Showing 66001 words to 69000 words out of 81012 words

Chapter 23 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

191

bafa ai da kilan tanada chance ko??

"Kallan Fiddausin tayi tana jikin maman har lokacin tace

"Eh kila,amma dai No"

Mama da zancen ya fara isarta tace

"To indai kin fara tinanin zaki bari uban naki yai auren ai anyi arziki tinda haka ya zaba na biye shirmen banza da tinanin wadda bama hankalin ne da ita cikakke ba"


Falaq bata fuska tayi tana kokarin tashi ta kalli maman tayi magana
Maman ta hanata tashin tana cewa

"Kina cemun witch ko oldLady zanyiwa bakinki mugun dukan da saiya fashe yayi tsawonda sbd muninsa ma ko Babanki bazai ganeki ba"

Shiru tayi tana sake bata fuska qasa qasa tace

"Cewa fa kikai banda hankali kwata kwata kuma kice zaki fasa mun baki,to ni ya zanyi"

Fiddausi dake hana dariyarta fita tace

"Mudai tinda an samu wadda ta burge Falaq Aziz a hakanma munyi arziki,
Kuma zan so na ga wannan din data burge ki"

Murmushi tayi tana cewa

"Banfa nuna mata hakan ba sbd kada taji dadi so kar kiyita fada ma taji"

"To ni ina zan ganta ma bare na fada taji amma dai zamu so ganinta ni da mama"

"Ku cireni a shirmenku bana ciki" mama ta fada tana zare qaramar veil din datake nade da kan Falaq din da ganin kanta daya isa sabon gyara.


Firarsu sukaci gaba da yi itada Fiddausi dake biye mata kamar qaramar yarinya suyita shirme da muguwan wasa shiyasa Fiddausin ta samu matsayi me kyau a familyn sbd yanda take saka Falaq nishadi hakama Falaq din tana sonta sosai.


Da daddare bai fito cin abincin dare ba acan aka kai masa fruits kawai da dabino masu kyau da baa rabo dasu a gidan sbd shi yana cinsu sosai musammam da black tea yake cinsu masu kyan da tsafta sosai.

Babu wanda ya sake ganinsa sai washe gari daya fito breakfast sanye cikin kyan sanyi sbd mura ce tai masa kamu me kyau sbd kwanan sararin da yayi a tafiyar tasu dan hakan nema ya dakatar da komai baya buqatan komai sbd ciwon kai ta sakar masa sosai.

Suna gama breakfast ya nufi office din gidan da Sayd dayaketa kulawa da schedules dinsa.

Zaunawa yayi yana sauraron bayanan Sayd dayake masa akan Sabon sakon ZAADENs daya taho na wannan karan Maheer Zadeen ne ya nemesa da kansa yanason zuwa da kansa dan ganinsa.

Numfashi me sanyi da nutsuwa ya sauke yana cewa

"Zuwa nxt month ka duba menene suke nema,
Yanzu banda time na hakan.
Yaya result da Baba Alhassan sun shigo?
A sauya masa likita.


"Ok insha Allah,
Zaadens dinma already na gama bincika komai akansu tin lokacinda suka fara turo request dinsu and they seems to be clean"

Batareda ya dena karanta abinda yake karantawa na report din wani project dinsu yace

"Zuwa nxt month sai muyi maganar amma yanzu inda abinda yafi koma me sukeso mahimmanci"

Tattaunawa sukaci gaba da yi har tsawon lokaci kafin suka fito.

Da yamma fita yayi tareda falaq din sai dare suka dawo,

Koda suka dawo dr na gidan yana jiransu Sayd ya riga ya kirasa.

Shi aka fara dubawa kafin aka duba falaq din dan itama yasan ta debo sanyi duk da bata mura amma dai ya saba sam baya wasa da lafiyarta.


Kwana biyu ya bawa falaq dasu mama time dinsa sosai kafin yayi tafiya tareda Sayd dan haka Dole mama da falaq din aka koma shiri tinda baya nan maman ce yanzu me lallabata.

Kullum Fiddausi ke tayata shirin school driver ya kaita ya dawo da ita
Da rana islamic/Arabic teacher dinta tazo suyi karatu har yamma kafin ta zauna waya da daddynta dare na yi suci abinci suyi dan hayaniya da Fiddausi tukuna tai bacci.


Haka rayuwarta ta taso haka take dan hakanne ta saba daga ita sai familynta take rayuwa ba wani shiga mutane sosai.

Duk sati biyu ake kaita gyaran kai saloon dan haka wannan satin ma shiryawa sukai Fiddausi ta fito a shirye dan itace me kaita suka nufi mota suka shiga mama tai musu a dawo lfy.

