Showing 72001 words to 75000 words out of 81012 words

Chapter 25 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

188

da kwarjinin gaske.

Sayd bai qaraso ba bedroom dinsa ya nufa yana wayoyi..

Yana gama wayar ipad dinsa da tinda suka dawo asibiti yake kai yana wani irin binciken dayake neman juyar masa da kai,

Gaba daya zarewa yake neman yi kawai daurewa yake sbd kada AZIZ yasan komai akan abinda baida tabbaci amma kuma ya tabbatarda dinkin kirjin Ummitah sabo ne kuma a asibitin data haihu ta samesa sbd ya sake tabbatar da cewan ranar da zasu tafi da ita koda ya saka mata kaya a jikinta babu raunin komai a jikinta bare dinki,

Kuma a yanzu bayan dawowansu ya rufe kansa a daki ya kira likitocin duniya sunfi goma zance daya suke basa akan abinda dr Raheem ya fada baa taba aikin komai a kirji kuma bangaren hagu saina zuciya hakama indai mace ta haihu babu alamar tiyata a qasan cikinta koda daga gefe ne to da kanta ta haihu ba cs akai mataba.

Dafe kansa yayi dayake juyawa yana neman zare masa idanuwansa sukai jajir,

A ranar da aka shiga cs da Ummitah babu kowa a bangaren kaman yanda babu ko hayaniya alamar kebantaccen guri ne dayake nuna alama da vip area ne na asibitin,
AZIZ baisan suna meyake faruwa ba bare yasan asibitin dasuke bare yasa a basu special treatment hakama Alh Saad baisan suna asibiti a lokacin ba sbd basu tsaya sanar da kowa ba sbd tashin hankali,,,,to meyesa aka kaisu Vip area din????

Ko sisinsu baa karba ba idan ya tina harsuka bar asibitin da gawar Ummitah........


Miqewa yai da sauri ya nufi windon dakinsa ya bude iska ta daki fuskansa ya rintse idanuwansa sbd sarqewa numfashinsa keyi yana neman zaucewa...

Iska ya shaqa numfashinsa ya dan dawo daidai ya dawo da sauri ya wafci ipad dinsa yana sake bin bincikensa daki daki sedai yasan shedan ne kawai keson illata zuciyarsa da tinaninsa dan babu yanda zaayi ace anyiwa Ummitah aikin zuciya basu saniba,

Kodai dataje rasuwa ne sukai kokarin hana zuciyarsa dena aiki sukai mata aikin zuciyar??

Me wannan tinanin yakeyi a kansane??
Menene yake damunsa?
Wane irin jahilin tinani ne wannan yake yawo akansa??

Laptop dinsa dake bude itama yana binciken da ita ya duk ya rikice yayi da wayarsa yayi da ipad yayi Laptop ya kira waya duk ya neman haukacewa yake neman yi......

Cikin wani irin zafi ya dauki Laptop din ya bugata da qasa yana yana dafe kansa tareda zubewa a couch yana rintse idanuwansa hannuwansa na dan rawa.

Numfashi yake saukewa da karfi karfi yana sauka ahankali yana kokarin dawowa daidai hayyacinsa.

Bude idanuwansa da sukai ja yayi Ahankali yana dawowa da tinaninsa daidai..

Akan tinanin Abinda yake shirin faruwa tinaninsa ya tsaya da hankalinsa..

"Bayyanar ciwon falaq na Bayyanar musu abinda basu sani bane ko me?
Kaddara ce ko Haske ne yake buduwa a garesu??

Numfashi ya sauke tareda miqewa ya fada toilet yayi wanka kansa ya dan sake alokacin ne ya shirya ya fito sallan magrib da suka fita da LIMBA.

A yanzu da suka dawo kaman yanda AZIZ ya saka a binciko masa qwararrun doctors din zuciya shima zaiso ganawar dasu dan tabbatarwan karshe dan haka a cikin daren ya saka babban Pa dinsa da kusan daga shi sai Fahad din a kusanci da kulawa da duk kadarorin LIMBA yace zuwa gobe a hado masa list na best qwararrun cardiologist da bayanansu ya tiro masa.

