Showing 48001 words to 51000 words out of 66006 words

Chapter 17 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

139

zanen garden Win yayi kokari saboda ya kiyaye yanayin flowers Win daya gani a gurin dukda sau Waya ya taSa shiga gurin

Hanyar bayi yayi domin ya watsa ruwa saboda ya samu damar yin barci cikin sukuni, sai dai har yanzu a cikin zuciyarsa yanaso ya gane ko kuma ya tuna a inda ya san ta, tabbas yasan Hafsat, amma to a ina? kuma yaushe? Amsoshin da bazasu samu ba sai dai a bakin Hafsat Win Domin shidai iya sanda ya taSa ganinta a kauyen su sanda governor ya bashi contract Win zanen yadda za'a fidda sababbin ajujuwa da bayika A makarantar su, iya wannan ne, sai sanda ya ganta a sahad store da peach colour Win doguwar riga, kuma Kafin ya ?arasa gurin ta ya nemeta ya rasa.
Sanin hakan da yayi saiya kauda tunanin gefe tare da goge komai daga ranshi zuwa gobe

?????????????????
Sosai Hafsat take farin ciki ganin ita tazo a third class, koda wasa bata taSa tunanin hakan ba! duba da irin Makarantar da tayi a baya, amma sai ta ajiye hakan a matsayin ribar addu'ar mahaifiyarta da mahaifinta, sai kuma malaman lesson dinta data san suma sunyi matukar kokari akanta.

Tana cikin wannan farin cikin ne diyana tazo wucewa ta gabanta, wata Irin muguwar hararar tsana ta jefi Hafsat Win da ita, sam Hafsat bata gani ba domin ita batada Irin wannan kwakwar, Amma Mr Naph da A'isha sun gani

Shiru sukayi suna tunanin a ina diyana tasan Hafsat? Kuma meye hadinsu da zata ri?a hararar ta? Amma ganin Hafsat Win bata gani ba sai suka ajiye zancen a ?asan ransu har zuwa sanda diyanar zata ?ara.

Numberta su A'isha suka amsa da nufin a cikin hutun zasu ziyarci juna in'sha Allah, shikuwa Mr Naph janta gefe yayi tare da tambayar ta idan tanada matsala, murmushi tayi mishi sannan tace "Banida wata matsala dear, kawai dai Kasan Aure ba kamar zaman gida bane"

Murmushi shima yayi donya karfafa ta sannan yace "kada ki samu damuwa, ai ibada kikeyi, kuma komai zaki saba dashi with time" haka dai ya bata shawarwari tare da ?ara mata kwarin gwiwa akan ta kwantar da hankalin ta, sosai Hafsat taji daWin maganganun Mr Naph
Hakan yasa walwalarta ta karu sosai, koda Sadeeq yazo daukar ta sai Abin ya bashi mamaki, Amma jin cewa tazo a third class Sai mamakin ya barshi saboda yadda ya lura tana son karatu sosai.


Sosai Sadeeq yake cikin tashin hankali Amma ya daure ya tayata murna da fatan Nan gaba ma ta zama First class, saida Hafsat ta daga kai ta kalle shi sanda yace hakan

Daga mata kai yayi cike da assurance "nasan zaki iya! Inada hope me ?arfin gaske akanki" sosai Hafsat taji Wani farin cikin ya kuma lullubeta, yau Kenan juma'ar ta musamman ce a gare ta, Hamdala tayi a cikin zuciyarta tare da yiwa Allah kirari

Tunda suka Wauki hanyar gida Sai motar tayi shiru, ita Hafsat mutumin garden ne ya dawo mata, shi kuma sadeeq yana tunanin Duk yadda za'a yi dole ya dawo da tafiyarshi ranar Monday saboda Abinda Ya faru yau,
Ya firgita matuka Ganin Irin jinin daya zubar yau da safe, tabbas ko ba'a faWa mishi ba yasan dole Akwai matsala, tunda ya fara zubar jinin be taSa zubar da koda rabin wanda ya zuba yau ba, shiyasa yakeso ya tafi da wuri domin a samu ayiwa tufkar hanci.


