Showing 30001 words to 33000 words out of 81012 words

Chapter 11 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

184

rayuwar da shima zai budewa wasu da daman ba.

Jannah zaaden kanta datake qaramarsu babu abinda ba designer ne a kayantaba ko abin amfaninta dan ko lipsticks dasu liner da cosmetics nata designers ne,su skin products nata ma kansu basuma san akwai wainda ba designers dinba dan haka koda ta taso batasan komai ba bayan luxuries kawai.


Itace tafara saukowa tana kokarin nufar dakin Mimi saiga Mimin ta sauko daga bangaren dad tareda dad din yana ganinta ya miqa mata hannu ta qaraso ta kama hannunsa tace

"Dad You look tired"

Murmushin karfin hali yayi yana cewa

"And you look pale Jannah Zad"

Murmushi tayi itama tana kallan Mimi dake murmushi itama.

Qamshim Maheer Zad ne ya sakata juyawa tana kallan hanyar fitowarsa sai gashi ta riga ganin Ammar daya fara fitowa qamshinsa na gaurayewa dana Maheer din yayi wani irin fresh na dan hutu da nutsuwan daya samu na yau din.

Kallanta yayi da fararen idanuwansa yana sake mata wani Murmushin daya sakata sakin dad dinta ta dawo gurinsa tana masa murmushi itama tana cewa

"My AmZad looking calm"

Murmushi me sauti ya sake yana cewa

"Yaya kikeji??

Just tired amma lafiya kalau.

Dining suka nufa wanda yake cike abinci da snacks da teas kala kala da fresh juices da cutlerys masu tsada da kyau.

Zaunawa sukai bayan Dad ya zauna Amah ce kadai takeda damar zuwa idan suna cin abinci dan cikin kaf masu aikin dan haka tana tsaye a gefe koda suka zauna ta matso tafara serving nasu a natse kuma tasan abinda kowannensu yake ci da yawan yanda yakeci.

Cikin nutsuwa sukaci abincin suna gamawa suka wuce Sallah.

Suna dawowa sallah a palon Dad suka zauna dukansu suna fira kaman yanda suka saba sunata kokarin hana Jannah sanin menene yake damunta har ta fara jin bacci sosai Saleem ne ya rakata har dakinta kafin ya wuce nasa dakin daga can.

Washe gari Maheer yafara fita office hakama saleem ya koma school Ammar kuwa a gida ya wuni bai futa koina ba yana tareda jannah da Mimi da dad.


Sai da akai kwana biyu dad ma ya warware ya koma Dzad dinsa ya fara fita office Ammar kuwa saida ya share sati biyu kafin yabi flight ya kom makaranta.

Jannah ta koma school itama sedai ranar datai sati biyu da komawa a school ta fara samun matsalar shortness of breath daya ringa sakata collapsing.

So biyu tana samun hakan sai school suka bata hutu sedai tana samun hutun sai gashi bata sake samun matsalar ba sai aka lallaba taci gaba da zuwa school.

Ko wasu kwanakin masu yawa bata sake ba ta samu attack daya saka zuciyarta kasa dauka ta yanke jiki a school din a rikice akai asibiti da ita sedai su Dad suka sameta a asibiti kaman yanda take wancan karon haka ta share kwanaki a kwance da oxygen kafin kafin Allah yasa ta farfado.

Hankalinsu bai qara tashi ba suka shiga asalin damuwa da tsoro da firgici saida ta ringa samun collapse a school wanda ta saka akan dole tasan Asalin menene yake damunta tayita kuka sbd ganin mutuwa zatai tabar iyayenta da yan uwanta.

Kuka da halinda ta shiga ya saka ciwonta tasowa sosai wanda ya sakata kwanciyar kusan sati biyu bata san wanda yake kanta ba.


A wannan lokacin ne Dad yasan dukiyarsa ba komai bace hakama shi din ba kowa bane a gaban ikom ubangijinsa dan haka ya rufe kansa a daki ya ringa rokon Allah ya rabasa da duk abinda ya mallaka ya bar masa Jannah din.

