Showing 21001 words to 24000 words out of 66006 words

Chapter 8 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

129

wadda zata iya zama matar Shiba, kuma matan ma basuda tabbas.

To shiyasa tun randa taje company Taga hafsat ta kwallafa ranta akanta kullum sai tayi addu'ar Allah yasa rabon sadeeq ce
_wannan kenan_.........


Washe gari tunda wuri hafsat ta shirya tayi wanka tasa abayar da sadeeq ya siyo mata da takalmi sannan ta rike clutch din a hannunta.


Murja nason ta tsokaneta Amma babu Hali.

Sai itama tayi wankan ta shirya ta samu gefen hafsat din ta zauna.


Wajen karfe biyu na rana hafsat tajiyo sallamar Abban ta, da gudu ta tashi "yauwa Abba yau yawo nakeso ka kaimu kaga weekend ne kaima babu inda zaka k........"

Shanye maganar tayi ganin sadeeq a bayan Abban Yana smirking.

Dan daburcewa tayi "Ehm uhm Abba sannu da zuwa!" Bata Jira ya amsaba tayi dakinta cike da sauri me kamar gudu...

Murmushi sadeeq yayi don ya gane ganinshin da tayine yasa ta rude but aranshi yaji Dadin ganin kayan daya siyan mata a jikinta.

"Kunya adon mace" ya fada a zuciyarshi, shi kuma Hakan da takeyi sai yake birgeshi.


Umma da baaba Indo ne suka shigo suka gaisa dashi inda baaba Indo ke cewa "Nagode fa sosai, don Naga gauta da goro cikin Leda, sai a firinji na zuba su sai dai na Rika dauka daya bayan daya. Inaga saina fi wata biyu Ina ci" ta gane shine kasancewar Abban hafsat yace shine me Companyn da yake aiki.

murmushi Sadeeq yayi "ko za'a karo Miki ne Uwargida"

"Wai! bari na gama da wannan tukuna"

"Hafsatou! Hafsatou!!
Ki fito kizo ku gaisa da Sadeeq"

Hafsat Dake daki a zaune ji tayi kamar ta zunduma ihu Jin Kiran da Abba yayi mata..


Salalau salalau ta taso ta fito, tundaga bakin kofa sadeeq ya zuba mata Ido, tana Karasowa Abba ya tashi ya shiga ciki don ya watsa ruwa.

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*10*

*MATAR RASHEED*


________A Warare Hafsat ta zauna a kujerar dake daura dashi "ina yini uncle"

Murmushi yayi "kina lafiya? Ya kuma gajiyar gudu da zufa?"

?an Murmushi tayi tana daWa cukuikuye fuskarta a mayafin abayar dake jikinta allamun jin kunya

"Hafsat naga alamun magana ma wahala take yi miki meyasa?"

"Babu komai" tace tana sonyin murmushi

"Nifa nazo ne na kaiku park din, zakije?

"Eh uncle zamuje" cewar Murja wadda ta fito da sauri daga inda ta labe tana lekensu "Amma gaskiya uncle akwaika da cika alkawari, ai da har na hakura ma da naga abinda yar uwar tawa tayi jiya"

"Murja kenan! kin wuni lafiya?" Cewar Sadeeq yana mamakin yadda murja bata gajiya da surutu

"Au banfa gaishekaba ko! wallahi tsabar murna ce "Ina yini?"

Shi dariya ma ta bashi, don ya harda yarinta ke dawainiya da ita "lafiya Lau! murja, ya hajiya ta ta kwana?"

"Lafiya Lau ta kwana Uncle "

"Masha Allah, haka nakeson ji, ku tashi muje to!"

Saida ya wuce tukuna hafsat ta mike suka bi bayan shi bayan sun leka sunyi wa Abba da umma sallama, kamar kullum yauma gaba ya Bude mata ta shiga ya rufe, talkative kuma ta shiga baya ta zauna.

Amma hakan bai hanata zankalo wuyanta gaba tana surutu ba, shi ma sadeeq ya biye mata an maida hafsat kurma.

