Showing 6001 words to 9000 words out of 66006 words

Chapter 3 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

125

Anan aka tattauna abubuwan da suka faru inda inna kulu tace tabar wasika sai dai in daukewa sukayi.
Shima malam faWa yayi ta yi mata akan "meyasa bata neme shi ba.

Sanda zasu tafi kowa yana alhinin rabuwa da juna, Haka aka rabu ba don ana so ba, Alhassan Da inna kulu saida sukayi kuka, da alkawarin lokaci bayan lokaci zasu rika ziyartar juna.

Hafsat taji dadin labarin da Alhassan ya faWa mata cewa inna kulu tana lafiya ita da sauran yaranta.


*Shekara kwana*

??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yanzu haka kimanin shekarar Hafsa da Alhassan sha biyar da aure amma bata kuma samun cikiba tun Sarin da tayi.

Sai dai zuwa lokacin Alhassan ya gama karatun engineering dinshi anan poly dake dutse a jihar Jigawa bayan ya Nemo takardar transfer.
Inda itama Hafsa da Usman kaninta sun gama secondary bayan Alhassan ya lallaba malam barau ya bari tayi domin da cewa yayi makarantar arna ce baza su yiba.

*August 2000*
Allah ya albarkaci Hafsat da Alhassan da samun ya mace kyakkyawar gaske, daka ganta kaga mahaifinta sak, sai dai Wan Abinda baza a rasa ba na mahaifiyarta
Kullum gidan a cike yake ana tururuwar zuwa ganin jinjirar.
Ranar suna Alhassan yasa ma jinjirar suna *Hafsat* namfa Hafsa ta fara faWa "don me zakasa sunana?
Ko sunan mama ko sunan inna kulu kasa ai yayi, yanzu ka kama kasa sunana gani za'a yi tsabar rashin kunyace ko kuma ni na saka."

Hakuri yayi ta bata, dakyar ya samu ya lallabata ta hakura.
Haka Hafsat ta taso gwanin sha'awa, duk tattalinsu a kanta kullum tsaf tsaf da ita.

Sanda ta shekara hudu ne ya sata a makantar firamare, arabi kuma dama tun tuni yana koya mata a gida.
Allah ya albarkaceta da ?wa?walwa sosai, irinsu ake cewa *gifted*, saboda duk abinda aka faWa take take haddaceshi.

Sanda zasu aji biyarma shida aka kaita wai ta wuce su duka a kokari.

Kuma Alhassan da mamanta sun taka rawar gani a ilimin ta don yanzu a Qur'ani ma tana wajen izifi ishirin ne.
Tana shekara goma sha biyu ta gama firamare inda Alhassan baiyi Wata Wata ba ya nema mata gurbi a makarantar gwamnati ta Mata dake nan malam madori...

Namma duk tafi yan ajinsu haza?a .
Suna jss 2 amma kowa yasan Hafsat.
Wani lokaci aka gayyacesu gasa inda Hafsat ce yazo na daya.
Lokacin da ake shagalin farin cikin nasarar da sukayi ne *Sagir* Wan kansilan kauyen su yayi arba da Hafsat, ai aranshi kawai ya ayyana ya samu mata, saboda duk wanda yayi arba da Hafsat saita tafi da imaninshi.
Saboda bayan kyawun halitta ta fuska tanada girman jiki (diri) sosai, saboda tanada kwankwaso irin wanda ko ta cikin hijabi yake juyawa dakan shi, kuma Masha Allah kirjintama a cike yake.
Shekarunta sha hudu amma idan ka ganta zaka zata takai 18, tsabar girman jiki
Duk sanda zata wuce idon samarin kauyen harda magidanta ya na kanta damma sunsan babanta da kakanta basa daukar raini ne.

Shiko *Sagir* beyi Wata Wata ba bayan an gama taron yabi bayan Hafsat yaga gidan data shiga,

Gida ya koma ya shirya ya dawo, sawa yayi akayi mishi sallama da Alhassan, inda ya shaida mishi shine Wan kansilan kauyen.
Yazo ne ya gaisheshi, da zasu rabu haka ya bashi kyautar dubu goma.
Shi dai Alhassan yanata mamaki, hakanan Wan gidan kansila yazo ya neme shi har gida, Sannan harda yi mishi kyauta!

