Showing 24001 words to 27000 words out of 81012 words

Chapter 9 - KALBIM HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

16 Sep 2025

185

hankalin mama dana baba alhassan ya kwanta sukasake duqufa adduar dawowan ABDULAZIZ.


Suna shiga ss3 Ummitah ta samu ciki wanda bayyanar rashin lafiya a tattare da ita ne ya saka aka san da cikin dan haka kulawan da ake bata ya qaru sosai.

Sayyid kuwa dadi ya ringa ji dan baima damu da rashin tsayuwarsa a rayuwa ba sbd tsananin son dayakewa Ummitah da duk abinda ya shafeta.

Bai taba ganin ABDULAZIZ ba amma kaunarsa yake mai tsafta da karfin gaske sbd irin tsananin son da Ummitah ke masa dan haka shima yake shirye daya bisa yayi masa biyayya har inda karfinsa ya qare.

Ahankali ahankali ciwon laulayi ya koma ciwo a jikin Ummitah,
Ga karatu wanda dole ta dena zuwa ga sanyi daya shigeta sosai kwata kwata cikin baizo da saukiba ko kadan dan haka mama taxo ta dawo da ita hannunta tana kulawa da ita.



*******Rashin jinsu kwata kwata tsawon lokaci me tsayin gaske ya saka ya shiga damuwar data taba aikinsa wanda ya saka masa dawowa da abinda yake yi baya dan kuwa lalacewa komai yayi sbd damuwa dan haka dole komai aka dawo farko kuma ba damar tafiya sbd aikine da zai sauya rayuwarsa gaba daya idan yayi nasara dan haka dole ya dage ya tsaya wanda hakan ne ya haddasa masa daukan tswon lokaci meyawa na shekaru bai dawo ba.


A cikin nasara da yardar Allah ya kammala tareda samun zuwa na daya wanda ya janyo masa wata irin suna da daukaka.

Murna da farin cikin mutanensa dasu alh saad suka shiga anata celebrating tareda tayasa murna hakama kamfaninsa take ya samu shiga jerin kamfanin da aka dan san dasu.

A lokacin ne babu bata lokaci ya tattara ya koma Italy daga can ko sati biyu baiyiba ya sauka Nigeria.

Bai kwana a abuja ba ya isa garinsu sbd daukosu kawai yakeda niyar yi su dawo abuja.

Lafiyayyan gida me kyau da tsari dan girma ya mallaka a abujan wanda babu abunda baa sakaba na jin dadin rayuwa wanda tin bai dawoba qasar aka gama komai na gidan da tsarinsa.


Da rana kwatsam ya sauka a garin wanda motarsa ta saka jamaa taruwa a kofar gidansu mama.

Ummitah dake zaune mama da sayyid na gefen suna kokarin ganin taci abinci da lemu da abarban data saka sayyid siyo mata sbd shima gaba daya ya haukace da nema sbd kulawa da ita da Buqatunta gashi kusan ya tare gidan maman shima sbd ita.

Mama na dagowa ta kallesa saida gabanta yayi mummunan faduwa sbd gabaki daya baiyi kama da ABDULAZIZ dintaba
Hawayene suka fara gangarowa daga idanuwanta masu tsananin zafi da batasan ma na menene ba.

Ummitah kuwa qamshinsa daya cike tsakar gidan ta shaqa da kyau har cikin cikinta taji wani irin sanyi na mamaye zuciyarta zuwa gangar jikin.

Itama hawaye ne suka fara gangarowa daga idanuwanta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa duk da kuwa tsananin kwarjinin dayake dashi na cikar haiba.

Sayyid hannuwansa biyu ya saka suna rawa yafara goge mata hawaye yana jiyowa yayiwa ABDULAZIZ din kallo daya ya sauke idanuwansa.

