Showing 12001 words to 15000 words out of 81012 words

Chapter 5 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

176

dan haka ta hakura itama bata iya cin abincin ba sbd har cikin rai da jininta take jin ciwo da radadin da fatima ke ciki sbd kaunar datake tsakaninsu me girman gaske ce wadda suka taso a cikinta tin yarinta sbd itace ta zama kamar gatan fatima tin suna qananu har girmansu sbd ita tanada mahaifiya sabanin fatima data taso ba uwa ba uba.


A gidan mama sakina ta kwana duk aike da fadan da baba ila yai mata bata koma ba dan haka ya zuba mata ido yaga gudun ruwanta.

Washe gari da safe shugaban gurin aikinsu Ayoub din ya taho gaisuwa ya kawo musu abinci sosai da abubuwan buqatarsu tareda biyan kudin makarantar Abdul din wadda yake a local government harya gama.

Yaso bada kudin dayake ganin kaman diyya ce zai biya amma ganin Abdul din yaro ne kuma matar ayoub din batada me tsaya mata hakama yan uwansa sun saka zalamar jiran ya bayar sai kawai ya fasa ya fadawa baba Ahmed idan Abdul din yagama karatu ya isa fara business zai basa da hannunsa insha Allah kuma zai rubuta hakan ya ajiye koya mutu bashi ne Abdul yake binsa zaa basa.

Babu wanda yasan da hakan sai baba Ahmed wanda yayi naam da hakan dan haka bayan tafiyar alhaji Kabir din shima Ahmed tafiyarsa yayi sbd ba maganar aiki a gurin yanxu sbd kamfanin dai ya mutu mutus sai ansake sabon ginin ma dan haka yanzu maaikatan duk sun tafiyarsu sai kuma an sake ginin kamfanin akan wannan tukuna.

Kwanan mama sakina bakwai a gidan yan kauyensu suka taho gaisuwa da matan kawun fatiman dashi kansa da wasu yan uwan sakinar da yawansu.

Fatima a cikin kwanakin ta zama abar tausayi sbd abinci ma bata iya ci haka kawai cikin jikinta ya hanata lfy sbd damuwa da tsananin quncin da zuciyarta take ciki.

Abdul ganin halinda mahaifiyarsa take ciki shima ya tabasa dan haka kwata kwata baya cikin walwala ko kadan daman babansa shine abokinsa kuma abokin wasansa sbd baya fita koina wasa bai sababa tin tasosawarsa.

Mama sakina ma bata cikin walwalan kwata kwata sbd ganin halinda suke ciki dan haka bayan yan garinsu sun koma itama ta koma gida sedai duk bayan kwana daya sai tazo ta dubasu.

Kawun fatiman da zai tafi ganinsu da abinci sosai baiji tausayi ko kunya ba ya diba abincin sosai ta tafiyarsa.

Yan uwan ayoub din ma da sukaga hakan suma suka taho suka debi abincin me yawa sosai da cewa ai suma sunada gadon Ayoub dan haka tinda baibai komaiba a basu abincin.

Abdul ne rayuwarsa tafara sauyawa sbd karatunsa daya fara rawa sbd kulawa da mahifiyarsa wadda ta kasa dangana da rashin baban dan haka lafiya kwata kwata tafara kaurace mata,

Ta rame ta koma kamar wadda bata taba lafiyaba rayuwarta,
Bata wani ci bata wani sha bata cewa komai sai dole ga cikinta yanata girma dan haka komai a gidan shine yakeyi masu,

Shine yake musu wanki,ya dafa musu abinci,ya kai mata ruwan wanka yayi shara ya nemo,ya kuma tafi makaranta,sannan ya zauna yasha kuka a duk lokacinda ta kasa riqe abinda takeji tafara kuka haka yake yi a tareda ita,idan ciwo ya taso mata ma shine me zaunawa ya kula da ita ba magana haka zatai ta warke sbd basuda komai.

Ahankali baba ila ya gaji ya hana sakina zuwa gidan kaman yanda ta saba dan haka duk abinda suke buqata sedai Abdul din yake ya karbo musu dan abincin da zasu ci da wasu abubuwan kaman sabulun wanka ko omon wanki.

Hakan ma baba ila ganin yayi kaman zaa karya tattalin arzikin gidansa duk da na sakinar ne take basu dan haka ya haukace musu yace ya hana,

Ahankali rayuwa tafara yi musu tsananin gaske sbd komai basuda shi basuda me basu basuda hanyar samu,

Umma ta koma masa kamar me tabin hankali yau lafiya gobe ciwo kwata kwata batada sauran lafiyar ma da zata san tawakkali da dangana bare tasan itace ya kamata ta dauki juriya ta kula da Abdul ta tsaya masa sedai shine ya koma ya tsaya akanta.