Washegari ma Sagir baiyi kasa a gwuiwa ba Ya shirya yaje gurin Malam barau wato kakan Hafsat shima ya mishi goma na arziki.

Ita kuwa Hafsat sun shiga jss3 inda ta kara dagewa domin Abbanta yace tayi kokari sosai zai kaita babbar makarantar mata bazaiyi mata aureba har saita zama likita.

*Ni ko cewa nayi anya haka zata yiwu ga Sagir ya fara bada toshiyar baki*

Saida Sagir yaje gurinsu sau uku sannan a zuwa na huWu ya tura mahaifinsa yaje ya tambayar mishi in an bashi izinin kula Hafsa,
To kasancewar Sagir ya nuna yanada hankali yasa Alhassan ya yarda da zancen, amma ya faWa musu cewa yana da burin Hafsat tayi karatu mai zurfi don likita ma yakeso ta zama.
Kansilan yaji daWi sosai kuma ya mishi alkawarin koda anyi musu aure baza'su hanata taci gaba da karatun taba.
Inda daga bisani ya kara da cewa *Nafito takarar Wan majalisar wakilai, idan har Allah yasa naci zan samar maka aiki kaima, kuma zamu tafi da ita Hafsat din achan Abuja ma zatayi karatu*
Alhassan kuwa gani yake kamar a mafarki saboda saida kansilan ya bashi kyautar dubu hamsin kafin su tafi, Hafsa ya samu da maganar inda ya shaida mata duka abinda ya faru.
Itama tayi farinciki daga bisani yaje ya samu malam barau wato kakan Hafsat ?arama ya shaida mishi, shima yayi farin ciki saboda Sagir akwai hankali ga shiga rai
Ranar dazai fara zuwa gurin Hafsat cikin gari ya shiga ya jido mata su sweet dasu chocolate da biscuits iri iri.
Anan falon Alhassan suka zauna, Ita dai Hafsat ko fuska ta kasa budewa tsabar kunya,
Gani tayi ya ciro wayar shi me botura a aljihunshi yana latsawa.
Sai sannan ta Wan saci kallonshi babu laifi shima kyakkyawa ne gashi tsaf dashi duk kamshin turarenshi ya cika dakin, ganin ya dago Kai yasa Hafsat tayi saurin chukuikuye fuskarta.
Mikewa yayi "To Sarkin kunya! bari nazo na tafi"
Ledar chocolate din ya ajiye mata a jiki ya dora dubu biyu akai sannan ya fita yanata murmushi.
Saida ta tabbatar ya fita sannan ta bude fuska tana duba abinda ya kawo mata, ai da gudu ta fita gurin ummanta "umma Kinga irin chakulet din da abba yake siyomin ranar cin kasuwa.

Baki ta bude tana mamaki bayan duka kayan ciye ciyen kuma harda dubu biyu.. kada fa daga baya suyiwa ?ar lelenta gori.

Duk sanda Sagir zai zo da nau'in abubuwan dazai kawo wa Hafsat.
Shi dai yana matu?ar son Hafsat shiyasa yakeson duk wani abu nata.
A hankali suka saba saboda duk bayan kwana uku saiya zo

Amma abinda ke ba Alhassan Da Hafsa tsoro shine duk wata sai an aiko musu da shinkafa yar gwamnati da jarkar mai da dubu goma wai suyi cefane.

Alhassan yace "nifa abinnan ya fara bani tsoro, kamar zamu saida ita.
Gurin Malam barau yaje yake faWa mishi abinda ke faruwa shima malam yace to ainima duk wata ana kawo min danayi bincike na gano yanawa mutane da yawa, duk kauyen nan yabonshi akeyi mutumin kirki ne.

Saura wata biyu Hafsat tayi jsce akazo rokar idan ta gama jarabawa don Allah a Waura musu aure koda baza'a tareba sunaso su tafi da ita Abuja taci gaba da karatunta achan saboda baban Sagir yaci Wan majalisa.