Kwata kwata bai lura da cikin dayake jikinta ba sbd abine da bazai taba kawowa akansa ba koda kuwa mafarki fararen idanuwansa masu wani irin kyau ya zuba mata zuciyarsa na samun abincin datai shekaru bata samuba ya ware mata hannuwansa ahankali tareda ambatar sunanta da wani irin sautin daya sakata fasa kuka tana miqewa da karfin da sayyid baitaba sanin ayanzu tanada shi ba sbd rashin lafiya ta tinkaresa da gudun gaske ta fada jikinsa yai wata kyakkywar runguma yana rintes idanuwansa wani irin farin cikim dayafi komai na rayuwarsa na rufesa.

Mintina sukai ahakan yana sauke ajiyan zuciya ita kuma tana kuka sosai tana kankamesa tana ambatar sunansa kaman zata bude masa zuciyarta yaga irin abinda takeji na kewansa datai da tsananin Buqatansa datake.

Mama ma kuka takeyi sosai wanda ya sakasa sassauta riqon da yayiwa Ummitah jin wani wani irin tudu ya dan tokaresa.

Bude idanuwansa yayi ahankali tareda zubawa mama yana kasa sakin Ummita wadda itama ta sake qanqamesa.

Wani irin ciwon kai yaji ya sara masa a tsakiyar gefen kansa ya lumshe idanuwansa da suka dan sauya ya bude yana zare Ummitah a jikinsa ahankali.

A gabansa ya tsayar da ita ya zubawa fuskanta datake sunkuye tana kuka ido yana mata kallan daya saba mata duk yazo na karantar meye ya sauya a tattare da ita.

Tin daga fuskanta yaji zuciyarsa na nauyi yafara gangaro da idanuwansa har zuwa cikinta daya fito qarami dashi.

Kaman cikin haihuwa yake gani a jikinta wanda yasan imaginations nasa kawai dan haka ya dago ya zubawa fuskanta ido yana son ta kallesa amma ta kasa dagowa sai kuka tasake sakarwa.

Mama data kasa dagowa ya mayarwa da kallansa sai lokacin ya lura da sayyid daya taho ya tsaya gefensu yana kallansu cikeda kauna da burgewa tareda rashin son kukan Ummitah.

Mama ce tayi karfin halin dagowa tanai masa sannu da zuwa share hawayenta ta nufi daki dauko masa tabarmarsa da haryanxu bata taba fiddawa wani ya hauba sbd dan shi suka siyeta.

Tana saka kafarta daya daki kafin ta saka dayar ya kasa shiru da muryansa me nutsuwa da taushi yace

"Mama meye wannan a jikin Ummitah??

Cak ta tsaya agurin batareda tayi gababa ko baya tana sauke numfashi da ajiyar xuciya me sanyi kafinta juyowa ahankali kai tsaye tana daukan matsayinta na uwa ba shakka tace

"Juna biyu ne a jikinta ga mijinta nan a tsaye ku gaisa bara na dauko maka gurin zama"

Tana fadar hakan ta qarasa wucewa ciki tana sauke ajiyar zuciya da numfashi sbd ba amfanin boye boye da tashin hankalin abinda ya riga ya faru ba sauyi kaddararsu taxo ahakan.

Shiru gurin yayi wani irin mummunan nauyi kansa yayi da maganar tareda wani irin nauyin kirji daya kusa taba ganinsa dan haka tabarman data shimfida ya qarasa baya gani sosai ya zauna yana kasa kallan maman sai Ummitah da rayuwarta ta riga ta lalace dan haka take idanuwansa sauya zuwa wani irin jajir kaman an zuba musu borkono.

Maganan bayan rabuwa da barka da zuwa mama ke masa amma kwata kwata baya jinta jinsa gava daya ya dauke iska kawai yake ji kaman yana kada masa hakama ganinsa yara rawa dan haka bai fahimci komai sosai ba saida Ummitah ta gama kukanta ta dago ta kallesa ta fahimci kwata kwata baya hayyacinsa ma kuma maganar aure da cikin ne yake neman zarar dashi kuma tasani babu abinda zai hanasa raba auren dan haka cikin sanyin murya ta bude baki tace

"HAMMA inasonsa zanci gaba da zama dashi"

Rintse idanuwansa da suka kusa watse masa yakeji yayi da qarfi wani nauyin gaske na danne kirjinsa.

