Showing 45001 words to 48000 words out of 66006 words

Chapter 16 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

145

naki ra'ayin koh?"

Marairaice fuska tayi "i'm sorry mum, Don Allah kiyi hakuri" dafa mata kafada Sadeeq yayi "mummy ta hakura"

Kyabe fuska tayi "Uncle ina wuni" Yadda ta kyabe fuskar saida Sadeeq da Hafsat sukayi dariya
"Lafiya lau daughter, ya makaranta?" A jikin Hafsat ta kwanta tare da cewa "Lafiya lau Uncle" daga bisani ta gaida Hafsat Win itama, da ido take ta ro?onta akan ta taso taje ta gani

Mikewa Hafsat tayi Tare Da cewa "mummy bari inje inga me zata nuna min?" A harzuke mummyn husna tace "au dama baki dena Maganar ba, tasata kika yi akan ta taso kuje koh?"

Da sauri Hafsat tace "A'a Aunty Allah ba ita bace kawai dai nima ina so na fita Wajen ne" girgiza Kai mummyn husna tayi tare da cewa "To saikun dawo"
Da sauri suka fita husna na cewa "masara da wake na shuka, shine Yau danaje na duba naga Duk sun fito" murmushi Hafsat tayi "muje ki nuna min gurin in gani"

Janta husna taitayi har zuwa garden, a Wani gefe chan daban tayi shukar, Kuma tsaff tayi komai dai-dai saidai Kunya kunyar ce bata yisu da fadi sosai ba "husna wa ya koya miki yadda ake yin Noma?" Hafsat tace tana Bin shukar da kallon sha'awa

"Malamin primary science Win mu ne ya koya mana, Kuma Yace kowa yaje gida ya gwada, wai Duk wanda tashi ta fito zai bashi kyauta"

"Wow Masha Allah, kinga Kenan kema zai baki kyautar tunda taki ta fito" sai murmushi husna take tanajin daWi

Cire hijabin Hafsat tayi ta ajiye a saman Waya daga cikin kujerun da suke garden Win wai zata ?ara gyarawa husna shukar

????????????????????

A Cikin daki Kuma mummyn husna ce ta tsare Sadeeq akan cewa saiya faWa mata Meke damunshi Saboda jiya taje asibiti kuma doctor ya tambaye ta ya jikinshi.

"Sis bazaki yarda bane, Amma Wallahi is not something serious, kawai dai Wani zubin idan ina kwance ko ina tsaye sai jini ya ri?a zubomin ta hanci na, to shine da naje Asibitin ya bani magani, kuma duka na shanye maganin Amma be dena zuba ba, to satin daya wuce na koma shine doctor Win Yace saidai naje Cairo"

Wani Irin zazzaSi ne ya rufe mummyn husna a zaune, gaba Waya tsoro da damuwa sun bayyana a fuskar ta "Bro jini ya ri?a zubowa ta hancinka Amma kace is not something serious?, Me kake nufi?"

"Aunty baki gane bane, jinin ne kawai ke zuba Amma wallahi banajin komai koda ciwon Kai ne ma kuwa"
"Yanzu yaushe Zaka tafi Cairo Win" mummyn husna tace Duk jikinta a sanyaye "jiya dai muka yi video Call, to na faWa mishi komai dake faruwa shine yace ya bani appointment inje next week zaiyi min generel check up"

"Bro please ka taimaka kaje kaji, and Ka kawo Hafsat Nan har zuwa ka dawo and pls Kada ka fadawa mummy me zai kaika Cairo Win, kaji?"

"Sis karki samu damuwa, zanje and kuma in sha Allah Babu komai"

"Allah yasa haka!" Cewar mummyn husna tare da mikewa "Bari na leko su Hafsat naga me sukeyi

Batafi minti huWu da fita ba ta dawo tana murmushi "Wallahi Sai dai abar Hafsat, suna chan garden ta biyewa husna wai Noma sukeyi"
Murmushi Sadeeq yayi yana tuna famar da shima yakesha kwana biyu, "Aunty pls bari naje na dauko Aadhil" Cikin mamaki take kallonshi "Aadhil dai Wan uwan Aakhil?"