"Yes boss by tomorrow insha Allah komai zai iso gareka"

Kashe wayarsa yayi yana kokarin daidaita kansa ya fito.

AZIZ na babban palon har lokacin zaune tareda Falaq dake jikinsa tana masa labari kala kala hadda na Ladyn datake ta magana akanta duk kwanakin wadda take cewa bata burgeta ko kadan amma ta kasa dena maganarta.

Tana ganin sayd gurinsa ta dawo tana fesa masa labarai kala kala yana biye mata shida mama sbd Daddynta kwata kwata baya cikin yanayi na iya biye mata sbd abinda yake cin zuciyarsa.

Abinci suka ci banda AY din wanda tea da dabino kawai yaci ya shige bayan Falaq tayi bacci ta shige kenan.
#MAMUH
#REVENGE
#LOVEANDHATRED
#LIMBAS
#ZADS


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
38
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494


*********
Koda ya shige bayan yayi shirin bacci cikin kayan bacci masu santsi zaunawa yayi yana lumshe idanuwansa Sanyin Ac na ratsasa ahankali sbd babu alamar bacci a tareda dashi tinani me zurfi da mutuwar jiki ya rufesa duk da bazai taba sakin kari ba akan ciwon nata zaiyi yawon duniya ya nema mata lafia sedai idan Allah yayi itama barinsa zatai tukuna amma yana roko da fatar Allah yasa ya fara barin duniya idan har Ciwon nan mai dauketa ne daga duniyar karta barsa..

Sayd kuwa saida yasha magani me karfin gaske kafin gaske kafin bacci ya iya daukansa.

Da asuba bayan sunyi sallah kowa ya koma bacci
Guraren 8 na safe wayar Sayd ta tadasa bacci kansa da yayi masa nauyi sosai sbd maganin daya sha ya daga yana bude idanuwansa daqyar ya kai hannu ya dauki wayar yana dorawa a kunnensa.

Fahad ne cikin girmmawa yace

"Goodmorning Boss,
Duka bayanan daka nema an hada na turo maka ka duba hotinansu da bayanansu tareda sunayensu suna nan"

"Ok,thanks zan duba yanzun nan,i will get back to you akan sauran bayanin"

Ok boss"

Kashe wayar yayi yana komawa bacci sbd koya duba babu abinda zai gane yanzu dan maganin dayasha bai sakasa ba ko kadan.



***********Ahankali ta tashi daga kwancen datake idanuwanta biyu ba bacci take ba ta jima da farkawa kawai tashin ne ta kasa sbd a macen da jikinta yake da tinanin fuskan data kasa gogewa daga idanuwanta,

Tinda ta dawo Nigeria ta rasa gane kanta da abinda ya maqale mata a tinani da ido wanda take ganin Shedan ne hakama tsananin ciwo da zafin hakan takeji sbd zuciyarta kwata kwata bata yadda tayi tinanin kowane namijin ba bayan Ammar Zad.

Numfashi me sanyi ta sauke ahankali tareda lumshe fararen idanuwanta ta budesu tana daukan wayarta ta qurawa hoton Ammar dayake gaban wayarta ido tareda Ambatar sunansa ahankali tace

"Ammar zad kai kadaine wanda zuciyar Jannah Zad ke so,
Kaine mijina,kaine farin ciki na,kaine abinda kawai nake buqata zuciyata ta kammala"

Rufe idanuwanta tayi ta bude tana ajiye wayar tareda ziro kafafunta qasa tana miqewa tsaye sanye da kayan bacci riga da wando masu kauri ta nufi toilet tana dafe zuciyarta dake bugawa ahankali tana jin kaman kalamanta ba daga zuciyar taya suka fito ba iya bakinta ne.

Numfashi me qarfi ta sauke tana qarasa shigewa toilet din dan fitar da tinanin komai a zuciyarta.

Brush tayi tana kallan fuskanta a jikin mirror wanda tayi fayau sbd tashinta kenan.

