Showing 18001 words to 21000 words out of 66006 words

Chapter 7 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

130

Mummy na niyyar cewa bari sadeeq ya kaiku idan babu inda zashi, Ta jiyo Muryar sadeeq nacewa "bari na kaiku kawai"

Mamaki ne ya cika mummy "a'a me sadeeq yake yi haka ne", amma sai ta basar bata nuna komai ba "tsaya nazo hafsat"

mikewa tayi ta shiga cikin dakin dake gefenta,
Ba'a Wauki lokaci ba ta Fito da babbar leda ta mikawa sadeeq "gashi idan ka kaisu sai ka bata.."

Amsa Sadeeq yayi yana murmushi suka fita...

Hafsat ta dawo donyi mata godiya yasha gabanta tare da cewa "muje"
Duk kunya ta cika ta haka ta juya badon tana so ba.

Seat din gaba ya Bude mata "Bismillah shiga"

Bayan ta shiga ya Maida kofar ya rufe ,
Dai dai Nan itama murja ta rufe tata kofar sai gumtse dariya takeyi.

Driver seat ya zauna inda yayi wa maigadi horn ya BuWe tangamemen gate din gidan ya nausa hancin motar waje.

Tunda suka shiga motar murja ke mamaki,
Kamshine iri iri masu Dadi da shiga Rai, ga sanyin Ac Yana dada karawa kamshin armashi

Suna zaune a motar ne Amma kamar suna cikin falour domin ko alamun tafiya akan titi basa ji.

Ta Sangare hafsat kuma Sabanin haka ne, domin ita ji takeji kamar ta ruga da gudu.
Zaman ya isheta kuma da alamun idonshi Yana kanta, ko kwakkwaran motsi ta kasayi

Cikin tsautsayi ta dago kanta zata gyara gyalenta dataji Yana Shirin zamewa suka hada Ido, take ya sakar mata wani irin classic murmushi Wanda kafin kasamu Mai irinsa saika shirya.

Bugun zuciyarta ne ya tsananta kamar zuciyarta zata fito waje, da sauri ta sauke kanta kasa tana Jan Galen ta zuwa fuskarta.

"Hafsat"
Taji ya ambaci sunanta in a low tune

"Na'am" tace a takaice tana tararrabin mezai biyo baya.

"Ko sau daya Baki taba ganina a makarantar kuba?"

"Eh" tace a takaice

"Amma ni dazu na ganki"

Murmushi tayi batace komaiba.

"Baki tambayeni a Ina na gankiba?"

Murmushi hafsat ta daWa yi, domin jinta take kamar anyiwa bakinta linzami

Tsinkayar muryar murja tayi tana cewa "Auncle ai sai dai kayi hakuri ita haka take Bata magana daga eh sai A'a idan ka matsa mata sai tayi maka murmushi"

"Wallahi tunda nazo garin nan naketa son in shiga gari inyi yawo Amma ta kunsheni a gida kamar Mai takaba
Daga makaranta sai gida a gidanma cikin daki sai fa idan na matsa ne, nake cin Sa'a ta kaini sahad ko chicken republic

"To fah haka hafsat din take?"

"Wallahi haka take Sam Bata kyautawa"
Cewar murja Jin Dadin ta samu abokin surutu.

"To kada ki damu kin samu me kaiki yawo daga yau, Amma daga Ina kikazo?"

"Daga Kano nazo, kusan satina uku Amma babu inda na sani, haka take so na koma ba tare danaje ko ina ba.

"Ai Sam yanzu kada ki damu saikin gaji da yawo"

Kallon hafsat yayi "kema saina koya Miki" hade da dage gira Yana sakar mata wani irin killer smile.

Mutum mutumi hafsat ta zama, itadai fatan ta a karasa company ta sauka,
Hakanan takejin tsoron wanna bawan Allahn gashi sai hada Ido suke, kuma idon nashi ma kanshi tsoronshi takeyi


Dai dai Nan suka Isa company, ai ko kyakkyawan parking Bata bari yayiba ta Bude kopa ta sauka da sauri Ko takan murja Bata biba ta nufi office din Abbanta

Tana shiga ta nufi fridge, ruwa ta Wauka hade da zama a saman kujera tana sauke ajiyar zuciya.