Sayyid daya shiga damuwa da tsoro numfashi ya sauke me sanyi yana kallan Ummitah da shi gava daya ganin ABDULAZIZ din ya tsinkar dashi.

Mama ma numfashi me sanyi ta sauke sbd a baya kam daya dawo da wuri yace zai raba auren bazata hanaba amma yanxu ga rabo ansamu kuma ace zaa raba auren bame yiyuwa bane.

Mama ce ta karbi zancen kai tsaye da cewa

"Sayyid yaron kirki ne kuma yana kaunar matarsa da abinda yake cikinta dan haka ba abin damuwa bane ga abinda Allah ya kaddaro,
A matsayina na uwa gareku ina umartanka da kada kace komai ka karbi hukuncin Allah da hannu biyu"

Bude idanuwansa yayi suna sake sauyawa kirjinsa na wani irin radadi me ciwon gaske sbd mata uku dayake so fiyeda komai a rayuwarsa da komai daya mallaka ga biyu a gabansa daya tace tana sonsa daya tace bata aminta yace komaiba.

Jin yayi zuciyarsa na neman bugawa dan haka ya sauke wani irin numfashi me zafin gaske ya dago ahankali ya zubawa sayyid idanuwansa sai yaji zuciyarsa ta sassauto sbd basan tayaya zaiqi abinda Ummitah ta bude baki ba tace tanaso.

Zaunawa sayyid din yayi suka gaisa
Nan mama da Ummitah suka fara yi masa gaisuwan nutsuwa da fada masa damuwar rashin ganinsa.

Baida nutsuwa da walwalan fira dasu sosai sbd abinda ya tadda din dan haka ba maganar tafiya ranar dole a haka koma sai washe gari ya dawo inda baba alhassan da mama suka sanar dashi komai na abinda ya faru.

Numfashi kadai ya sauke tareda yi musu godia baice komai akan dangin mahaifinsa ba ya sanar dasu tafiyarsu.
#MAMUH
##ZADEEN'S
##LIMBAS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
14
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah >?p?=?L? Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k>?m? Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
=????=????=????=????=????=???? ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA=؃?


***********
Washe gari yana zuwa baba alhassan baiyi musu ba akan tafiya da zaayi harda sayyid sbd shi hakanma yai masa dan haka babu bata lokaci aka fara shirye shiyen tafiya sai kuma daga baya baba alhassan da mama suka roqesa akan yabari su Ummitan da sayyid su gama exams dinsu da aka fara ta waec.

Bai yadda ba amma hakanan mama ta tirsasa ya amince dan haka aka sake haukata kauyen gaba daya da abubuwan alkhairi sbd hatta gidan baba alhassan saida akai masa sauye sauye hakama ya bawa baba alhassan din kwangilar gina masallaci da rijiya Allah yakaiwa inna da iyayensa ladan.

Akan dole ya koma abuja kafin su gama exam din sedai yana zuwa ko kwana biyar baiba ya sake dagawa zuwa lagos daga canma wata tafiyar yayi.

Su kuwa su mama renan cikin suka ci gaba dayi dan daman sun boye masa ciwo dataketa fama dashi akan cikin sbd a samu yabarta ta kammala exams din sbd shi a nasa so yayi idan sun tafi saita haihu saitayi exams dinta aguri me kyau har ita har Sayyid din wanda ya dage sosai sbd so yake ya zama me ilimin da shima zai bata kulawa kaman Hamman.

Yanayinta da yanda ciwo yaketa gaba ya saka baba alhassan ya daukesu sukaje capital a wani asibiti me kyau akai mata register na awo dan ta ringa zuwa akai akai kuma har lokacin basu sanar da ABDULAZIZ ba sbd kada su saka masa damuwa gashi baya ma kasar.