Tafiyar minti 37sukayi suka isa *KEJE GRILLS City park* Dake Ahmadu bello way.

A Parking lot yayi parking sannan ya fita ya budewa hafsat kofa, gaba daya ita kunya ma yake Bata, ace Babba kamar sadeeq ya Rika Bude mata kofar mota?!

Murja kuma tuni ta fito tayi gaba tana rarraba Idanuwa...

Babban symbol din Dake gun ta nufa tana mamakin abubuwa iri iri Dake gurin "ikon Allah,uncle haka gurin yake?

Murmushi yayi "to ki bari a shiga ciki yadda zakifi jin dadin yin tambayar da kyau"

Hafsat na biye dasu ahankali, sam hankalinta ma baya gurinsu tunanin halin sadeeq takeyi "babban mutum ne Amma Sam bashida girman Kai"

Ji tayi tayi Karo da wani abu "dumm"

Da sauri ya riketa Yana kare mata kallo "sannu! tunanin me kikeyi haka?"

Ita kuma hafsat kunya gaba daya ta rufeta ganinta a jikin namiji, da sauri taja baya tana sauke ajiyar zuciya, domin gaba daya ta dimauce.

"I'm sorry please, don Allah kayi hakuri" hafsat ta fada tana kallon mutumin

Akalla zai Kai shekara Arba'in Amma daka kalleshi kaga d'an kwaya domin ko a yanzu a bige yake Amma saika lura zaka gane.

Ganin bataga su sadeeq ba yasa ta ruga da gudu don shiga cikin gurin.
bin bayanta yayi Amma saiya juyo ganinta tsaye da sadeeq don yasan waye shi.

"Hafsat me kika tsaya yi?, ai ban San Bakya bin muba Saida na waigo naga babu ke a bayan mu"

Murmushi tayi batace komaiba.

Dan matsawa kusa da ita yayi "to muje"

Gaba ta shiga ya bita a baya, inda ta hango murja a zaune ta karasa itama ta zauna..

Sit din Dake kallon na hafsat ya zauna "murja je kiyi mana bulking Win shiga ciki"

Da sauri ta mike ta nufi inda Taga kowa na zuwa.


Gyaran murya yayi "Hafsat I need all your senses here, and banso ki fadamin abinda ba gaskiya ba"


Dan natsuwa tayi sannan tace "to uncle"

"Meyasa duk sanda kika ganni sai ki daburce ki rude?"


Kamar saukar aradu haka taji tambayar, Kara daburcewa tayi duk yanda taso ta saita kanta Amma ta kasa.

Wannan shu'umin murmushin nashi yayi "Again!, daga tambaya sai cibi ya zama 'kari?"


"To ki kwantar da hankalinki domin yau nagama gane wacece ke, dama duk Mai yin irin laifin da kike aikatawa a boye idan ya ganni haka yakeyi"

Kwalalo idonta waje tayi "wallahi uncle babu abinda nake aikatawa a Soye ka yarda Dani"

"Inji wa? Bayan na gama gane komai"

Hankalinta ne ya dad'a tashi "wallahi uncle ka yarda Dani babu wani laifi da nake aikatawa a boye"

Farin ciki ne ya kamashi ganin ya samu hanyar da zasuyi hira babu Jin kunya "kinga ni 'Dan binciken farin kaya ne a Soye kuma babu Wanda ya sani, yanzu zan Miki wasu yan tambayoyi idan kinada gaskiya ki kwaci kanki idan bakida ita kuma hmmm"

Zuciyar tace ta buga da karfi "na shiga uku wai wane laifi nake aikatawa? Tambayar da tayiwa kanta kenan a cikin zuciyar ta.


Amma a zahiri matso da fuskarta tayi kusa dashi "nayarda uncle! ko wace tambaya ce kamini kuma innayi Maka karya kamini koma menene" ya lura a kwaita da firgici ga yarinta da yagani yanzu gaba daya a tattare da ita wadda da bai lura da itaba, don shi a zatonshi takai sa'ar Maryam kanwarshi


Dariya ce ta kufce mishi Amma sai yayi saurin basarwa "hmm shikenan to shekararki nawa?"