Driver ke jansu suna baya suna kallan wani abu a wayar Fiddausi
Falaq din na kwance jikinta suna dariya kamar daga sama sikaji wani irin qara tareda wani burki me karfin gaske daya saka falaq din samu wani irin firgita.

Cikin sauri Fiddausi ta rungumeta tana kallan gabansu.

Cikin sauri shima drivern ya juyo yana kallan falaq yana cewa suyi hakuri accident ne suka tashi yi amma Allah ya tsare.

Falaq shiru tayi zuciyarta na bugawa da karfi sedai bata iya cewa komaiba ta lafe a jikin Fiddausi wadda itama ta tsorata sosai.

Qarasawa sukai saloon din yayi parking suka fito suka qarasa ciki daidai Jannah itama tai parking a gurin ta fito sanyeda doguwar maroon arabian gown da silk scarf a kanta sai handbag dinta da wayarta dake hannunta ta nufi ciki suka shigo kusan a tare.

Itace ta fara ganin falaq ta miqa hannunta zata tabota sedai hannun nata bai qarasa sauka akan falaq din ba falaq ta yanke jiki a gurin ta zube qasa.

Cikin matsanancin tashin hankalin da Fiddausi bata taba shiga ba ta zube qasa tana kamo falaq din wadda idanuwanta basu rufe ba sedai kokarin rufewan suke tana qanqame hannun Jannah data kama hannuwanta itama cikin tsananin tashin hankali da tsoro.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
35
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494



**********
Fiddausi ce take kiran sunanta da karfi jikinta na daukan rawa sosai tana rikicewa sbd abu ne da bai taba faruwaba tinda falaq din tazo duniya hakama tsoro da tashin hankalin fuskantar AZIZ LIMBA ne yake neman zautata dan haka ta qarasa rikicewa tana girgiza falaq din koina tana kiran sunanta.

Jannah ma sosai ta shiga tashin hankalin sbd itama kwata kwata bata saba da ganin irin wannan rikicewan lokaci daya ba da kuma ganin falaq din a zube.

Kokarin fara kwantarwa da Fiddausi hankali tayi tana cewa ta nutsu tukuna.

Ma'aikatan gurin da suka san falaq sosai tini sukai saurin fara kiran ambulance dan bata taimakon gaggawa.

Jannah ce ta zare hannunta cikin na falaq din da kamar rai ya fita a jikinta ta kamota daga jikin Fiddausi dake neman kamuwa da ciwon zuciya sbd tashin hankali da tsoro.

Jikinta ta kwantar da ita tana shafa fuskanta tana karanto mata adduoi tana kallan kofa da fatar Ambulance din tazo kan lokaci.

Fiddausi data kasa hakura a rikice ta miqe tana cewa

"Bazan iya jiraba muje asibitin kawai,
Muje,muje asibitin i can't take the risk na jiran se lokacinda ambulance tazo,
Pls pls mu tafi nidai...

Yanda take magana a rikice bata tsayawa jin komai ya saka Jannah daukanta cak gaba daya duk da tai mata nauyi.

Fitowa sukai driver dake zaman jiran gamawansu yana ganin fitowarsu da falaq din kamar ba rai a jikinta mugun faduwa shima gabansa yayi ya taso daga inda yake zaune da sauri yana nufosu ko isowa baiyiba Fiddausi data kasa magana da hannu ta nuna masa mota ya juya da gudu ya taho da motar gabansu suka fada dukansu har jannah din wadda Fiddausi ta riqeta tana rokon kada ta tafi sbd tsoro takeji kar abarta da Falaq din ita kadai zuciyarta zata iya bugawa sbd tashin hankali da fargaba.

Yanda ta roketa da yanda itama zuciyarta ta kasa barin Falaq din wannan halin ya sakata binsu suka nufi asibiti tana goga tafin hannun falaq din da sauri sauri ko zata farfado amma sam ko zuciyar falaq din bata bugawa ko kadan.

Kafin su isa asibiti hannuwan Fiddausi rawa sukeyi sosai tana kokarin controlling kanta ta ciro wayarta a jaka ta nemo sunan Mama ta saka kiranta tana sauke numfashi me karfi dayake dan yankewa.

Mama na daga wayar kannewa tayi tace

"Mama muna hanyar asibiti falaq ce,
Bansan meya sameta ba ta fadi bata motsi,bansan meya faruba,bansan yaya akaiba....

Kasa riqe jarumtar tayi ta qarasa zancen muryanta na karyewa da yanayi me damuwa sosai.

Mama ma kanta ne taji ya sara ta zauna daga tsayen datake tana cewa

"Innalillahi wainnna ilayhi rajiun,
Ita falaq din?
Kuna isa ki turomun location ganinan tafe yanxu kuma karki sanar da Sayd sbd kada AZIZ ya sani tukuna"

Kashe wayar Fiddausi tayi sbd sun iso asibitin.