Tana gamawa zare kayan jikinta tayi tana qarasawa bathtub ta kunna ruwan dumi ta shige.

Ta jima kafin ta fito daure da blue towel ta nufi wayarta dake ringing ta duba taga sunan MAN dinta ne dan haka ta dauka tana zaunawa gaban mirror da wata muryan data sakasa ajiye Ipad din datake hannunsa yana duba sako ya ajiye akan table dayake gabansa na bedroom dinsa yana jinginar da bayansa muryan na kashe kowane irin kuzarin jikinsa da zuciyarsa yace

"How are you Love??
Kin tashi?

Numfashi me sanyi ta sauke tana kallan fuskanta tace

"Goodmorning Love,
Na tashi ina shiryawa am coming out for breakfast"

"Ok take your time and kinsha maganinki kuwa?

"Yes love" tafada tana kallan drawer din da maganinta suke ciki.

Aje wayar sukai yana cewa ta kula gurin shiryawa kada ta wahalar da kanta.

Shiryawa ta fara yi a natse tana gamawa ta saka free skirt da riga na Dior da scarf ta ziro flat versace ta fito riqe da wayarta wani lafiyayyan qamshi na tashi a jikinta na woodyLeather.

Kai tsaye palon Dad ta nufa wanda yake palon zaune yana waya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tareda manyanci da Duniya data gama tsaya masa.

Yana ganinta ya bude mata hannunsa daya ta qaraso ta zauna kusa dashi tana rungume hannunsa a jikinta ta bude baki cikin tsananin kaunarsa da sakewan datake tsakaninsu duka familyn tace

"Goodmorning BestDad" (hakan itama take kiransa tin tana qaramarta)

Murmushin farin cikin ganinta kafai da yayi ya fara sakewa kafin ya kashe wayar dayake yace

"Morning My Angel,
Kin tashi lafiya?
Yaya maganinki kinsha kuwa?

"Nasha kaima kasha naka Bdad?

Amsawa yayi da cewa yasha yana murmushin jin dadi..

Shigowan Mimi ne ya sakata sake lafewa gefensa tana murmushi tace

"Goodmorning Mimi,
Kin tashi lfy?

Qarasowa tayi tana zaunawa gefen dad din tace

"Lfy kalau,kinsha maganinki?

Yes" tace sbd tasan kowa a familyn babu ranar da babu wanda baya tambayar tasha maganinta.

Ko gama magana da Mimi bataiba qamshin Ammar yafara shiga hancinta ta dago idanuwanta ta zubawa kofar sai gashi ya sako kai cikin wani irin class da nutsuwa sanyeda Ash balmains.

Maheer ne shima ya sako kai tareda Anny tana gafensa kowannensu yana fidda nasa kalan qamshin na shegun designer Turaren dasuke amfani dasu masu tsadan gaske.

Akan Ammar idanuwanta suke tana jifansa da kallan daya sakasa zuba mata nasa idanuwan yana jin idan da ya rasata a bayan da yanzu baya duniyar dan wlh bazai iya rayuwa babuta,

Wani irin masifaffen sonta ne Allah ya halitta masa a zuciya da kirjinsa da ko tinanin rasata kadai idan yayi yake qarewa a hannun therapist dinsa sbd zarewa yakeyi gaba daya da iya wannan tunanin dan hakanne yasa yariga yasan babu rashinta a kundinsa saidai idan karshen tasa rayuwar ne yazo dan hakan ne bai taba jin komaiba a rayukan da suka hallakar dan nema mata zuciyar datake bugawa a kirjinta hakama da yau zaa ce wannan dinma ta gaza to tabbas zai koma farautan zuciyoyin mutane matacci da rayayyu dan nema mata lafiya kawai.


Gefen Miminsa ya qarasa ya zauna yana kallan dad da murmushi da farin ciki a fuskansa yace

"Goodmorning Dad"

Amsawa dad yayi yana amsa gaisuwan Maheer shima kafin ta Anny wadda itama ta zauna gefen mijinta.

Saleem ne ya shigo karshe yana waya fuskansa gabaki daya ba walwala.

