Showing 9001 words to 12000 words out of 66006 words

Chapter 4 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

128

Gashi kuma an fara saida Form din Shiga SS1, kuma yanzu baban ta beda kuWi, sannan tana tsoron kada malam barau ya tada balli. Ana cikin wannan halin Allah yasa wasu kudi masu Wan nauyi suka shigowa Alhassan, cewa Hafsat yayi ta shirya suje yayi mata registration.
Sanda suka je gurin director din makarantar sai yayi musu sau?i sosai,
Ganin Hafsat Win da yayi, har lemu da ruwa yasa aka kawo musu.
A ransa ya ?udiri niyyar duk yanda za'a yi saiya aureta..

Koda suka dawo daga makarantar sai Alhassan yace su biya ta gidan kakan Hafsat Wato Malam barau su gaishesu......

Jin Cewa Alhassan ya nemar wa Hafsat gurbin ci gaba da karatu "Nan malam barau ya fara faWa ta inda yake shiga batanan yake fita ba,
"Alhassan dama bokon nan dakayi nasan dole ta maidakai nasara! Ace yarinya kamar wannan amma a?i yi mata aure sai wata bokon banza,,

To gaskiya bazai yiwu ba, a samu mai hankali cikin masu sonta ace ya turo, inyaso bayan sunyi auren sai ya barta taci gaba idan yana so, Idan ma beso to shikenan dama ba dole ba ce.


Jin irin maganganun da malam barau keyi yasa Hafsat fita daga gidan cikin sauri zuciyarta na bugawa, gida ta nufa domin bazata iya jurar gama jin abinda malam barau ke faWa ba. ji take kamar ta rusa ihu ?ila ta samu sauki a tu?u?in da zuciyar ta keyi mata.

Shi kuwa Alhassan ji yayi kamar malam barau ya buga mishi tabarya a tsakiyar kanshi, shiba yana so Hafsat tayi karatu bane don ya maida ita jari ba, face yana so tayi karatune don ta taimaka wa yan uwanta mata

Amma ya lura malam bazai gane ba ,gashi bazai iya yi mishi musuu ba Saboda yanda yaba shi gudummawa a rayuwar shi, ya daukeshi uba, malami, yaya Kuma suruki..

Haka ya tafi gida jiki babu kwari, koda ya fadawa umman Hafsat itama bataji daWi ba, amma ya zasuyi tunda ga abinda Malam Win yace.

Zaune suke a tsakar gida dukan su, Hafsat tana wanke wanke Ummanta na gyara shinkafa, Abbanta kuma yana duba Al Qur'ani mai girma.

Ibi ne ya shigo Cikin gidan da gudu yana haki Alamun yayi gudun ne iya karfinshi "baba wai kansila yace kazo, kuma yana Kofar harda sojoji....