Ciki akai da ita da sauri sukuma suka zauna waiting area bayan ta turawa mama location din tana kai da kawo kama zata shiga taji menene ya sameta.

Jannah kuwa jin tayi itama fargaba da tsoro haka kawai yana shigarta,
Jin take kaman wanzuwarta a gurin bai kamata ba amma kuma ta kasa tafiya sbd haka kawai tausayin yarinyar ke rufeta sbd tana tinawa da lokacin da kuruciyanta take gaba daya a yawon asibiti ta qareta.

Kanta taji yana neman juyawa sbd tinanin halinda ta taso rayuwarta da babu komai a cikinta sai ciwo da kadaici da qunci,
Dafe kirjinsa tayi sbd bugawan da zuciyarta tafara da karfi tana harbawa.

Jakarta ta bude ta ciro maganinta ta bude tayi saurin sakawa a bakinta ta hadiye tana rufe idanuwanta da suka fara cikowa da hawaye sbd itama ciwonta data fito ya zamar mata tamkar trauman da bata iya tinawa sai ta shiga wani hali.

Hankalin Fiddausi bai tashi ba saida aka dauki lokaci baa samu falaq ta farfado ba doctors na shiga serious bincike akanta.

Mama ma data iso samun ba wani bayani akan hakan hankali tashi yayi.

Muryan data sakata juyowa ne ya sauka kunnenta ana cewa

"Ina wuni"

Jannah din ta zubawa ido tana jin yanayi kaman na sani akan jannah din sedai kuma bata taba ganin fuskanba dan haka jikinta na sanyi ta amsa gaisuwan tana mata godia akan kawo falaq din asibitin.

Jannah dataji tsananin tausayi da mutuncin Dattijuwar ya shigeta girgiza kai tayi ahankali tana sunkuyar da kanta daga kallan fuskan maman data cika mata ido da yanayi me sanyi da kauna haka kawai idanuwanta na cikowa da hawaye ta juya da sauri tana maidasu.


Acan gida mama na fita motar data daukosa daga airport tana shigowa dan haka suna shiga securities suka sanar dashi maman ce ta fita yanzu da mota.

Shiru yayi batareda ya dagoba daga wayar dayake dubawa sedai ya dakata daga abinda yake.

Sayd ne ya kalli gurin ajiye motacin gidan yaga babu motar Falaq da ake fita da ita yace

"Falaq fa?

"Ms Falaq sun dade da fita itada Fid"

Sai a lokacin LIMBAn ya dago idanuwansa ya kalli Sayd wanda take ya ciro wayarsa ya saka kiran wayar mama wadda taketa ringin bata daukaba.

Ciki sika qarasa kai tsaye bangarensa ya nufa ya ajiye wayoyinsa ya fada wanka dan sauya kayan jikinsa.

Bai jima ba ya fito sanye da sweatset Off-white na Prada qamshinsa na na tashi a hankali ya dauki wayarsa ya saka kiran maman da kansa.

Ringing ta fara harta yanke baa daukaba.

Ajiyar zuciya me dumi ya sauke ahankali yana kallan time idanuwansa na sauyawa a natse.

Rayuwarsa abu dayane kowa ya sani ya tsana kuma yakewa tsananin qi wato ya kira na gida aki daukan wayansa sbd da hakanne aka boye masa ciwon Ummitah data rasu batareda yazo ya ganta ba,

Ummitah ta dade tana ciwon da aka boye masa wanda ya saka idan ya kira baa dauka sbd kada ya sani,

Hakama Ummitah ta rasu kowa ya dena daukan wayarsa sbd kada a sanar masa har Ummitah tai kwanaki da rasuwa yana duniya da rai da lafiya amma bai taho ga koda gawarta bane duk akan rashin daukan wayansa hakanne ya saka duk duniya baida abin qi da mafi tsana irin ya kira aqi daukan waya sai kuma Nigeria daya yanke zuwa gaba daya sbd baida komai da kowa a cikinta.

Dan hakanne ya saka kwata kwata duk wanda ya sansa baya wasa da rashin daukan wayarsa,

Business koda na billions ne idan ya kira kaki dauka to ko waye kai ya gama Business dakai koda zai rasa billions din shima kuwa shiyasama kwata kwata bai cika kiran mutane ba sedai a kirasa kokuma Sayd da kusan shine yake kulawa da duka calls dinsa sbd sunsha rasa manyan kudaden gaske akan wannan akidar tasa da kuma dole kowa yake binta.


Kaf duniya mama ce kadai take masa rashin daukan waya batateda fushi ko bacin ransa ya bayyana sbd kasancewanta uwa dan haka yanxu dinma bai sake kiranta ba
Wayar Sayd ya saka kira.