Gurin Malam barau Alhassan yace suje.
Malam barau ya yarda yace ai babu komai tunda yanzuma shekarunta sha biyar,

Saboda itama mahaifiyarta tana Kamar Hafsat Win aka aurar da ita.
Kuma ma wasu sa annin Hafsat dinma duk sunyi aure.

Shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin Sagir Da Hafsat domin Sagir mutumne mai kula ga kauta sam abinshi bai dameshiba.
Duk sanda yayi tafiya ya dawo saiya Winkowa Hafsat kayan sawa hakama zai siyo mata littattafai dasu kayan za?i da yake ya lura Hafsat Win sha zumamuce.

Zaune suke a bakin kogi suma kallon ruwa "Sarkin kunya" sunan da sagir yake kiranta kenan
"Kinga yanzu saura wata Waya bikinmu Koh? me kika shirya mana"
Rufe fuska tayi da hijabi wai ita kunya, "Allah ya Sagir ka bari nifa kunya nake ji"
"Af! to kin manta sunankine, to yanzu dai akwati nawa kikeso na miki?"
DaWa rufe fuskar tayi batace komai ba
Cewa yayi "guda goma sunyi"
Da sauri ta dago Kai takalleshi cike da mamaki, daga mata gira yayi da sauri don dama so yake ta kalle shi.
"Ko sunyi kadan?"
Namma shiru tayi, oh ni Sagir nifa kunyar nan taki na damuna ace magana ma kunyar yinta kikeyi"
"Yanzu dai bani karamin yatsanki", dakyar ta ciro ta mika mai
Wani kyakkyawan zoben azurfa ya sa mata sai dai ya Wan yi mata yawa amma ba sosai ba.

"Ki dauki zoben nan a matsayin bugun zuciyata, duk rintsi kada ki raba shi da yatsanki."
" Yanzu tashi muje in rakaki gida"
Mikewa tayi suna tafiya suna hira saidai yawanci shine ke maganar

Bayan ya koma Abuja ita kuma Hafsat sun gama jarabawa.
Ya rage saura kwana biyar a daura musu aure duk ahalin gida biyun sunata hidima
A ranar Sagir ya dawo don aci gaba da shirye shiryen bikin, gidansu Hafsat ya fara zuwa yakai mata tsarabar kayan zakin ta da abubuwan da baza'a rasa ba.

Bayan nan ya koma gida aka ci gaba da shirye shirye.

*Wayyo Allah na!!! wayyo Ni Allah Mai nayi maka nashiga uku!!!*
Abinda Alhassan ya jiyo kenan asubar fari a tsakar gida.
Da sauri suka diro shida hafsa daga gado suka bude kofa.
Mamar *Sagir* suka gani hannu akai tana rusa ihu, gaba Waya ta fita daga hayyacinta.

Cikin kidima Hafsa ta rike ta tana cewa "lafiya? Meya faru?"

Tana sharar hawaye tace " jiya da daddare ne ciwon ciki ya kama Sagir, dakyar ya lafa mishi har barci ya dauke shi, to yanzu naje tashinshi yayi sallar asuba amma shiru yaki ko motsi"
Ai da sauri Alhassan yace "ina sauran mutanen gidan?"

Cikin kuka tace "ai banbi takan su ba nayo nan tsabar kidimewa da nayi"

"ku biyoni muje" Alhassan yace yana fita daga gidan cikin sauri Hijab Hafsa tasa ta ri?e maman sagir suka bi bayan shi zuciyar kowa na tsinkewa.

