Showing 24001 words to 27000 words out of 66006 words

Chapter 9 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

132

Bayan hafsat ta gama hada kayanta da kansu suka Rakata har gidan Haj Khadija wato mummyn husna, sukayi mata godia sannan suka Kara da cewa don Allah idan Taga hafsat din tayi ba dai dai ba tayi mata fada saboda yaro Sai ana kwaba mishi.

Anan gidan Abban hafsat ya bar motarshi saboda sadeeq ne zai kaisu airport din.

Tun sanda Taga sun shiga screening room taji idonta ya cika da kwalla Gani take kamar sun tafi kenan bazasu dawoba... Ga tunanin yanda zata iya zama a gidansu husna bayan Bata saba dasuba...
Kuma Bata tabayin nisa da iyayenta kamar yanda zatayi dasu ayanzuba ..

Hawayen da take rikewane suka zubo sharr a Saman kumatunta

"Subhanallah Noor kuka kuma? Please kada kiyi kuka addu'a zakiyi musu Allah yasa suyi ibada karbabbiya kuma Allah ya kaisu ya dawo dasu lafia..."

Dan nauyin shine ya kamata tayi sauri ta goge hawayen sannan tace "Ameen" a hankali

Murmushi yayi "good girl ko kefa"

Dan Jan hijab dinta tayi ta rufe idonta dashi.

"Yauwa!! aikuwa yau saikin fadamin meyasa kikeji kunyata?"

Kasa tayi da kanta tace "Nifa banajin kunyar ka uncle"

"Hmmm Noor kenan to ko tsoro na kikeji?"

Da sauri ta girgiza Kai "A'a uncle ko daya kawai dai Ina girmama Kane saboda bantaba ganin mutum Mai mutunci irinkaba, sai marigayi sagir kuma ko Shima bai Kai kaba"

Cewa yayi "Nidai yau a taimakamin abani labarin sagir dinnan..."
Igniting motar yayi Yana tafiya a hankali..

Ahankali cikin sanyinta ta fara bashi labarin sagir da irin gudummawar daya yi musu a rayuwarsu, babu abinda ta boye mishi

Kwallar data Dan cika idonshi ya faki idonta ya goge "Allah sarki munyi babban Rashi, Allah ya jikanshi yayi mishi Rahma"

"Amma kenan fa da yanzu ke matar aure ce Koh?"

Kunyace ta kamata "Nifa bani nace Amin aureba, kakanane ya matsa a lokacin, saboda a kauyen mu tun yara na shekara Sha uku ake musu aure gashi kuma sai zuwa ake ana mishi maganata..."

Murmushi yayi "to kila rabo nane"

Ita dai tajishi Amma tana shakku me yake nufi, barin zancen tayi kila kunnenta ne ya jiyo mata ba dai dai ba,
Domin ayanda sadeeq yake me zaiyi da ita kyakkyawa ajin farko ga tsafta da kamshi ga natsuwa da kwarjini.

Kuma ita kanta tasan ya girmeta nesa ba kusa ba.


"What are you thinking of? Kidena damuwa insha Allah kamar yau zakiga sun dawo"

Allah sarki ita ga abinda take tunani Amma shi ya damu, Yana birgeta yanayin yanda yake kula da damuwar wani

Ahankali suke tafiya Yana Dan janta da hira, duk da ba wani magana takeyi sosai ba, Amma shi Yana enjoying moments din sosai.
Hafsat na birgeshi gata karamar yarinya ga natsuwa Sam batada rawar Kai irin na yammatan zamanin Nan, sanyinta Yana birgeshi sosai "oh Allah kaga abinda ke cikin zuciya ta ya Allah ka kawomin mafita, sonta zai iya kasheni Allah! Allah"
Sadeeq ke faWa a zuciyarshi...


Parking yayi a ShopRite yace mata "ki zauna yanzu zan dawo okay.":&?