*#SAGIR* L'
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*

```pls comment and share```
*IZAYAR RAYUWA*

*5*

*MATAR RASHEED*


______Qur'anin ya ajiye a jefe suka fita tare shi da ibi,

Ile kuwa kansila ne wanda ayanzu Wan majalisa, tare yake da DSS masu tsaron lafiyar sa ba sojojiba kamar yadda ibi yace.

Hannu ya mika mishi sukayi musabaha, haWe da ?ara yiwa juna ta'aziyya .

Bayan yan gaishe gaishe, baban Sagir yace "Nazo ne na cika alkawarin dana dauka da wanda Sagir ya dauka"

"Na samar maka aiki a wani Companyn da nake da hannu jari a ciki achan Abuja, sai kuma hafsatou itama na samar mata gurbi a American secondary School dake Abuja, Abinda Ya rage yanzu zaka bani takardun makarantar ka dana Hafsat in tafi dasu, Idan an gama komai zan turo mota saiku kwashe kayanku ta kawo ku chan Abujan"

"Itama iyalina yau zamu tafi tare da ita"

Alhassan Ya kasa magana tsabar farin ciki, sai dai kuma ga ?oshi ga kwanan yunwa
Yana tararrabin Anya surukinshi malam barau zai yarda kuwa? Sannan kuma ina shi ina Rayuwar birni bayan rayuwar ?auye ya saba.

Godiya sosai yayiwa baban Sagir daga bisani ya kara da cewa "Amma yallabai da zaka taimaka min don Allah kaje gurin Malam ka sanar mishi domin ina tunanin idan ni naje mishi da Maganar dakyar in zai yarda, amma Nasan idan ya ganka zaiji nauyi"

Daria baban Sagir yayi "kada ka damu dama daganan chan gurinshi zan wuce.."

Basu rabu ba sai da yayi mishi goma na arziki, kuma yana daWa jaddada mishi cewa su shirya domin zai iya turo mota ko yaushe.

Alhassan Yana shiga gida ya sanar wa umman Hafsat da ita Hafsat din.
Gaba Waya sai farin ciki da murna sukeyi da fatan ALLAH yasa malam ya amince da wannan tayin, amma suna tsoron yadda zasu rayu a cikin birnin, sai dai kuma murnar ta danne tsoron.

Ko da baban Sagir ya je gurin Malam barau, hannu bibbiyu ya amshe su, bayan sun gaisa, malam barau ya ?ara yiwa kansila gaisuwa.

"Baba dama nazo ne na faWa maka cewa a cikin kujeru biyar na Saudiyya da gwamnati ta bani kyauta, Na ware maka guda Waya"

Malam barau yace "banganeba Wan nan?"

"Eh to dama ina nufin insha Allah aikin hajjin bana da kai za'a yi, Sannan na samarwa Alhassan aiki a chan Abuja, sai hafsatou itama na samar mata gurbin cigaba da karatun ta a can"

Malam barau rasa wace irin Godiya zai yi wa baban Sagir yayi, sai kawai ya fashe da kuka, nan ya rika yi mishi addu'o'i Da fatan Alkhairi a Cikin rayuwar shi,

"Oh wai yau nine zani Saudiyya" cewar malam barau yana goge ?walla.

"To baba ya zancen Alhassan da hafsatou?"

"A'a kada ka damu na amince su tafi, sai dai lokaci bayan lokaci su rika zuwa Dubamu"

"To baba mun gode Allah ya saka da alkhairi, kuma insha Allah zasu rika ziyartar ka sosai"

"?an nan ai nine da Godiya, ka gama min komai, dalilinka zanje naga Annabin rahma"

"Baba kada ka damu kaima ai kana bada gudunmawa sosai a kauyen nan, idan ba'a yi maka ba wa za'a yi wa?"

Sallama sukayi bayan yayi mishi alkhairi kamar yanda ya saba, da shedar zai Turo wanda zai mishi bayanin lokacin tafiyar idan yayi.

Washe gari umman Hafsat ta aike ta gurin kakarta takai mata abincin juma'a, Anan ne malam barau ya shaida mata cewa kansila ya biya mishi Saudiyya.

Da murna ta koma gida ta shaidawa mahaifinta Da mahaifiyarta zancen malam barau,

