Showing 42001 words to 45000 words out of 66006 words

Chapter 15 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

142

tunda haka ne kuwa kasha zamanka in an kwana biyu saika tawo"

Murmushi shima kawu shehu yayi ganin Allah ya taimakeshi malam din ya sauko.

Saida kowa yayi mamaki ganin kawu shehu da malam barau sun fito suna dariya sabanin dazu da suka shiga falon kamar Wadanda zasu dambace.

haka dai kowa ya gama hada abinda zai hada suka shiga cikin motar da Abban Hafsat ya kawo musu wadda zata kaisu har kofar gidajensu, gwanin tausayi sanda driver ya kunna motar, su Aunty Rafia sai dagawa umman hafsat dasu murja Hannu suke.

Gidan saiya koma daga umman hafsat sai kawu shehu da murja da baaba indo, Tashi baaba indo tayi don fara gyare-gyare saboda gidan duk ya fita daga hayyacinsa, ita kuma murja cikin dakunan ta fara sharewa kafin ta goge.

Umman Hafsat kuma daki ta shiga don ta samu ta dan huta, shikuma kawu shehu sai yayi waje gurin Abban Hafsat.

?????????????


Koda sadeeq ya koma gida Allah ya taimakeshi babu wanda yazo, illah dai mummyn husna ta aiko musu da abinci sai maigadi ya amsa ya ajiye.
A saman dining ya ajiye basket din, shikuma yayi cikin bedroom din hafsat ya kwanta.
Shiru yayi yana tunanin ta inda zai samu mafita gameda abinda hafsat take yi, yanason suyi muguwar shakuwar da daya bazai iya Yin barci ba idan babu daya, to amma ta yaya? Wata zuciyar ce tace mishi "tunda yanzu jarabawa sukeyi ka bari suyi hutu sai ka fara yakinka cikin salama" jiyayi 100% ya gamsu da wannan shawarar, rigingine yayi yana tuna ranar daya fara ganin Hafsat a gidan mummyn Husna ita da murja.

Damshi damshi yaji a cikin hancinshi, da sauri yakai hannu ya taba, aikuwa kamar yadda yake tunani jini ne, yana dagowa ya fara zuba, Allah yasa ya tara hannunshi da duka saiya bata gadon, cikin bayi ya shiga da sauri ya dukar da kanshi a cikin sink, saida jinin ya zuba da dan yawa sannan ya tsaya, wanke hancin yayi sannan ya wanke fuskarshi duka, ya dade a cikin bayin sannan ya fito, zuwa yanzu ya fara gajiya da zubar jinin nan, Sannan yana tsoro kada wata rana yayi mishi haka a cikin mutane.
Tun sanda ya fara Zubar mishi kusan wata biyar baya yaje asibiti akan a duba meye matsalar, amma sai likitoci Suka ce mishi babu komai bayan sun bashi wasu magunguna Sukace idan ya shanye jinin zai dena zuba.

Gashi kuma jinin be tsaya ba, Yanzu ma abin ya fara yawa saboda da befi ya zuba sau daya a sati ba, amma yanzu sai ya zuba kusan sau uku kuma me yawa yake zuba, hanyar falour yayi yana tunanin kilafa saiya kuma komawa asibitin, idan kuma abin yafi karfinsu Yanaga Kasar waje zai fita kila yasamu mafita.
Rasa me zaiyi a cikin gidan yayi sai kawai ya kuma daukar mukullin motar da nufin ya tafi asibitin yanzu kawai tunda babu abinda zaiyi.

???????????????


Sai wajen karfe tara Abban su Aadhil ya fita gurin Aiki, ita kuma Zaituna tana gida dayake sun gama Exam hutun ne dai ba'a riga da an basu ba, Mummy kuma kitchen tayi don dora abincin rana saboda ta saba gamawa da wuri, da Aunty salma ce takeyi to bayan tayi Aure kuma sai mummyn takeyi, wani zubin kuma zaituna tayi idan ba mai wahala bane.