"Sannu Abba mun dawo"

"Yauwa noor! yakike ta zufa? Kuma Ina murja?"

"Zafine ya dameni, itama yanzu zata shigo"

Ruwan ta Bude ta kafa a bakinta, Saida Tasha kusan ra??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bi sannan ta ajiye robar Saman table.

Murja ce ta shigo da sauri "waike hafsat meye haka? Wulakanci fa babu kyau"

"Ban saniba uwar surutu, ke wallahi da surutu na kisa saiya kasheki, Bakisan mutumba kin saki Baki kina zuba kamar famfon daya burr......"

Dif hafsat tayi ganin sadeeq ya shigo cikin office Win.
Me murja zatayi in Ba dariya ba.

Da sauri Abban hafsat ya Mike "yallabai yau Kaine ka kawo mana ziyara?" Hade da Mika mishi hannu don yin musabaha.

"Wallahi Abba! aini na dawo dasu hafsat"

Kallon hafsat Abba yayi "shine Baki fadaminba?"

Shagwabe fuska hafsat tayi "Abba nifa ban sanshiba"

"Tashi ku fita ku bamu guri, shine fah me companyn Nan"

"No Abba barsu mana dama dai na leko ne na gaisheka, sunce zasu amshi sakone a gurinka sai na kaisu gida kawai"

"A'a bazai yuwuba kabari kawai suhau adaidaita"

"Murmushi yayi Karka damu Abba" Yana barin office din hade da cewa murja "Ina jiranku a waje"

Gallon biyu ya Mika mata na madarar shanu "Maza tashi ku tafi kada ki Bata mishi lokaci"

A kumbure hafsat ta Mike ta fita murja na biye da ita a baya tana ?ar dariya mara sauti.

Kamar dazu yanzuma shi ya Bude mata kofa tashiga ya rufe.

Me makon suyi hanyar gida Amma sai Taga sunbi wata hanyar daban.

Gashi murja ta biye mishi sai surutu sukeyi.

A bakin ShopRite yayi parking.

Da fari hafsat taki fitowa Saida yayi da gaske tukuna ta fito Shima sai raba idanu take kamar mara gaskiya.

Ciki suka shiga yace su zabi duk abinda sukeso.

Murja sai rawar Kai take, dauki wannan dauki wancan.
Ita ko hafsat ko motsi taki yi, Saida yaga dagaske bazata daukaba tukuna ya fara diban duk abinda hannunshi yakai Yana zubawa a cikin shopping basket...


*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment```
*IZAYAR RAYUWA*

*9*

*MATAR RASHEED*


_______ Haka hafsat ta Zama kamar wata hamshakiyar hajiyar da aka rako shopping, domin Shine dauki wannan dauki wancan, har canzawa murja yake idan yaga ta dauki abinda baiyiba, saboda shi yake rako hajiyarshi da kannenshi shopping.

Saida suka gama tsaff ita dai hafsat nata ido don biye take dasu kawai duk inda sukayi.

Abin yana ta ba hafsat mamaki, domin duk inda suka bi sai taga anata girmama sadeeq, gashi shi kuma yazo yana biye musu.

Kayan ma Webo musu akayi akakai mota, sannan suka shiga don yin gida.

Sun zo zasu wuce ta gurin tsohon da yake saida su gauta da goro hafsat tace *"uncle zanyi siyayyah a can"* hade da nuna gurin tsohon da yatsanta manuniya.

Kallon ta yayi "mezaki siyo?"

"Goro da gauta"

Kwalalo ido yayi =?3? "wazai ci?"

Da sauri murja tace "saka ranka a inuwa baaba ce zata ci ba ita ba" >?-?

Murmushi yayi "ai nasha ?anwar tawa tsohuwace" yana langabar da kanshi gefe irin na yara.