Kallansa sukai ganin yanayinsa ya saka yana gama wayar Maheer ya kallesa yace

"Issue din Approval na wanda kakeson ne ko yaya??

Wayarsa ga ajiye gefensa yana sauke numfashi me zafin gaske yace

"Yes,sunata rejecting din proposal dina batareda ma an tsaya andubaba"

Da mamaki gabaki dayansu suka kallesa sbd jin wai rejection ga ZAADENs.

Cikin rashin Bawa zancen mahimmanci sbd yasan bama abu bane me yiyuwa rejecting zaadens dad ya kalli Maheer yace

"Handle the situation,koma waye ka tabbatar masa da yasan Zaadens ne zasuyi masa alfarma"


Maheer saleem din ya kalla shima cikin hana ransa baci sbd baya buqatan sakawa kansa ciwo akan mutanen da basuda mahimmanci a taqaice yace

"Wats the name???

"LIMBAs EMwrld"

Ammar ne ya dago ahankali ya kalli saleem din hakama Dad da shi kansa Maheer din sbd sun san Kamfanin A suna sbd kusan duka abokan businesses nasu suna Yi dashi sosai hakama yana cikin masu kudin dasuke gogawa dasu duk da basu taba sanin junaba amma sunsan sunan hakama shima dole yasan sunansu.

"AZIZ AY LIMBA the lucky Monster" Maheer ya fada yana kallan Saleem din.


Yes" ya fada yana jin daci sbd LIMBAn kadaine wanda zai basu abinda sukeso a sabon business din nasu wanda yanaqi dole sedai suyi da qananun kamfani wanda ba girmasu bane hakama ci bayane garesu da kuma bazasu habbaku akaiba yanda sukeso.

Ammar dayaji sunan Har cikin zuciyarsa kallan Maheer yayi yace

"Banajin business dashi zaiyi amfani sbd yafara da zafin kai,
Waye shi?" Ya tambaya yana kallan Saleem wanda ya dauki wayarsa daya ajiye gefensa ya nemo bayanin komai akan AY din dayake dashi sbd sosai yake bibiyarsa sbd shi ba qaramin aiki yakeson yayi a tareda Limban ba tamkar burine dayakeson cikawa na aiki dashi.

Horonsa ne yana sanye da Fararen kaya da fcap zaune a kujera da qaramin table gefensa Asalin kyansa da kwarjininsa me tsanani a bayyane suke ko a hoton da alama gurin golf ne yake sbd kayan dayake jikiksa ya nuna hakan.

Maheer kallo daya yayi masa ya karanto izzar data sakasa rejecting Zadeens dan haka ko bayanin komai bai tsaya karantawa ba yace da kansa zai gansa.

Dad kuwa kallo daya yayi masa ya dauke kai sbd maheer zaiji da komai sedai yana hango zafin kai a tattarda da aura dinsa.

Ammar ne ya zubawa AY din idanuwansa yana kallansa...

Wani irin yanayi na qi da makamancinsa yaji yana shigarsa akansa,
Dauke idanuwansa yayi akai yana sake qaramin tsokin inda AY din ya samu guts na rejecting dinsu.

Jannah kuwa bisa ga rashin sani idanuwanta suka sauka akan fuskansa wani irin sanyi taji yana sauka jikinta tana zuba masa idanuwa zuciyar na harbawa ahankali cikin sanyi da nutsuwa.

"AZIZ LIMBA" sunan ya sake shiga kanta ahankali tana sauke numfashi tareda dauke idanuwanta daga fuskansa tana maidawa kan Ammar ta zuba masa ido tana kalla jikinta na mutuwa.

Jin idanuwansa akanta suna magana dasu dad ya sanyashi kallanta

Murmushi me sanyi da kyau ta sakar masa tana bude bakinta batareda sautiba ta motsasu da cewa

"My love"

Murmushi ya sakar mata zuciyarsa na wankewa daga duka takaicin Limban daya cikesa.

