayi yana kokarin dago fararen idanuwansa da sukai jajir ya zuba mata yana zuciyarsa na nauyi.

Rikicewa tayi gabaki daya tana musu ihu da kukan daya saka duk jamaar gidan fitowa cikin mamaki da tsoro sbd basu saba ganin hakan ba.

Mama sakina ganin yanda Ummitan ta haukace gaba daya ta fice hayyacinta take ya sakata fara kukan itama,

Inna ma kukan ta fara hakama duk yan gidan da suka shigo bangaren sanyi jikinsu yayi sbd kallo daya zakai musu ka tabbatarda wata irin kaune ce tsagwaronta babu sarki.

Rungumeta yayi qam a jikinsa tsawon mintina yana tofa masa addoin samun nutsuwa dana kariya daga sharrin duk wani sharri kafin ya zareta jikinsa da karfi yasakata jikin mama sakina data qanqameta da karfi.

Kudi ya ajiye musu mara wani yawa ya juya ya fice idanuwansa a qasa sbd jan da sukai ya fice gidan.

Se dare ya iso gida ya zauna wasu hawaye masu zafi da radadi sika gangaro masa ya rintse idanuwansa yana adduar Allah ya tsare masa Ummitah daga sharrin komai dayake duniyarnan har lokacinda zai karbeta ta dawo hannunsa.

Tinda dare ya tsala yake zaune akan abin sallah yanawa rayuwar Ummitah da tasa tareda iyayensa wanda mama sakinana ciki addua har asuba.

Wanka ya fara yi kafin yayi alwala yafice masallaci sallah sbd a lolacin aka tada.

A masallaci yana fitowa ya hade da kawunninsa biyu wanda suka kallesa amma sam baima dagoba bare ya kallesu sbd Allah ya haliccesa da wata irin kafiya akan abinda yake qi koya tsana hakama kafiya akan abinda yake tsananin so da kauna dan haka idan ya tsani abu to har abada bayajin zai taba kaunarsa.

Su kansu sunsan yanada kafiya da taurin zuciyar da bazai taba ko kallansu ba.

Yana isa gidan daman ya hada komai nasa dan haka jakarsa daya siya ya saka yan kayansa daya siya ya dauka ya goya a bayansa ya tattara komai nasu ya ajiyegefe ya fito ya rufe dakin ya saka padlock ya rufe ya juya ya fice gidan.

Yana fita ya hau keken wani abokin aikinsa daya hadu dashi a hanya ya kaisa har hanyar mota daga can ya hau mashin zuwa tasha.

Yana isa ba jimawa motarsu ta cika suka daga zuwa abuja inda acan zaibi motar lagos.

Sai dare suka isa abuja dan haka baima bari gidansu Alh Saad suka san yana abuja ba yakwana a tasha karfe dayan dare motarsu ta tashi zuwa lagos.
#MAMUH
#LIMBAS
#AZIZ LIMBA


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
11
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci? cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA? NEW PROMO YA KAMMALA=؃?

*********
********
A lagos kai tsaye Alh saad yai masa registration daman hardana hostel da komai tini daman aka basa takardun komai suna hannunsa dan haka yana isa wanda Alh saad ya basa numbernsa ya kira suka hade yakaisa har hostel har cikin dakinsa.

Shima students ne wanda aka hadasa dashi dan haka washe gari shiya zo ya jasa suka qarasa sauran registration dinda baa qarasaba da sauran abubuwan.

Kwanaki ya dauka Muhammed yana nuna masa komai na makarantar da yanda zai muamalanci mutane da Guraren lectures da da komai seda ya dan fahimta tukuna Muhammed ya kyalesa duk da kusan kullum suna haduwa.

Karatu da rayuwa a cikik kabila da kuma mutanen da bama ka saba ganin irinsuba abu me tsananin azaba da wuyar gaske tareda gajiyawa musamman dayake akwai kabilanci sosai da banbancin rayuwa sai abin yaso yai masa nauyi,

Amma kasancewansa wanda ya taso gwagwarmaya da tsananin rayuwa tareda rashin sabawa da muaamala da mutane sosai sai hakan bai dade yana wahalar dashiba ya bada himma kawai gurin karatu da dan aikin daya fita da kansa ya nemowa kansa a wani shagon hada lalatattun computers wanda yake samun dama biyu ana biyansa kuma yana koyan computer tareda saninta sosai.

******karatunsa yayi nisa ahankali kaman yanda aikinsa yayi nisa sbd acikin qanqanin lokaci ya zama dan gari ya samu zama babban me kulawa da office din computer din hakama karatunsa sosai yake tafiya yanda yakeso duk da akwai wahala amma ya dage sbd AERONAUTICAL ENGINEERING? ne yake karanta wanda karatune dayayi focusing akan development da production of aircraft.

Aiki yake sosai da business tareda karatu wanda ya sakasa sauyawa a kankanin lokaci sbd rufin asiri dayake cikinsa sosai.