Murmushi tayi tace "to" ahankali

Baifi minti goma da fita ba ya dawo rikeda shopping bags, a back seat ya ajiye sannan ya shiga suka dauki hanya

"Sorry nabarki ko"

"A'a ai baka dadeba ka dawo"

Tafiyar ?an mintoci sukayi ya iso gidan, Horn yayiwa me gadi ya Bude musu suka shiga ciki,
Bayan yayi parking suka fito suka nufi main parlour
Anan suka tarar da mummy da husna zaune suna kallon sunnah tv.

Sannu da gida ta musu sannan ta zauna a kujerar Dake dama da tasu, da gudu husna ta fada jikinta "Aunty Kun dawo? Naji dadi da mummy tace Zaki zauna Dani kinga saimu rikayin komai tare Koh?

Murmushi hafsat tayi "Eh hussy in'sha Allah"

Itama dariyar tayi mekyau irin ta yara sannan ta taba gashin idon hafsat "Aunty malamin makarantar islamiyar mu fa yace babu kyau sa false lashes"

"Husna ba false lashes bane haka idona yake" hafsat tace a hankali tana yi mata murmushi

"Hmmm indai husna ce sai kin gaji da surutunta" cewar Mummyn husna tana hararar husnan

Murmushi sadeeq yayi "Gashi ita kuma ba gwanar surutuba, don asurutu tsaff husna zata iya Saida ita"

Dariya mummyn tayi "Tashi muje in nuna Miki dakinki keda husnah naga kamar kin takura anan"

Mikewa tayi tabi bayanta dama zaune take a faloun don babu yanda ta iya ne, don duk sanda ta dago Kai sai sun haWa Ido da sadeeq...


Suna shiga Cikin Wakin hafsat ta cire hijab domin dama zafi ya isheta ga gashin kanta duk ya jike da gumi, zaunawa tayi a sofa din Dake gefen gado a kunyace don hakanan Allah ya Dora mata Jin nauyin mummyn.

Zaro Ido ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?mummy tayi "hafsat zo"

Hafsat Tasha wani abun tayi, sai hakan yasa ta mike a sanyaye ta nufota a hankali "Gani mummy" tace kanta a kasa bayan ta Isa gabanta

Gashin kanta Wanda ya sauka har tsakiyar gadon bayanta ta kama guri daya ta rike "hafsat duk wannan gashin kine?"

Murmushi hafsat tayi Jin ba laifi tayiba

"Amma duk uban gashin Nan shine bakyayin retouching? Lallai dole kuwa kiyi ta zufa, Masha Allah gobe zamuje saloon sai a gyara Miki shi Koh?"

"To Mummy nagode"

"Ni yayar kice ki Dena yimin godia" cewar mummy tana murmushi

Karewa hafsat din kallo takeyi a fakaice "tab wannan wace irin halittace? kyan ?irar da Allah yayi a wajen tayi yawa, Ace wannan ce yar shekara Sha shida, Anya sadeeq ba rainamin wayau yayi ba kuwa, hmm ai zan sani yanzu tunda Muna tare"

Mikewa hafsat tayi bayan mummy ta fita, ta shiga bayi donyin wanka.

Tana fitowa husna tace "Aunty mummy tace muje muci abinci ansha ruwa"

A gurguje tadan goga lotion a jikinta sannan ta samu bakar doguwar riga tasa bayan tasa undies
Kohl tasa da Wetlips sannan ta yafa gyalen rigar tana cewa husna "muje to"


Tsayawa husna tayi tana kallonta "Aunty ko kece suhani ta film din junooniyat?"

"A'a mekika Gani?"
"Allah aunty kece, nasan bazaki fada min bane saboda kada nace ke yar film ce"

Rike hannunta tayi "husna muje kada mummy ta gaji da jiranmu"

Suna shiga faloun ta kwace hannunta ta fada jikin sadeeq "uncle don Allah ba Aunty bace suhani?"

"Wace Suhani?" Cewar sadeeq don be fahimci inda husnah ta nufa ba

"Ta Film din junooniyat mana?"

