Showing 69001 words to 72000 words out of 81012 words

Chapter 24 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

197

da fuskanta a lokacinda ya wuceta batareda yasan da akwaita bama,

A rayuwarta kaf tinda ta taso bata samun kanta a inda aka taba nuna baasan da existence nataba,

Idan baa kulata da bata kulawa tareda nuna mata mahimmanci ba sbd Sunan familynta to zaayi sbd dukiyar datake dashi kokuma sbd kyau da daukan ido datake dashi amma a karo na biyu an nuna baama san da matsayinta n yar adamba kuma duka daga mutum daya.

Tsananta bugawa zuciyarta keyi hakama ta kasa juyowa ta kalli bayanta da dukkaninsu suka nufa dan bin bayansa zuwa ga doctor.


Muryansa daya ambaci sunan doctor dashine a wani irin nutsuwa ya saka numfashinta fita da wani irin tsananin sanyi daya sakata juyowa ahankali sedai ta kasa kallansa sbd yanda zuciyarta ke bugawa.

Juyawa tayi tabar gurin tana fitowa harabar gurin sbd jin tai tana suffocating.

Tana ji wayarta na ringing kuma tasan Ammar Zad ne amma bata iya dauka sbd nunfashinta toshewa yake haka kawai sbd bugawan da zuciyarta keyi.

Ringing wayar taci gaba dayi amma sam bata iya ko dauko wayar daga handbag dinta.

Taxi ta tare ta fada tabar asibitin ta koma saloon sbd motarta nacan ta baro.


Doctor kuwa kallan AZIZ din yayi yana sauke ajiyar zuciya me tsananin sanyi da nutsuwar abinda yake son fada masa kafin ya bude baki yace

"Muna saka ran zata farfado kowane time sedai a abinda muka bincika ya kawo mata collapsing shine ta samu bugawan zuciyan da yayi triggering matsalan datake dashi a zuciyanta wanda muna jiran fitowan sakamakon duka binciken da muka fara yi mata na dan abinda muka gani tukuna.""

Shiru gurin ya dauka sbd babu wanda ya motsa a cikinsu kallan likitan suke kamar basu fahimci abinda ya fadan ba dan haka ya kallesu shima likitan daya bayan daya tukuna ya tsayar da kallansa akan AZIZ da shima bayanin yake buqatan sake ji sbd a lamarin daya shafi iyalinsa yanason a ringa masa dalla dalla.

Ganin hakan dr ya sauke ajiyar zuciya yace

"Mun dan gano tanada matsala a zuciyarta sbd yanayin bugun zuciyar nata da muka duba vayan dawowansa ba bugun zuciya bane na cikakkiyar lafiyayya,
Bai taba bayyana va sai yanzu data samu bugun zuciyan dayayi munin daya bayyanarda ciwon gaba daya,
Amma muna jiran sauran result da kuma wainda zamuyi mata dan tabbatarda komai"

Hawaye ne masu tsananin zafi suka tsinkewa Fiddausi suna gangarowa akan fuskanta tayi baya tana komawa nesa dasu ta zauna tana cusa kanta cikin kafafunta.

Mama kuwa gaba daya bata gane turancinba dan haka sayd da AY din take kalla tana jiran reaction dinsu ya bayyanar mata lafiya ko ba lafiya ba.

Sayd wani irin nauyi ne ya danne kirjinsa da daci dayake gauraye bakinsa gaba daya idanuwansa na sauyawa sedai bai bari hakan ya bayyanaba ya danne tareda dagowa ya kalli AZIZ AY LIMBA wanda kafafunsa suka so kasa daukansa duk jarumtarsa.

Saurin taresa mama da sayd din sukai tare ya kasa dago idanuwansa ya kalli ko dayansu sbd yanda sukai jajir a take cikeda mafi girman 'dacin zuciya da wani irin nauyin daya danne kirjinsa da babu komai a cikinsa sai fili da tarin quncin daya taso a cikinsa.

Kujeran aka kawo masa da sauri ya zauna har lokacin bai iya dagowa ba bare iya cewa komai.