"Eh shi Aunty" Cikin zumudi mummyn husna tace "yi sauri kaje ka dauko shi"

Fita yayi zuwa parking lot ya fitar da motar Bayan me Gadi ya buWe mishi gate, ya Wauki hanya yana bin location Win da Aadhil ya turo mishi, befi minti ishirin da Biyar ba ya isa gidan su Aadhil, Babu Yadda Aadhil beyiba akan sadeeq ya shiga su gaisa dasu mummy amma fir yace ya bari su fara tafiya Yanzu inyaso Daga baya shima zai zo yayi musu yini.

Hakanan Aadhil Win ya kyale shi, hira sosai suke sanda suka Wauki hanyar gidan mummyn husna, Sadeeq yanaso yace mishi yayi Aure Amma kuma yana tsoron faWan da Aadhil zaiyi mishi na?in faWa mishi da baiyi ba lokacin bikin, hakanan dai ya bari akan Zai faWa mishi bayan sun kimtsa.

Koda suka isa gidan mummyn husna shima Aadhil sai yace ba zai shiga ciki ba, Babu yadda Sadeeq beyiba amma shima ya shafe idonsa da toka akan sai dai su zauna a garden, da dai ace gidan mummyn shine to zai shiga direct, amma ko bazai shiga gidan wani ba haka siddan, dariya Sadeeq yayi tare da cewa "ka rama Kenan koh"
"Allah ba zancen ramawa bane, kai kasan idan mijinta ya dawo bazai ji daWi ba yaga wani a cikin gidansa gurin iyalinsa ba tare da yasan da zuwan sa ba"

Girgiza kai kawai Sadeeq yayi tare da cewa "To ?arasa garden Win ganinan zuwa"

A hankali Aadhil ya nufi hanyar garden Win, tafe yake yana kallon yanayin gurin, sosai garden Win yayi mishi kyau duba da Yawan flowers Win da suke gurin, koda ya karasa ciki sai ya nufi inda ya hango kujeru
Sanda ya ?arasa gurin kujerun sai yaga hijab fari kar sakar ?asar Malaysia a ajiye a saman kujera guda Waya, kallon hijab Win yayi yana tunanin wa ya ajiye shi a nan, harya zauna sai ya fara jiyo kamar magana ?asa ?asa a Waya gefen garden Win, mikewa yayi a hankali ya nufi inda yake jiyo Maganar

Su biyu ya gani a tsugunne gaban fond suna jefa wani abu a ciki, sosai yanayinsu ya bashi sha'awa, Dukansu tsaff suke kuma kowa gashin shi a gyare yake, saidai ta baya bazaka iya gane shekarun su ba, a ranshi yake ayyana cewa "hijab Win nan kenan na Waya daga cikin sune"
Be gama wannan tunanin ba Hafsat ta mi?e tare da juyowa tana cewa " husna zo muje mu kira Uncle yazo yaga yadda muka gyara gonar"
Saida ganinshi da jinshi suka dauke na yan seconds sannan suka dawo, zuciyarshi wani irin gudu takeyi saikace wanda yayi ido hudu da mayunwacin zaki

Idan ba karya idonsa yayi masa ba, Hafsat ya gani ta nufo inda yake, da sauri ya juya baya saboda rudewar da yayi yama rasa me zaiyi saboda Gaba Waya ji yayi ?wa?walwarsa ta dena Aiki.

Ita kuma Hafsat Ganin mutum a dan nesa da ita sanye da fararen kaya saita zata Sadeeq ne yake neman su, alamu tayiwa husna da tayi shiru kada tayi magana, Cikin sanWa ta nufi Aadhil ta baya tana kunshe dariya, shikuma yana tsaye a gurin kamar an dasa shi sai kokawa yake da zuciyarshi don ta dawo dai-dai Amma ya kasa, tunani ya cunkushe mai ?wa?walwa, shidai ganin Hafsat na Farko daya Fara yi tun tana malammadori ne, yanzu kuma ya ganta Anan gidan, sunada ala?a da Sadeeq kenan?