Shekara guda ya share cur bai tafi gida ba sbd yanayin aikinsa dayake shine yake kulawa da komai gashi yana karatun sosai harma dana addini dan haka waya kawai yakeyi sosai dasu Ummitah wadda tafara zamowa yan mata.

Koda zai taho ganin gida siyayyar da yayi musu saika dauka shagon sayarda kaya zai bude musu a kauyen dan ko takarman sakawan Ummitah da maman zasu kai kala goma goma koma fiye hakama kayan sakawan ummita da panties ma kadai dozen uku ya siya mata sai singlet da small small hijabs da kayan shafa da turaruka,

Akwati ma guda biyu ya siyo musu manya na saka kayan,
A taqaice kaman wanda zaiyi aure haka ya hado musu lafiyayyan lefen kaya ya biyo hanya,
Saida ya sauka a local government ya siya abinci shima kaman hauka ya dauki mota guda da kayan ya nufi gidan.

Ummitah na islamiya ya iso dan haka da gudu akaje aka sanar mata

Kallan wadda ta fada mata tayi da kyau da fararen idanuwanta masu shegen kyau da haske wanda suke kama sak da nasa tace

"HAMMAN UMMITAH ne kin tabbata ya dawo?
Idan bashine ba kikasa na tafi fada zamuyi"

Da sauri yarinyar tace

"Eh shine da kaya sosai da mota yazo"

Shiru tayi tana shiga bugawar zuciyar sbd Hamman Ummitah kaman yanda take kiransa yanzu ne to ko sunansa aka fada bugawa zuciyarta takeyi sbd tsananin farin ciki shiyasa ake tsokanarta da cewa yazo.

Allonta dayake hannunta ta ajiye gefenta ta miqe bata tsaya komaiba ta falfala da mugun gudu tabar makarantar.

Tin daga nesa ya hangota a guje tana zuwa daman shima tin dazu ana sauke kayan idanuwansa n hanyar makarantar kaman zuciyarsa zata bude sbd tsananin buqatan ganin hasken idaniyarsa farin cikinsa bugun zuciyarsa kuma.

Dan haka yana hangota idanuwansa sukai wani irin sanyi zuciyarsa na karba itama hakama gangar jikinsa da duminta kawai yake buqata a jikinsa ko zai samu karfin mutuwar da jikinsa yayi na rashin ganinta.

Daidai lokacin mama sakina ta fito daga gida da sauri itama cikin tsananin farin cikinda batasan yaushe ta fara hawayen ganinsa ba.

Hannuwansa ya warewa Ummitah yana tafiya zuwa gareta daidai tana isowa da gudun gaske ta fada kansa yayi sama da ita ya rungume da tsananin karfi yana sauke ajiyar zuciyar dayayi shekara nawa bai saukeba idanuwansa na kadawa zuwa ja.

Itama qanqamesa tayi tana fasa kukan farin ciki tana jin kaman ta bude cikinsa ta shige sbd tsananin kewa da kaunar datake tsakaninsu.

Sun jima a hakan anata kallansu wasu na mamakin irin tsananin so da kaunar dake tsakaninsu wasu kuma na tausaya musu wasu kuma na gulman yanda ya rungumeta.

Kasa sauketa yayi duk da tafara girma ahaka suka juya zuwa cikin gidan bayan angama shigar da kayan mama sakina ma hawayen takeyi ya kama hannunta sukai ciki.

Inna ma duk da idanuwanta basa gani tayi farin ciki da dawowansa sbd kunnuwanta zasu huta da rigimar Ummitah idan taso rashin arzkinta kuka take zaunawa ta ringa musu akan saiya dawo.

Yan gidan ganin tarin kayan arzikin da akazo dasu ya saka suka ringa shigowa yi masa barka da zuwa harda masu kawo lafiyayyar fura dataji madara me tsafta.

Godia yayi musu mama sakina ce ta karba ta ajiye sbd bataga alamar zai iya sha ba sbd ya sauya musu gaba daya ya koma wani ABDULAZIZ din daban.

Ummitah datake jikinsa gyara zamanta tayi a jikinsa yana share mata hawayenta da handkerchief dinsa me qamshi yana kallan idanuwanta da hancinsa dasuke sak nasa kaman shine ya haifeta,
Tayi haske sosai tama kusan kamosa a haske gata fes fes kusan ta banbanta da yan kauyen sosai sbd ya tsaya sosai akansu yana musu aike sam baya wasa da duk abinda ya shafi cinsu da buqatansu.