Mimi ma tayi kuka ta fadawa Allah daga karshe ta dangana ta barwa Allah ikonsa sbd ganin duk mazan gidan babu wanda yakeda jarumtar halinda Jannah din ke ciki sai ita ta koma tafisu karfin hali da mamakin irin yanda Allah ya jarabcesu da yiwa jannah so mafi girma akan komai banda ita datake jin ma ko acikin yayanta tafi kaunar Ammar dan haka ta koma tafi su karfin hali da jarumta akan ciwon na jannah sbd ta saddakar tasan jannah bame tsawon rai bace.

Jannah a cikin qanqanin lokaci Allah ya maidata abar tausayi babu abinda dukiya da gatanta zasuyi mata sai yanda Allah yaso yi da ita.


Kallansu dr Abraham yayi a karo na ba adadin zaman sharawa dasu ya fara koro musu bayanin,


"Yawan collapse datake samu yana qara tsananta raunin zuciyarta dake failing wanda kaman kwanakinta na raguwa ne sa sauri,

Ya kamata a kiyaye sosai tareda nesantata da doguwar hayaniyar da zata ringa ma sakata tinane tinanen dasuka fi karfin kwakwalwanta datake bawa zuciyarta stress"

Cikin sanyi Ammar ya kalli dr Abraham din ba kuzari a muryansa yace

"Wat happens wen the heart fails???

Da sauri dukkaninsu suka kallesa banda Mimi data ita likitan ta kalla wanda yayi shiri kafin ya sauke ajiyar zuciya da numfashi me sanyi yace

"Bama fatan hakan Mr Ammar Zad,....

Kallan dr yayi da idanuwansa da sukai jajir ya sake bude baki yace

"Ina tambaya ne sbd we cant lose her,
She has to liv,i cant lose someone again sbd zuciyar da ake buqata,
Meyasa bazaa saka mata zuciyar duk wanda aka samu ba....

Mimi ce tayi saurin riqesa tana kallansa cikeda mamaki da fargaba tace

"Ammar,me kake fada?idan ana samun hakan da zayneb tana tareda mu yanzu
Zuciyar mutum ake magana ba qaramin abu ba,
Samunta abu ne me wuyarda sedai mu dauki dangana mu barwa Allah zabi mu gode da lokacin da suka rage mata a duniyar muyi Appreciating hakan.....

Ta qarasa zancen idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan su gani.

Dad ne ya dago ya kalleta tana fadar abinda yakejin shima kaman bazai iyaba,
Ammar kuwa dr Abraham ya kalla cikin rashin ja da baya yace

"Heart transplant shine kadai abinda take buqata ta rayu right Dr??

Gyada kai dr Abraham yayi yana rarraba ido a tsakaninsu ganin dukkaninsu sun sauke jajayen idanuwansu akansa suna jiran amsarsa.

Maheer ne ya matso shima cikin karfin zuciya da kasa yadda da zasu iya kallo har zuciyarta tayi failing gaba daya ta rasa ranta yace

"Wat are the chances??

"with the right matching donor,90 percent"

Da sabon mamaki da wani irin shock din samun qwarin gwiwa me karfin gaske na zancensa suka kallesa Maheer na maimaita 90 percent din cikin farin ciki.

Dad ma dagowa yayi ya sake kallan dr Abraham din yana neman qarin bayani.

Dr Abraham ya jinjina musu kai yana cewa

"Idan aka samu donor datai matching zata rayu insha Allah cikin aminci kaman kowa,
Sedai samun donor na zuciya abu ne me wuyar gaske sbd candidates are placed on a national waiting list so kafin ma ta samu time dinta zai iya cikawa
Hakama donors na wuyan samune sbd yawanci masu donating sai wainda suke fama da brain injuries ko wainda ke gabanin mutuwa."