Ai nan labari ya dawo sabo, baban Hafsat ne yace "Amman shine Ni be faWa mini ba Kafin mu rabu? Lallai Allah dai ya biyashi da Aljannah"

"Ameen domin babu abinda zamu iya yiwa ahalin Sagir sai dai fatan Alkhairi" cewar umman Hafsat.

Ita kuma Hafsat mamakin irin karamcin baban Sagir takeyi, to da ace ta auri sagir Win pa?

Kowa sai farin ciki yakeyi cikin kwanakin, tsakanin zuwan kansila da kwana takwas ya Turo motar da zata kai su Hafsat da iyayenta Abuja.
Haka makwabta da abokan arziki akayita koke koke, saboda su Alhassan da matarsa Hafsa basa sawa basa hanawa ba ruwansu da rikici.

Balle Hafsat da ita daga makaranta sai gida, saboda tun tashin ta dama bata saba da kowa ba face umman ta, kullum tana naki?e da ita, Allah ya dasa musu ?aunar junansu sosai.
Haka dai aka rabu babu daWi, kowa sai alhinin rabuwa da Wan uwansa yake.


??????????????

Sun sha zaman mota, tun Hafsat na kalle kalle tanajin daWi har ta gaji tayi barci, barcinma isarta yayi ta koma juye juye.


Basu suka kai Abuja ba sai tara na safe, dayake dama tafiyar yamma lis sukayi.

A Wani madaidaicin duplex Win gida driver yayi parking, Ko da suka shiga cikin gidan Babu kowa amma akwai mota guda Waya a parking lot,
Gyara parking drivern yayi Sannan ya sauke musu kayan shirginsu.

Anan ya shaida musu gidan nasu ne halak malak, saboda shi tsarin Companyn har dai ka fara aiki a Cikin shi to za'a baka gida da mota sai a rika cirewa a albashin ka.

Mukullan gidan ya ba Alhassan "gashi wannan duka mukullan gidan ne akwai mukullin ko wane Waki a jiki, Ni zan tafi gurin Honorable saboda yasan mun iso lafiya, Sannan gobe zan dawo na kaika Company da kuma inda honorable yake zama, Ita kuma hafsat sai ranar Litinin zanzo mutafi makarantar da zata fara zuwa, a takaice dai yanzu nine drivern ku kafin kusan cikin gari"

Godiya sosai suka yi mishi sannan ya tafi.

Kofar data nuna alamun itace ta main falour nan suka bi, koda suka bude kofar kasa rufe baki sukayi domin basusan abubuwa da damaba aciki.

Tsaye sukayi a bakin kofar suna kallon ikon Allah, wato yanzu wannan ?aton gidan da dakin yan gayun nan nasune?
Allah mai yadda yaso ga bayinsa.

Ko a mafarki Basu taSa tunanin Wata rana zasu samu irin gidan nan ba, A hankali suke tafiya akan milk Win tiles Win daya cika dakin ga coffee din center carpet a tsakiyar milk colour Turkish cussions din da suka ?ara ?awata Wakin, gaba daya Wakin tsarin Turkiyya ne hatta da wallpaper din dake jikin bangon, Tv stand Win ma da yanayin dining area din komai turkey ne

Hafsat ko mutum mutumi ta zama "wai dama irin hotunan da sagir yake nuna mata a waya yana cewa irin da?in da zai haWa mata idan sunyi aure, wai dagaske dama akwai su?"

Iko sai lillahi, bin Wakin akwai suke dana mujiya, ?ofofi hudu ne a cikin foloun kowacce a rufe, rasa wadda zasu fara buWewa sukayi.
umman hafsat ce ta nuna ya fara bude Wadda ke hannun dama, Nan ma dai wani abun al ajabin suka gani, shima dai king size Turkish bed ne da wardrobe din shi mai kofa takwas sai madaidaicin fridge a gefe bayan wanda ke falour,
A tsakiyar Wakin shima Chinese carpet ne medium size me kama da ciyawa.

Fita Abban hafsat yayi ya bude Waya Wakin, shima dai kamar wanda suka fara buWewa haka yake sai dai shi mbf bed ne da closet sai dan li?e li?e a bango alamun dakin yan mata ne

Na ukun da suka shiga kuma kitchen ne haWe da store