Dai dai nan Hafsat ta rungume shi ta Baya tana cewa "Uncle nasan mu kake nema" a jikinta taji cewa wannan ba Sadeeq bane, duba da wannan Win yafi Sadeeq tsawo harma da faWin jiki, sannan kuma kamshin wani turaren yake yi ba irin na Sadeeq ba, shima kuma Aadhil Wani iri yaji sanda ta rungume shi din

Hakan yasa ya kama hannuwanta tare da juyowa suna Fuskantar juna, tsoro ne ya kama hafsat sosai ganin wani sak kaman Abban ta sai dai shi Wannan ba Tsoho bane, take jikinta ya fara rawa kamar Wadda akace za'a yi wa danbanzan duka "Don Allah kayi hakuri Wallahi nasha Uncle Sadeeq ne" Abinda Hafsat ta iya cewa kenan jikinta sai Sari yake

"Calm down, bakiyi laifi ba ai" tsinkakken miyau hafsat ta hadiye jin muryar shima sak irin ta Abban nata
Sosai ya zubawa fuskarta ido kamar me Nazarin wani abu, still dai hannuwanta na cikin nashi _"what is your name?"_

Cikin sanyin jiki tace _"My name is Hafsat Al-hassan"_ jinjina kai Aadhil yayi tare da sakinta yana cewa _"Thank you_, Amma dai pls ki rage tsoro"

Bata ko saurareshi ba tayi inda hijabinta yake ta dauka tare da yin Cikin gida da sauri, itama husna bin bayanta tayi da gudu, basu suka tsaya ba saida suka shiga cikin Dakin husna sannan suka faWa saman gado suna sauke numfashi.


Dai dai lokacin kuma Sadeeq ya ?arasa garden Win dauke da tray a hannunshi "Afuwan ya akhie, na barka kai kaWai koh? Wallahi mummyn husna ce tace saina tsaya ta haWa maka Abu na tawo maka dashi, sannan tace ita zata zo ku gaisa tunda Kai kace kafi karfin kaje"

Kama baki Aadhil yayi yana murmushi "ina na isa nace nafi karfi? Pls ka rufamin asiri, ai tafi ?arfin ma aje a gaisheta"
Hararar wasa Sadeeq ya jefe shi da ita tare da cewa"kamar da gaske"

Haka dai suka zauna sunata hirar bayan rabuwa, Anan ne ma Aadhil yake bashi Labarin yadda Aakhil ya rasu, ashe ciwon ciki ya tashi dashi, sosai Sadeeq ya tausaya mishi, daboda Mutum ne shi freely kayi ne yayi maka.

Sosai Sadeeq yakeso ya fadawa Aadhil yayi Aure, Amma Sam ya kasa na Dalilin dayasa be faWa mishi ba Lokacin saboda bashida kwarin gwiwar dazai kare kansa, shima dai ta Sangaren Aadhil Win ya kasa mishi magana akan Hafsat daya gani, ya bari saiya kara dawowa Sai yayi mishi magana akanta yaji me zaice mishi

Haka suka sha hirar su amma Aadhil be taSa komai da sadeeq ya kawo mishi ba, Sadeeq har ya gaji da korafi akan beci komai ba amma ya?i ci

Hafsat gaba Waya tsoro ne ya kamata, gani take yi kamar aljani ta gani, saboda tunda take bata taSa ganin wanda yayi mugun kama da mahaifinta kamar wannan ba, to waye shi? Dai dai nan itama husna tace "Aunty waye wanda kika rungume dazu"
Kallon husna tayi tana tunanin me zata ce mata, tasan husna da surutu kuma tsaff zata iya fadawa Sadeeq cewa ta rungume wani, wani tunani ne yazowa Hafsat, kallon husna tayi tace

"Aljani ne wanda muka gani dazu, kuma kiyi shiru kada ki fadawa kowa kinji" Waga kai husna tayi tare da assuring Win Hafsat cewa bazata faWawa kowa ba.