*Tofa >??*

*#SAGIR*
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*

```pls comment and share```
*IZAYAR RAYUWA*

*4*

*MATAR RASHEED*


______A kwance suka tarar da sagir a saman gadon shi,
Du?awa Alhassan yayi daidai sagir Win yana dudduba shi, duk wata gaSa da alamu da zasu nuna Mutum Ya mutu ya nuna sagir ya mutu.
Mikewa Alhassan yayi Ya fita daga Wakin be kula kowaba.
Masallacin dake kofar gidan ya fita yasa aka tara Mutane ya sanar dasu cewa yaron kansila Allah yayi mishi cikawa.

Yayan Sagir ne Ya
kira mahaifinsu (kansila) ya sanar dashi Allah yayi wa Sagir rasuwa, ba ?aramin tashin hankali ya shiga ba, amma yafi so yazo gidan don yaga anya shin da gaske ne?

Maman Sagir kam gaba daya ta fita hayyacinta, gani takeyi kamar mafarki "wannan wace irin kaddara ce, ace saura kwana biyu bikin mutum amma ya mutu"
Maman Hafsat kuma tunda sukazo da asuba bata koma gidaba, kuma ita Hafsat ma batasan meke faruwaba.

Cikin ?an?anin lokaci aka yiwa Sagir wanka aka shiryashi kafin mahaifinsa ya iso daga Abuja .

?angaren Hafsat kuma bayan fitar iyayenta ta tashi daga barci, dayake bata sallah shiyasa basu tashe ta da asuba ba.

Ganin basa gidan yasa ta shiga tunani "ko ina suka tafi da safennan kuma basu tashe taba"

Kofar gida ta leka ko zata samu yaro, Ibi tagani (yaron makwabtan su) ya dawo daga shago.

"ibi dan Allah ko kaga ummana da Abba na"
"Eh nagansu, lokacin Da muka dawo daga sallar asuba tare da matar kansila sunbi hanyar gidan kansila"

"To Nagode ibi" Cewar Hafsat hade da komawa gida, bata kawo komai a rantaba don tana tunanin kila maganar bikin sune.

Isowar kansila wanda ayanzu yake matsayin Wan majalisa cikin kauyen Malam madori yasa kowa yasan da rasuwar Sagir.

Ganin har yanzu su Ummanta da Abbanta basu dawoba yasa tayi Wumame ta share gidan tayi wanka, Sa?ar ta ta dauko ta cigaba dayi sai dai zuciyar ta nayi mata wani iri.

Tabawa ce ta shigo cikin gidan da sallama, amsa wa Hafsat tayi hadi da gaisheta.
Kujerar tsuguno (tayani tsegumi) Hafsat ta ajiye mata
"Inna tabawa zauna" cewar Hafsat gami da yin hanyar kitchen "Bari na zubo Miki Wumame"

Da sauri tabawa tace "hafsatou bar tuwon nan dama gaisuwa nazo na muku"

Cikin rashin fahimta Hafsat tace "waye ya mutu inna tabawa?"

"Hafsatou kar dai kice baki saniba"

"Wallahi inna tabawa bansan anyi rasuwa ba, don Allah wa ya rasu?"

Numfasawa tabawa tayi daga bisani tace "Sagir ne ya rasu tun jiya da dare sanadin ciwon ciki daya kamashi, amma naji mamaki ace bakijiba gashi can ma an tafi kaishi"

RuWewa Hafsat tayi, gaba Waya bata ma bi takan tabawa ba ta dauki hijabin ta dake saman kyaure tayi waje da sauri ta nufi hanyar gidan su Sagir.

Tun kafin ta ?arasa kofar gidan ta fara cin karo da mutane, hakan yasa kukan da take ta ri?ewa ya kufce mata ta fara zunduma ihu tun a cikin zaure.

Tuni idon kowa dake cikin gidan ya dawo kanta, "Hafsat sai hakuri domin amma tafi kaishi makwancin shi" cewar wata makwabciyar su Sagir.
Jiri ne ya dibi Hafsat jin maganar da matar tayi ''wato da gaske ne kenan Sagir ne ya mutu?" Sulalewa ?asa tayi warwas.

Nan mata akayi cha akanta inda sai sannan maman hafsat Win da maman Sagir suka fito daga ?aki jin hayaniya a tsakar gida.

Hafsat suka gani kwance hajaran majaran.