Katsesa Dad yayi da cewa

"Zuciyan da zaa dasa mata kawai ake buqata right?

Yes but se wanda zaiyi matching"

Maheer ne da Ammar suke hada baki gurin cewa

"Zata samu zuciyar da zaa dasa mata kuwa kota yayane koda hakan na nufin zasu rasa komai.

Mimi saurin kallansu tayi sedai Dad baima bari tai magana ba yace saleem ya tafi da ita kawai.

Dad numfashi me sanyi ya sauke sbd a yanzu kam baisan komaiba bayan neman zuciyar da zataiwa 'yarsa kota waye yana so a shirye yake barar da dukiyarsa gurin nema.

Maheer ma a nasa bangaren ajiyar zuciya ya sauke sbd a yanzu bayajin sunada buqatan sake bude wani kamfanin bayan na asibitin da zasu nemarwa kansu zuciyar da suke buqata.

Ammar ma jin yayi wani sanyi yana mamayesa dan kuwa koda zai karar da komai nasa ne saiya nemowa Jannah matching din da zatai mata sedai kuma sbd yanda yake da natsi da son sanin komai akan matsalar Mahaifiyarsa data rasu da jannah yana buqatan neman ilimi akan ciwon dan sanin komai da kansa baya buqatan kowa nai masa bayanin komai da kansa yakeson sanin komai.
#MAMUH
#ZADEENS
#LIMBAS



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
17
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?

**********
Mimi suna dawowa gida kasa shiru tayi ta kalli dad wanda fuskansa take a hade ba alamar bata fuskan maganar ma da duk take son yi wadda ta danganci cewa a hakura a zuba ido batareda kokarin komaiba Jannah kwanakinta su qare bayan Allah ya basu damar da zasu iya samar mata lafiya ta rayu.

Duk da rashin bada fuskansa Mimi daurewa tayi itama ta bude baki tace

"Me kuke nufi da nemo donor kota halin yaya?
Dzad zuciyar mutum fa ake magana ba wani abinda zaa iya zuwa kasuwa a siyo ba...

Maheer ne ya katseta da cewa

"Mimi ki dena maganar zuciyar mutum kaman wani abinda bazaa iya samuba,
Kina sanesa yanzu ma da kudade ana siyan mutane ko nawa kakeso??

Jiyowa tai tana masa wani kallan mamaki da takaici tace

"To wainda suke siyan mutanen suna siyansu ne dan rabasu da wani abin a jikinsu ne??suna siyansu ne dan bauta da wani aikin wahalar daban
Kadama ka sake kawon wannan zancen dan ko anayi mu meza muyi da safarar mutanen?

Sai alokacin dad ya dago yai mata wani kallo yana mamakin zancen dayake fita a bakinta na rashin tinani da nazari.

Bai samu damar tankata ba dan maganarta ma hanya take safarar mutanen zasu fara babu abinda yasha masa kai indai sa kudi ake safarar baida matsalar wannan.

Maheer ma kallan dad din yaga ko kallo mimin ma bata ishesa ba dan haka ya dawo da kallansa kanta yana cewa

"Mimi pls ki bari zanyi handling komai a yanda ya kamata batareda abinda kike tinanin ba"

Wani kallan ta sake masa kafin tayiwa Dzad din ta juya tabar palon tana mamakin tayaya suke tinanin neman abinda Allah ne kadai yake halitatta ba kaman abinda ake siya bane tinda da kudin na siyan zuciyar da zayneb kila tana raye.

Ammar dayake zaune palon bai samu shiga zancenba sbd Abinda yake karantawa a laptop yana dafe goshinsa dayake jin kaman kansa zai rabe biyu sbd tinane tinane da abubuwan dayake ji cikin kan.

Juyowa Maheer yayi ya kallesa zaiyi magana Dad ya hanasa yace ya kyalesa sbd yasan Ammar din shima bazai iya bari Jannah ta rasa donor ba kota halin yaya.