************
A bangaren ZAADENs kuwa suma komai na tafiya daidai tinda suka samu farin cikin rayuwarsu hasken idaniyarsu,

JANNAH ZAADEN wadda wani lokacin suke kira na JAN ta taso cikin rayuwar kulawa da wani irin gata da asalin hutu da tarin arzikin da koyaushe yake qaruwa a familyn,

Basusan menene rashi ba kwata kwata sai na iyaye da kanni da suka rasa sai kuwa asalin farin cikinsu dayar sanyin idaniyarsu wato zayneb wadda a yanzu Jan ce ta maye musu gurbin nata,

Babu abinda suka sani a rayuwa bayan samu da hutu tareda jin dadi da kwanciyar hankali sai zurfafa ilimi da yawon qasashe.

Tsananin son da Ammar yakewa Jannah kusan har mamaki yake bawa Mimi sedai duba da Mum dinsa ce sai ta dena mamaki.

A familyn zaadens babu wanda ba rayuwar class da wayewa tareda tsatsan kudi yakeyiba,
Kyawawane suma kusan suma duk kamanninsu daya hakama kana ganinsu zakace familyn black Americans ne musamman Ammar dayafi su haske sbd mum dinsa nada haske fiyeda su Dzad.


Jan nada shekara 9 a school school dinta suka fara noticing kwata kwata batason duk wank physical activities da farko suna mata dubarun ta ringa yi amma sam bataso da suka dam takura saisuka lura tana farawa take fara zufa harma da shortness of breath.

Dayake school din masu kudi ne sosai sam basa zaqewa akan komai na student saida izinin iyayensu dan haka suka sanar da iyayenta akan a lura da hakan kokuma akaita checkup.

Dayake Mimi sukai magana da ita sai bata wani dauka serious ba dan haka bata fadawa su Dad ba tinda ba wani zama yake ba sukuma yayun nata sunata fama da karatunsu.

Kasancewan Jan din ta taso cikin yayunta maza sai iyayenta da masu aiki sai batada wani rawan kai ko hayaniya gata yayi mugun mata yawa dan haka take da wani irin class tin tana yarinya sam bata son mutane sosai itama sedai zuciyarta nada wani irin sanyi da tausayi tareda rashin karfin hali kawai dai batason shiga mutane ne sbd bata sabu dasu ba a cikin gidansu ne kadai take sakewa tayi wasa da tsalle a cikin yayunta datake tsananin so itama.

A karo na biyu school suka sake yiwa Mimi maganar yanayin jannah din amma still tace zata sanar da yayunta ko dad dinta sukace to.

Da jannah din ta dawo school kallanta Mimin tayi taganta healthy da ita dan haka sai ta sake tinanin sunason fara takurawa yara ne school din dan haka ta share zancen.

A makaranta sunga sam jannah din babu wani sauyi hakama iyayen sunqi cewa komai sai kawai suka kyale aka dena tirsasata duk wani physical activity sai kuwa hakan yayi mata dadi ta dena damuwa ta sakewarta da friends nata.

A haka karatunta yafara nisa tafara zama yan mata kwatsam ranar da sukai family dinner na murnan gama karatun mahir zadeen kwata kwata ya zama cikakken chairman na ZADEENS GRP sunata murna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali irin na masu kudin da babu hayaniya.

Ammar ne ya iso da daddaren sbd flight da bai samu ba daga italy daya tafi dan haka koda ya iso dukkaninsu suna open dinner a dayan lafiyayyan dining dinsu dake kusa da swimming pool na gidan qamshin ruwan me tsafta dana flowers dake zagaye da gurin yana tashi ahankali hakama ga iska me sanyi da nutsuwa yana kadawa ga haske koina dake gurin.

Isowansa ya saka Jannah tasowa da w
Gudun gaske ta tinkaresa shima cikin farin ciki da kaunar dayake mata wadda sam batada sirki ya bude hannayensa ta qaro gudun gaske.