Mama sakina kuwa sosai take kulawa sa Ummitan harma mantawa takeyi da ba itace ta haifeta ba sbd so da kulawa da tattali dan hakanne ma Ummitah ta banbanta sosai da duk yaran garin ko yayan me gari va abinda suke nuna mata,
A bangaren gata da sakartawa kuwa kusan kaf garin babu kamarta sbd mamah ta sakartata sosai gata take nuna mata sam bata mata fa kuma Allah bai saka tafara lalacewa hakama sam bata barinta wani fita wasa ko yawo koyaushe tana killace daga makarantar boko da aka sakata ABDULAZIZ din na aiko kudin me mashin din dayake zuwa kaita ya daukota wanda shima da maman ake zuwa a kaita a dawo da maman gidan hakama idan zaa daukota sai anzo an dauki maman aje a daukota a dawo dasu tare sbd sam bai yadda a ringa daukanta ita kadaiba sbd tsaro da kiyayewa.

Dan hakan ne daga makarantar bokon sai Islamiya bata zuwa koina,
Kitso da lalle ma idan zaayi mata mamanta ce take kaita ta dawo da ita daga baya ma kudi ABDULAZIZ din yake aikowa idan zaayi sai azo gida ayi mata duk da tana yarinya qarama sai hakan ya saka gaba daya garin Ummitah ta koma kaman wata 'yar sarki.

Fira yakeyi da mama wanda kusan itace da inna masu maganar shi kuma sbd bai cika magana ba sai maganarsa take a taqaice gashi gaba daya hankalinsa yana kan Ummitah sbd wani irin kallan nutsuwa da kiyayewa yakewa koina nata sbd ganin tabon rauni daya a bayan hannunta ya sakasa bin koina nata da kallan nutsuwa a natse batareda? kowa ya lura da hakan ba.

Mama ta lura da hakan sedai tasan irin tsananin son dayakewa Ummitah bazai nutsuba ganin rauninta dan haka taji shima ta qara tsananin kaunarsa.

Ummitah ma dogayen yatsin hannuwansa dake farare tas kaman wanda yake cikin tsananun hutu take wasa dasu tana basa labarin duka abubuwan datake da baya nan da yanda mamanta ke sangartata da tsananin sonta.

Inna ce basa shiri sosai sbd yanda Maman ta daurewa Ummitah tana girma amma batada aiki sai kukan banza idan taso dawowan ABDULAZIZ din.

Wani irin sanyi zuciyarsa da jikinsa yayi ya dago idanuwansa da suka dan sauya ya kalli mama wadda tai qasa da kanta cikin taushi da muryansa me nutsuwa yace

"Mama Allah ya saka da mafificin khairi ya saka da gidan Aljannah"

"Amin" inna tace tana jin kaunarsu dukansu kaman jikokinta na jini da sakina ta haifa.

Mamar kuwa ajiyar zuciya ta sauke tana bude baki tace

"ALLAH yai muku albarka ya baku kariya da arzikin da bayajin kashewa yai maka budi ya daukaka rayuwarka ya baka duk abinda kake nema duniyar nan yaji qan iyayenku ya tsareku daga sharrin duk me sharri"

Amin" ya amsa dashi a sanyaye yana dorawa da godia.


Abinci lafiyayye maman tayi masa tabarsa yana fira da Ummitah datake ta faman yamutsashi tana basa labarai kala kala yana saurarenta sbd sautin karatun Al'qurani ne kadai yafi masa dadin muryanta da labaranta dan haka wani sanyayyan murmushi ne da babu me gani a fuskansa yake mata yana kallan bakinta yana tina ummansu wadda ita mama ta maye mata gurbinta sbd yanda ya lura tsananin so takewa maman nata shi kuwa har abada bayajin gurbin dayake zuciyarsa na kewan ummansa zai cike sbd yanada qawa zucin mahaifiyarsa duk da mama sakina maye gurbi me yawan gaske a rayuwarsu da kusan yake jinta kaman uwar data haifesa.


Kiran magrib da akai ya sakasa fitowa sukai alwala tareda Ummitah tukuna shi ya fice zuwa masallaci ita kuma tayi sallah tareda mamanta.

Yana dawowa aka jere masa abinci a tsaftacen guri tareda sabuwar tabarmar da maman ta siya sbd zuwansa kawai dan haka ya zauna.

Tareda Ummitah yaci abincin kusan ma duk ita ya tsaya kalla tana cin abincin saida ta koshi kafin shima yaci wanda ta rage sbd ragin nata yakeson yaci sbd son dayake mata irin wadda ko qazantarta abar tsananin so ce garesa,

haka kawai wani lokutan idan ya zuba mata ido yana kalla sai yanajin idanuwansa na sauyawa zuciyarsa na sanyi sbd jin kaman ya maidata cikinsa ya adana daga sharrin duniya dana mutane,
Tsananin So ne me tsafta da babu sirki irin wanda uwa da uba kewa 'dan dasuka haifa yake mata sbd jin yake kaman a tsatsansa ta fito tinda shine uba kuma uwarta,
A hannunsa aka haifeta,shine ya reneta,shine wankanta,fitsarinta da kashinta ma,shayarwa ne kadai mahaifiyarta tai mata dan haka bai sauke kansa daga uwa kuma ubanta ba.


Har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login