Showing 48001 words to 51000 words out of 81012 words

Chapter 17 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

203

daga karshe dole yaga dr karshe admitting nasa akai likita yace stress ne da damuwa kawai daya sakawa kansa.

Sosai ya kwana asibitin wanda ya saka likita hanasa ko taba wayoyinsa aka kashesu.

Amma hakan kusan hana zuciyarsa samun nutsuwa yayi wanda yake jin yana rasa nutsuwarsa da hankalinsa kwata kwata dole doctors suka basa wayarsa dan yayi magana da familynsa dan samun nutsuwa.

Wayarce gabaki daya ta kasa samuwa yanda yakeso sbd a cikin mutum uku da suke familynsa kwata kwata ya kasa jin ko daya dan haka kai tsaye ya nemo numbern drivernsa Latif wanda yake bayerabe ya saka kira.

Kiran na shigowa wayar latif gabansa yayi mummunan faduwa sbd bai kira yayi masa gaisuwaba sbd tsoro da tausayin halinda yake ciki jin rasuwar Sanyin idaniyarsa dama su gaba daya tinda suna sonsa dole sike kaunar Ummitan sosai.

Tana gap da katsewa ya daga kiran cikin tsananin sanyin muryan data saka ABDULAZIZ din sauke ajiyar zuciya.

Gaidasa Latif ya fara cikeda girmamawa yana rasa ta inda zai fara masa gaisuwa.

Kafin ya amsa gaisuwarsa kai tsaye da muryansa datai kauri kirjinsa a toshe da bacin ran yanda kowa a gida wayarsa ta koma kaman batada amfani a taqaice yacewa latif

"Inason magana da mama,Sayyid or Ummitah ka kaiwa daya daga cikinsu wayar........

Tsabar rudewa Latif da yarensa yace

"Sir you say???

Cikin hade fushinsa yace

"Do i have to repeat wat i said??

Da sauri latif na qarasa ridewa ya nufi cikin gidan yana hada gumi yace

"Yes,no no sir"

Duk ya rikice ya rasa me zaice jin sunan Ummitah dan haka ya qara sauri zuwa cikin gidan yana godewa Allah dabaiyi saurin yi masa gaisuwaba yafara ji daga bakinsa..

Yana knocking kofa fiddausi dake palo tana hadawa Baby madara tanata kuka me qarfi ga mama tana sallah Sayyid ma yana masallaci ta taso ta bude kofar wanda ya bawa ABDULAZIZ saukan kukan babyn kai tsaye cikin kunnuwansa daya sakasa tashi ahankali daga zaunen dayake zuwa tsaye yana dago wayar daga kunnuwansa ya kalla ya sake mayarwa yayi shiru kukan babyn me qara yana shiga kunnuwansa sbd tana hannun Fiddausi data taso ta bude kofar tana kallan Latif daya miqa mata wayar da sauri muryansa har tana rawa yace

"Sir na son magana da Mama or oga Sayyid and......

Shiru yayi yana kallan babyn da sai alokacin ya tina da Sir din zaiji kukanta.

Fiddausi na jin abinda ya fada tayi baya tana qin amsar wayar ta juya da sauri dan kiran mama.

Hanata tafiya latif yayi yana gwale mata idon ta karba kada tai masa haka dan yasan yana saka wayar a kunnensa maigidan zai iya jeho masa kowace irin tambaya.

Fitowan mama tana idar da sallah batareda ta tsaya addua ba sbd kukan babyn ya saka latif saurin jeho qafa palon da sauri ya miqawa mama wayar tana amsa ya juya da sauri.

Fiddausi ma barin palon tayi jikinta a sanyaye.

Mama saida wayar ta shiga hannunta ta gane waye akai take qafafunta sukai sanyi daidai lokacin sayyid ya shigo palon hakama Babyn a lokacin ta sake fasa wani kuka me qarfi na jirirai sabuwar haihuwa ba kakkautawa wanda hake shiga kunnuwan ABDULAZIZ direct yana wucewa zuwa zuciyarsa da bugunta ya sauya ya kasa cewa komai sbd yanda yakejin kukan babyn har cikin tsakiyar zuciyarsa ya tabbatar masa da kukan babyn Ummitah ne.