Sayd ne ya kalli dr din da jajayen idanuwansa da suka sauya sosai shima sbd su bazaka iya controlling nasu ba ya bude baki yana kokarin daidaita kansa yace

"Ok dr zamu jira results din da duka sauran bayanan,thank you"

Juyawa dr yayi ya koma ciki tareda nurse data fito kiransa.

Shiru gurin yayi babu wanda ya iya magana sai sayd da mama take sake tambayar ayi mata bayanin meya samu Falaq din sbd itama tin bata jiba ganin yanayinsu ya sakata jin ciwon zuciyarta na neman tasowa dan kirjinta toshewa yafara yi fargaba na shigarta me girma.

A taqaice sayd yayi mata bayanin abinda aka fadan yana dorawa da kada ta damu insha Allah khairan.

Duk yanda taso daurewa kasawa tayi kirjinta ciwo yake mata dan haka Fiddausi dake kuka sayd ya saka ta kawowa maman ruwa ya bata yana cewa nurses su kira doctor ya dubata.

Yanda ya zauna baice komaiba shiru yayi sukaci gaba da zaman jira.


Sallah sukaje sukai suka dawo cigaba da jira amma ba wani zance karshe dai an fito da falaq din zuwa vip room dayake can sama dan haka suka koma can.

Shiru dakin babu maganar komai sbd uban gayyar baicewa kowa komaiba har lokacin
farfadowan falaq din yake jiran gani tukuna har doctors din ya samu magana dasu kafin su wainda suke tareda ita da abinda ya faru.


Mama dai dole aka maidata gida sbd duk ta rikice jikin nata ya tashi dan haka gida aka maidata gida tareda Fiddausi ma da nurse da sayd ya daukan mata.

AZIZ dinne ya kwana a asibitin a zaune sai sayd da shi duk inda ko inuwar AZIZ take yana nan.

Guraren 8 na safe ta farka cikin tsananin sanyi da rashin walwala ta ciwon daya sauyata a lokaci daya.

Tana bude idanuwanta akan Daddynta ta fara saukesu hawaye masu dumi suka gangaro mata ta gefen fuskanta ta bude baki Ahankali tace

"BestDaddy"

Har cikin ransa yaji saukan sanyin muryanta wani irin daci da qunci yafara cike koina a zuciyarsa ya bude idanuwansa da suka kasa komawa daidai ya zuba mata yana tayar da ita zaune ahankali yana dora hannunsa akan fuskanta ya shafa ya bude baki da muryansa me nutsuwa yace

"Hey Falaq Aziz limba,how are you feeling?

Wasu hawayen ne suka gangaro mata ya ciro handkerchief dinsa yana goge mata ahankali yace

"Yaya dai?kina jin ciwo ne?
Where?a aina?

Kwantawa tayi jikinsa tana girgiza masa kai alaman batajin ciwo koina.

Dr ne ya shigo ya qara dubata dakyau kafin yace zuwa anjima ma zasu iya tafiya gida ba damuwa ko matsala bane.

Angama dube dube da sauran duka test da full checkup da AZIZ yace ayi mata sbd yanason a bayyane masa komai daya danganci abinda yake damunta komai yanason a bincika a sanar masa zai nema mata lafiya indai Allah ya yadda ta samu lafiyar koda zai rasa komai daya mallaka.

Koda suka dawo gida gabaki daya babu wata walwala ko haske ko kadan a tattare dashi suma duka gidan jikin kowa a mace yake sedai sbd falaq din su Fiddausi da mama suka sake sunata kulawa da ita da wasa dan ta sake kuma tafara sakewan sbd rashin qarfine kawai na wuni da kwana a kwance yake Damunta sai kuma asalin weakness da ciwon yake sakarwa meshi datake ji.


Doctors sun sanar dashi results da binciken duka suna kammaluwa zasu kirasa yazo ayi masa bayanin komai dan haka duka schedules da ayyukansa na wannan lokacin ya saka sayd yayi cancelling nasu ya bawa falaq time dinsa sosai wanda hakan ya sakata komawa daidai rigimarta da komai ya dawo musamman dataga mama ta dena mata fada dan haka murna ta ringa yi da ciwon datai.

Ryan kuwa tini ya sallamesa aka daukan mata wani drivern bayan an sanar da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????shi daga lokacinda yayi wani gangancin da ita a mota ya gama aikin.