"Next month zan ciki 16years"

"Hu'um! lallai shekara Sha shida? Sai kace broiler chicken, duk wannan girman jikin nata?" Sadeeq ke zance zuci......


"Ke wace yare ce?"

"Ban saniba Amma dai mamana shuwa Arab ce babana kuma kanuri ne, ni bansan me za'a kiraniba"

Gyada Kai yayi "okay to wane aji kike a school?"

"Ina ss1"

"Maza nawa kike kulawa a makaranta?"

"Waje ta dada fito da idonta nifa da bana kula kowa daga baya nema na fara kula su fidya sai Mr naph shi bama ni ke kulashiba shine yake yawan yi mini magana"

"To izu nawa kike a Al Qur'ani?

"Aina sauke Al Qur'ani"


Lallai ba karya dole ta kasance Mai nutsuwa, abinda sadeeq yace kenan a zuciyar shi, a fili kuma yace "good work Zaki iya karanta mini ko wace sura nakeso?"

"Eh zan iya"

"Samarin ki nawa"

"Uncle Banida saurayi, Ko Ada guda Waya ne wani sagir a garinmu kuma ya rasu"


Zoben hannunta ta kama tana murzawa da sauri da sauri batasan tana yiba dalilin Tuna sagir da tayi...

"Shi yabaki zoben nan kenan"

Murmushi tayi "eh"

"Allah sarki, to Allah ya jikanshi"

Murja ce ta karaso gurin "uncle nifa naje bansan yanda akeyiba."


Murmushi yayi don jinshi yake sakayau ya samu abinda yakeso cikin sauki "shiyasa hausawa sukace duk Wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi"


Kallon hafsat yayi "taso muje na nuna Miki wani abu"

Da sauri ta Mike domin bataso tayi wani abu yace tayi laifi"


Guri guri ya Rika kaisu yana nuna musu, ita kanta hafsat abin ya burgeta sosai sai murmushi takeyi..

Ya lura da Hakan shiyasa Saida ya nuna musu ko Ina daga bisani ya musu order din chocolate and vanilla ice cream da burger sai apple and pineapple smoothie..

Cikin Mota suka koma murja sai sambatu takeyi "Aini ko iya Nan nazo nasan nazo abuja, Amma da kullum Ina Waki a ?unshe!!"

Kallon hafsat sadeeq yayi "yanzu Ina kikeso nakaiku?

Murmushi tayi "kabari sai gobe kakaimu wani gurin yanzu gida nakeson mu koma"

Murmushin yayi Shima "to shikenan Allah ya kaimu goben lafiya"

Saida ya tsaya a sahad ya ciko musu Leda da kayan Zaki da makulashe Tukuna yadau hanyar gida.

Koda yayi parking yau sai yaga hafsat Bata fita ba kuma batada alamun fita.

Murja cema ta kwashi ledoji tayi cikin gida tana washe Baki.

A hankali ta Bude kofar ta fita, ya lura da magana a bakinta Amma sai bece mata komai ba.


Ta juya kamar zata tafi sai kuma ta dawo "Uncle pls ka yarda dani, babu wani mugun Hali da nakeyi a boye Allah!"


Murmushi yayi don yasan za'a Yi haka "Eh na lura da hakan Amma saina ?ara yin bincike akai tukuna"

"To uncle mungode sosai ka gaida mummy da husna"

Yaji Dadi sosai yanda ta nuna ta damu da nashi, Yana kallonta har ta shiga gida sannan yayiwa motar key ya nufi gida shima


???????????????????

A falour ya tarar da mummyn husna ita da Maryam suna hira.