Shiru dukkaninsu sukai har Sayyid wanda yaga sunan SIR LIMBA akan wayar hannun mama ya san shine take jikinsa yayi mugun mutuwa radadin zuciyarsa na dawowa sabo.

Shirun lokaci mai dan tsayi sukai kafin ya iya bude bakinsa da yayi masa nauyi jin bazasu ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fada masa komaiba bayan sunsan yaji kukan babyn da sauti me tsananin nutsuwa da sanyi yace

"Ummitah ta haihu ne???

Shiru sukai hawaye na gangarowa mama tana qanqame babyn jikinta.

Shiru ya dan yi yana jiran amsarta kafin ya sake cewa

"Ummitah kece?
Kin sauka dinne?

Kukane yake kokarin kwacewa mama ta miqawa Sayyid babyn wanda yaune ranar farko data shiga hannuwansa.

A tsananin taushin sautin dayake sake qara nauyin zuciyarsa yace

"Ummitah??

Kuka me qarfin gaske mama ta fashe dashi tana kasa riqewa sbd yanda yake ambatar Ummitan da bazata amsaba har abada sai lahira kila..


"Mama" ya furta cikin tsananin mamaki da sanyi yana cewa

"Mama kuna lafiya?
Lafiya kuwa?
Meyake faruwa ne wayoyinku basa tafiya?
Ummitah ta haihu dinne mama???


Maganganunsa kashe mama sukeyi kukanta na tsananta ta kasa cewa komai

Jin ya kasa jeho tarin tambayoyin dake kasheta cikin kuka mai ratsa zuciya da kashe jiki tace

"ABDULAZIZ kana buqatan dawowa,
Muna tsananin buqatanka a gida.....


Rintse idanuwansa yayi abinda yake ji yana fara fin karfinsa daga lokacinda take kukan daurewa kawai yakeyi dan haka cikin tsananin karfin hali da dauriya ya bude baki yace

"Mama zan aje duk abinda nake na dawo,
Ina Ummitah?zanyi magana da ita"

Sayyid na jin hakan ya juya yabar gurin rungume da babyn wadda tayi shiru a jikinsa tana sauke numfashin bacci da zata koma.

Mama shiru tayi ta kasa basa amsa kukanta na komawa sbd tsoron abinda batasan me zata fada masa ba.

Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke ahankali cikin sake nutsar da kansa yace

"Mama nace insha Allah duk abinda nake nabarsa zan dawo,
A kiramun Ummitah,
Kuma baki ban amsan haihuwan ba,
Ummitan na lafiya?yaya babyn itama lafiyanta kalau?
Ko akwai matsala ne mama??

A cikin wani azababben ciwon daya taso ya danne zuciyarta da sabon kukan data kasa riqewa tace

"ABDULAZIZ MUNYI MUMMUNAN RASHIN DA HAR ABADA BAZAMU WARKEBA DAGA GARESA"

#MAMUH
#AZIZ AY LIMBA
#JANNAH ZAADEN
#ZAADENS
#SAYYEED


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
26
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


*************
Shiru yayi yana gama sauroron bayaninta da bai gane inda ya nufa kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya bude baki da nutsuwa sautinsa na sanyaya yace

"Mama meya faru?
Me yake faruwa?

Kukan dayafi na baya ratsa zuciya takeyi sosai tana kasa bude idanuwanta kaman yana gabanta tana breaking tace

"Mun rasata gurin haihuwa......

Wani irin Numfashin daya saka maman kasa qarasawa ya sauke da wani irin sauti me tsananin nutsuwar son fahimtar abinda ya kasa fahimta yace

"Ita Ummitan???

Kasa amsawa tayi sbd kukan dayaci karfinta mara sauti.

Dif taji yaji kashe wayar batareda yace komaiba.

Wani mummunan jiri ne ya dibesa kafafunsa suka sare da karfi gwiwowinsa suka daki qasa da karfi wayar hannunsa na faduwa qasa.