Ita kanta hafsat saida abin ya bata dariya amma ta gumtse.
Gyara parking yayi a inda bazai shiga ha??in mutane ba Sannan ya sauka, bayan kamar minti uku ya shigo ri?e da ?atuwar ba?ar leda.

Cigaba da tafiya sukayi murja nata zuba, shi kuma yana biye mata.

Dai dai gidan yayi parking "to yaushe zanzo mu tafi park din?"

"Gobe" murja tace da sauri.

"Ke kadai zaki amma ko?" cewar hafsat tana hararar ta.

"Tab Wallahi kafata kafarki tare zamu"

"Ai sai mu gani inkin isa kisa naje dole"

"Inni ban isaba ai Abba ya isa Koh?

Hannu tasa da nufin Bude kofar don ta fita daga motar Amma saita jita gam a rufe, basarwa tayi ta gyara gyalen kanta.

Duk move dinta Yana kallo amma sai ya basar kamar be gane me take nufi ba.

"Murja ki Kai kayan ciki saiki dawo mu tsaida magana don naga kamar an Bata wa hajiya ta Rai" cewar Sadeeq yana kallon hafsat ta gefen ido, Bude securityn kofar baya yayi saboda Murja ta fita

"To uncle" murja tace hade da yayibar kusan Leda uku tanayin cikin gida dasu.

Jigum hafsat tayi sai bugun zuciyarta daya Kara tsananta, ga sanyin Ac Amma gumi ne yake zirarowa daga cikin gashinta Yana wucewa ta gefen wuyanta.

"Subhanallah hafsat menene"

?an murmushi ta kakalo "babu komai"

"A'a da komai gashinan kina zufa kuma alhali motan babu zafi, ko bakida lafiya ne mu tafi asibiti?"

"No uncle lafiyata kalau"

"Ko tsorona kikeji?"

"Da alama" cewar murja da tazo don kwashe ragowar kayan.

"Wai murja Ina wasa Dake ne Koh?" Hafsat tace a kufule

"Ayya Aunty rabu da ita bakya wasa da ita, kuma idan ma tsorona kikeji ki Dena ki saki jikinki ni yayan kine"

Ita dai Batace komai ba illa jujjuya purse dinta da takeyi.

"Na dawo" cewar murja tana sako kanta ta windon Dake gefen hafsat.

Securityn kofar ya cire "Hafsat matsa mata ta shigo sai mu tsaida ranar da zan kaiku park din" Ai da sauri ta Bude kofar ta ture murja gefe ita kuma tayi cikin gida da gudu, tana jiyosu suna mata Daria Amma Bata damu ba.
Don ji take kamar zata fashe idan ta cigaba da zama a cikin motar.

A falour ta tarar da baaba Indo "kawalli yau da goshi kika fita kenan murja tace kin samo mana zankadeden miji"

"La baaba karya takeyi gaskiya! Mai Companyn su Abbane fa ya rage mana hanya da mukaje gidansu"

"Karyane Allah ninasan uncle sonki yakeyi don duk ga alamu Nan sun nuna" Cewar murja wadda shigowarta kenan

Kwafa kawai hafsat tayi Bata iya cewa komaiba

Ummanta ce ta fito daga kitchen "wai meke faruwane naji anata musu"

"Umma uncle sadeeq ne Mai companyn da daddy yake aiki yace Yana son aunty hafsat" murja tace tana bubbude cikin manyan shopping bags din Dake zube a tsakar falourn

"Kingama duk shi ya siyan mata wadannan kayan"

"A'a madalla da wannan fitar gashi munyi miji" cewar baaba Indo tana Waukar wani flat shoe Mai kyau Wanda akalla kidinshi zai Kai 14k

Fashewa hafsat tai da kuka tashige dakin ummanta, kan gado ta fada taci gaba da kukanta

Umman ce ta biyota "haba *Noor* meye abin kuka? Kinsan dai bazan yarda da maganar wani Sama da taki ba Koh"

Dagota tayi "fadamin meya faru?"