Bin bayanta Aadhil yayi "mummy me zakiyi?"
"Af Aadhil biyoni kayi"
"Eh mum so nake kije ki kwanta ki huta"

"Aadhil ina naga damar kwanciya?, girki zan dora mana" mummy tace tana tara tukunya a famfoo
"Me zayt take da bazata dora ba" Cewar Aadhil yana hada girar sama data kasa

"Ai girkin me wuya ne zaituna bazata iya ba, sakwara zanyi da miyar ridi, Abbanku kuma yace na dan tuka mishi tuwon alkama Dan kadan"

"Mummy! Wallahi bazai yiwuba, yaza'ayi duka ke kadai kiyi wannan aikin sai kace wata baiwa, inaa sam bazai yiwuba wallahi, gaskiya ankai gejin da ko bakyaso saina kawo miki yar aiki"

"Aadhil wai a matsayina na matar aure idan ban girkawa mijina abinci ba me zanyi?"

"Hmm mum gaskiya abin yayi yawa, yanzu dai hakuri zakiyi a samo yar aikin nan, inyaso saiku rikayi tare"

Jinjina kai kawai mummy tayi domin tasan Yanzu ankai gejin da Aadhil bazai hakura ba, kuma dama ba tun yau yake mita ba akan zai kawo mata yar aiki ba, amma taki yarda.

Hannu yasa ya kunna gas sannan ya dauke tukunyar bayan ya kashe famfoon, a saman gas din ya dora sannan Ya kama hannun mum yana cewa "to muje ki kwanta, zanyi girkin"

"Aadhil jiya fa ka dawo, ko hutawa bakayiba zaka ce Kuma zaka shiga kitchen"

"Mum pls kije ki kwanta kawai no more words"

"To shikenan Allah yayi Albarka ya kyautata rayuwa yasa yayanka suyi maka fiyeda wanda kayi mana".

"Ameen Ameen, ko kefa mum" cewar Aadhil yana jin wani irin farinciki dalilin Addu'ar da mummy tayi mishi.

Cikin kitchen din ya koma ya shiga store ya kwaso doya yana ferewa, tsaff yake firar cike da natsuwa da kwarewa, saida ya gama ya wanke ya zuba a cikin ruwan zafin dake saman gas.
Freezer dake cikin kitchen din ya bude ya dibi naama da kayan miyan da zaiyi amfani dashi sannan ya wuce sink don gyarawa, nidai sai binshi nake da ido ina mamakin wannan abu *_(yau naga wanda yafi NAWAZ son girki)_*
_*(IYA GIRKINSHI YA SAMO ASALI NE DAGA SABON DA SUKAYI DA AUNTY SALMA, DOMIN TARE SUKE GIRKIN KULLUM, WANI ZUBIN MA IDAN YAYI SAI YAFI NATA DADI, SABODA SHI YANAYIN KOMAI NE CIKIN NUTSUWA DA TSARI BABU GAGGAWA)*_

???????????????

"Hello! Eh inaji" cewar hajiya bilki (mamar diyana)
Ta chan bangaren kuma interpreter din boka dan china ne yake magana "Hajiya boka fa yace a fada miki an samu matsala a aikin nan"
"Meya faru interpreter?"

"Cewa yayi in fada miki cewa taurarin yarinyar nan dana mamanta karfi garesu, sannan baban yarinyar yanada tsari me karfi a jikin shi saboda shi ko irin nashi taurarin ya kasa gani"

"Innalillah to yanzu meye abinyi?"

"Eh to yace dai yana tunanin sai an raba mamar da baban kafin ki samu damar shiga cikin wannan gidan"

"Ai inma haka ne da sauki, kawai kace ya kasheta"
"Okay to babu matsala, sai anjima"

Ajiye wayar tayi tana ayyanah gata ta zama matar Abban hafsat ita kadai, ada tana tunanin zata iya zama ta biyu, amma tunda diyana tace bata kaunar hafsat komai ya chanza, itama duk saita kara tsanar su.