Tsana me tsananin gaske Baba ila da yan gidansu Ayoub sukai masa sbd yanda tin yan yaro ya tsayu kan uwarsa gashi yai neman taimakon a gurinsu amma sun bayyanar masa da tsanar da sukaiwa mahaifinsa a fili dan haka sai yaji yafisu jin tsanarsu me tsananin gaske dan haka bai sake ko bi ta hanyar kofar gidansu ba Dan yafison mutuwa ta daukesa kaman yanda ta dauko babansa daya sake zuwa gurinsu.

Baba ila kuwa sbd tsananin kaunar datake tsakaninsu da mama sakina dayake jinta kaman ummansa data haifesa yasa yake danne ciwo da radadin tsanar da yayi musu sbd mama sakina ta tabbatar masa har abada kada yace zai rabu da ita sbd itama uwarsa ce ko fatima na raye ko bata raye.


Rayuwa tafara yiwa mama sakina tsanani itama sbd baba ila daya dena bata komai sbd kada ta taimaka musu daman matansa da yayansa kwata kwata basa kaunarta,
Abincin da zata ci kansa ankoma a gidan a qaramar roba ake bata shi wanda ita kanta baya isarta amma a hakan wata ran take juyewa a leda ta bawa Abdul din ya kaiwa fatima wadda da kansa yake bata itama bata wani ci kadan take ci sbd yanayinta.

A haka ya dage yana karatunsa duk da wata rana yaje ne wata ran baya zuwa amma a hakan yana kokari sosai
Suma malamansa da suka gaji da dukansa aka fahimci tsananin rayuwar dayake ciki sai aka dena dukansa aka barsa a hakan idan yazo shikenan idan baizo ba shikenan.

Mama sakina ta koma sabulun da zatai wankan ita kanta batada shi batada ko man shafawa masifar rayuwa tafara sakota gaba dan haka Abdul din daya fahimci hakan saiya rage zuwa kwata kwata gurinta yafara aikin wahala da wanda zai iya da wanda bazai iyaba haryafara sabawa idan ya samo yana dan siya musu harma da ita mama sakinan yana bata omo ko wani abin idan ya siya musu.

Sun wayo gari sitirar sakawa tai musu wuya daga shi har ummansa sbd sata da aka ringa sakasu gaba da ita saida suka rasa komai a gidan bayan tabarma data mutu sai karamar katifar da itama ta mutu sai kuwa buta daya da bokitin wanka da tukunya shi kadai suka rage musu.

Cikin ummansa ya tsufa harya wuce lokacin haihuwa a lokacin ne katangar gidan ruwa ya zubar musu da ita aka sace duk kwanon langa langar gidan da sauran abubuwan dan haka suke a rabe a gefe cikin gidan wanda har dakin da suke ruwa yake daga saman sbd har saman anhau an sace langalanga kadan aka bar musu dan haka idan ana ruwa suna gefe dan ruwan yana dan shigowa kadan kadan ta sama.
#MAMUH
#BESTLOVE
#BESTROMANCE
#HOT
#STRUGGLE
#BILLIONAIRES WAR
#AY LIMBA


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
8
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


*************
Koda cikin Fatima ya isa haihuwa karfin da zatai naqudar arziki batada shi sbd yunwa da ciwo tareda cikin da duk ya janyeta ta koma kana ganin qashin bayanta ya fito dosai da duk qashin kirjinta kana ganinsu idanuwanta sunyi ciki sosai tayani muni dik ya gama sauya kamanninta sbd ciwon da yunwar da bayan Allah da yayita babu abincin da zai dawo da ita yanda take kila.

Abdul yana kokarin daya fi na shekarunsa sbd har local government yake zuwa nema da aiki harma da tallan rage wadda bayayi da yawa sbd baya iya dadewa waje yake komawa gida gurin ummansa dan komai shine yake mata sbd baba ila ya rabasu da Mama sakina wadda take cikin tsananin daci da ciwon rai na hakan amma Abdul dinne ya roketa akan kada ta rabu da baba ila sbd su shiyasa kawai take zaune a gidan amma aurensa gabaki daya ya fita daga zuciyarta ba sauran sonsa ko qwaya daya a ranta gashi daman Allah bai bata haihuwaba tayi neman haihuwar harta gaji ta barwa Allah.

A cikin wannan halin da suke ciki ne Allah ya kawowa Umman naquda cikin ciwo da ukubar rayuwa tareda yunwar data gama kame duk wani kayan cikinta da gangar jikinta ta haihu,
Haihuwar data taho musu da sabuwar kaddarar da babu yanda zasuyi bayan rungumar rayuwa a yanda taxo musu batareda taimkon kowa ko kulawan kowaba bayan ta mama sakina da suke samu jefi jefi Abdul ya reni kanwarsa da mahifiyarsa wadda ta koma masa tamkar UMMITA wadda take yar shekara biyu zuwa uku dan kuwa duk inda zashi dasu yake zuwa sbd fita sukeyi su tafi yawo dan haka duk inda zashi yanzu suna tare dan haka da yawa ake musu kallan almjirai ko yan yawon neman sadaka duk da yana iya kokarinsa akansu gurin ganin ya tsaftace su.