Shima cike yake da kayan amfani irinsu gascooker, electric stove, kettle, Su oven da dai sauran abin amfani irin wadanda ake samu a cikin kitchen din zamani na masu hannu da shuni.

?aki na huWun kuma madaidaicin gado ne kawai aciki sai hangar kaya, dukkan alamu dai ya nuna Wakin ba?i ne.

Mamaki duka ya kashe su babu wanda yake iya yiwa Wan uwansa magana, duk gani suke yi kamar mafarki suke.

Hafsat ce tayi karfin halin cewa "Abba dakin farko shine naku ko? Nikuma nasan na biyun ne nawa"

Ummanta tace "hafsat kenan harkin raba dakunan koh? Bama kya mamakin Irin wannan kashe kuWin "

Hafsat tace "umma ai bansan sanda zan dena mamakiba saboda ko a mafarki Ban taSa zaton zanga irin gidan nan ba"

"Hmmm Allah sarki sagir Allah yayi mishi Rahma yasa ya dace, duk ta dalilinsa muka samu wannan sauyin rayuwar domin dabai zo yace yana sonkiba ina zamu ga kansila balle har ya nemar mini aiki?" Cewar Abba hafsat yana nuna alhinin mutuwar sagir Win.

"To amma Abba koda sagir yace yana sona da bakayi karatunba to da waWanne takardun za'a neman maka aikin?" Cewar hafsat tana kallon abbanta .

"Ai dama Komai yanada Dalili" cewar umman hafsat

"Inama malam yananan yaga abinda bokon danayi ta samar mana, kuma wallahi da ace malam nanan dasaina kawo shi gidan nan mun zauna tare" Yana kaiwa nan kuka ya suSuce mishi, kusa dashi suka dawo suna bashi hakuri,

"To amma ai inna kulu tananan, ka dauko ta mana" cewar hafsat tana jiran wace amsa babanta zai bata.

"Eh to haka ne *Noor* Amma inna kulu bazata yarda ta biyomu nan ba saboda ko malam babu yadda baiyi da itaba akan ta dawo nan malammadori mu zauna tare amma fir ta?i"

Bayi hafsat keta nema don ta rage mararta amma babu shi babu alamarsa, a'a ya za'a yi gida babu bayi, kuma dai babu wanda baya fitsari da bahaya balle ince ko ?an birni basayi.

Saida suka kuma buWe Wakunan sannan suka lura akwai karamar kofa a cikin kowane daki.

Bayi ne irin na zamani, Akwai shower da bathtub sai pampo a gefe, sai kuma squat na bayan gida mai flusher _kasa gane yanda zasu yi amfani dasu sukai sai dai sun iya kunna famfo amma basusan me ake yi da squat da bathtub ba, Alhassan ne kawai ya sani shima don polytechnic Win da yayi ne_

_Alwala sukayi sannan suka koma palour dan yin sallolin da ake binsu_ _koda suka idar tashi sukayi suka yi nafilolin yiwa Allah godia ga ni'imarsa garesu_

Kitchen suka shiga domin nemawa cikinsu mafita amma sam sun kasa gane ya za'a yi a dafa abinci domin sam babu ko risho balle ice.

Hakura sukayi suka dawo falour suka zauna *ina iya cewa tsoron Wakunan ma suke yi*

_Sai alokacin Alhassan ya tuna da fanken da suka siya a hanya sanda suka isa kano, tashi yayi ya fita domin yama manta da kayan su da suka tawo dasu daga kauye wanda driver ya zuba musu a wani daki dake harabar gidan._

Sai sannan ya lura da tsakar gidan, akwai ?ananan dakuna guda biyu a jere sai wani da ya nuna alamun kitchen din wajene amma babu komai a ciki sai bayin waje da dakin me gadi a kusa da gate.
Gaskiya gidan yanada girma bayan parking lot din daya kunshi gurin parking din mota guda uku.
Sai kuma harabar gidan itama zata iya cin motoci hudu ko biyar .

Kayan ya bincika ya dauko musu fanken, sunyi farinciki sosai da suka ganshi ya tawo da fanken, debo ruwa hafsat tayi sunaci suna korawa=?
?