Angon hafsat bada kanka a sare..... Cewar mummy tana dariya "sai yanzu"

"Wallahi sai yanzu sister kuma na gaji sosai"

"Ai aikin noorol Ayn Dinka kayi shiyasa"

Murmushi yayi "kumafa sunan yayi, *NOOR* Haka ma zan Rika ce mata"

Tashi tsaye yayi daga du?on da yayi a kafadar kujera "Banga husna ba"

"Tana barci" cewar Maryam....


"Okay bari na watsa ruwa, yanzu zan sakko"
Sannan yayi hanyar stairs cikin hanzari


????????????????


Koda hafsat ta shiga gida a falour ta tarar da murja sai zuba surutu takeyi tana ba baaba Indo da umma labari, sannu da gida tayi musu tace bari ta watsa ruwa, tayi hanyar dakinta

Ko bayan ta fito daga wankan tayi sallah Bata fita faloun ba saita kwanta tanata tunanin maganar da sukayi da Sadeeq, to ita wane laifi takeyi?

?????????????

A kwana a tashi asarar Mai Rai, kusan duk weekend haka sadeeq zai zo ya daukesu ya kaisu yawo.

Babu Wanda baisan labarin soyayyar su ba, don har ya rigada ya faWawa Abban hafsat cewa Yana sonta.
Kuma ya zama ?an gida, kuma duk sanda yaga dama zaije gidan su hafsat din suyita hira shida baaba Indo.


Ita kuwa hafsat Sam Bata kawo komai a ranta ba tunda bai taba cewa Yana sonta gaba da gaba ba....

Murja ta koma gida don hutun Makarantar su ya ?are, gaba Waya gidan sai yayiwa hafsat babu Dadi, har kuka Saida tayi sanda murjar zata tafi "oh Ashe kowama yanada ranarshi.
Yau ga ranar murja=?
?


Wayar hannunta Samsung Galaxy wadda sadeeq ya siyan mata ita da murja taketa jujjuyawa, sadeeq take so ta kira ya kawo mata husna Amma ta kasa kasancewar tunda ya Bata wayar Bata taba kiranshiba kuma da numbershi a ciki yayi saving...


Shahada tayi ta danna, ai kamar Yana Jira tana shiga ya katse ya biyota..


A nutse ta daga tasa a kunnenta "barka da rana uncle"

"Barka Noor"

Mamakine ya kamata ya akayi sadeeq yasan mamanta nace mata Noor, tasan daga Abbanta babu wanda ya sani, ko murja da baaba Indo basu saniba, toshi ya akayi ya sani, kasa hakura tayi tace

"Uncle ya akayi kasan ana cemini Noor?

Murmushi yayi don ya farajin Dadin hirar tasu "Aini na damu Dake shiyasa, ke kuwa babu ruwanki Dani, ko flashing pa Baki taba yimin ba"

Ji tayi tabbas Bata kyautaba, "To uncle kayi hakuri zan ri?a kiranka"


"Kada ki damu ai bakya laifi, ya umma da kawata baaba indo? Kice mata inanan zuwa anjima.

Dadi taji Jin zaizo gidan sai ta fasa ce mishi ya kawo husnar tunda dama kadaici ne ya isheta, kuma gaskiya tanajin Dadin hirar da sadeeq yakeyi da baaba Indo dukda Bata sa musu Baki Amma tana jinsu.

Gashi kuma tsaftar sadeeq da kwalliyarshi suna burgeta, ga kamshin turaren sa masu Dadi, hakanan wani zubin saita Rika Jin kamshin turaren a hancinta Koda baya gurin.


"To zan fada mata In'sha Allah"

"Gobe zaku koma makaranta ko?"

"Eh uncle"


"To shikenan ki kula da kanki sai nazo"

"To" tace sannan ta katse wayar, da sauri ta faWa bayi donyin wanka, a gurguje ta shirya ta fito falour ta zauna kafin yazo

Ai kuwa yauma hirarsu sukasha shi da baaba Indo, ita dama umma idan ya shigo dakinta take komawa ta zauna ko tayi kwanciyar ta.

Hafsat na gefe a zaune, sadeeq na burgeta musamman idan Yana Daria sai Taga ya Kara kyau.