Rawa hannuwansa suka dauka ya miqasu da sauri yana lalubar wayar hannunsa data fadi sbd ganinsa dayake kokarin daukewa da jinsa dab dif yake jin.

Yanda hannuwansa ke rawa sosai yasaka ya kasa samun inda wayar take duk da tana gabansa sam baya gani.

Kokarin kasa bugawa zuciyarsa keyi amma ya kasa barin hakan,

Hannuwansa ya saka ya murza idanuwansa da karfin daya kusan raunana kansa kafin ganinsa kadan ya dawo ya duba wayar da sauri ya dauka hannuwansa na tsananta rawar datake kokarin hana wayar tsayawa hannunsa.

Daqyar ya iya gano sunan Alh saad sbd rashin ganin da yake sake rufe idanuwansa kwata kwata.

Ringing din da wayar keyi duk daya tafiya yake da numfashinsa dayake fara sarkewa yana suffocating.

Alh saad cikin nutsuwa ya dauki wayar tareda sallama cikin mutuwar jiki sbd duk lokacinda Ko sunan ABDULAZIZ din yagani jikinsa ke mutuwa.

"Ummitah ta haihu??
Meya sameta?
Tana ina?
Inason magana da ita,No i want to See her on a Videocall,
Meyake faruwa,
Why are you quite?
Meyasa mama ke kuka?
Ina Ummitah.
Say something..........

Alh Saad bai zubarda hawaye a rasuwar Ummitah ba amma take yaji idanuwansa na kokarin cikowa da hawayen dake girgiza jarumtarsa da manyancinsa sbd yanda Yana jiyo wani irin mummunan breaking da ABDULAZIZ ke kokarin a muryansa,
Gabaki daya tamboyinsa baya hayyacinsa yake jehosu babu abinda yakeson ji bayan amsa daya.


Acan bangaren cikin sautin daya tabbatarwa da Alh saad jikin ABDULAZIZ din yai tsananin sanyi da wata qasqantacciyar murya yace

"Ta haihu?
Is she okay?
I really want to talk to her,
Am coming back tomorrow amma i cant without hearing from her,
Please,
Please......a cikin wani irin mummunan sauti me tsananin sanyi da rashin kuzari ko kadan ya ringa maimaita pls dinsa data saka Alh saad karasa karyewa ya sunkuyar da kansa yana shanye hawayensa ya bude baki shima a sanyaye cikin tsananin rashin kuzari yace

"ABDULAZIZ karka manta Duk mai zai dandana mutuwa,
Ka rasa iyayenka ka samu dangana a yanzu ma zaka dangana ne sbd Allah ya riga ya karbeta sbd lokacinta ne yayi,
Abinda ta haifa tananan Lafiya kalau ita kam sedai Mu bita da Add.....

Dif yaji wayar batareda ya qarasa maganar dayake ba,

Daga wayar yayi ya kalla yaga tabbas ta yanke,

Saka kiransa yayi da sauri yana miqewa daga zaunen dayake.

Ringing wayar takeyi harta yanke baa dagaba
Sake saka kiran yayi yana fatan ya dauka sedai harta kuma yankewa baa dagaba.

Cigaba yayi da kiran kaman mahaukaci shima yana fatar a daga amma baa daga dinba karshe ma shiru ta dena shiga kwata kwata.

Damuwa yaji duk ta cikasa sbd baisan irin damuwar da ABDULAZIZ din zai shigaba gashi bai tsaya sauraransaba bare ya kwantar masa da hankali duk da yasan babu abinda zai kwantar masa hankali a yanzu idan ba addua zasu duqufa yi masa ba.

Gaba daya zuciyarsa kasa nutsuwa tayi yaji hankalinsa yana kasa kwanciya dan haka ya dauki wayarsa ya kira Sayyid Wanda aka siyawa sabuwar babbar waya dal yana dauka Yace

"Sayyid Kunyi magana ne da ABDULAZIZ?