Numfashi me zafin gaske Ammar din ya sauke yana dago idanuwansa da suka sauya ya fara kallan Maheer kafin ya dawo da kallansa kan dad dayake jiran Abinda Ammar din zai fada.

"Dad ina son zama cardiologist,
Zan fara daga farko,inason sanin komai akan abinda ya shafi zuciyar dan adam...

Maheer kallansa yayi da sauri jin zai koma baya a karatunsa dayake kammalawa.

Dad kuwa ajiyar zuciya me sanyi ya sauke wani nauyi daya danne kirjinsa yana sauka sbd abinda yake tsananin buqatan kenan a cikin yayansa dan kuwa suna buqatan sanin abubuwa akan zuciyar da suke nema ta hanya me kyau da mara kyau dole saida nasu dan bazasu bari likitoci su zama sune zasu ringa sani da sanar dasu.

Maheer kuwa shiru yayi yana nazarin zancen sbd idan har waninsu yayi likitanci sbd hakan matsala zata iya zuwar musu gaba sbd career dinsa zata iya lalacewa har abada da hakuncin da duk kudinsu bazasu iya kubutar dashi ba,babu abinda yafi musu irin su samu kwararrin doctors din da zasuyi aiki dasu wainda daga baya ko careers nasu sun lalace zasu basu kudade masu yawa ne kawai su kama gabansu tinda su buqatansu ta biya.

Dan haka kallan dad yayi yana zaunawa cikin nutsuwa yafara cewa

"Dad Ammar baya buqatan sauya career dinsa akan wannan matsalar,
Hakan is very risky ga rayuwansa da zaadens gaba daya,
For this All we need professionals kuma best cardiologist wen we got abinda mukeso shikenan ba ruwansa da abinda zai iya biyowa baya,
Aiki ne da zaayi without leaving any traces so the best abu da zamuyi a hakan shine hana family ko daya zama cikin aikin."

Dad ma yayi tinanin hakan tin kafin Maheer din ya fada sbd bazai bari sunan zaadens ya fito a duk wani barnan da zaayiba amma kuma yana tsananin son wani a cikin nasu yasan komai akan hakan indai samun zuciya wa jannah zaiyi wuya to tabbas saisun zaba boyayyar dirty hanya.

Ammar cikin tsananin son karantar duk abinda ya shafi zuciyar ya bude baki baki yace

"Idan har zamu samu abinda mukeso daga baya sai ayi tinanin yanda zamu fita clean but dad i really need to be a cardiologist ba akan Jannah kadaiba har akan wanda zamu samu gaba a family me wannan ciwon,
Mun rasa Mum we cant l...

Kasa qarasawa yayi sbd bama zai iya tinanin rasa Jannah ba.

Maheer ma cikin dagewa da nasa zancen yace

"No Ammar bazai yiyu ba,ba lallai sai kayi karatun ne zaa samu yansa akeso ba bama fatan ma har ka kammala karatun baa samu yanda akeso ba"

Hayaniya ce take neman tashi a tsakaninsu duk da Maheer din yana gaban Ammar din sosai amma Ammar sam baida niyar fasawa sbd jin yake ko bayan rasuwar Mum dinsa tabbas yanason karantar ciwon da yayi ajalinta sbd yaji irin azabar data shiga a lokacin jinyarta da yanaji yana gani sedai ya kalleta a kwance bata cewa komai ciwone kadai yake cinta bata ko iya Hayaniyar azaba.
Hakama a yanzu da jannah take cikin irin wannan yanayin babu wanda yasan abinda take ji sai Allah daya doro mata ciwon dan haka koda zai rasata itama yanason sanin komai akan ciwon sbd kaucewa rasa wani a agaba.