Sai sannan yakai dubansa ga hafsat wadda karasowarta kenan. Fuskarta dauke da murmushi


Kusan rasa nutsuwarshi yayi "wai ita wannan yarinyar kullum kamar canzata akeyi, babu kwalliya Amma kullum kyaunta karuwa yake"

"Sannunku Mummy da uncle"
Ya jiyo zazzaka kuma sassanyar muryarta tayi amo cikin kunnenshi

"Yauwa sannu hafsat har kinyi wankan?"

Murmushi hafsat tayi "eh Mummy nayi"

Shi sadeeq Yama kasa magana sai binta da yayi da Ido, Duk abinda yake mummy ta ankare dashi, Amma Bata nunaba.

Zama hafsat tayi Sannan mummy tayi serving din kowa, ahankali suka fara cin abincin Amma Banda hafsat wadda keta faman Juya chokalin a cikin abincin.

"Sadeeq dauki abincinka ka koma falour, cewar mummy tana kallonshi"

Babu musu ya dauki plate din yabar dining area din.

"Ikon Allah wai sadeeq wane irin mutum ne mara girman Kai?
Abinci yakeci akace ya tashi Amma haka ya tashi babu ko musu"
Ji tayi ya birgeta matuka.


*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*12*

*MATAR RASHEED*


_______Bayan sun gama cin abincin ne mummy tace "mu koma falour sai muyi hira achan Koh?"

Murmushi Hafsat tayi "to mummy" sannan ta rike hannun husna suka nufi cikin falourn tare, a two sitters couch suka tarar da sadeeq ya kishigida sannan yayi pillow da hannunshi kuma idonshi a rufe,

Da gudu husna ta kwace hannunta ta faWa kanshi "Uncle nasan ba barci kakeyiba ka tashi muyi hira"

A hankali ya bude idonshi da yafarayin ja alamun barci ya soma daukar Sa "husna barci nake yi kaina ne yake ciwo"

"Sannu Uncle, kasha paracetamol?"
"A'a" cewar sadeeq yana rufe idon shi

Da sauri Hafsat taje gurin mummy "mummy kan Uncle yana ciwo Please ki bani paracetamol in Kai mishi yasha"

"To bari na dauko" stairs ta hau tana mamakin ya akayi hankalin Hafsat ya tashi sosai daga ciwon kai? "to kodai itama tana sonshi ne? Amma ko danafi kowa jin dadin hakan" zancen zuci taketayi har ta dauko paracetamol Win ta dawo...

Da sauri Hafsat ta amsa sannan ta koma cikin falourn, fridge ta bude ta dauki bottle water mara sanyi sannan ta karasa kusa dashi
"Uncle tashi kasha paracetamol, na amso a gurin mummy"

A hankali ya bude idonshi jin soft voice dinta cikin kunnenshi.

A tsaye ya ganta da alamun damuwa a fuskarta hannunta rike da table water da paracetamol.

Mamaki abin ya bashi domin shi ya faWi hakane don husna ta rabu dashi don yasanta da rigima zata iya cewa saiya tashi ya zauna gashi kuma yaji dadin kwanciyar, amma Sam shi babu wani ciwon kai dayake damunshi.


Tashi yayi ya zauna sannan ya amshi tablet Win data ballo mai guda biyu ya zuba a bakinshi sannan ya kora da ruwan, yayi hakane don kada ya Gwale ta.

"Sannu Uncle maganin ya isa ko sai kaje asibiti?"

"Kada ki damu ba sosai bane, idan na tashi zai dena insha Allah..."

"To Allah yasa" Hafsat tace a marairaice

Rufe idonshi yayi yanajin wani irin farin ciki, yanda Hafsat ta nuna ta damu dashi ba karamin jin daWin hakan yayi ba.

Hakama ta bangaren mummy dake tsaye a dining area tana le?ensu, ji tayi Hafsat ta daWa burgeta itadai tana fatan su auri junansu.