?aki aka kaita bayan an samu wasu yan mata guda biyu sun Wago ta, addu'oi akaita tofa mata sannan aka samu ta dawo daidai.

Ajiyar zuciya ta sauke alamun ta farfaWo, sai dai bata buWe ido ba sai bayan kamar minti uku ta fara magana a hankali "ya Allah kasa mafarki nake yi, ya Allah kasa ba gaskiya bane! ,ya Allah ka taimakeni.."
A hankali ta fara bude idonta, ganinta a cikin Wakin maman Sagir yasa ta fashe da kuka.
Tabbas Sagir ya rasu ga idon kowa nan ya kumbura alamar sunyi kuka sun gaji.

Maman Sagir ce ta tallabo ta "Hafsat ki Dena kuka? Allah Baiyi keda Sagir zaku auri junaba, kuma a halin yanzu Sagir addu'ar ki kawai yake bukata."

Cikin sheshe?ar kuka Hafsat tace "mama dagaske ya rasu kenan! innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un" kara fashewa tayi da kuka tana jin tausayin masoyinta sagir, ashe bazasu sake haduwa ba.

Sai bata baki ake yi amma Hafsat ta kasa Dena kuka "yanzu shike nan Sagir ya mutu, bazan kuma ganinshiba? shikenan munyi maganar karshe?" Duk a zuciya take wannan lissafin

Gaba daya malammadori babu inda ba'a ji rasuwar Sagir ba! saboda akwai shi da kyauta ga girmama na gaba dashi.

Daga lungu da sa?o sai zuwa gaisuwa akeyi, kuma kowa ka ganshi zaka ga alamun damuwa a fuskar shi.

Ita ko Hafsat tama kasa tafiya gida, kuma ko abinci ta kasa ci.

Ganin halin data shiga yasa Ummanta tayiwa Abbanta magana akan a barta anan har zuwa ayi addu'ar bakwai tunda akwai mutane sosai a gidan, ganin su zai ri?a Webe mata kewa, domin idan aka dawo da ita gida ita kadaice zata ri?a zama, damuwa kuma zatayi mata yawa.

Cikin yan kwanakin da akayi da rasuwar Sagir duk wanda ya kalli Hafsat saiya gane tana cikin mawuyacin hali, saboda duk ta rame har duhu tayi.

Yau ya kama kwana bakwai da rasuwar sagir, anyi sadakar bakwai da addu'o'i tun safe, mutane ma?il a kofar gida kamar wani babban mutum ne ya rasu, kansila yaji mutuwar Sagir sosai, kawai dai yana dannewane kada rakinshi ya fito Fili, domin kaf ?a?an shi babu wanda Allah ya Wora mishi sonshi irin Sagir.


Sai bayan komai ya lafa, Hafsat zata tafi gida aka buWe wani sabon fagen kuka, saboda sati dayan da Hafsat tayi da maman Sagir saida sha?uwa mai karfi ta shiga tsakaninsu...

Koda Hafsat ta koma gida zama tayi kamar marainiya sai dai tayita zama a daki tana tunane tunane, ko tsakar gida bata son fitowa.

Su kansu iyayen Hafsat Win sunji mutuwar Sagir sosai, saboda dalilinsa abubuwa da yawa sun faru.

Maman Hafsat Win cema taketa kwantar mata da hankali tana daWa janyo ta jikinta.
Shima babanta ba'a barshi a bayaba saboda duk sanda yake gida shima haka zai rika kwantar mata da hankali.

Dayake yau da gobe bata bar Komai ba! A hankali Hafsat ta hakura da Sagir, sannan ta cire rai da zama likita musamman yanda taga maza sunyi mata cha.
Domin idan wannan yazo yau, to gobe ma wani ne zai zo, ita burinta a yanzu bai wuce ta ga ta gama koda secondary ne. saboda tasan babanta baida halin da zai iya sata a University.

Gashi kuma wanda yayi al?awarin zai sata Allah ya amshi kayanshi.

Cikin ?an kwanaki Damuwa tayi mata yawa musamman mazan da suke yi mata chaaa! Idan kuma bata kula suba sai su tafi gurin kakanta suna kamun ?afa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login