Shi da Sayd ne a cikin damuwa sosai akan tinanin ciwon nata wanda basu gama sanin yaya yakeba dan haka koyaushe cikin jiran kiran doctors yake hakama sayd Ciwone yake cinsa na tsakanin Uba da 'ya tinda aka fada ciwon sedai kawaicinsa da yanda yabarwa AY ita bai nuna damuwarsa a fili ba dan haka ya fara bibiyan bayanan ciwon zuciya da matsalolinta.

Ganin hakan sai mama ma suka nuna mata ba wani damuwa bane falaq will be ok insha Allah,

Da wannan maman ta sake itama ta koma yanda take.

Tinda ya taso bayan rasuwar mahaifinsa zuciyarsa tafara bushewa daga mutane da lamarin duniya,
Ya rasa Mahaifiyarsa zuciyarsa ta karbi hakan cikeda jarumta da taurin zuciyar daya reni qanwarsa dashi,
Ya rasa Ummitah dayafi so a duniyarsa fiyeda komai da kowa zuciyarsa ta rasa duk wani emotions daya wuce na falaq,

Ba masu fada ba shi kansa yasan zuciyarsa a bushe take shiyasa a duniyar tycoons ake kiransa da monster amma baisan meyasa yakejin zuciyarsa na neman karyewa akan ciwon dayake tafe ga 'yarsa daya tak da itace kuzarin datake riqesa daga collapsing a duk lokacinda rashin Mahaifiyarta ke neman illata kwakwalwa da tinaninsa tareda jinsa da ganinsa.

Rufe idanuwansa yayi Ahankali yana hadiye abinda yake cikeda zuciya da kirjinsa.

Sayd ne yai knocking ya bude kofar palon y shigo a natse yazo gabansa ya tsaya cikin girmamawa da nutsuwa yace

"Hospital sun kira the results are out da komaima"

Bude idanuwan yayi Ahankali tareda zubasu akan sayd din wanda ya sauke nasa idanuwan.

Shiru gurin y dauk kafin ya miqe yana daukan wayarsa dake gefensa yana cewa

"Lets go"

Bayansa sayd yabiyo yana zuwa inda keys din motocin gidan yake ya dauko key yana biyosa da sauri.

Mota suka shiga zuwa asibitin batareda kowa yayi magana a motarba har suka isa.

Suna isa kai tsaye office din dr A Raheem suka nufa wanda shine babba gaba daya a asibitin suna isowa shine da kansa ya budewa AZIZ din kofar shiga yana masa barka da zuwa.

Amsawa yayi yana gaisawa da doctors biyu dake dakin wainda manyan neurologist ne wanda sune zasuyi masa bayanin duk abinda ya shafi ciwon yarsa.

Shiru office din yayi bayan Dr Raheem ya gabatar masa dasu fara koro bayaninsa yayi cikin tsananin nutsuwa.

"Mr LIMBA kaman yanda aka fara sanar da kai tabbas 'yarka na dauke da ciwon rashin qwarin zuciya wanda dashi tazo duniya sedai baya nunawa sbd the more tana girma the more yake kokarin fara bayyanarda kansa,

A yanzu ya bayyana ne sakamakon shock ko mummunan bugawan zuciyar data samu,
Ciwone chances din warkewansa yake 20%
Zaici gaba ahankali ahankali zuwa lokacinda zuciyarta zata buqaci heart transplant maana dashen zuciya kafin tata ta iya dakatawa,

Ciwon wasu yakan zo musu da rami ne a zuciya kaman hole haka".... ya fada yana kunna musu qatuwar screen din dake office din yana nuna musu yanda ciwon yake.
#MAMUH



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
37
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga? jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

********
Screen Sayd ya zubawa idanuwansa yana kallan yanda ake nuna musu cutar take a zuciyar dan adam.

AY idanuwansa da sukai jajir har suna radadi ya zubawa dr din kunnuwansa na ji masa mummunan labarin dayafi rasa komai da komai daya mallaka muni.

