Showing 3001 words to 6000 words out of 66006 words

Chapter 2 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

123

buhu, danyar masarace suka debo a gona za'a dafa.

Kallon Al-hassan malam yayi yace "sati Mai zuwa zani Zaria an turomin da sakon gayyata za'ayi taron malamai na garuruwa"
" To Allah ya kaimu malam, saimu tafi tare" cewar Al-hassan yana gyara buhun dake rataye a kafaWarshi
" A'a" cewar malam, "kayi zamanka zanje ni kadai , Kai saika kula da gida da Kuma almajiran , ga makarantarka banaso ka Rika fashi don zaka iya Dena fahintar karatun"
Badan ya soba yace to, suka ci gaba da tafia.

Gidan malam suka shiga, anan ya tarar da hafsa sunata Hira da Inna kulun suna dariya.
Da sauri Hafsa ta Mike ta amshi buhun masarar ta ajiye a gefe,
Ruwa ta debo ta zauna tana gyarawa,

Cikin yan d'akiku ta gama gyarawa ta Dora a wuta,
Kamshine ya bade gidan alamun ya dahu, Ai zumbur hafsa ta nufi kitchen, saukewa tayi ta juye takai d'aki
Su malam ta dibar mawa da makwabtansu aka Kai musu, sannan ta dibarwa Inna kulu dasu zainabu

Jikinta har rawa yake tana barewa, bata damu da zafin taba ta fara ci
Ganin yadda hafsa take cin masarar yasa inna ta gano akwai ajiya a cikin marar hafsa , wato tanada ciki, saboda da Sam bata iya sakewa taci abincin kirki a gidan.
Amma yau jikinta har rawa yakeyi, saida taci guda hudu sannan ta kora da ruwa, Nan take barci ya kamata ta kwanta anan.

Farin cikine ya rufe Inna, ai bata Bari su mallam sun shigoba ta aika aka kirasu,
Suna shigowa ta fara waka tana tafi irin nasu na mutanen da, "wayyo niya duniya tai mini dad'i, wayyo niya duniya asha shagali"
Malam Yana murmushi yace "a'a yau Kuma wane irin abun farincikine ya faru haka ?
Cikin madaukakiyar fara'a Inna kulu tace "Na kusa zama kaka in'sha Allah, Hafsat keda juna biyu"

kunyace ta rufe Al-hassan yayi waje da sauri Yana murmushi....

malam ma haka ya nuna farin cikin shi sosai sai fatan alkhairi yakeyi,
Take Kuma yaji gabanshi ya fadi daya tuna da ina ahalin al-hassan suke..