Basu fito breakfast ba sai bayan kusan mintina suka nufi dining room tana gefen Dad ammar na gefen Mimi Anny kuwa tana gefen mijinta tana tinanin inda ta taba ganin fuskan AZIZ AY LIMBA dinnan dasuka gani yanzu,

Tabbas ta taba ganinsa ko wani me kama dashi duk da kamannin suna bace mata amma dai tasan ta taba gani sedai kuma ta manta kokuma kila shi dinne ta taba ganin hotonsa a media ko tv.

Makeken dining me kujeru da yawa an cikesa da abinci kusan kala hudu sbd kowa da abinda yafi buqatan breakfast dashi.

Maheer sun rigasa zama sbd saida yayi waya da PA dinsa akan yanason bayanin komai akan AZIZ AY LIMBA kuma yana son shi da shi su hadu akan business din Zadeens.

Angama yace masa yana fara abinda aka sakasa,
Shi kuma Maheer wayar ya kashe yana zaunawa dining sbd tabbas yanason haduwa da AZIZ LIMBA sbd yaga iya power din dayake dashi dan su sune power din da kansu.


************
Sayd sai karfe goma da mintina ya farka daga baccinsa kansa yayi masa tsananin nauyi ya bude idanuwansa yana tashi zaune kansa na sake masa nauyi sosai.

Time ya kalla ya sauke ajiyar zuciya tareda miqa hannunsa ya dauki wayarsa yaga misscalls da yawa dan haka ya miqe da sauri duk da AY bazai fita aiki ba hutu yake amma shi akwai abubuwa da yawa dazai handling ciki harda top qwararrun cardiologist da aka hado zai gabatarwa AZIZ din.

Ipad dinsa ya dauka dan duba sakon da Fahad ya turo akan binciken..

Kunnawa yayi tareda shiga sakon kai tsaye..

Hoton DR ABRAHAM SMITH ne abu na farko daya fara bayyana akan screen din tareda sunansa da manyan baqi tareda bayaninsa da qwarewansa.........

Kansa da bai gama warwarewa bane yaji yayi masa dum kafafunsa suka kasa daukansa ya zube qasa a gurfane yana riqe ipad din datake kokarin subuce masa yana qura idanuwansa da suka bude gaba daya baccin cikinsu na fita sbd Shin babban Likitan da yayi aikin Ummitah dan bazai manta fuskansa ba abada dashi da sauran likitocin biyu daya dr Nicolas dayan dr ismail.....

Rawa hannuwansa suka fara yana kasa riqe Ipad din ya lalubo wayarsa ya saka kiran Fahad.

Yana dauka ya jefa masa tambayar

"DR ABRAHAM SMITH likitan zuciya ne kokuwa gynecologist?????

"Babban likitan Zuciya ne kuma kwararre shine top a list dinmu,
Yayi aiki a Nigeria tsawon lokaci kafin ya koma Greece,bai taba zama gynecologist ba akwai dansa Dr Nico yana cikin list din shima cardiologist ne kwararre so......

Datse wayar Sayd yayi wayar na subuce masa daga hannu kansa na juyawa hakama zuciyarsa bugawa takeyi kaman zata faso kirjinsa ta fito......

Fuskan Dr Abraham ya qurawa idanuwansa da ganinsu ke ragewa yana fara ganin dishi dishi harya dena ganin komai ya zube a gurin.
#MAMUH
#THE ZAADENS
#THE LIMBA
#BILLIONAIRESWAR/REVENGE
#CRAZYLOVE
#HEARTACHE
#AZIZ LIMBA
#JANNAH ZAD
#AMMAR ZAD
#FALAQ
#LOVE AND HATRED



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.

https://chat.whatsapp.com/IyDlSVdw1rDIlCNNQMel68

Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494


***************
Neman toshewa kirjinsa yakeyi yana jin numfashinsa na neman yankewa idanuwansa sukai jajir ya daga hannunsa daqyar baya gani sosai ya kamo wayarsa dake yashe a qasa ya saka kiran fahad sedai kafin fahad din ya dauka numfashinsa ya sarke a gurin.

Fahad na dauka cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login