Dr kuwa cigaba yayi da cewa

"Zaa dorata akan activities da zaa fara kiyayewa da dorata akai tin yanzu batareda an daga mata hankali tasan meyake damuntaba dan tayi qanqanta data san hakan kuma sbd Nata baiyi nisan da zaa cire rai ba sedai kuma bamusan abinda gaba zatai ba wadda idan har ankai stage din da baaso to sai anyi mata heart transplant din wanda samun donor shine abinda yakeda wuyar datafi komai a duniyar nan"

Hotuna da videos na yanda ake heart transplant ya kunna yana cigaba da musu bayani cikin kwantar musu da hankali da kokarin ganin ya fahimci komai tareda sanin ba wani abu ne me mugun tashin hankaliba sbd ciwonta baiyi nisa ko girman da zai gagaresuba insha Allah.

Sayd dagowa yai ahankali daga jinginen dayake yana saukar da idonsa da kyau akan hotinan dake yawo akan babban screen din na heart transplant da asalin tabon dayake bari a kirjin da duk aka cire zuciyar ko dasata.

Kasa dauke idanuwansa yayi daga hoton wanda ya saka kunnuwansa daukewa daga jin sautin bayanin da doctors keyi sbd mamaki me tsananin gaske da shock dayake neman shigarsa sbd sanin wannan shine irinsa sak a kirjin Ummitah wanda bai taba saninta dashi ba dan ko ranar da zaa kaita asibitin haihuwa shine ya saka mata kaya da kansa dan bazata iya ba kuma babu wannan dinkin a kirjinta sai bayan rasuwarta ya gansa.

Juyawa kansa ya farayi sedai kuka Cs akai mata aka ciro Falaq,
Ana cs na haihuwa a kirji ne??
Girgiza kansa yayi idanuwansa na sauyawa yana kokarin tina babu dinkin cs da akai mata a mararta.

Jin yayi ya dena gane komai kansa na yin dum..

Jajayen idanuwansa da suka sauya gaba daya a take ya kalli dr Raheem ya bude bakinsa muryansa a shaqe yace

"Dr a wane gefe na kirjin ake aikin?
A jikin dan adam akwai inda zaa iya masa tiyata a cire 'da bayan cikin?
Meye dinki a kirji kuma a bangaren hagu yake nufi??

Kallansa dr yayi yana mamakin tambayarsa
AY kuwa sam bayama cikin cikakkiyar hayyacinsa na fahimtar me Sayd din yake tambaya yana zaune shiru idanuwansa sunyi laushinda ayau zaka gane rauninsa a bayyane.

Cikin bude masa komai da kyau dr yace

"Babu inda ake iya cirewa mace baby bayan cikinta maana qasan cikinta wanda wasu ana yankan tsaye wasu kuma na kwance,amma idan har kana magana ne akan wannan yankan na setin zuciya wanda ya tafi daidai irin wannan da kake gani to idan a jikin rayayye ne akwai tabbacin antaba masa aiki a zuciyar, idan kuma matacce ne to tabbas shima anyi masa aikin ne a zuciya kokuma ma an cire zuciyarne tinda a macen yake"


Jiri ne ya dauki Sayd daga zaunen da yake sbd kansa kasa gane komai yai
Jin yake kamar bai taba zama aji karatu ba sbd jin yayi turancin ma kamar ya dena ganewa dan haka ya juyo idanuwansa da sukai nauyi sosai ya kalli AZIZ wanda shima kwata kwata jinsa yai qasa akan bayanan likitocin gameda ciwon daya bayyana lokaci daya a tattareda rayuwar yarsa wadda bayan kuruciya ma yanzu babu abinda zata gane a ciwon ko anmata bayani.....

"Innalillahi wainnna ilayhi rajiun,Ya salam"

Ya fada yana tallafe goshinsa da hannuwansa biyu idanuwansa na rufewa ya budesu tareda jimawa shiru kafin ya dago ya kalli kowannensu ya bude baki baki yayi musu godia tareda miqewa.

Sayd ma miqewan yayi baa hayyacinsa ba sbd yayi mugun zurfi da nisa da tinanin dayake sake toshe kansa.

Ta email akaiwa Sayd forwarding copies na results dinta da sauransu sbd duk inda zasu sauya ganin likita ko qasar ma zai zamana sunada record dinta.