*#SAGIR*
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*

```pls comment and share```
*IZAYAR RAYUWA*

*2*

*MATAR RASHEED*


_____Tundaga wannan ranar Hafsat take samun kulawa ta musamman a gurin Al-hassan da Inna kulu, harma da Malam Win..

Sam basa son abinda zai bata mata rai..

Saboda Inna kulu bata kwana biyu bataje gidan Al-hassan ta duba taba, kuma duk abinda tasan masu ciki na sha'awarsa saita dafa ta aika mata dashi.

Yau ne ranar Da Malam zai tafi Zaria, har tasha Alhassan ya raka shi , yana ta mishi addu'ar dawowa lafiya....

Bayan motar su malam ta dauki hanya ya dawo Gida yaci gaba da ayyukan gidan kamar Malam nanan....

Dayake ya saba dama ko malam Win yananan shi yake yin komai, sai hakan yasa besha wuya ba.

Shuru-shuru Yau har sati Waya malam be dawo ba, Kuma acewar sa kwana uku zai yi.

Ai tuni hankalin Alhassan ya tashi amma ya?i Bari Inna kulu ta sani, saboda yasan sai hankalin ta yafi nashi tashi.
Washegari Da sassafe ya samu Inna kulu a Waki yake ce mata "malam ya aiko da wasi?a wai naje Zaria na sameshi mu tawo tare"
"To" Inna kulu tace tare dayi mishi addu'ar Allah ya tsare hanya.
gidan malam yace hafsa taje ta zauna tare da inna kulu kafin ya dawo, Sannan shima ya Wauki hanyar Zaria.

Kasancewar Bai taSa zuwa Zaria ba yasha wahala sosai kafin ya gano inda akayi taron.

Wani mutum ya samu yake tambayar shi "ina Malaman Da akayi taron dasu suke?"
*Tashin hankali ba'a sa maka rana.* Anan ake faWa mishi ai sunyi hatsarin Mota a hanyar komawarsu gida, Waya ta Kama da wuta Waya kuma ta bigi bishiya, amma ba duka bane suka mutu, Wasu suna asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Ai tuni Alhassan ya Fara zufa, koda akaje asibitin baiga malamba acikin majinyatan, babu kuma inda be duba ba , Anan Ya tabbatar malam ya mutu.

kashirSan yake kuka ya rasa yanda zai yi, Cikin kwanaki uku Da yayi a Zaria ya zama kamar zararre tsabar damuwa.
Haka ya dauki hanya ya koma Maiduguri, inda ya sanar da Inna kulu Abin da ya faru.
Tuni gida ya cika anata koke koke, yan uwan malam duk sun cika gida ana zaman makokin da babu gawa.

Shi dai Alhassan zuciyarsa ma ta bushe ko kuka ya kasa tsabar damuwa, Sai dai duk ya rame yayi ba?i.

Ranar da akayi bakwai ne ?annen malam da yayyenshi suka zo wai za'ayi rabon gado,
Dayake dama duk haushin malam din suke ji saboda yafisu wadata.

Komai sun kwashe tun daga kan gonakin malam har gidajenshi ciki harda wanda yaba Alhassan, wai karya ne Bai bashi ba.
Cewa Inna kulu sukayi ta kwashe kayanta tabar musu gida suka haWa ta da buhun masara guda Waya na dawa biyu.
Wai shine gadonsu ita da yaranta wai shi dama Alhassan Wan tsuntuwane.

Bakin ciki yasa ta tafi gurin mai gari ta faWa mishi, amma dayake sun siyeshi da cin hanci korarta yayi wai babu ruwan shi Baida ilimin rabon gado.

Kwanansu uku suna tunanin inda zasu koma amma sun kasa samun mafita, gaba Waya abin ya taru yayiwa Al-hassan yawa.
Suna zaune da rana Hafsat ta gama dafa abinci akayi sallama a gidan, wai ana neman Alhassan.
Kofar gida ya fita don ganin waye, yan sanda ya gani wai an basu dama ne su zo su musu watsi da kaya tunda sun ?i tashi.
Hakuri Alhassan yake basu amma haka suka kutsa kai cikin gidan, kayansu suka ri?a fitowa dasu waje, Sai Da suka gama tass sannan suka maida mukulli a gidan.

Makwabtan su ya ro?a ya shigar da kayan wani Waki da ba'a gama gyarawa ba, suka nufi gidan Inna kulu, itama abinda yaje ya Tarar anyi mata kenan..
Alhassan ya rasa kuka zaiyine ko me, abin duniya ya taru ya mishi yawa, dama haka Duniya take? Ace daga rasuwar malam yau kwana goma amma ji yanda rayuwarsu ta juye? Lailai wannan karin maganar me cewa *wani nacin darajar wani* gaskiya ce.

Nan makwabtan ya ro?a aka shigar da Kayan inna kulu sannan yace suma su zauna zai je ya dawo...
Gurin wani abokin shi Wanda suke polytechnic yaje, nan ya faWa mishi duk abinda ya faru, ya tausaya mishi matuka yace yanada wani gida amma ba'a Gama ba idan zasu iya zama kafin su samu wani

Har gidan ya kaishi sannan ya bashi mukullin gidan, mai akori kura ya nemo yaje ya kwaso kayayyakin su suka kai gidan sannan yaje ya tawo dasu Inna kulu da hafsa.

Bayan an gama shirya inda zasu samu su rika kwanciya ne Inna kulu ta fara tunanin mai za'a dafa da yamma.

Ita kuwa Hafsat tunanine fal cikinta "ace wai duk garinnan suna kallo ana wulakanta su amma babu wanda ya iya bada hakuri balle ya hana. Lallai duniya ta zama abin tsoro

Ji tayi cikinta ya murWa da karfi har Sai Da ta saki yar kara, ai ba'a daWe ba taji wani abu na bin cinyarta
Koda ta duba jini ne jajir dashi Yake Binta yana zuba,
Shiru tayi taki magana ganin irin halin da suke ciki, saida taga kamar zata mutu tukuna ta fara kiran Inna kulu,
Ita kuwa baiwar Allah tana chan tana fama da wuta,
Saidata daWe tana kira sannan ta jita, da sauri ta tawo tana cewa "lafiya kuwa Hafsatou?"
Ai ma?alewa Maganar inna kulu tayi abakinta "ta fara salati da sallallami , "Ahmad maza je ka kiramin yayanku a waje"
Ko kafin ya shigo Hafsat ta suma saboda yanda jinin ke zuba.
Da sauri ya dauke ta sukayi waje ana neman mai amalanke , dakyar aka samu wani guda Waya zai fita cikin gari, samu sukayi suka shiga zuwa general hospital da ita , emagency aka amsheta kuma sunata musu faWa wai basu kawota da wuriba.