______Hajiya bilki irin tsofaffin yan duniyan nan ne, wanda duk abinda sukasa agaba sai sun sameshi Kota halin 'ka'ka, yar asalin garin kebbi ce, tun tana budurwa ta gudo daga gida ta dawo Abuja, anan ne ta fara karuwanci daga baya kuma ta samu wani Alhaji ya Aureta, tare dashi nema ta haifi diyana, daga karshe dai ita ta kasheshi saboda ta mallake dukiyoyin shi.
Ta fara ganin Abban hafsat ne a lokacin data raka wata kawarta companyn da yake aiki, ba komai ya birgeta dashi ba irin surarshi da yadda taga anata haba haba dashi, tun anan ta fara bibiyar rayuwarshi, sosai ta kwallafa rai akan saita aureshi.

?????????????????

*SADEEQ*

Zaune yake a cikin office din babban likitan asibitin bayan ya fito daga dakin da akayimai gwaje gwajen, magana Doctor yake yi mishi akan yanaga fa akwai wata matsalar, amma su gaskiya har yanzu na'urar Su bata nuna musu komai ba
"Okay to yanzu doctor me kake ganin za'ayi?"

"Eh to a nawa tunanin gaskiya ta fita waje ne saboda su sunfimu kayan aiki musamman kasar EGYPT tunda kaga su tun zamanin da Allah ya yarje musu a Harkokin lafiya"

"To shikenan likita nagode sosai" cewar sadeeq yana tashi bayan yaba likitan hannu sun kuma gaisawa

Yana fita daga office din kiran hafsat ya shigo wayarshi, sauri yayi ya karasa makarantar don kar ya barta tayita tsayuwa a bakin hanya.
Tum sanda ya daukota hafsat ta lura akwai alamun damuwa a tare dashi, gyaran murya tayi tare da cewa "Uncle kana lafiya kuwa"
Murmushi yayi don ya gyara fuskarshi sannan yace "lafiya nake Noor, kawai dai stress ke damuna gashi har yanzu ban samu na huta ba"

"Ayyah sannu Uncle muje gida kaci abinci saika kwanta"

"Okay Noor thanks" cewar sadeeq yana maida hankalinshi tukin da yake yi

*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*20*

*MATAR RASHEED*


_____Ko bayan sun isa gida ma haka sadeeq ya kasa cin abincin, kaWan ya tsakura yace wa Noor ya koshi.
Sosai ta lura yana cikin damuwa kawai dai ya?i faWa mata ne, samun kanta tayi dajin ta cikin damuwa itama duk da bawai tasan hakikanin meke damun shi bane.

Saida yayi bulking din appointment din hira da likita via video call sannan ya samu saukin damuwar da yake ciki, duk da P.A din likitan Yace sai nan da sati daya zai samu damar magana dashi saboda mutane sunyi yawa.
Tashi yayi yai wanka sannan ya fito falour, a zaune ya tarar da Noor tayi shiru alamun itama wani abu yana damunta "Noor zoki kunna mana kallo"
"Uncle pls abar kallon nan yau"

Mamaki sosai abin yaba Sadeeq, Ita da take raba dare tana kallo yau kuma itace me cewa abar kallon, gyara zama yayi sannan ya kuma cewa "Taso kizo nan"
A hankali ta taso ta nufo inda yake zaune, "uncle gani"
Gefen shi ya nuna mata tare da cewa "zauna anan"
Zama tayi tana kallonshi ta kasan ido "Noor meke damunki"
"Babu komai, kawai dai naga kamar bakada lafiya ne kuma bakason ka faWa mini"
Murmushi yayi yana mamakin ya akayi tasa abin a ranta "Ayyah _i'm sorry!_ Bawai naki fada miki abinda ke damu na bane, kawai dai aikin office ne suka yimin yawa kuma dole ni zanyi su duka"

"To Uncle ka Wauko sai in tayaka muyi yanzu"

"Bazaki iyaba noor, Saboda duk na riga na fara kuma aikin ba kaWan bane"