Sayd dayake fitowa wanka yana ganin kiransa ya daga yace

"Yes"

"Ina buqatan location na inda Falaq Aziz take zan daukota da kaina" ya fada a taqaice yana kashe wayar ya ajiye gefensa.

"Ok yes" sayd ya fada yana nemo numbern Fiddausi ya saka kira.


Fiddausi na ganin kiransa kanta y sara ta dafe goshinta jikinta na sanyi ta daga kiran sbd bata isa qin daukan wayarsa ba tana aiki a karkashinsu kuma kiransa kaman kiran LIMBA ne da kansa dan shine yake isar da sakon duniya kowanne iri ne na LIMBA.

Tana dauka ta bude baki zatai magana ya katseta da cewa

"Turomun location naku right now LIMBA is coming"

Dago jajayen idanuwanta tai ta kalli mama wadda take zaune ta zubawa jannah idanuwanta cikin nutsuwa tana kallanta sedai damuwa ce a zuciyarta fal gashi tana kallan kiran AZIZ ta kasa dauka sbd batasan ta sakasa damuwa kuma tasan rashin daukan waya shine babban asalin bacin ransa.

Kashe wayar sayd ya saka dukkanin jikim Fiddausi sanyi ta tura masa location din sbd batada yanda zatai kuma dai ciwon Allah ne ya kawo kaddarars koma menene daman tsoronta kada ace ganganci tai bata iya bawa falaq din kulawaba.

Tana tura masa ta kashe wayarta ta ajiye gefe tana dafe goshinta tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare.

Sayd na samun location din cikin mintina kadan ya shirya ya fito qamshinsa me tsada yana tashi sanye da three quarter da riga na Burberry milk da key a hannunsa da wayarsa.

Fcap LIMBA ya fito da ita sanye yana kashe wayarsa gida dan bawa falaq time dinsa a hanyar dawowansu gidan duk da zuciyarsa gaba daya tana karban rashin nutsuwa ne da falaq din kawai yake buqatan gani.


Sayd sam bai lura da location dinba saida suka shiga mota ya tayar yana budewa yaga asibiti ne.

Shiru yayi tareda juyowa ya kalli AY dayake shigowa a natse ya zauna.

Jan motar yayi baice komaiba suka nufi asibitin.

Saida suka shiga asibitin yayi parking tukuna AY ya dago ya kalli asibitin kafin ya kalli Sayd kafin yayi magana idanuwansa suka sauka akan motar Falaq sai kuma ta mama duk a guri daya.

Baici komaiba aka bude masa motar cikeda girmamawa ana cewa

"Welcome boss"

Ryan ne drivern Falaq din dayake zaune a cikin damuwa shima yana ganin motar ya taso.

Kafafunsa ya ziro waje yana fitowa Sayd ma fitowan yayi yana rufe motar suka nufi ciki Ryan na cewa

"Ms Falaq Aziz is...

Bai fada abinda zai fadaba Sayd yayi masa alamar yayi shiru kawai sbd LIMBAn da yasan a yanzu daya riga ya gama sanin Falaq ce a asibiti baya buqatan jin bayanin kowa saina likitoci kawai.

Fiddausi da mama ne suka juyo a tare suna kallan hanyar daya sako kai sbd qamshin BLACK VIOLET daya ratso gurin cikin sanyi take suka san shine yake tahowa
a natse ya tinkarosu sayd na gefensa Ryan ba bayansa.

Sunkuyar da kai Fiddausi tayi cikin girmmawa tana bude bakinta a natse tai masa barka da dawowa.

Mama fuskansa da kowannensu ya kasa karantar halinda take ciki ta kalla tana cewa

"Barka da dawowa,
Sayd ta kalla dayake gaidata ta amsa gaisuwansa tana maida kallanta akan AZIZ din daya gaidata kai tsaye ba tareda bayyanar da yanayin komai da komai dagewanka bazaka iya cewa ga yanayinda yake ciki ba ya wuce kai tsaye gurin likitan daya bude kofar emergency room din yana fitowa

Nufarsa kofar yayi daidai da juyowan Jannah dake waya tin dazu a natse da murynata mara hayaniya.

Tana juyowa yana kawowa gefenta wanda qamshinsa ne ya fara shiga hancinta daya sakata dagowa daidai isowansa gap da ita sedai ko alaman yasan da mutum a gurin baiba sbd fararen idanuwansa dake akan dr din daya fito ya rabeta ya wuce.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
36
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494



***************
Kasa motsawa tai daga inda take tsayen hakama iskan qurin ta sauya gabaki daya da qamshin data tabbatarda nasa ne sbd shine ya doki hanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login