Showing 60001 words to 63000 words out of 81012 words

Chapter 21 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

190

laushi da duvet dinda laushinda da kaurinsa ya cike gadon.

Hannu Fiddausi ta miqa ahankali ta kunna wutar dakin dake gefen gadonta tana kallan Kyakkyawan fuskan falaq din da batabar komai na Mahaifiyarta ba da kuma wasu kamannin Sir AZIZ LIMBA dinba.

Zaunawa tayi bakin gadon ahankali tana shafa fuskanta cikik kulawa da kaunar da itama take mai tsanani tana murmushi me kyau tana cewa

"Falaq,
Falaq baby,
Alhmdulillahil lazi ahyana baada amatana wa ilayhir nushr,
Good morning Bestien Daddynta,
Time to wakeup"

Bude idanuwansa tayi ahankali tana motsawa tareda maimaita adduar tashi daga baccin da Fiddausi ta gama karanta wanda ta sabane tin tana baby sun saba duk wanda ta tashi bacci gurinsa saiya mata dan haka ta saba duk zata tada bacci saita mata ita wani lokacin tareda adzkhar na tsari sbd Daddynta daya saba karanta mata shi a duk safiyar duniya koda baya nan tana farkawa shine yake fara kiran waya ya karanta mata tin tana baby haryanzu data fara girma.

Tashi zaune Falaq tayi tana kallan Fiddausi cikin sake yar Kyakkyawar fuskanta da murmushi tace

"Anty Fiddausi kinsan meyasa na tashi da smiling face?

Wuyanta Fiddausin take shafawa ganin shatin wuyar rigarta daya kwanta mata tana murmushi itama tace

"No Ms Falaq Aziz saikin fada witch dinki na sauronki"

Wani Murmushin ta sake saukewa har tana dariya tace

"Best daddy nai mafarki zai daukeni mi tafiyarmu mubar OldLady din gidan nan ta dena mun fada ta denawa BestDaddy fadan kawo mun Mummyn danace banaso"

Dariya tayi tana Cewa

"To amma hardani zaa tafi ko??
Sbd BestD din naki kinsan da bestMan dinsa zai tafi sbd babu inda yake tafiya batareda dashi ba dan haka kema da bestWitch dinki zaki tafi ko??

Kallanta tayi alamar shawara kafin tace

"No,ke da Oldlady halinku daya kinason Daddynah yayi aure kema ai na taba jin kin fada a gaban Maman kuma kinfi bin bayan Maman.......

Cikin komawa kaman qaramar babyn itama Fiddausi tace

"Wat,inji waye yace inason Daddyn falaq Aziz yayi aure?
Idanma na fada to inaga bana hankalina tinda kince dukanmu witch na possessing namu amma nikam banason kowace mace ta shiga zuciyar BestDaddy sbd zuciyarsa ta babynsa ne kadai ba gurin kowa,
Babu wanda zataxo ta bata mana space"

Qarasa zancen tayi tana danne dariyarta tareda nuna da gaske take.

Kallanta falaq tayi tana karantarta kamar wata babba tana cewa

"Should i trust you Fi??

100 percent ma kuwa" Fiddausi ta fada tana bata hannunta cikin dariya.

Qin bata hannunta tayi tana miqewa tace

"Saina tambayi BestDaddy ko zan sake yadda dake coz oldLady tayi brainwashed naki i dont trust you both"

Toilet take kokarin nufa da gudu
Fiddausi ta riqota tana miqewa tsaye ta durqusa tana zare mata socks din baccin dayake kafarta me laushi kafin ta saketa ta nufi toilet dan brush ita kuma gyara dakin tafara wanda fadan luxuries dake cikinsa ma bata time ne.


Koda Falaq ta fito Fiddausi ta gama gyara dakin tsaf ta kunna ac sbd Daddyn tin tana baby ya saka dokar baa kwana daki da ita har safe da ac
Zata kwanta dashi qasa sosai kuma asuba nayi ake kashewa a tada ita sallah batareda duban qananun shekaruntaba sbd ta saba da sallan asuban akan lokaci tin tana rigima sosai idan an tadata da asuba harta fara sabawa sbd duk qarancinta to duk abinda Daddy dinta yakeso tana kokarin yinsa koda bataso da kuma duk yanda ya lalatata da gata sbd ba qaramin tsananin so takewa Daddyntaba.


Tsananin son datakewa Daddynta ya saka sam batason kowace mace na sonsa ko ayi maganar yayi aure sam batason kowa ya rabi Daddyn sai ita kadai,

Duk da akwai kuruciya sosai a lamarin nata amma da gaske har ranta batason daddynta yaso kowa sbd ganin takeyi idan yaso wani zai dena sonta ko ya rage ita kuma batako kaunar kwatanta Daddyn ya hada sonta da kowa ta kuma saka hakan sosai a ranta wanda ya fahimci da gaske take sai yaji baida raayin aure ko kadan a kusa barema baida time na mace bare Soyayyar duk da yana samun tayin aure daga manyan mutane ga yayansu amma baya buqata kuma baya boyewa yake dakatarwa sbd shi dan kai tsaye.