????????????????


Aadhil be sakko ba saida ya tabbatar ya gama zanen shi Saboda tunda ya dawo daga sallar asbah yaci gaba da zanen Kasancewar yanada fitiloli na musamman wanda yake kunna wa idan zaiyi zanen, shiyasa ko karfe nawa Zai Kai baya taSa samun matsalar duhu

Sanda ya sakko sanye yake da yadin cuba onion colour sakar ?asar India, yadda aka tsara Winkin sosai ya zauna a
Jikinshi kamar donshi kaWai aka sa?a yadin, riga da wando ne yan ciki saidai rigar tsayin ta bazai wuce gwiwar shiba,
A gaban rigar wani irin style me Winkin yayi kamar gidan zira botira saidai wannan da ba?in yadi me taushi yayi shi sannan kuma ya kwanta sosai a gaban rigar

Sanda ya gama saukowa a tare kowa ya juya gareshi Domin gaba Waya turarenshi (hayaati) ya gama gauraye Wakin, murmushin dake kwance a saman fuskar shine ya disashe ganin Wasu ?an mata guda biyu zaune a saman sofa kuma sunbi sun zuba mishi idanu
Siririn tsaki yayi sannan ya ?arasa gurin mummy tare da yin hugging Winta ta baya "good morning my lovely mum, fatan kin tashi lafiya!"

"Lafiya lau Aadhil, ya ka tashi kaima?"


"Nima Lafiya lau amma na tashi cike da kaunar ki"


Saida murmushi yayi nasarar kufcewa mummy, ta rasa wani Irin ?a Allah ya bata, wanda shidai a kullum burinshi ya ganta Cikin farin ciki da walwala, duk yadda taso kannewa saiya saukar da murmushi a fuskarta

Kafin ta kuma cewa komai yace "ina Abba"

"Yana ciki, Amma Yanzu Zai fito ya wuce gurin aiki saboda sanda na fitoma tsaff ya gama shirin nashi"

"Okay bari naje mu sakko tare" cewar Aadhil yana nufar balcony Win Wakin Abba

Ba'a fi minti biyar ba saigasu sun fito tare, Abban yana sanye ne da fara kar Win shadda ?an ciki da babbar riga sai ba?in sau ciki da ba?ar hula dara data zauna rass akanshi, sosai yayi kyau kuma kamarshi ta daWa fitowa ziryan shida Aadhil Win, illah dai shi Aadhil Akwai yarinta da gwarzontaka a tare dashi da kuma girman jiki daya fi Abban
Ri?e Aadhil yake da jakar office Win Abban, a tare suka iso gaban Mummy, "To madam nizan tafi, Aadhil yace shi Zai kaini yau" Abba yace yana gyara zaman malinmalin Win a jikinshi

"To Allah ya tsare, a dawo Lafiya" cewar Mummy tana hararar Aadhil

"Mummy me nayi kuma?"

"Ai ka sani! Duk sanda ka dawo baka bari ina samun ladan daukowa mijina jaka"

"To ai Mummy ke nakeyi wa, saboda wallahi na yafe ladan, nakine halal malak, so nake kawai ki huta"

Girgiza kai kawai tayi tare da cewa "To ka bishi mana! Yafa fita"


Da sauri Aadhil yabi bayan shi yana murmushi
Har Cikin office saida ya tabbatar yakai Abba Sannan ya juyo ya tawo gida bayan ya sanar da Abban cewa zai dawo wajen ?arfe Waya su tafi masallacin juma'a, a hanya ya tsaya ya saiwa Mummy gallon biyu Na dararar shanu da fura roba guda saboda yasanta da son fura sosai
Sanda ya isa gidan still dai ?an matan Nan Basu tafi ba, yanzuma shi suke kallo, sosai ya tamke fuska saboda shi bayason kallo sam, kuma ma wai ubanme suke yiwa mutane a cikin gida da hantsin nan?, Hanyar Wakin mum yayi donya Kai mata madarar ta sannan ya tambaye ta ''me wadannan suka zo yi?"