Girgiza kai Hafsat tayi, tare da cewa "to yanzu me zanyi maka"

"Just ki zauna tare dani muyi hira" matsowa tayi kusa dashi sosai tana murmushi "to Un??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????cle na zauna"
Numfashi ya zuka ya furzar sannan ya kalleta, sanye take da doguwar riga light purple colour me shortsleeve, tsayinta iya kwaurinta, kanta babu dan kwali.
koda ya gama kallonta duka sai Allah ya kareshi sam beji komai gameda shigar tata ba. Sosai yake yiwa Allah godia najin yadda kwana biyu yaji libido din shi ya ragu, soboda dama yanaso ya bata _Enough time_ tunda tace Mai bata shirya wa Auren ba

Ahaka suka zauna sunata hira kaWan kaWan har zuwa yammah Domin Sallah ce kawai kesa su tashi, inda wajen gefin magrib saiga dan aike mummyn husna ta kuma aiko musu da wani abincin

????????????????

A kwana a tashi babu wuya, yau kusan kwana goma da bikin su hafsat
Abubuwa da dama sun faru, inda ita Hafsat ta gama Exam dinta saura jiran abasu hutu, shikuma Sadeeq ya samu ya kammala Ayyukan Company da suka yi mishi yawa.

Kuma achan gidan su hafsat yaune kawu shehu zai koma gida, Allah ya taimakeshi babu abinda ya faru har ya ware balle malam barau yace shine sila, Abinda yasa ma ya?i zuwa gidan hafsat Win kenan.
Ta bangaren umman Hafsat kuma kewa ta isheta, don ma Allah yasa murja bata koma ba, kuma suna samun isasshen lokaci da baaba indo, amma duk da haka ji takeyi kamar tayi tsuntsuwa taje taga Hafsat din.
Yauma kamar kullum, Hafsat ce zaune a two sisters Couch tana kallo, Gaba Waya hankalinta ya tafi zuwa TVn, yanzu ta ?ara sakewa sosai da Sadeeq Win, Duba da sam Yanzu Baya yunkurin taSa jikin ta, kuma haka zai yi ta biye wa shirmenta.
Sadeeq kuma yana three sisters Couch a kishingide yana danna waya, A kunne ya kara wayar tare da cewa "Barka Aunty, ya gida? Ya husna din? Ina fatan tana Lafiya?" Shiru yayi na yan sakwanni sannan ya kuma cewa "Okay to ganinan zuwa yanzu In sha Allah" tashi yayi ya nufi bedroom don canza kaya, yana so yaje yaji meyasa yayar tashi take son ganinshi?

Befi minti goma da shiga ciki ba ya fito sanye da Wani farin yadi mai uban taushi, anyiwa aljihun Gaban rigar ado da Wasu Irin bakaken botira, sai ya saka bakar hula, kafarshi kuma ba?in Palms ne mara nauyi, koda ya karasa gaban Hafsat du?awa yayi daidai fuskarta "dear mummyn husna ce tace tanason mu hadu zamuyi wata magana shine zan tafi, amma bazan dade ba Yanzu zan dawo"

Anan nefa Hafsat tayi tsalle ta dire akan itafa Wallahi Sai dai su tafi Tare, Babu Irin dabarar da Sadeeq beyiba amma tsaff Hafsat ta murje idonta da toka akan itafa saita je.

Ganin bazai iyawa rigimartaba yasa yace to taje ta shirya sai tazo su tafi, nanma cewa tayi bata yarda ba, wai guduwa zaiyi ya barta sai dai kawai ta saka hijab su tafi, kallon rigar jikinta yayi batada maraba da sleeping dress, butter colour ce me spaghetti hand kuma daga sama ansa rubber har zuwa ciki sai aka sake ta, hakan saiya sa ta sama ta tsuke Duk tudun kirjinta a fili, ta ?asa kuma saita buWe Tare Da hips dinta, a takaice dai duka surar jikinta a waje, kuma kanta babu dan kwali sai twisting da tayi guda huWu ta zubo su gaba, ragowar gashin kuma tayi parking dinshi da butter colour ribbon

"Noor please kije kisa Atampa ko lace, Wallahi i promise zan jiraki" girgiza Kai Hafsat tayi "A'a Uncle, kawai muje ai hijab zansa!" Badon yaso ba yace to "Sa hijab Win muje" Cikin zumudi Hafsat ta zira hijab Win wanda dama Yana ajiye ne a saman hannun kujerar tare da zira soft Palms dinta dake ajiye a tsakar dakin tana yin hanyar waje da sauri.