Goge hawayen fuskar ta tayi "umma kinga fa ni bece Yana sonaba, kawai dai yana ta kallona ne gashi nikuma tsoronshi nakeji, kuma Ko sanda na fara ganin shi Saida zuciyata ta buga kamar zata fashe"

"Haba *Noor* to wannan ne abin kuka?" Goge mata hawayen tayi "kada ki Kuma yin kuka kinji, idan ma cewa yayi Yana sonki ai babu komai"

"Umma ai murja ce taketa tsokanata har dariya taketa yimin tun a cikin motar"

"Nace kidena damuwa sadeeq yaro ne nagartacce, saboda abbanki Yana yawan bani labarinshi"

"To umma nadena damuwa kiyi hakuri!"

"Noor bakimin komaiba kawai dai ni bana son ganinki cikin damuwa ne, kinsan kece haskena Koh?"

Dariya hafsat din tayi "Nice noorin ummata"

Sanyi maman hafsat taji a ranta ganin hafsat din ta saki ranta (haka akeso iyaye mata su kasance masu Jan yayansu a jiki inba hakaba sai suje su Fadi damuwar su a inda za'a Basu gurguwar shawara)

Falour ta koma Bata ko Kalli murja ba, wadda ta dage sai gwada wani golden din dankunne fashion take a kunnenta.

Dakinta ta shiga, kaya ta tarar akan gado iri iri.

Wata golden clutch ce ta dauki hankalinta, daukanta tayi ta Bude tana duddubawa
Ji tayi ta burgeta sosai
Agogo ta dauka a gefe Shima golden, kayan taketa kallo kamar ya shiga ranta yaga abinda takeso.

Wata Leda ta Gani a gefen gado babba
Dauka tayi ta Bude ta ciro kwalin Dake ciki.
Wata irin peach colour Dubai abaya ce Mai kyau anyi mata ado da Swarovski crystals stones daga wuyanta har kasa, haka Shima hannun.

Ga mayafinta Shima duk stones Win ajiki.

Rungume rigar tayi tana murmushi "Rigar nan ta shiga raina"

HaWa duka kayan tayi ta zuba a Cikin wardrobe, ita kadai taketa murmushi tana duba inda take ajiye kaya marasa nauyi tanaso ta chanza.

"Sister don Allah kiyi hakuri wallahi banyi niyyar Bata Miki Rai ba I'm just trying to have fun" cewar murja dake tsaye a bakin kofa ri?e da labule.

"Ke kika sani aini ban damuba"

Karasowa tayi ta rungume hafsat "haba my sweet sis I'm sorry please"

"Rabu Dani ya wuce"

Tsalle murja tayi "dagaske sisy?"

"Nodding din Kai hafsat tayi "eh na hakura"

"Yanzu kina nufin zakije park din kenan?

"Eh zani" cewar hafsat tana cire doguwar rigar jikinta tayi hanyar bayi donyin wanka.


?????????????????

Sadeeq na Isa gida ya fada kan 2sitters couch Yana Maida numfashi "ukhty wallahi na gaji"

Harararshi mummy tayi "kada ka cikani da mita naga dai bani nace ka kaitaba don kanka ka kaita, Da nice nace zanci arziki da kirikiri zaka nuna min ban isaba, Amma dayake aikin kankane ba jiran umarni...."

Husna ce tazo gabanshi rike da bottle water Mai sanyi "uncle Sha ruwan nan zaka Daina Jin gajiyar, malamin islamiyar mu yace mana ka kyautawa Mai kyautata Maka, kuma kaga kana siyo min ice cream"

Dariya sadeeq yayi "thank you daughter anjima ma zan siyo Miki wani In'sha Allah"
Dariya tayi itama tabi hanyar dakinta da gudu.

Kallon mummyn husna yayi "sister kinga yarinyata ta fanshe ki"

Dariya tayi "to Ina gimbiya hafsat din take"

Sosa Kai yayi "gimbiya kuma?"


Dariya ta kuma kyalkyalewa da ita "ainaga hafsat dince Bata raga makaba ba, data tashi satar ba iya zuciya ta sace ba harda tunaninka da ruhinka"

"Ina kallonka sanda ka kalleta Saida ka kasa gaba ka kasa baya"
Murmushi yayi "Lallai ukhty Kin zama yar jarida?"