_*nidai cewa nayi Anya kuwa hafsat kodai kodai*_


Sadeeq ne zaune a office din Abban hafsat "Abba dama nazone na sanar dakai na biya muku Umrah kaida umma"


Da sauri Abban ya Wago Kai "haba sadeeq duk hidimar da kakeyi Bata isaba saika dorawa kanka wata hidimar ta daban?


Murmushi sadeeq yayi"Abba babu wata hidima da nakeyi Neman Albarka ne kawai, kuma ma ai duk wani Alkhairi da ake samu a companyn Nan sanadinka ne Abba, idan ban kyautata makaba wa zan kyautatawa?"

Godia sosai Abba yayi mishi sannan ya Kara da cewa "kafin mu tafi dama inaso naje gida, to idan mukaje ma kawai sai inbar hafsat achan har sai mun dawo."

Zuciyar sadeeq ce ta bada dammmm Jin za'a rabashi da abar kaunarsa, Aida sauri yace "A'a Abba! ba saika kaita chan ba ka barta a gurin mummyn husna mana ai duk dayane idan babu matsala"


"To shikenan sadeeq babu abinda zance sai dai nace Allah yasa gyatuminku Yana Aljannah kuma kaima Allah ya baka masu Yi Maka fiye da abinda kakeyi mana" cewar Abban hafsat domin yaji daWin tayin da Sadeeq yayi mishi saboda be son yakai hafsat can Malammadori domin zai kuma tsokano malam barau ne duba da kwana biyu ya danyi sanyi dayin maganar auren hafsat Win.

Fita yayi cikin Jin Dadi, yana ayyana zasu Rika kwana cikin gida daya da abar kaunarsa hafsat, yasan dole zaifi samun damar cusa mata sonshi dukda yanzuma ya fara ganin alamun nasara....


*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*11*

*MATAR RASHEED*


_______Acikin satin da zasu tafi umrar Abban hafsat shida ummanta suka tafi jigawa don yiwa yan Uwa da abokan arziki sallama.

Aikuwa malam barau ya anshesu hannu bibbiyu yanata farincikin suma Allah ya kaddara zasu ?asa Mai tsarki.

Sai dai yau ya kasa ya tsare kan batun zancen hafsat "Alhassan na lura bakaso Ina Yi Maka zancen auren hafsatou Koh? Shiyasa ma kaki zuwa da ita ka fake wai saboda makaranta"

"Wai nace idan ta mutu Boko za'a tambayeta kome? To wallahi ka tabbbatar kuna dawowa daga kasa Mai tsarki za'a yi bikinta Koda saurayin da takeso ne ko da waninshi.... Dan bazan zauna Ina kallo yarinya ta zama uwar mata ba Amma tana zaune a gida"

Dukar dakai kasa Alhassan yayi "Anzo gejin da banso aka kaiba" ya fada a zuciyarshi..

A zahiri kuma cewa yayi "To Abba Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen! kadaiji na faWa Maka, in kuma bakaima ka zama Nasara bane"

"Baba ayi hakuri wallahi ko daya kawai don naga yaron yanada hankaline shiyasa nace adan jirashi Amma yanzu idan muka dawo ko bai shiryaba saika Samar mata wani a Nan din cikin masu nemanta"

Washe Baki malam barau yayi "kaga Dan Albarka nasan cewa bazaka yada karatun addini ka zabi na Boko ba saboda Kai din rainon amininane malam musa, kuma nasanshi ciki da bai, Allah dai yajikanshi ya haskaka makwancinshi, Kai kuma Allah yayi maka Albarka..." "Ameen" Alhassan yace cikin Jin Dadi, Nan akabar wannan zancen aka Dora da wani.

Kwanansu daya a jigawa suka koma abuja
Tunda Abban ta yace mata gidan mummyn husna zataje ta zauna har sai sunje saudiyya sun dawo zuciyarta keta dukan uku uku.

Ita kuma baba Indo tace zataje gida (Zaria) kafin su dawo tunda dama tunda tazo Bata koma ba...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login