A harkan business dinsa baida tausayi ko emotions ko kadan business kawai hakama tamkar wani mugun maye yake a duk abinda ya saka hannu sai wata irin nasara me girma taxo shiyasa manyan da suka kaine yanzu kawai abokan businesses dinsa shi kansa manyan da suka amsa sunane kadai ke hulda dashi sbd nasararsa binsa take koina ya saka hannunda kafa hakan ya saka yayi wata irin suna da shaharar da sunansa yake yawo a tsakanin manya da duniyar masu abin duniya kawai.

Lucky Billionaire Monster ake kiransa a cikin Business tycoons da suke hulda dashi gashi da wani irin farin jini da kwarjinin dayake sakasa samun respect fiyeda shekarunsa a gurin manyanma hakama kudinsa ya saka respect dinsa yake ninkuwa gashi da kamewan datake saka manyanma da yawa shakkarsa.

Bayan businesses dayake da companies dayake dasu qasashe da Nigeria a harkan Business na motocin Business dinsu da Alh Saad wanda shima ya gama miqawa yayi nisa sosai a daula da samun power Shine yake ranking No 2 a business na motoci kaf dan haka gaba daya ma yake wahalar gani.


Zaunawa sukai da Fiddausi a gaban mirror tana tayata shiryawa kafin ta nufi closet dinta tana dauko mata kayan da zata saka tana sake mata dadin bakin itama batason BestDaddy yayi aure.
#MAMUH
#AZIZ AY LIMBA
#FALAQ AZIZ
#JANNAH ZAD
#REVENGE
#SAYD

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
32
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci? cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA? NEW PROMO YA KAMMALA=؃?
*******
Sauraronta Falaq kawai keyi tana cewa

"Sai nayi shawara da BestDaddy zan san should I trust you or not"

Fiddausi dariya takeyi tana cigaba da tayata hada kayan zuwa camping din dazasu na school na yara tana cewa

"Na bar team din Mama na dawo team Falaq...

Katseta falaq din tai da cewa

"Falaq Aziz"

Sorry na falaq Aziz na manta princess din gidan batason ana raba sunanta dana Daddynta"

Straight jean daya lafe jikinta da white Cardigan me kauri da tsayin datazo har cinyarta ne Fiddausi ta tayata sakawa sai kuma jacket itama me kauri da qaramar veilhijab da iyakacinta wuya da sai socks data saka ta duba time ta zare jacket din tabar Cardigan kafin a tashi fitan,

Qamshin turarenta me sanyi ne na yara irin shekarunta yake tashi a jikinta da dakin, ta nufi kofa tana ficewa zuwa gurin daddynta sbd tana tsananin farin cikin ta wayi gari ace daddynta na gari zata gansa a safe kafin komai.


Tana fitowa palonsa take kokarin nufa Kofar palon Mama ta bude maman na fitowa tana kokarin saka kiran numbern data kasa nemowa da kanta tana kiran Fiddausi tazo ta nemo mata.

Cikin ihun daya saka maman firgita tana saurin ja da baya wayar hannunta na faduwa falaq ta saki tana rufe idanuwanta da sauri tana cewa

"No no no,bazan fara saka Mama a idonaba,
Ina fara ganinta shikenan idona zai zama wani iri ayau,
Idona babu wanda zai fara gani se the No 1 handsome and the most beautiful and amazing BestDaddy in Falaqs Universe..So i can't let my beautiful eyes su fara da ganin oldLady.

Fiddausi datake bayanta maman ta kalla tana danne dariyarta

Mama kuwa data saba da wannan iya shegen na Falaq din hade fuska tayi sosai tana gyara tsayuwarta daga firgitan datai tana cewa

"Fiddausi dakyau,
Kina kallan yarinyar nan ta zuba wannan ihun tana kusa dake baza kiwa bakinta mugun dukan da saiya fashe ba kika tsaya a bayanta kina dariya tana cewa Uwar ubanta mayya ko??

Falaq na jin hakan ta saka hannuwanta tana rufe kunnuwanta tana bin bango idonta a rufe tana cewa

"Har muryan kowa bazanji ba Muryan datafi na kowa dadi and Nutsuwa"

Nufota mama ke kokarin yi tana cewa

"Kamo mun ita Fiddausi ki ban nan...