Tana gap da isa gurinsa kirjinta ya kasa daukan stress da rapid breathing din take tsaya cak idanuwanta suka juye ta yanke jiki a gurin ta zube.

Ammar dinne ya ambaci sunanta da sauri yana qarasowa da sauri kanta cikin matsananin tashin hankali da mamaki.

Juyowa kowa yayi yai jin yanda ya ambaci sunanta suka ganta zube a qasa kaman ba rai a jikinta.

Idan akwai abinda ya taba saka zuciyoyinsu tsayawa cak suna dauke wuta to wannan mugun ganin ne musamman Dad din dayaji jininsa na neman hayewa take kasa motsawa yayi.

Maheer da saleem ne da Mimi suka taso da sauri sunayi kanta wanda tini Ammar ya daukota gaba daya yana kiran sunanta idanuwansa na qanqancewa.

Da karfin gaske yace a kira doctors bama doctor daya ba,

Saleem ne yayi saurin dawowa ya dauki wayarsa yana budewa yafara neman likitoci maheer kuwa bayan Ammar din yabi shima yana fidda wayarsa dan kiran wata asibitin.

Mimi ma bayansu tabi dad ma sai alokacin yaji wani mugun karfi ya zuwar masa ya miqe yabi bayansu shima yana kokarin daidaita wayarsa a hannunsa dan kiran wani likitan.

Sama sukai inda dakin jannah din yake sedai ko isa basuyiba suka juyo sbd maheer daya dauko keys na mota sbd ganin bazasu iya tsayawa isowan likitocin da suka kira ba.

Kusan keys hudu ne a guri daya ya kwaso su a palo ya watsar da sauran akan sofa suka nufi kofa har lokacin tana hannun Ammar wanda yake jin kaman zai zare sbd ganin zufan datake tsananin yi bakinta na bushewa kaman wani abin sihiri.

Dad ne ya budewa Ammar kofan motar ya shiga da ita kafin shi ya shiga Mahir yaja suka bar gidan da wani irin speed.

Saleem ne ya fiddo wata motar yabi bayansu suka Mimi gida tareda masu aiki da suketa mata sannu da fatan Ba wani abin ne yake damun Jannah dinba.

A hanyar zuwa asibitin maheer ne kadai idanuwansa ba akan Jannah din yake ba sbd yana drivin ne amma Ammar da Dad shiru sukai kowannensu ya zubawa fuskanta idanuwansu da suka sauya.

Ammar yanada trauma da bata warke ba tin ta rasuwar Mum dinsa a duk lokacinda yaga wani a kwance kamar ba rai a jikinsa sai kansa yayi kaman zai juye sbd tinda aka haifesa mum dinsa take kwance cikin ciwo harya girma ta rasu a kwance take dan haka abin ya taba kansa sosai duk da Allah ya taimaka an samu ya dawo daidai amma haryanxu wannan trauma din tana cikinsa,

Ganin jannah a wannan yanayin yanzu ya sakasa kansa neman zarewa dan haka hannunwansa suka fara rawa ahankali ahankali wanda ya saka Maheer fahimta duk da yana tuqi ya dan juyo ya kalli Ammar din ya kalli dad yace

"Dad, Ammar"

Ammar din dad ya kalla cikin karantar yanayinsa ya miqa hannunsa ya kama nasa tareda dan damqewa.

Dago idanuwansa da suke sauyawa yayi ya kalli Dad din cikin sanyi da kokarin hana hannuwansa dake rawa rawan.

Kallan kwantar da hankali dad din yayi masa yana kasa cewa komai sbd shima kwarin gwiwan yake nema a basa sbd ya yadda ya rasa fiyeda rabin dukiyarsa akan Jannah tayi ko ciwon kai ne amma Ammar ma wani bangaren ne na rayuwarsa dayakewa wani irin kauna wadda take ta kasancewansa jinin zayneb data bar musu a duniya dan haka yake jinsa a ransa sosai.


Suna isa asibitin a cikin gaggawa aka karbeta akai ciki da ita doctors din da duk suka kira suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login