Yanzu sun dena zuwa irin guraren dake kaman kasuwa ko tasha gurin aikin nema ko sanaa sbd bayason ana kallan ummansa da ummitan dan haka Local government yake zuwa dasu har makarantarsa wadda yake gaf da kammalawa yanzu.

Har ciki a ke barinsa shiga dasu saiya kaisu bayan ajinsu yace su zauna karsu tashi saiya gama ya fito.

Haka zasu sauna suyita wasa a gurin harya gama batareda da damuwa da abinda dalibai ke fada akan mahaifiyarsa da rabin ransa dayake jinta kaman shine babanta sbd BAABAH take kiransa dan bata san kowa ba bayanshi da ummanta hakama shi take kallo ubanta tinda umman ta koma kaman ita tare suke wasa duk da umman ta dena magana.

Daga makaranta shagon dayake aiki yake wucewa dasu ya siya musu abinci suci ya ajesu guri daya suyita walwalansu harya gama se yamma su nufo gida sbd baya kaiwa dare sbd su duk da megidansa yana son ya ringa kwana shagon sbd yadda dashi da yayi da kuma kokarinsa tareda amanarsa amma sam baya iya hakan sbd kare mutuncin ummansa da Ummitansa dan haka duk abinda yake samu a aiki ko sanaa yamma nayi yake wutowa gida dasu su wanka suci dan abinda ya samu ya ringa koyawa ummita dan karatun yara har suyi bacci itada umman ya gyara musu gurin kwanciya ya kaisu su kwanta shima ya zauna gadinsu dan baccinsa rabi da rabi ne akansu sam bayada wata irin yadda da kowa gashi basada koda rabin gidan a zube dan haka baya wani bacci akansu.


Ranar wata alhamis ya samu wani aiki a wani sabon kamfani da zaa gina a local government na gyaran shinkafa me kudin dayafi tsaron shagon dan haka ya karba ya hada biyu yana yi sedai aikin gurin akwai hadari dan haka dole yake barin su ummita a gida amma saiya fada musu yafi so ashirin kada su fita koina.

Sunji maganarsa basa fita dik ya tafi harya dawo baya cikin nutsuwa amma yana tarar dasu a gida basa fita koina sedai gidan zai tarar anyi masa kaca kaca hakama sunyi wata irin dauda hakanan zai tsaftacesu ya gyara gidan ya basu abinci suci su koshi suyi sallah wadda tasa ce kawai ta arziki su kam ture ture sukeyi a gurin sallan tsakanin umman da ummita yana jinsu zai kyalesu a gama a hakan.

Akwai wata irin kauna da so me tsananin gaske tareda shaquwar datake basa tsoron da baisan na mene ba a tsakaninsa da Ummansa da Ummitansa haka suke sakasa wasa dasu dole wanda su kadai ne suke ganin dariyarsa da walwalwansa dan Allah ya sako masa wani irin kame kai tin yana yaronsa shiyasa ya taso hakan.

Tin yana fargaban barinsu a gida yaje ya dawo harya dan rage fargaban yana aikinsa cikin dan nutsuwa amma bawai hankalinsa baya gidan bane dan baya kara ko minti daya yana tashi aiki yake komawa gidan dan ya dena zuwa makaranta exam kawai yake jiran ranar yinta yazo ta gamawa tinda suka shiga ss3 ya dena zuwan waec kawai yake jiran yi.

A yau tinda ya kamo hanyar zuwa gida yakejin baida nutsuwa dan haka ya qara sauri yana jin kirjinsa na nauyi ya kuma saba da hakan a duk lokacinda bay taredasu jin yake zuciyarsa ta ringa shiga damuwa da nauyi kenan.

Yamma ne sosai dan haka bai biya gidan mama sakina ba dan bata sabulu da omon daya siyo harda ita ba dan haka ya wuce gida saiya dubosu saika ya fito dasu yaje ya kai mata batareda ya shiga gidan ba san anjima da baba ila yai masa iyaka da shigar masa gida sedai ya tsaya daga waje gefen gidan mama sakinar ta fito ko kawai ya aika mata ummita ta shiga takai ta fito shikuma yana waje yana jiranta su koma.

Yana doso gidan tin bai karasa ba ya hango Ummita tana fitowa daga hanyar bayan gidansu tana kuka hannuwanta da kafafunta qasa da jini.