Koda suka gama, tsakar gidan suka dawo suka zauna tsumu tsumu kamar waWanda aka sace.

"wai to mu yanzu haka rayuwar mu zata koma babu inda muka sani kuma babu wanda muka sani, cikin gidanma tsoron shi muke ji?" Muryar hafsat ta katse shirun da suka yi.

Umman hafsat ce ta kyalkyale da dariya
"Lallai hafsat wa yace miki tsoron gidan muke yi?"

Kafin hafsat ta bata amsa suka ji ana buga gate, komawa sukayi suna yiwa juna kallon kallo

Hafsat ce ta mike ta nufi gate din ta buWe, wata yar dattijuwar mata sukagani wadda shekarunta baza su gaza hamsin da uku ba, amma irin masu kwarin jikin nance.

Murmushi tayiwa hafsat "a'a jikata ke kika buWe min kofar?
Ina umman taki?

Kauce wa tayi ta bata hanya ta wuce, tana nuna inda mamanta take zaune, gata chan itama ta na mayar mata da murmushin data yi mata

Ciki suka shiga anan matar take shaida musu honorable ne yasa aka kawota, don ita zata nuna musu yanda ake amfani da komai na gidan sannan kuma ta rika yi musu wasu ayyukan gidan zuwa wata biyu kafin su gane komai, idan kuma sunason cigaba da zama da ita zasu iya cigaba da biyanta

Dadi sosai maman hafsat taji, domin tasamu yar hira kuma sai take ganin tayi mata yanayi da inna kulu

Ai ba'a dau lokaci ba ta nuna musu abubuwa da dama har yanda ake kunna gas, dadai sauransu

Kan kace me har abinci ya sauka, Ita kuwa hafsat ta li?ewa baaba indo _sunan matar kenan_

Washegari driver ya dawo ya dauki Alhassan ya kaishi gurin honorable, nan Alhassan yayi tayin godiya har sai da honorable ya dakatar dashi da cewa _haba surukina ai duk abinda kaga nayi maka burin sagir na cika, kuma ina fatan hakan ya zama rahma a gareshi, domin kaf cikin ?a?ana babu wanda Allah ya dora min sonshi irin sagir shi yasa ko bayan ranshi nayi kokarin cika mishi burikanshi_

ALLAH sarki sagir Allah yakai rahma da haske cikin kabarinshi.

Sai lokacin aka kaishi Company dazai fara aiki, babban Company ne yanada da branch a America suna dealing ne da abubuwan solar kamar wiring din solar company da gidaje irin su tv dasu fanka dadai sauran abun electric.


Office din shi aka nuna mishi da ayyukan dazai fara yi kafin ya gama gane abubuwan Companyn

Ita kuwa Hafsat da ummanta suna gida tare da _baaba indo_ sunata hira inda take daWa wayar musu dakai

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*

```please share and comment```
*IZAYAR RAYUWA*

*6*

*MATAR RASHEED*



______Sun ?aru da baaba indo sosai, saboda irin wayayyun matan nanne Sosai, gashi batada son jiki ko kaWan, komai zatayi bilhakki da Gaskiya take yinshi.

Kuma da alamu ta zauna a gidan manyan mutane, tunda duk wani abu na ?an birni ta iya shi.

Ko da yamma tayi baaba Indo tace zata tafi gida, anan zance ya chanza, duk Sata rai sukayi "To baba ai munsha anan zaki ri?a kwana? Cewar hafsat tana ri?e mata hannuwa ta gefe.

"To idan kunce na rika kwana anan ma babu matsala tunda dama mijina ya rasu kuma yara biyu gareni mata, duk sunyi aure a Kano, sai dai lokaci bayan lokaci suna zuwa tare da jikokina suyi min hutu, Ni dama asalin yar Zaria ce aiki ne ya dawo dani Abuja, shima dalilin wani dan Majalisar wakilai achan Zaria, wato *Babawo* Matarsa ce ta tawo dani, kuma sai Allah yasa garin ya amshe ni"

"Ikon Allah! Ashe dai baba kinyi yawo da yawa?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login