Numfashi Sayyid ya sauke ahankali kafin yace

"Yayi magana da mama dazu sedai basu gamaba ya kashe tace"

Numfashi Alh saad ya dauke yana sake shiga damuwa yace

"Inata kiransa baa dauka,
Waye ya sanar dashi??

Cikowa idanuwan Sayyid sukai da hawaye masu zafi yana kallan Babyn datake rungume jikinsa tayi bacci a sanyaye yace

"Babyn Ummitansa ce ta sanar dashi da kanta ta iso duniya...... qarasa maganar yayi hawayensa na sauka akan gefen fuskanta har saida ta dan motsa kadan.

Shiru Alh Saad yayi yana sake shiga damuwa da rashin nutsuwar zuciya yace

"Kukanta ya sanar dashi an haihu kenan??

Kasa magana Sayyid yayi sai daga baya yace "Eh"

"Sayyid kuyita kiransa a samu wani yayi magana dashi pls kaji"

"Ok insha Allah" Sayyid ya fada a sanyaye.

Kashe wayar Alh saad yayi take Sayyid din ya saka kiransa sedai ma ko tafiya batayi yana saka kiran kiran yake yankewa da kansa.

Ringa saka kiran yayi ba kakkautawa amma babu alamar ma kiran zai tafi.

Fitowa yayi ya bawa Fiddausi babyn ta goyata shi kuma ya fita yanata sake kiran Hamman zuciyarsa na tsananin jin son magana dashi sbd tinda Akai rasuwar haryanzu bakinsa da nasa bai haduba bayan yana buqatan jin muryan Hamman ko zai samu Sassaucin rashin Jinin Hamman da yayi.

Mama ya dawo ya sanarwa Baa samun ABDULAZIZ din dan haka itama ta dauko wayarta kowannensu yanata kira amma ba saa.

Har dare suna kiransa akai akai amma sam babu sauyi.

Da daddare mama da kanta ta shirya babyn a cikin kayan sanyi masu tsada da kyau ta kwantar da ita gefenta tareda Zuba mata idanuwanta tana tina ranar farkon haduwarta da Fatima Asalin mahaifiyarsu ABDULAZIZ din wanda tin daga lokacin kauna me karfi da tsafta a tsakaninsu.

Fatima ta tafi tabarta,
Inna ma ta tafi tabarta,
Ummitah ta tafi tabarsu itama tabar musu 'ya kaman yanda Fatima ta tafi tabar musu Ummitan tana qarama,

A yanzu batasan yaya zatai da ABDULAZIZ datasan duniyarsa ta rushe gabaki dayanta,
Yaushe zai samu farin Zamowa ahali daya daya rage a zuriar fatima,
A yanzuma zai sadaukar rayuwarsa ne gurin kulawa da tattali tareda ingata rayuwar 'yar da Ummitah tabar masa,
Yaushe zai samu rayuwar farin ciki da walwala kaman kowa??

A yanzu basusan halinda yake cikiba a can qasar dayake daya samu wannan mummunan labarin.

Hawaye ne sike gangaro mata ahankali ta gefen ido suna sauka akan pillon da kanta yake kai batareda ta dauke kallanta daga kan babyn wanda itama Sunan Fatimar ne sunanta sbd Shine Sunan da ABDULAZIZ yakeso fiyeda kowane suna kuma shine sunan dayace zaa sakawa Babyn daman idan an haifeta sbd Ummansa Fatima ce hakama Ummitansa Fatima ce dan haka a yanzu ma ga wata fatimar ya samu wadda tasan zai iya bada rayuwarsa akanta itama.


Sayyid kwana yayi yana kiran Hamman sbd gaba daya yaji shima bayajin nutsuwa tinda baya tareda su yasan yana can cikin mawuyacin mummunan halin dayafi duk wanda suka shiga baida wanda zai rungumesa ya rarrashesa bare quncin rasuwar Ummitah yana ninkuwa ne sbd ko gawarta bai samu gani ba bare janazah dinta wanda har abada bazai dena jin wannan radadinba a zuciyarsaba kuwa.


Shi kansa Alh Saad akai akai ya ringa sake kiran Amma ba bayanin komai.