Tana jin hakan da gudu ta qarasa hanyar palonsa tana Kiran sunansa da karfi sbd tasan Fiddausi na kaita Dukanta Maman zatai sbd a duniya ita kadaice take dukanta ko zaneta Daddynta baya ko dago kai bare iya cewa komai amma ko school baa dukar masa 'ya sam bai nuna zai yadda ba dan haka kaf rayuwanta maman kadai take tsoro duk da hakan baya hanata fadan magana sedai maman ta bige bakin amma bayan mama sbd Daddynta daya tsaya mata bata tsoron kowa duk da tana qarama amma sam batajin tsoron kowa a ranta sbd ubanta ya tsaya mata.


Ihun kiran Daddynta datake ya isa har makeken dakin Sayd dayake bacci cikin lafiyayyan gadonsa sanye da kayan baccin Logous Ash cikin duvet dinsa me laushi dayake tashin qamshin jikinsa da gama kama turarensa..

Sama sama yake jiyo ihun nata yana shiga kunnensa dan haka motsawa yayi Ahankali tareda miqa hannunsa daya batareda ya bude idanuwansa ba ya janyo wani pillow dayake gefensa ya rufe kunnuwansa yana komawa baccinsa.

Mama cewa tai "Fiddausi idan baki kamo mun ita kika kawo mun ba zaki fuskanci bacin raina kuwa ayau"

Falaq na jin hakan ta qarawa kafafunta gudu tana isa kofar palon ta miqa hannu zata bude aka bude kofar palon..

Wani irin nutsatsiyar qamshi mai sanyin dadi dayake tabbatarda tsadarsa a shaqa daya sanyin ac ya kado waje daga cikin palon wanda har inda mama take tsaye yakai yana sauya numfashin main babban palon gaba daya..

Bude kyawawan idanuwanta da suke sak nasa falaq tai tana kallo tin daga fararen yatsun kafarsa dasuke wani irin fes kaman baya fita dasu sanye cikin versace slippers,

Sanye yake da black pyjamas Basu tsantsi sai jacket me girma daya sako dazai fito daga bedroom dinsa sbd tashinsa kenan daga bacci muryanta ta fiddosa.

Fuskansa datake wani irin fresh ta kalla ko morning face dinsa ganin takeyi tafi duka daddies din duniya kyau dan har fada takeyi a school da fahari Daddynta is the most handsome mutum dayafi kowa kyau.

Hannuwansa dake cikin aljihun jacket din jikinsa ya zare yana bude hannuwansa kafin ma ya karasa kai hannuwan nasa akan fuskanta ta fada jikinsa tana cewa

"Yesss BestDaddy idanuwan Falaq Aziz suka fara gani ba Oldy ba"

Da farin ciki sosai a muryanta da yanayinta ta qarasa zancen tana qanqamesa cikeda tsananin son mahaifin nata.

Wani Kyakkyawan murmushin daya saka Fiddausi saurin sauke kanta sbd yanda ta kusan dauke wuta agurin ya sake mai sauti yana durqusawa ya ajiye gwiwowinsa qasa sbd ta rungumesa da kyau ya rungumeta shima yana gyara mata veilhijab dinta ya bude baki da muryansa dake cike da wani irin nutsuwa da steez daya gama kamasa yace

"Bazaki dena tsokanar Mama ba ko?
Kinason ta dokamun bakin my one and only Falaq Aziz"

Sakinsa tayi tana juyawa ta kalli Hanyar da maman take tana riqe hannunsa cikin nata tace

"To ni kasan ai bazan yadda na fara ganinta ba banfara ganin My Besty ba"

Hancinta ya shafa yana kallan Fuskan Ummitansa akan tata ya sake sakin murmushin daya fito daga asalin zuciyarsa yanajin kaunarta data uwarta da bata duniya suna yiwa zuciyarsa yawan da yakejin ko tinanin komai bazaiyiba akan basu ransa,

Idan yana kallan fuskan falaq duniyarsa nutsuwa take tana samun sanyi da nitsatsen farin ciki me yawan gaske duk da rayuwarsa na cikin wani irin bushewan da har abada bazata sake jiquwa ba sbd rashin Ummitah wadda rashinta shine asalin ciwonsa da ba warkewa bawai na rashin iyayensu ba.


"Amma falaq Aziz tasan cewa Maman itace maman Bestyn nata fa,kuma shi Bestyn Ai yana son mamansa sosai...

Bata fuska tayi tana cewa

"Ai sbd itace ta maman Bestyna ya saka nake tsoronta,kuma idan baka nan ai ina jin duk abinda ta fada,
Nidai Daddy karka bari ta dukarmun baki,
Duk ta qara masa tsowo sbd duka gashi yanadon ya dena kama da naka"


Mama data nufosu taji abinda take fada cikin quluwa tace

"AZIZ kana jin abinda take fada sai murmushi kake mata ko?