Tsayawa yayi a bakin kofar mum har saida ta bashi izinin shiga "Mummy ga abincin fulanin naki na kawo miki" cewar Aadhil a lokacin daya isa gaban Mummy Wadda ke zaune a bakin gado ri?e da hisnul Muslim a hannunta
"Hmmm Wan albarka! Nagode Allah yayiwa Rayuwa Albarka, Wallahi kamar kasan yau tunda na tashi naji inason nasha fura"

"Mummy babu Godiya tsakanin mu, domin idan ma Akwai to nine yakamata nayi ta gode miki har ?arshen rayuwa ta koma fiye da haka"

Mummy Ta rasa Irin halin Aadhil, baya taSa son ace yayi sai dai kullum yace ita ta gama yi mishi komai, "Allah yayi maka albarka, ya kuma kare ka daga Dukkan abin ?i dake a sararin duniya, sannan ya cika maka duka burikanka na Alkhairi"

Sosai Aadhil yaji zuciyarshi ta samu salama, ya rasa meyasa koda cikin damuwa yake idan iyayen shi suka sa mishi Albarka sai ya nemi damuwar ya rasa, "Mummy Nagode Allah ya saka da Alkhairi, amma mum wai suwaye ne a falour kuma me suka zo yi?"

Sanyi Mummy taji a ranta kila ko Aadhil Win yaga wata a ciki yana sone, sosai takeso taga Aadhil yayi Aure Amma tunda take bazata taSa cewa ga rana Waya dataji zashi zance ba ko taji wani yace ga budurwar Aadhil ba, shi kanshi Abba Abin yana damunshi Amma ganin Aadhil Win a kame yake basa tunanin yana yin wani abun banza shiyasa suka kyale shi har zuwa sanda shi yayi maganar da kanshi "mummy bakice komai ba" Aadhil ya kuma yiwa mummy magana don yaga kamar ta shiga tunani

"?awayen zaituna ne, zuwansu kenan ka fito, gashi ita kuma ita ta tafi gidan salma tunda duku duku, shine nace su zauna su jirata tunda ba dadewa zatayi ba"

"Mum! Memakon kice su bita gidan Aunty salma Win kawai, jifa yadda suka cikawa mutane da?i"

"Kaniyarka Aadhil, duk girman faloun nan ne zakace sun cika shi?" Cewar Mummy jin cewa ba burge shi suka yiba

"Mum Allah ni sun sika min guri, kuma inaso na zauna a faloun nasha iska" cewar Aadhil yana shagwabe fuska

Mummy tasanshi Sarai da Rashin sakin jiki da mutane shiyasa kawai tace mishi yaje tana zuwa "yauwa mum Godiya nake"

Kallonshi kawai tayi tana tuna Aakhil, tasan da shine zama zaiyi har yayita jansu da hira har zuwa zaitunan ta dawo, "ooh Allah me iko! Komai nasu iri Waya, amma sai Allah ya bambanta halayyar su" Abinda Mummy tace kenan tare dajin wani nauyi a cikin zuciyarta


Koda Aadhil ya koma faloun saiya sa hannu a aljihu ya ciro kuWi tare da ajiye wa a saman table Win da Mummy ta ajiye musu lemu "Gashi kuyi kuWin mota kuje gidan Aunty salma Win ku sameta"abinda yace musu kenan ya kara tsuke fuskarshi

Abinda bai sani ba shine su Hakan da yayi sai suke ganin kamar sun burge shine, ko kuma yana neman damar dazaiyi musu magana ne
Cikin kwainane Waya daga cikin su ta Wauki kuWin tare da cewa "To mungode yaya Aadhil"

Hannu kawai ya daga musu yana tsaye a yanda yake, Waya hannunsa yana cikin aljihun wandonshi
Sanda zasu fita har wani rangaji sukeyi wai irin su ?ara jan ra'ayin sa sosai, sai dai Abinda basu saniba babu Wadda zai iya cewa ga kalar kayan datasa ko ga kalar furkarta domin sam shi be kalle suba saboda shi bega Abin kallo a tare dasu ba