Ita dai Hafsat bata kuma bi takan zancen ba har sanda mummyn husna ta kirasu don suzo suci abinci sai dai lokaci bayan lokaci yakan faWo mata arai, dai dai lokacin da zasu fara cin abincin shima sadeeq ya shigo falourn ya dawo daga maida Aadhil gida, tare sukaci a dining duk da Hafsat Win bata wani ci da yawa ba don tunda Abin nan ya faru take jin zuciyarta ba dai dai ba.

????????????????

*AADHIL*

Koda ya koma gida kasa zama yayi, ya rasa yadda zaiyi da wannan farin cikin shi Waya, kuma ya rasa wanda zai faWawa, yauma a yanzu ya kuma ganin amfanin Aakhil a gurin shi, da ace yana nan da shine zai iya fadawa kanshi tsaye ba tare da wani haufi ba

Har zuwa yanzu ji yake kamar tattausan hannunta yana cikin nashi ne, kuma har yanzu hancinsa yana rike da cool kamshin turaren ta, ganin tunanin bazai kara mishi komaiba sai kawai ya shiga Dakin sketching Win shi don ya zana ta, kuma a ranshi ya kudurta zanen dazaiyi yanzu shine farkon kyautar dazai fara bata.
_*Fans nima fa harna fara tausaya wa Sadeeq wallahi*_

*KUNSAN NAYI MAGANA AKAN BAZAKU RI?A SAMUN UPDATE ASABAR DA LAHADI BA, TO DUBA DA WANNAN SATIN BAKU SAMU UPDATE DA YAWA BA SABODA BA?IN DA NAYI, SHINE NACE YAU BARI NAYI MUKU A MATSAYIN BIYAN BASHI, FATAN ZAKU YIMIN ADDUA*

*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*21*

*MATAR RASHEED*


_______"Mummy wai har yanzu ba'a Gama duka abin da za'a yi bane"

"Diyana wai mesaya bakida hakuri ne sam? Jiya fa tare dake naje Wajen bokan nan Saboda kiji Abinda ke wakana amma duk da haka bazaki rabu dani na huta ba"

"Mummy Yanzu shikenan babu ta Yadda za'ayi ki Aure shi Win?"

Girgiza kai tayi tana mamakin tsantsar wautar diyana "kinaji fa yace na Wan bashi Lokaci, ai hakan Yana nufin akwai Wani Abu da yake tunanin zai iya yi, shifa boka Wan China ba Irin bokayenmu na Hausawa bane, da ace aikin Nan bazai yiwu ba to da tuni ya faWa min, Yanzu dai kinaji Yace baza'a iya kashe matar tashi ba, toya kikeso nayi, koko so kike na matsa Ni Kuma Wani Abu ya sameni"

"Yi hakuri Mummy, bawai haka nake nufi ba kawai dai harna fara hango kaina ne a Cikin gidansu Hafsat Win, Domin wallahi saina Azabtar da ita"

"To ai saiki jira lokaci yayi bawai ni ki dameni ba, Kuma ina so ki Sani cewa Babu Abinda ake samunshi Cikin dare Waya, Dole komai saikayi hakuri ka jira tukuna zaka cimma burinka, koda kuwa ba Alkhairi bane" tashi mummyn diyanar tayi ta shige dakin dake kusa da ita, ita Kuma diyana saita Dada gyara kwanciyarta a saman kujerar da take tana kissifa abubuwan da zasu faru muddin mummynta ta samu ta shiga gidansu Hafsat din

???????????????

Sai Wajen 9 na dare su Hafsat suka koma gida, koda suka isa gidan Babu Wani Abu da suka yi illah wanka, saboda saida mummyn husna ta tabbatar sun koshi sannan kuma ta Zuba musu Wani a Cikin warmer tace su tafi dashi, koda suka yi wankan falour suka fito suka kunna kallo, sai dai Sam hankalin Hafsat baya kallon idontane kawai kafe a TVn amma zuciyarta ta tafi tunani akan mutumin data gani dazu, tanaso tasan waye, kuma tanaso tasan ya akayi yayi Kama da abbanta sosai haka da har Muryar su ma ta zama iri daya "kodai da gaske ne da ake cewa kowa a duniya yanada me kama da shi guda bakwai?" Idan kuwa ta tabbata hakan ne to Lallai yau taga me kama da Abbanta,

Sadeeq yaso ya lura da chanzawar yanayinta amma kuma ganin yayi mata Magana ta amsa mishi Cikin murmushi saiya kauda tunanin hakan a ranshi, Yanzu yafi tunanin kila gajiya tayi

"Noor ko zakije ki kwanta ne?" Naga Kamar kin gaji koh?