Dagowa yayi yana kallan Maman da sauran murmushin akan fuskansa dake cikeda da kwarjini ya kalli maman yana cewa

"Mama barka da safiya"

Amsawa tayi tana kallan Falaq din data boye bayansa tana cewa

"Arzikinki daya yau tafiya zakiyi da sai kin kwana biyu bakinki baiyi magana ba a gidan nan"

Turo baki tai tana qin cewa komai sbd maman na cewa Daddynta ya matsa gefe matsawar zaiyi dan haka tai shiru tana turo baki.

Shi kuwa murmushi kawai yayi sbd mamance kadai take discipline na Falaq din sai Sayyid da shima yake dan bude mata ido amma idan baa gaban Babanta bane.

Maman magana zatai dashi dan haka Falaq din ta shige palonsa shi kuma suka koma palo da maman sukai maganar rashin lafiyar Baba alhassan tukuna ya koma dan shiryawa sbd lokacin fitowansa ma baiyiba rigimar falaq dince ta fiddosa.

Yana shiga palon tana zaune tana duba abu a ipad dinta tana dariya sosai,

Kai tsaye Bedroom dinsa ya nufa ya rufo

Kayan jikinsa ya zare lafiyayyar fatarsa ta bayyana tana daukan ido sbd samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau.

Toilet dinsa dayake da girka sosai ya shiga tareda nufar shower ya sakarwa kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa ruwan na sauka akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna dumama jikinsa.


Bai wani jima sosai ba yana wanka dasu gyaran fuska da sauransu kafin ya fito daure da babban towel me kauri brown jikinsa na fidda qamshin shower Soap dinsa na Ocean seaweed.

Goge jikinsa yayi a natse sa wani clean towel din kafin ya fara shafe jikinsa da bodymilk da mix na oils na Ngenas da suke saka jikinsa glowing da kyan gani da wani irin soft ya shafa perfs dasu bodyMist da sauransu kafin ya gyara fuskansa yai brushing gashin kansa dayake a kwance da santsi irin na asalin filani.

Bai dauki mintina sosaiba bayan gamawa ya shiya cikin Navyblue jeans da White long-sleeved shirt data nutsu a jikinsa sbd tasan kudin daya siyeta.

A cikin tarin tsadaddun designer agogayensa dake jere a doguwar glass drawer daya ya bude ya dauko black cartier ya saka sai navy blue Lv fcap daya sako ya fito yana daukan wayarsa ipad dinsa datake iri daya sak da 'yarsa.


Yana fitowa koina a palon an sake gyarasa kamshi da sanyin ac komai neat dukda bawai datti ko wani hayaniya a palon komai unique,simple and luxuries ne kawai.

Fiddausi ce take gyara komai na bangarensa dana Falaq saina Sayd da mama amma sauran gidan masu aiki ne ke aikin.

Tana ganin fitowan Daddyn nata ta ajiye abinda yake hannunta ta miqe tayo gurinsa tana cewa

"You're morethan handsome MyBesty"

Juyowa yayi kalleta tana hada hannunta da nasa ta riqe yace

"And you??

Dariya tayi tana dawowa gabansa tana tafiya da baya suna tafiyar a haka tace

"I'm my father's daughter,so I'm the beauty itself"

Murmushi me nutsuwa kawai ya sake mata suna fitowa palon inda suka tarar da Mama na zaune tana magana da Fiddausi dake fada mata yanda sukai da Falaq da safen tana dariya.

Sayd kuwa a tsaye yake shigowansa kenan palon yana waya ganinsa ya sakasa qarawa ya karbi ipad din datake hannunsa yana masa barka da fitowa ya koma gefe yana cigaba da waya akan baqin da zasu tattauna dasu gashi AZIZ din yau ranar 'yarsa ce sbd da kansa zai rakata sbd kowa iyayensa zasu tafi dan haka shima yace a dakatar da duka schedules nasa na kwana biyu sai Falaq Aziz ta sun gama camping dinsu.


Hakan yasak yaketa kokarin ji da ayyukan da baqinsu tareda clearing schedules din yaji da komai.

Dining suka nufa dukkaninsu Falaq na sake boyewa gefensa tana leqa mama da ko kallanta bataiba tace masa

"Daddy zan bata da Anty Fiddausi tana fadawa mama sirrina"

Kallanta yayi yana cewa

"Oh no indai hakan ne taci Amanar Falaq Aziz"

"Yes Daddy,Kuma tace tana bayana amma tana maganar sirrina da mama i heard them not once"

Mama data juyo tana harararta ta kalla tana qara shige masa tace

"Did you just see that Daddy?
Jira take kayi tafiya zata dakeni for sure akan na fada gaskia"

"No Falaq bakinki ne is to talkative shiyas Mama ke dukansa so ki dena kiga bazata dakeki ba"
#MAMUH



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
33
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga? jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login