Suna fita yayiwa kanshi mazauni a three sitters sofa tare da mi?a hannunshi yana Waukar remote control, tashar ya chanza zuwa saudi Qur'an, sosai yaji nutsuwa tana saukar mishi yayinda kunnenshi yayi arba da ?ira'ar marigayi Sheikh Aliyu Abdullahi jabir (Rahimahullah)

Dai nan Mummy ta iso falourn ri?e da madaidaiciyar shopping bag a hannunta "Aadhil ina yarannan suke"

Saida ya cuno baki sannan yace "Mummy ce musu nayi suje gidan Aunty salma Win su sameta"

Kama haSa Mummy tayi tare da rafka uban salati "Lallai Aadhil! Yanzu korarsu kayi?"
"Mummy Wallahi ban yi musu wani abu mara kyauba, kawai gani nayi da zaman banzan da sukeyi gara suje su sameta achan Win suyi Abinda zasu yi, ai ya kamata mutum ya ri?a girmama lokaci koh"

"Ai ka riga kayi Abinda kaga dama, kuma nima zanyi nawa" Abinda Mummy tace kenan ta juya da nufin komawa

Ai Aadhil besan sanda ya ganshi a gaban Mummy ba, duk yabi ya kanainayeta "Mummy Don darajar Annabi kada kiyi fushi dani"

Yadda Mummy taga ya ruWe saida Abin ya bata dariya, waishi sam meyasa Aadhil beso yaga tayi fushi ne dai-dai da kwayar zarrah? Amma hakanan ta kanne don ta tabbatar da gaske ne ya tsorata? "Muddin kanaso na hakuri to saika amshi jakar nan kabisu gidan salmar ka kai musu, da sauri ya amshi ledar yana cewa "kawo inyi sauri"
Tausayi sosai ya bata ganin shifa duk Abinda zaiyi daga zuciyarshi yakeyi, gashi sam baya mata karya koda kuwa shine beda gaskiya, ri?e ledar tayi tana murmushi tare da cewa "Na yafe jeka cigaba da sauraron karatunka, Allah yayi maka albarka"
A raunane ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Aadhil ya sauke wata Irin ajiyar zuciya da take nuna tabbas ya shiga tashin hankali, "Nagode mum" Abinda Ya iya cewa kenan yaja ?afafuwan shi da suka yi mishi sanyi ya koma saman sofa, sai dai a maimakon ya zauna saiya kwanta ya rufe idonshi karatun na DaWa tsuma mishi zuciya
Bashi ya tashi a gurin ba sai wajen ?arfe sha biyu saura kwata, sama yahau ya ?ara yin wanka ya chanza kayan shi zuwa farar shadda saboda samun ladan sunnar ranar juma'a,
Sosai kamalarshi da kwarjinin shi suka daWa fitowa muraran, shi kawai a yanayinshi kana kallon shi sau Waya zaka tabbatar da shi Win mai natsuwa ne koda kuwa tafiyarshi ka kalla

A gaggauce ya sauko ?asa yana ?arasa sa cuff links dinshi da bai ?arasa sawa ba, a gaban dining yaga Mummy tana jera abinci "Mum waiko meyasa Aunty salma bata turo miki wadda zata fara tayaki aikin bane?, Kumafa tun ranar na kirata a waya nace ta samar miki yar matashiyar da zata ri?a tayaki aiki!"

"Munyi waya da ita jiya, tace ta samu wai zata turota yau naga ko tayi min"

"Masha Allah! Me kika dafa"

"Jallof Win taliya ce"
Murmushi Aadhil yayi tare da cewa "ai nasha kin karya alkawarin da kika Waukar min na cewa bazaki kuma dafa abinci me wahala ba har sai mai aikin ta iso"

"Kaniyarka Aadhil! nice ma zan karya maka alkawari"

Dariya yayi tare da du?awa yana sumbatar goshinta sannan yace "Mummy saina dawo"

Addu'oi tayi mishi tare da fatan su dawo Lafiya!