Wani irin abu ne ya daki kirjinsa da tsakiyar kansa dan haka da sauri ya qaraso ya tarbeta tareda ajiye kayan hannunsa ya jawota gaba daya jikinta yana kallan hannuwanta muryansa dayake da wahalar ji shima dan baya wani magana sosai sbd baida abokin firar yace

"Ina ummah?
Meya faru?

Kuka takeyi sosai ta juya bayanta ta nuna masa hanyar data fito tana cewa

"Umma ta tafi,
Dodo ya bita da gudu ta tafi......

Wani mummunan yawu me dacin gaske ya hadiye yana daukan ummitan ya nufi hanyar data nuna batareda ya tsaya fahimtar me take fadaba yana jin kaman kansa zai zare.

Duhun magriba yayi amma sam baya ma gani ya doshi hanya yana tafiya yana duba umman kaman zai zai haukace a take yaji yana ji dan haka ummitan dake jikinsa ya sake qamqamewa yana jefa kafarsa duk inda ya samu yana adduar Allah kada ya jarabcesa da wannan jarabawar me girman gaske akan mahaifiyarsa da ita da ummita sune rayuwarsa da hasken dayake gani a wannan rayuwar ko yaya ummansa ta koma yana tsananin buqatanta a hakan.

Tafiya yakeyi harya isa wani kauye duhu yai sosai amma kwata kwata baya hayyacinsa.

Kaf kauyen babu ummansa babu wanda ya ganda dan haka ya juyo ya dawo kauyensu lokacin tini akai ishai amma be zauna ba ya zagaye kauyen tas nanma babu umman ga ummita wahala da zazzabin raunikan jikinta sun saka tayi bacci a jikinsa jikinta zafi sosai.

Bai taba shiga mafi munin tashin hankali da firgici irin daren ba na rashin umman amma bai damu da daren ba haka ya doshi wani kauyen a cikin tsananin duhun dare nemanta idanuwansa sunyi wani irin mummunan jajir.

A cikin dare mafi tashin hankali a rayuwarsa kauyuka uku ya zagaye amma kwata kwata babu ummansa babu wanda ya ganta dan haka ya yanke jiki ya fadi qanqame da ummita zazzabi me mugun karfi ya gama gabalaitar da ita a jikinsa.

Jamaar kauyen daya somen suka yo kansa sbd lokacin har anfito sallan asuba gari ya waye sosai suka yo kansa suna son cire ummita a hannunsa amma yai mata wani irin mugun riqo da dole tana jikinsa aka zuba musu ruwa a tare.

A tare suka sauke ajiyar zuciya sedai kowannensu a galabaice musamman ummita shi kuwa ganin yayi kaman baya ganin komai sbd azaba da wahala tareda galabaita da tsananin tashin hankali.

Tashi zaune yayi yana gyarawa ummita zama a jikinsa yana sake rungumeta da kyau wasu zafafan hawayen daya manta rabonsa daya zubo suka gangaro daga fararen idanuwansa da suka koma jajir ya ambaci sunan umman ahankali yana rokon ALLAH ya kawo masa kowacce irin jarabawa indai ummansa zata dawo garesa zai jure ya runguma kaddarar.

Tausayinsa ne ya rufe jamaar gurin dan haka aka taimaka masa aka tayasa bincika neman umman tasa a kauyen amma har yamma babu labarinta kuma har dayan kauyen suka tayasa nemanta amma babuta.

Kauyensu ya nufo ummita na jikinsa a some sbd ruwan saman da akeyi sosai duk ya qare akansu.

Koda ya dawo kauyensu ana sallan ishai duhu yayi sosai,

Kofar gidan ya shiga wanda ruwan sama ya cika gidan kai tsaye dakinsu ya nufa ya bude ya shiga
Taku daya yayi zuwa biyu kafafunsa suka kasa daukansa ya zube a gurin yana fasa wani irin kuka me karfin gaske Ummita dake jikinsa azaba ta farfado ta bude idanuwanta daqyar batada karfin motsawa anan ta sake lumshe idanuwanta suka rufe jikinta ya sake sakewa alaman ta sake fita hayyacinta.

Kuka yakeyi sosai yana wani irin jijjiga zuciyarsa kaman zata fashe akan abinda yake ji,
Shima zazzabine sosai me karfin gaske a jikinsa amma ya kasa sakin Ummita barema yasan shika halinda yake ciki.

Kuka me yawa sa karfi sosai da idan da ba ruwa akeyib kusan duka makotan dake kusa sai sun jiyosa amma karfin ruwa bai bari anjisu ba.

Ummansa yasan a duk inda take tana cikin wannan ruwan da duhun dare wanda zai firgitata ta qarasa haukacewa mutane su kyareta su qyamacet su hantareta shikenan ta shiga gagarin da babu wani gata ko rufin asiri gareta........

Wannan ke saka zuciyarsa daukan wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login