A one sitter couch ta zauna amma duk saita ke jin babu daWi, ko kaWan bataso wani abu ya samu wani balle sadeeq daya zame musu garkuwa kuma jigo a cikin rayuwarsu, da ace zata iya cire ciwon kan ta dawo dashi jikinta to babu abinda zai hanata yin hakan.


Ganin yanda Hafsat Win tayi sanyi yasa husna tace "Aunty kada ki damu zaiji sauki kinji"
Murmushi Hafsat Win tayi "to husna Allah yasa haka"

"Ameen Aunty" cinyarta ta hau ta zauna tana kallon fuskarta "Aunty Allah ke yar India ce, bakyaso ki fadamin ne kawai "

"Husna Ni shuwa Arab ce, bansan me zance Miki ki yarda cewa Ni ba Yar India bace"

"Aunty menene shuwa Arab?"

"Yaren mamana ne"

"Kema kin iya?" Cewar husna tana kallon cikin kwayar idon hafsat sosai"

"Ban iya ba" tace hakan ne saboda kada tace saita yi mata

"La! Aunty kwayar idonki ba baka bace light Brown ce!"

"Husna barci nakeji don Allah"

"To Aunty zo muje ki kwanta" tashi tayi daga jikinta sannan ta ri?e mata hannu har zuwa Waki.

"Aunty ki kwanta nidai gurin mummy zani"

"To husna saikin dawo" hafsat tace tana janyo wayarta don ta kira murja


????????????????????????


Cikin yan kwanaki sadeeq ya cusawa Hafsat sabo dashi, saboda duk inda ta zauna shima yana nan, daga yayi mata wannan labarin sai yayi mata wancan..

Kuma bini bini ya kaisu shopping, ita har kayan sunyi mata yawa...

Kuma yawancin abubuwan da yake siyowa basa wuce doguwar riga abaya sai clutch da flat shoes... Sai su Wan kunne da agogo..

Ta Sangaren Hafsat kuma wata irin soyayya takewa sadeeq amma bata saniba, Sam bataso tayi nesa dashi gashi kullum kara burgeta yake yi, ko fita yayi zuwa Company kosawa takeyi ya dawo...

Ko kwanciya tayi haka zatai ta tunaninshi har sai barci ya dauketa..

Shima ta bangaren sadeeq Win wata irin tsantsar kaunar Hafsat ce ke Dawainiya dashi, daurewa kawai yakeyi..

Musamman yanzu da mummy ta dage da gyara Hafsat Win, don ta kaita saloon an gyara mata gashin kanta kuma an mata dilke sannan akayi mata jan lalle hannu da kafa irin na zamani..

Ranar sadeeq rasa yanda zai yi yayi, don shi gaba daya chanza mishi tayi kamar ba itaba, saboda dawowar shi kenan daga office ya hango mummy a dining..

Karasawa yayi dining Win "tunda naji ansha ruwa naketa sauri na dawo amma shine ko jira na b......."

Maganar ce ta ma?ale mishi a wuya, ganin Hafsat rike da jumbo warmer ta fito daga kitchen, sanye take da riga da skirt na atampa kuma Winkin ya zauna mata das ajiki kanta babu Wankwali sai madaidaicin Gyale dake hannun husna wanda alamu ya nuna zamewa yayi akan Hafsat Win ya fadi shine husnan ta Wauko mata.

A saman dining Win ta Wora warmer Win, "mummy gashi mun gama"

"Sannu da ?a?ari hafsat" mum tace tana buWe warmer Win , wani kamshine mai daWi ya bigi hancinsu.

Shi kuma sadeeq tsaye yake kawai ya zuba ido wa kunshin Dake kafa da hannun hafsat wanda yayi wani irin pure maroon, kasancewar ta farar fata.

Kunshin ya burgeshi matuka, Wagowar da zai yi itakuma hafsat na gyara gashin kanta zuwa baya dayake sanda zata ajiye warmer Win a saman dining ya zubo ya rufe mata Ido...