Tafiya suke babu me magana hakama babu wanda yake cikin cikakkiyar hayyacinsa har suka isa mota suka shiga kowannensu yayi shiru.

Sayd kasa tada motar yayi sbd bayajin zai iya driving cikin daurewa ta juyo ya kalli LIMBA da babu abinda yake iya cewa sai yaji tsananin tausayinsa dan ganin rauninsa da karyan kowa ne yace ya gani.

Jin yayi jarumtarsa ta dawo dan shine tamkar bangon dayake taresa a duk lokacinda rauninsa ya taso dan haka yake koyaushe a shirye daya basa kariya koda shi zai rasa nasa ran sbd kaunar Ummitah data hadasu haduwa ta har abada.

Numfashi me sanyi da ciwo ya sauke yana dora hannunsa ya tada motar yana tattaro nutsuwa da karfin hali ya hau hanyar gida.

Tafiya ce ta damuwa da rashin haske ko kadan a cikinta sukai har suka isa gida..

Suna isa kai tsaye babu wanda ya gansa ya shige bangarensa ya rufe kansa sai alokacin yaji kirjinsa nai masa radadi da ciwon daya sakasa zubewa palo qasa yana dafe kirjinsa yana lumshe ido yana karban radadin sbd babu yanda zai iya dauresa.

Yana jiyo ihun falaq din da Fiddausi da dayar me aikinsu a baya suna wasan daya sakasa rintse idanuwansa yana jin inama shi Allah ya kaddarowa wannan ciwon ba Falaq ba sbd harko yaushe yana fatar kasancewa da Ummitah koda a fatalwa ne idan har zasu hadu.

Falaq ce jinin Ummitah daya rage masa a duniyar,
Falaq itace take rage ciwon radadin rashin mahaifiyarta daya bar zuciyarsa empty idan har ciwonta barazana ce ga rayuwarta da zata iya rasa zuciyar da itace rayuwar yaya zaiyi da wannan kaddarar da Allah daya kaddaro masa shi kadai ne zai kawo masa dauki...

Zuciya ce zata buqata idan lokaci yayi wanda ba aba bace da tarin dukiyarsa zata siya,
Meye amfanin kaf abinda ya mallaka idan har bazasu nemo masa abinda zai buqatan ba?


Falaq dake wasan ruwa da water guns dasu Fiddausi farin ciki kawai take jin kanta yana ciketa wasa sukeyi sosai batama san daddynta ya dawo ba kuma yana jiyota radadin zuciyarsa na qaruwa duk dariyarta ta shiga kunnuwansa sbd ahankali ahankali wannan farin cikin da dariyar zasu disashe daga rayuwarsu kenan.

Sai magrib suka dena wasan suka dawo ciki Fiddausi na janta daki ta sakar mata ruwan zafi sosai sbd sanyin da sukai wasa dashi karya kamata.

Cikin jallabiya milk me tsadar gaske ya fito fuskansa tayi fresh sbd wankan da yayi ya fiton,.

Fuskansa babu walwala ko kadan sedai sam fuskansa bata bayyanarda fushi,

Sayd ne shima ya fito sanyeda riga da wandon fendi masu haske suka nufi masallaci wanda saima anyi tafiya da mota ake zuwa.

Koda sukai sallan magrib basu dawoba a masallacin suka tsaya AZIZ din karatun AlQuran ya ringa yi har lokacin isha yayi akai sallah suka fito suka kamo hanyar zuwa gida.

A hanyar ne ya dan kalli Sayd din a natse kafin ya maida kallansa kan Wayarsa yace

"Kafin gobe a saka binciken qwararrun manyan likitocin zuciya na duniya gaba daya zan gansu"

"Yes AY" Sayd ya fada yana ciro wayarsa dan fara saka binciken.

Suna isowa gida ya nufo ciki yana sako kai falaq dake fitowa hanyar bedroom din mama da gudu tayo kansa tana murmushin farin cikin ganin halittar datafi mata kowa da komai tana cewa

"BestDaddy"

Rungumeta yayi yana sauke boyayyar ajiyar zuciya da wani lafiyayyar murmushi daya sakawa fuskansa wani irin sabon nutsuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login