Dad shiru yayi yana sauraronsu kansa na sarawa yana shiga nasa tinanin maganar kowannensu sbd idan har suna son fita clean kaman yanda Maheer ke cewa dole sai Ammar ya shiga ciki dan kada doctors din dazasuyi amfani dasu suyi musu wata hanyar dragging nasu dan haka duka biyun zasuyi,

Ammar zaiyi karatu amma ba anan qasar ba hakama duniya bazata san asalin professional dinsa ba.

Shiru sukai jin abinda dad din ya fada

Maheer shiru yayi yana juya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? zancen Ammar kuwa bai damu da komaiba idan har zai samu abinda yakeso.

Ammar baima tsaya jin wani sabon zancen ba ya fice daga palon dauke da laptop dinsa yana fidda wayarsa dan waya.

Maheer dad ya kalla wanda ya riga yayi maganarsa dan haka babu damar cewa komai.

Shima miqewa yayi zai fice

Dad yace

"Ka tabbata an samar masa admission da komai a taqaice batareda bude identity dinsa sosaiba"

Numfashi ya sauke a hankali kafin yace

"Yes Dad" ya juya ya fice yana fidda wayarsa shima dan saka kira.


A tsakaninsu su uku aka bar zancen Mimi da saleem basu sani ba sai Daddy mahmoud wanda ya karbi ragamar karatun na Ammar yace Maheer yabar masa komai.

Mimi tin daga lokacin bata sake sanin komai akan ciwon jannah ba sedai idan ciwon ya tashi ayita fama ana lallabawa harta dawo daidai.

An sakata a waiting list na neman donors a qasashe daban daban duk da sun zuba wasu irin kudi sun saki akan duk inda suka samu a riga basu sbd akwai wainda suke gabansu duk da ba yawa amma samun ne yakeda wuya sbd da yawa suna rasuwa ne batareda sun samu donors ba wanda ciwon kaddara ne ba kowane yake tashi ba samun donors na zuciya abu ne me tsananin wuya da hadari.

A bangarenta ita jannah din ahankali ahankali ta tashi daga yarinya me walwala da farin ciki ta koma yarinyar datake rayuwar nutsuwar jiran cikar kwanakinta da rashin walwala hakama ta koma shiru shiru kwata kwata bata iya hayaniya ko sakewa a cikin mutane,

Wani irin tsaro me karfin gaske ake bata sbd koina tana iya collapsing shiyasa a duk inda zaa kaita cikin tsaro take babu daga kafa,
Nurse aka daukan mata wadda duk inda zata tare suke tafiya,

Damuwa da rashin walwalan datake ciki wanda ya sauya rayuwarta kwata kwata ya saka ciwon yake yawan tasar mata yakuma fara nunawa duniya sbd ta qanqance kwata kwata bata girma ko qara jiki sai haske takeyi wanda hakan ya daga hankalim familyn suka sake duqufa a gurin neman donors tako ina amma babu labari.

Ahankali ahankali aka ta dena zuwa school sbd bazata iya ba sunaji suna gani aka tattara karatunta aka ajiye bata fita koina hakama kwata kwata sun boye ciwonta da matsalarta ga duniya iya doctors nasu ne kadai suka sani sai nurse dinta saisu family.

Rayuwarta ta tashi daga yar gata ta koma abar tausayi sbd karatu malamai aka daukan mata a gida ake zuwa koyar da ita shi shima baa wani jimawa ake bari sbd yawan gajiya datakeyi.

A bangaren Ammar kuwa yana india yana karatu sosai bayaji baya gani ya tattara komai ya ajiye karatun yakeyi sosai ba wasa ya duqufa gashi da qwaqwalwa me gashi kuma ya qwallafa rai dai ya zamana yana samun haske a karatun nasa,

Saleem Zad ma yana makaranta yana karatu dan haka sai ya zamana gidan daga Mimi saisu dad ne suka rage suna kulawa da jannah din wadda kallanta kadai yake karya zuciyoyinsu.

Maheer sosai ya dage yana kulawa sa companies dinsu yana bin every step na dad da daddy mahmoud wanda yake yawan zuwa duba jannah.

A Nigeria

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login