Washe gari Sayyid duka yan gidan saida ya karbi wayarsu ya ringa kiran Hamman Amma sam duk abu daya ne batama alamar shiga take yankewa.

Haka suka wuni cikin damuwa da sanyin jiki suna nemansa babu haske ko kadan.

Washe gari ma hakan ce ta faru har aka sake kwana suna kan abu daya.

Alh Saad suka kira suka sanar masa ya kwantar musu hankali da cewan ABDULAZIZ din a ranar da sukai magana ya sanar dashi zai dawo a washe gari amma tinda an kwana biyu a sake basa kwana biyu a gani tukuna kila ya daga tafiyar ne sbd shock na rasuwar.

Hakura sukai suka zuba idanuwan dawowan nasa duk da hakan bawai sun dena kiran bane musamman Sayyid dayake jin yana neman sabuwar zarewa
Mama kuma kulawa da babyn yana dan hanata damun lokacin kanta ma sbd ga manyanci ne ga kula da jaririyar 'ya duk da ga Fiddausi tana kama mata sosai danma wani abin bata iyawa sedai Fiddausin tai mata.

Baba alhassan ne ranar da akai bakwai ya iso da manyan ragunansa guda biyu da na yankawa jaririyar suna.

Dayake ba wai hidimar farin ciki akeba yasaka addua kawai akai aka yanka mata Sunan FATIMAH kaman yanda sukasan ABDULAZIZ yakeda buri.

Koda Baba alhassan ya iso shima Alh Saad ya riga ya siya ragunan suna dan haka aka hada duka aka yanka akai sadaka sosai tareda yiwa mahifiyar babyn Addua dashi kansa ABDULAZIZ da basusan halinda yake ciki.

Baba alhassan bai komaba sbd ganin rayuwar qunci da 'dacin dasu Sayyid sukeyi gashi shima ya shiga tsoro da damuwar rashin ABDULAZIZ din dan haka ya fasa tafiya sai ansan halinda yake ciki.


*****Lamarin da tin suna lissafi har suka dena suga shiga mummunan damuwar datake take rashin da sukai sbd kwata kwata ba ABDULAZIZ ba labarinsa sun duqufa rokon Allah da sadaka,

Mama ta rame sosai ciwo yana neman rufe rayuwarta sbd damuwa da tinani,

Sayyid ma ya koma gabaki daya ko magana bayayi sosai daga daki sai masallaci dayake kusan wuni acan yana karatun Alqurani da adduar bayyanar ABDULAZIZ tareda fatar yana cikin koshin lafiya.

Baba alhassan ma gida ya koma aka ringa yiwa ABDULAZIZ din adduar dangana akan rashin da yayi da fatar yana cikin koshin lafiya.

Alh Saad duk inda zai saka a dubo masa ABDULAZIZ a bincika masa shi a italy abin ya gagara sbd dukkanin wasu hanyar communication da zaa iya jinsa ko labarinsa ta toshe musu sbd Alh saad duk wanda ya sani a qasar italy dazai duba masa shi basa qasar daman duka duka mutum biyu ne ya sani acan baida mutane acan ba kamar uk ko Greece ba ko wasu daidaikun qasar.

Dan haka shima hankalinsa ya tashi sosai gashi ana maganar wata uku ba labarin komai,
Su mama sun koma abin tausayi sosai sbd ciwon tsaye takeyi gadan gadan,

Sunso tattarawa su koma gida shikuma Sayyid yana tinanin kota halin yaya zai neme abinda zai kaisa qasar da ABDULAZIZ din yake ya nemesa sbd zuciyarsa radadi takeyi masa sosai yanaji a jikinsa ABDULAZIZ na cikin matsanancin halinda yake buqatansu.

Mama kuwa gaba daya a yanzu tafara gazawa dan haka Alh Saad ya hanasu komawa gida yace su zauna anan Shi zai tafi qasar ya dubo ABDULAZIZ da kansa.
#MAMUH
#AZIZ LIMBA
#FALAQ LIMBA
#SAYYEED LIMBA
#ZAADENS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
27
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login