Koda ya Isa companyn su Abba a harabar companyn ya samesu, Abba ne zaune da wani amininsa sai P.A dinsa, da alamu Aadhil Win suke jira
Du?awa yayi ya gaishesu sannan da sauri ya mi?e ya ?arasa don buWe musu motar, sosai abokan Abba suke son Aadhil saboda yadda yake girmama duk wani lamarin daya shafi na gaba dashi, addu'a suketa yi mishi da fatan shima Allah ya bashi masu yi mishi


Bayan an idar da sallar ne Abba yaketa gaisawa a abokansa waWanda suka saba haWuwa a masallacin, gefe Aadhil ya koma yana jira zuwa sanda Abban zai gama saiya maidasu office Win shikuma ya wuce gida

Abin ya bashi mamaki sosai ganin sadeeq a gaban shi yana yi mishi dariya, bayan sun gaisa ne Sadeeq yake cewa "Aadhil kayi wuyar gani"
"Gyara zancenka, cewa zakayi munyi wuyar gani" cewar Aadhil yana murmushi,
"Hakane abokina, toya gida ya Mummy"

"Suna lafiya, ya kwana biyu, idonka kenan kace min kaima zakazo ka gaisa da Mummy amma shiru" cewar Aadhil yana dafa kafadar Sadeeq Win

"Wallahi abubuwa ne sukayi min yawa, yanzuma Allah yayi zamu haWu ne kafin na tafi Cairo"

"Me zakayi a Cairo" cewar Aadhil cikin mamaki

"Wallahi banida lafiya ne, shine nakeso naje gurin doctor Win daddy yayi min general check up"

"Ayyah Allah ya sauke, Allah ya bada lafiya, zuwa yaushe zaka dawo kenan?" Cewar Aadhil cikin alhini

"Gaskiya ban saniba sai dai zamuyi waya idan na sauka"

"Okay to Allah ya tabbatar da Alkhairi, yanzu gidan Mummy zaka ko gidan mummyn husna?"

Shiru Sadeeq yayi tunawa da yayi Aadhil besan yayi aure ba, saida ya Wauki wasu seconds sannan yace "aboki nayi maka laifi fa! Domin wallahi nayi aure"

"Kayi Aure fa kace? Amma shine baka faWa min ba, why?" Cewar Aadhil ranshi a Wan Sace

"Wallahi kuwa komai ne yazo min a gaggauce domin Ni kaina ban taSa zato ba" cewar Sadeeq yana tuna sanda malam barau yace mai ya turo

"Wace ita? Na santa?"


"Ba Lallai ba gaskiya, saboda ba'a nan suke ba, zuwa sukayi daga Jigawa state kuma ma dai gaskiya karamar yarinya ce, sunanta Hafsat"

Kamar gunki haka Aadhil ya koma, tabbas idan ba yayi shirme ba malammadori a jahar jigawa take, kuma Hafsat yar chan ce, and kuma tabbas ya ganta a gidan mummyn husna, that means itace wadda Sadeeq ya aura?

Cikin seconds goma ya hada duka wannan a cikin kwakwalwar shi, tabbas ya gaza, domin jinshi yayi kamar duka anbi duk wata laka ta jikinshi ne an tsinketa, bakinshi kanshi yayi mishi nauyi Amma haka ya aro dauriya da jarumta ya Wora a saman fuskarsa "gaskiya nayi farinciki, Allah ya sanya Alkhairi ya kade fitina ya zaunar daku Lafiya"

A gaggauce Sadeeq ya amsa tare da cewa Aadhil sai sunyi waya saboda wanda yake jira ya karaso, sallama sukayi sannan ya wuce


Wata irin ajiyar zuciya Aadhil ya sauke mai dumi, tabbas Hafsat ce Sadeeq ya aura, kenan shi ?addara ta sakashi son Abinda bazai taSa samu ba, yanzu kenan da Auren Sadeeq a kanta ta rungume shi, shima kuma yayi mata kallon qurilla tare da ri?e mata hannu?, Yanzu dama duk matar wani yake bege?

Jin da yayi jiri na neman kada shi yasa ya ?arasa ya shiga cikin motar ya zauna, kafin wani lokaci zazzaSi me ?arfin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login