Dakyar aka samo kan Hafsat saida aka kara mata jini leda uku ga wankin cikin da za'a yi Mata saboda ance Sari tayi.

Duk Anan kudin da hannun Alhassan suka kare, ita kuwa Inna kulu kuka kawai take kashirban "oh Allah kasa mu cinye Wannan jarabawar taka, daga wannan Sai wannan"

Alhassan kuwa ko zama ya kasa, gani yakeyi za'a ce mishi ta mutu.

Saida suka shiga suka ganta sannan hankalinsa ya kwanta,
Ita kuma Inna kulu gida ta ka ta haWo abubuwan da za'a nema idan hafsatou ta farfaWo.

Kwanansu uku a asibitin aka sallame ta, cikin ya zube kuma ba'a so a ri?a Sata mata rai, sannan kuma sunce ta dena Waukar abu me nauyi.

Duk wani kudi na gurin Alhassan sun kare, gashi ance abinci mai gyara jiki za'a ri?a bata Kuma za'a sai mata magunguna.


Ganin zama bazai yi mishi ba yasa ya Shirya ya fita, duk shagon da yaje neman aiki sai suce basa neman mai aiki suna da masu yi musu,
saida ya wuni a haka sannan ne ya shiga layin yan dakon sumunti
Dakyar ya samu kudin da za'a yi cefane a dafa abinda za'a Kai bakin salati.
Washe gari ma haka gurin dakon yaje dakyar ya samo abinda baza'a rasa yanda za'a yi ba
Cikin ?an?anin lokaci Al-hassan ya canza kamanni daboda wahalar tamishi yawa.
Makarantar ma bai zuwa, ana ta abinda za'a Kai baki ina zuwa wata makaranta!

Zama inna kulu tayi tana tunani "ya kamata na tafi garinmu, idan na zauna a garinnan wahala zata Iya kashe Alhassan, waWanda ma muke dolensu sun watsar damu balle shi, Gara na tafi kawai, inyaso sai yaji da kansa da matarsa, duk da kona koma ba wani daWi bane saboda mama ta rasu baba kuma ya tsufa, amma Gara na koma".
Sallamar Alhassan ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga "Barka da rana inna, dama zamu koma asibine wai ciwon cikin nata ya?i bari, kuma likita yace idan bai bariba mu koma, shine nazo in Miki sallama zamu tafi.

Murmushi inna tayi "to Alhassan Allah ya kiyaye hanya, kuma don Allah Alhassan duk rintsi banaso ka canza daga halin da na sanka dashi, komai wuya komai rintsi kada kaci haram.
Domin zamu iya jure yunwa amma ba zamu iya jure azabar Allah ba gobe kiyama.
Nasihohi ta ri?a yi mishi masu tsuma zuciya, daga bisani tace "to sai kun dawo Allah yayi maka albarka"

Duk sai Alhassan yaji shi sukuku, kamar beda lafiya, maganganun inna kulu sai sukayi mishi kama da wasiyya.

Suna fita inna ta haWa iya kayansu na sawa tashirya su zainabu, bayan tayi rubutu da ajami ta ajiye a inda idan su Alhassan suka dawo zasu gani "Alhassan nidai natafi garinmu, ina rokon ALLAH' ya Dada hada fuskokin Mu da alkhairi, ga kayan munan kuyi amfani dasu kafin Allah ya warware mana, zan dawo insha Allah, inna kulu"
Tasha taje tasamu direban ta mishi bayani, dayake mai tausayi ne ya basu kujera biyu kyauta sukayi Bauchi.

Bayan su Alhassan sun dawo ne suka tarar babu inna kulu babu su Ahmad.
Kuma babu duk wanin abin amfani a cikin gidan an kwashe.

"Bayan su baba kulu sunje Tasha Ashe tsalha kanin malam Musa ya gansu, shine ya dawo yasa aka bude mai gidan, cikin Sa'a kuwa ya tarar da takardar da inna kulu ta ajiye wa Alhassan.
Murna ya fara yi ya tattara duka buhun masara da dawar da aka basu, harda su gadon ?arfe dasu katifar inna kulu ya kwashe.
Bai barwa su Alhassan komaiba saima tasu katifar daya Wauke

Alhassan yasan inna kulu bazata kwashe musu kaya ta gudu ba.
Amma yana mamakin meya faru, "Anya lafiya kuwa"
Gidan mai gari ya tafi don ya sanar dashi abinda ya faru, amma ga mamakinsa daga isarsa yaji ana cewa "yawwa gama shinan ya kawo kanshi.

Besan hawaba baisan saukaba sai ji yayi an kamashi an daure yana cewa menayi?
Amma babu wanda ya kulashi aka kaishi akasa a turu.

Hafsat na zauna duk abin duniya ya sata a gaba, da ace ana kiran mutuwa to saita kira mutuwarta yau ta dauketa, jummalace ta shigo da sauri tana haki "Hafsa kiyi sauri ki hada kayanki ki gudu ga maigarinan ya aiko wai a Wakko ki, kuma an kama Alhassan an sashi a turu"
"Meyayi?" Hafsat tace cikin tashin hankali
"Nima ban saniba mamanmuce tace na kawo miki wannan kudin wai ki gudu gida kada kema su kama ki"
Tsofaffin chukurkuWaWWun kuWi ta mika wa Hafsa.
Jikinta har rawa yake ta Wibi abinda zata diba tayi bayan gari tabi ta gonaki saboda idan taje tasha za'a iya ganinta.

Tasha wahala har sai da dare yayi tana tsaye a bakin titi ta kasa samun mota.
Sai wajen goma saura duk tsoro ya gama kamata sannan ta samu wani mutum yayi lodin kwandina ya tsaya ya dauketa, gashi motar batada gudu, sai washe gari suka isa Jigawa
Motar malam madori ta samu ta hau.

Da kuka ta shiga gida, hankalin mahaifinta yayi mugun tashi ganin yadda Hafsa ta koma
"Meya faru? Ina Alhassan din da malam?"
Lokaci Waya ya jero mata duka tambayoyin

Tana kuka ta fada musu abinda ya faru tun daga ranar da aka fadi malam ya mutu

Zuciyar malam barau kamar ta fashe saboda ba?in ciki, "yaushe malam ya mutu bai saniba," yan uwan malam ne suka yiwa ahalin malam Wannan tozartar saboda babu idon malam, me zumunci ya zama ne yanzu?"
*Allah yasa mu dace*

Washe gari da sassafe ya shirya ya dau hanyar zuwa maiduguri.

*#SAGIR*
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*
```pls comment and share```
*IZAYAR RAYUWA*