Tana fita bata jira komai ba ta buWe mota ta shige ciki, ko baba me Gadi bata gaisar ba saida ta tabbatar ta samu masauki me kyau sannan ta gaisheshi daga cikin motar
Shima Sadeeq shiga motar yayi tare da barin gidan Bayan sun gaisa da baba me gadin, tuki yake a hankali yana tunanin rikicin Noor, Ita kuma haka take, to ko Kunyar mummyn husna bazata jiba? Sai kuma ya tuna ai yarinya ce, da ace yar 19 ce ko Yar 20 duk baza ayi haka ba, wayar shi dake gefe ce ta hau ?ara, hannu yasa ya Wauka tare da duba sunan, saida ya Wan zare ido sannan yayi murmushi
"Assalamu alaikum, ka iso ?asar tamu ne?" Shiru yayi sai kuma yace "Au haba! da gaske kake wai?" Kuma yin shiru yayi sai Bayan Kamar second ishirin yace "Okay to Yanzu Abinda za'a yi shine pls ka bani minti talatin, dakaina zanzo in Wauke Ka tunda naga ba Wata tazara bace sosai tsakaninmu"

Kashe wayar yayi sannan ya kalli Hafsat "kinsan waye?" Girgiza Kai Hafsat tayi tana kallonshi, murmushi yayi Mata Tare Da cewa "Aadhil ne, wanda daga jin Labarin shi kika hau kuka"
Cikin zumudi tace "Allah sarki! Yazo ne?", Daga Mata Kai yayi tare da cewa "yazo, Abinda yasa ma ya kira Ni kenan, wai yanaso mu haWu"
"Kace dama idan zakaje dani zaka koh?" Kama baki Sadeeq yayi "Lallai Noor bakida mantuwa, ai Yanzu ki kwantar da hankalinki har gidanmu Zan kaishi, kinga ko saikin gaji da ganinshi"
Murmushi Hafsat tayi batare data ce komai ba, Yan mintoci kaWan suka ?ara a titi suka Isa gidan mummyn husna, bayan yayi parking Win motar a parking lot ne ya fito don ya bude wa Hafsat, ai tuni tama buWe tayo waje abinta
Murmushi yayi "wai duk zumudin na meye"
"Wallahi Uncle daWi kawai nake ji" girgiza Kai yayi sannan yace "to muje"
A Tare suka shiga falourn da sallama, sosai fuskar mummyn husna ta fadada da farin ciki ganinsu da tayi tare
"Maraba maraba! Sannunku da zuwa!" Murmushi Hafsat tayi tare da cewa "ina yini mummy" tare da chukuikuye fuskarta Cikin hijabi
Dariya abin yaba mummyn husna "dear zauna ki huta tukuna saimu gaisa daga baya" a hankali Hafsat ta zauna, sai Yanzu ne taji wata Irin muguwar kunya ta Kama ta
Ita ko mummyn husna ko a jikin ta, Kayan ciye ciye ma ta shiga jibga musu a gabansu kala kala
"Mummy! mummy!! Mummy!!!" Husna ce wadda ta shigo da gudu keta rafkawa mummynta kira "hohoho husna wai Duk kiran nan na meye?"

Ai da gudu husna ta chanza akalar tafiyarta zuwa wajen hafsat, "Aunty zo muje kigani"

Tsawa mummynta ta daka mata "ke husna bakida hankali koh? Tukunama kin gaishesu da kika zo, amma shine kika kama hannunta kina ja akan ta taso taje ke tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login