Sakin baki yayi yana mamaki "duka wannan gashin natane? Ai be gama tsinkewa da lamarin ba saida idonshi ya sauka a kirjinta, runtse ido yayi yana yiwa Allah godiya dayasa Saida aka sha ruwa hakan ta faru

"Tabb bazai yuwuba Gara na faWa abinda ke raina kafin wani ya rigani" zancen da sadeeq keyi a zuciyarsa kenan, "wai dama haka yarinyar take? Hu'um lallai doguwar riga ma sirrin gareta"

Dai dai nan hafsat ta gama daura gelen a kanta "sannu da dawowa Uncle"

A Wan daburce yace "sannu hafsat, yau ban daukoku daga school ba, aikine ya mini yawa kuma koda na duba agogo sainaga lokaci ya riga ya wuce.

Murmushi hafsat tayi "ai daya ke mun fara revision, shine aka tashi 11:am to sai muka biyo school bus kawai..."

"Okay yayi" haka kawai Sadeeq ya iya cewa domin jinshi yake kamar bashi ba, husna ce ta karasa kusa dashi tana wani yarfe hannu alamar yanga "Uncle kalli lallena!

Murmushi yayi "yayi kyau hussy! amma sai dai na Auntyn ki yafi naki kyau"
Chuno baki husna tayi "munyi faWa ma Uncle, kuma babu ruwana dakai"

Sam be san meya ceba Saida husna ta ruga stairs da gudu tukuna Abin ya dawo mishi.
Kunya yaji ta kamashi, bin bayan husnan yayi da sauri, tasa hannu a handle kenan zata buWe kofa ya ri?e hannun
"I'm sorry husna daga wasa? Be kamata kiyi fushi ba.."
"Kinsan yanda nake sonki koh?"

Murmushi husna tayi "to uncle nawa yafi kyau ko"

Murmushi shima yayi mata "eh naki yafi kyau, sosai ma"
Falourn ya kama hannunta suka koma, a dining table suka tarar dasu har sun fara cin abincin

"Mummyn husna sai kunshe dariya takeyi domin duk Abinda Ya faru ta sani, ita Kuma hafsat ko a jikinta domin batasan ma wainar da suke toya wa ba!

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*13*

*MATAR RASHEED*

______Kujera ya jawa husna ta zauna sannan shima ya zauna.

Hafsat ce ta mi?e ta zuba musu sannan ta ajiye wa kowa nasa a gabansa.


Shiru gurin yayi kowa da abinda yake tunani, shidai sadeeq mamaki yakeyi a ina hafsat ta iya abinci haka mai daWi gata kuma ?aramar yarinya.

Itama ta Sangaren mummyn husna ma haka mamaki takeyi sosai.


Hafsat kuma gabanta ne keta faWuwa ga wata irin fargaba data cika mata zuciya...

?agowar da zatayi suka yi ido huWu da sadeeq, da sauri ta kauda kai tana murmushi domin bata iya kallon cikin idon shi saboda wani irin kaifi da kwarjinin da yake yi mata.


Ita kanta yanzu ta rasa wai meyasa take jin tsoron shine!

Dakyar taci abincin, shima kaWan sannan ta mike "Aunty babu aikin da za'a yi Miki?"

"Hafsat na lura sam bakya son cin abinci, fisbilillah ace ka wuni baka ciba kuma asha ruwa ma kaki ci? don Allah ki ri?a ci kada iyayenki su dawo suga duk kin rame su zata bana kulawa da kene.."


"Mummy Allah na koshi, ya isheni, wane aiki zanyi Miki yanzu"

Murmushi mummy tayi "Hafsat Bakya gajiya, duk uban aikin da kikayi yau amma baki gajiba wanima kike nema, je ki kwanta ki huta, zanyi sauran kuma akwai gobe insha Allah"

Sadeeq dai duk yanajin abinda suke cewa amma be kulasu ba sai yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login