*3*

*MATAR RASHEED*

______Koda malam barau ya isa Maiduguri babu inda ya zarce sai gidan mai gari.
Anan ya tarar dasu tsalha sunata shan hira, malam bai raga musu ba nan ya sauke musu duk wani nauyi da zuciyarshi tayi ya kara da cewa "in dai duniya ce ta isa kowa riga da wando, kuma duniya ma na jiran wanda ba'a haifa ba."

"Kubar ganin malam ya rasu, to kuma taku tana hanya, shidai mai gari yayi tsuru tsuru ya kasa cewa komai tsabar Kunya."

Anan aka fito mishi da Al-hassan, fadan malam barau sabo ya dawo ganin yanda Al-hassan ya koma,
"Koda bazakuba Al-hassan wani abu a dukiyar malam ba to ku sani kulu da yaranta sune masu gadon malam amma bakuba."

"Amma saboda son zucia shine kukayi yanda kuka ga dama, kada ku manta Allah baya barci..."
Haka dai aka rabu abin babu daWi,
motar Wiban kaya ya samu suka kwashe ragowar kayan da aka bar musu suka dau hanyar Jigawa.

A hanya malam yake yiwa Alhassan faWa "meyasa ko ta wasika baka sanar da niba?
Da duk haka bata faruba daka sanar dani tun tuni, amma haka Allah ya tsara."

Hakuri Al-hassan ya bashi da karin cewa hankalin shine ya tashi ya manta komai tsabar rudanin daya shiga.
"Aiba fushi nayiba dama, Allah ya shige mana gaba" Cewar malam barau

Sai wajen sha Waya na Dare suka isa malammadori.

Cikin farinciki Hafsat da mamanta suka tarbe su, kayan abinci kala kala aka jere a gabansu.
Bayan sun kammala malam yasa aka gyarawa Alhassan dakin zaure, anan ya kwana.
Da sassafe malam ya fita cigiyar gidan da zai siyawa su Alhassan, domin gani yake idan yabar Alhassan ya wahala kamar yaci amanar malam Musa ne.
A Wan gaba dasu aka samu wani madaidaici .

Bayan anyi ciniki ya biya su, aka kwashe kayansu aka kai gidan inda malam barau yasai musu wata sabuwar katifar da abubuwan da baza a rasa ba.

Alhassan ya kasa gane wannan wane irin karamci ke tsakanin aminan biyu.
Babu abinda basu yi mishiba a rayuwa, sai dai yayi ta yi musu fatan alkhairi ALLAH ya saka musu da gidan aljanna.

Haka rayuwa taci gaba kamar babu abinda ya faru sai dai lokaci bayan lokaci malam Musa yana faWo mishi sai dai yayi ta mai addu'a.

Bayan komai ya dai daita ne malam yasa Alhassan ya shirya domin suje Bauchi suga ko inna kulu na can saboda sanda aka je neman aurenta a Bauchi tare dashi aka je yasan garinsu da gidan iyayenta.

Koda suka sauka achan suka tarar da ita. Alhassan ba karamin daWi yajiba don ji yayi kamar malam ya gani.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login