"Hmm aini Dadi naji tunda Kai so kake ka tsufa ka rasa me aurenka, ko hafsat dinma sai dai tayi maneji dakai"


"Tab aunty zakiyi zunubi fa, ki Kalli gentle kamata kice za'a Yi manage Dani?"

Saman stairs ya tashi ya haye ita kuma tanata kyalkyale dariya, wani farin ciki taji Yana ziyar tarta domin ta Dade tana addu'ar Allah ya kawo mishi matar aure, kuma ga dukkan alamu hafsat will make a good wife.


*WANENE SADEEQ?*
Abbakar sadeeq Aliyu shine cikakken sunanshi.
?a ne ga babban Dan kasuwa Alh Aliyu gwani likoro,

Su hudu Allah yaba iyayensu, shida yayar shi Khadija wato maman husna sai Maryam da Zainab Wanda suke gida tare da mahaifiyarshi.

Ya kasan ce duk wani burin mahaifinshi Yana kanshi saboda shine da namiji tilo da Allah ya bashi, duk da kasancewar shi Mai gawurtaccen kudi Hakan be Hana yaba Yaran shi kyakkyawar tarbiyya ba.

Sun taso cikin so da kulawa .
Tsakanin Khadija da sadeeq shekara dayane shiyasa tare ake musu komai harta da ajinsu ma daya kuma Koda suka girma Basu Dena likewa juna ba sai dai ayi faWa a shirya.
Mamansu Bata sake haihuwa ba tunda ta haifi khadija da Sadeeq, Saida sadeeq ya shekara goma sannan aka samu cikin Maryam bayan shekara daya aka kuma haifar Zainab daganan kuma haihuwar ta tsaya.

Sanda suka gama secondary ne Abban su yace yanaso yakai sadeeq Oxford yayi karatun engineering achan, ita kuma Khadija ta zauna tunda ita macece ta tsai da miji ayi mata aure.

Ai tuni duka suka fara ciwo kamar zasu mutu musamman Khadija tunda dama ita tafi kawazucin shi saboda itace yayar shi.

Ganin abinda ya faru yasa aka kaisu duka su biyun chan Oxford din ..

Cikin ikon Allah suka gama karatun su a shekara huWu suka dawo gida, a lokaci Maryam nada shekara Sha biyar ita kuma Zainab Sha hudu.

Nan mahaifinshi ya dukufa nuna mishi duk wata harkar kasuwancinshi daga bisani ya mallakamai companyn da Abban hafsat yake aiki kyauta.

Ba'a dau lokaci da ba Sadeeq Companyn ba Allah yayi wa Alh Aliyu rasuwa, inda gaba daya Ahalin Saida suka girgiza haka gidan ya koma shiru babu Dadi, kowa ya zama sukuku, ko Abinci babu me iya ci.
Don ma Allah yasa sadeeq akwai kula sosai. ahankali ahankali ya Rika cire musu damuwar, yau yakaisu shopping gobe gidan zoo jibi park har dai kowa ya hakura.

Ana haka Allah ya fitowa da Khadija miji wato Alh sulaiman Shima a companyn Sadeeq yake aiki,
Akayi biki amarya ta tare, ai batafi wata biyar ba sadeeq ya kwashe kayanshi ya koma gidan da zama don yafi sabawa da ita fiye da mahaifiyarshi, Amma duk da haka kullum sai yaje gidansu ya ga ummanshi.


Haka komai tare sukeyi tun Alh sulaiman na damuwa har ya Daina, ko cikin husna tare sukayi laulayi shine Mai dauko bawo idan za'a Yi amai, ya kwashe ya goge idan tayi a kasa. duk abinda tace tana so saiya nemoshi zai dawo gida har Allah ya sauketa lafiya.


Yanzu husna nada shekara bakwai, Sadeeq kuma talatin da uku, Khadija talatin da hudu sai Maryam ishirin da uku itakuma Zainab da biyu

Tun tuni Khadija ke fama dashi yayi aure Amma Sam yaki wai bega

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login