Tashi Hafsat tayi tare dasa tafin hannun damanta tana rufe bakinta saboda hammar da taji ta kama ta "goodnight uncle"
Murmushi yayi Mata "goodnight dear, ayi Barci da yawa, kinsan gobe zakije ki amso report sheet dinki ko"

Murmushi itama Hafsat tayi tare da cewa "eh Uncle" sannan ta juya tayi balcony Win dakinta

Idonshi yana kanta har zuwa sanda ta shige dakin, mamakin zamansu yake yi, saikace ba ma'aurata ba, a kwana tare a kuma tashi tare ba tare da Waya ya bukaci Waya ba duk da yasan kusan matsalar ta Sangaren shi ne, Amma shima kwana biyun nan ya fara mamakin kansa, saboda ada idan ya ganta Allah ne kaWai ke rufa mishi asiri, amma yanzu gashi gata kuma a Matsayin halalinshi amma ya dena jin komai game da ita..

Ta Sangaren Hafsat kuwa koda taje ta kwanta Win sai tunanin ya karun mata a maimakon ya ragu, sosai take so tayi maganar da wani ko zata samu amsar da take son ji, gashi yanzu Babu kowa kusa da ita inba Sadeeq ba, kuma gashi bazata iya faWawa Sadeeq ba Saboda ta rungume shi, kuma tasan idan yaji bazaiji daWi ba, barin maganar tayi da nufin duk randa Allah yasa taje gida saita tambayi umman ta.


???????????????

*AADHIL*

Bashi ya fito a Wakin zanen ba sai dalilin sallar magrib, koda ya fito sai be koma ba ya jira Abba ya dawo sukayi dinner tare, hira sukayi zuwa lokacin da aka kira sallar isha'i
Bayan sun dawo ne yayi ma kowa saida safe, ita kuwa mummy saida ya tabbatar yaje ya kwantar da ita sannan ya shige ciki don ya ?arasa zanen nashi

Sosai ya tsaya ya zubawa zanen nashi ido cike da natsuwa, yanaso ya gane a inane yayi kuskure ya gyara Saboda dama haka dabi'ar shi take, duk sanda yayi zane saiya bata kusan awa daya yana Nazarin zanen, idan yaga kuskure ya gyara, idan kuma be gani ba sai yayi wraffing dinshi ya ajiye zuwa sanda za'a amsa

Natsuwar da yake da ita a cikin zanen shi ita tasa manyan companoni suka daukeshi a Matsayin permanent architecture dinsu, saboda duk wanda yayiwa aiki sai yaji yanaso ya kara yi mishi

Drawing pen Win ya dauka inda yaci gaba da zana kitson twisting Win Hafsat wanda yake gaban goshin ta, yanaso ya ?ure fasahar shi a yau, yanaso yayi zanen dabe taSa yin irinshiba tunda yake, shiyasa ko a colours Win yayi Amfani da Very expensive one's,

Yaso ya gama duka biyun a yau Amma ya sare, ganin ya fara hamma yasa ya mi?e daga gaban allon yana yin mi?a tare da cewa "la'ilaha'illalhu Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam" ajiye pen Win dake hannunshi yayi sannan ya kai dubanshi ga wanda ya gama tun dazu, Hafsat da husna ne wanda suka juya baya suna wasa a fond, sosai zanen yayi kyau dukda babu fuskarsu amma kana kallon gyararren gashin kansu musamman na Hafsat wanda ya sauka har zuwa gadon bayanta
Kuma still ko a yanayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login