Showing 12001 words to 15000 words out of 66006 words

Chapter 5 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

126

"Hafsatou nayi yawo sosai! domin yawancin aikina a gidan ?an siyasa nayi shi, wasu muji dadin zama dasu wasu a rabu tsiya tsiya, wasu kuwa wahala kesa na gudu da kaina"

"Akwai gidan wani minista da nayi aiki, yaranshi takwas kuma kowa saina yi mishi girkinshi daban, kuma hakan bai hana idan nayi suce ba abinda na dafa suke soba saina kara dafa musu wani, kuma ga raini da gori"

Ai tuni sukayi ta hira, barin hafsat dama akwai son labari sosai.

Sai gurin shida na yamma abban hafsat ya dawo, bayan yayi wanka ya shirya ya ci abinci shima ya fito aka ci gaba da hira dashi, tunda duka a matsayin uwa suka dauki baaba indo duk da ba wani girmansa tayi sosai ba.

Sai da dare yayi kowa ya nufi makwancin sa, anan hafsat tacewa baaba indo tare zasu rika kwana a Wakin ta....

Washe gari tunda asba baaba Indo ta gama komai na gidan, kamar su shara, wanke bayi, goge goge dadai sauransu.

Kafin bakwai ta gama karin kumallo.

Koda suka tashi mamaki suke tayi "Baaba bakya gajiya" cewar maman hafsat.
"Hmm ?ar nan ai nan ba komai nayiba, nida nake dafa abinci lamba talatin da safe, da rana ma haka.
Da dare ma tuwo da miya"

An tsokano wa hafsat abinda take so tuni ta sako tata tambayar "to baba kuma duk kina iyayi?"

"Hmm hafsatou ina iyayi, ai duk gidajen dana zauna babu wanda naji dadin zama dasu irin gidan wani senator, Shima matarsa Waya ?ar sa Waya, yanda kika ganku Win nan, akwaisu da mutunci ga tsafta.
Kuma duk wata saina raka ?ar su *Safna* gyaran gashi da gyaran jiki, ke nifa a gurin ta na koyi abubuwa da yawa domin hatta da ?umba (Akaifa) sai anje wani katafaren shago an gyara ta hannu data ?afa"

Umman hafsat ce tace "baaba muje mu karya, ki kyale jikar nan taki naga alamu idan kika biye mata bazata rika barinki ki huta ba"

"Ki kyaleta, ai matambayi baya Sata, sannan tambaya ai Mabudin ilimi ce" Cewar baaba indo tana mikewa da nufin zuwa dining area don haWa abincin.

Hafsat???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da Baaba Indo ne suka Ci anan, Umman hafsat kuma dibar musu tayi ta tafi Waki sukaci tare da maigidanta.

Koda driver yazo domin kai hafsat makaranta tare da abbanta suka fita saboda shi zai rakata makarantar.

Anyi mata interview babu laifi, tasan abubuwa da yawa sai dai wand ba'a rasa ba, uniform suka bata, farar long sleeve shirt ce sai skirt Blue black wanda da kaWan ya wuce gwuiwa da Safa fara iya gwuiwa, sai kuma mini hijab iya kafaWa shima fari.

Ba?in cover shoe aka bata da kuma littafan da zata rika amfani dasu.

Bayan an gama komai director din section dinsu yace "sai ranar Alhamis zata fara zuwa saboda suna da hutun mid term.


Office Abban ta ya wuce, ita kuma hafsat driver ya maida ita gida.

Da murna ta shiga falour, aikuwa ko zama batayiba ta fara basu labari tana buWe musu kayan da aka bata.

"Umma wallahi Makarantar harda turawa, kuma kowa na makarantar dan gayune"

"To uwar zakwaWi ki bari kici abinci saiki bamu labarin" cewar maman hafsat itama tana jin daWi a ranta jin cewa burin Hafsat nayin karatu mai tsawo zai cika.

Dariya baba Indo tayi "To ai yarintar kenan, don Allah ki dena gwaleta, domin gwale yaro yana sa mishi fargaba da Rashin karsashi"

?????????????

Yauma Abban hafsat kamar yanda ya dawo jiya haka ya dawo, sai dai yau Wauke yake da kaya ni?i ni?i.
Amsar kayan umman hafsat tayi suka shiga falour tare.
Ruwa ta kawo mishi da abinci, bayan ya kammala ne tayi mai tayin ko zai yi wanka amma sai yace "tabarshi sai anjima"

Ledojin ya janyo ya buWe yana ciro kayan ciki, Atamfofi ne da hijabai sai takalma da dai sauran abubuwan amfani na mata
Wasu daga cikin atampopin ma an Winka.

Baki umman hafsat ta bude tana mamaki "Mai gida ina ka samo wadannan kayan haka?"

"Wallahi baban sagir ne ya aiko masinjansa ya kawo min office Wazu, wai tashi gudunmawar kenan kafin a fara biyana albashi, wai yasan kayan mu ba irin wanda za'a iya sawa bane anan, Kuma harda dubu hamsin wai na sayi kayan abinci."

"Dana tashi a gurin aiki ma saida na biya nayi mishi godia kuma na faWa mishi hidimar tayi yawa, Amma sai cewa yayi mun zama daya."

Umman hafsat ta kasa gane wane irin mutum ne baban sagir, tun suna kauye yake hidima dasu yanzu ma haka bai dena ba.

Waigawa abban hafsat yayi "wai ina *Noor* ne?"

"Tana Waki tare da baaba, kasan jininsu ya haWu, Nasan yanzu haka ma bataji zuwan kaba da tuni ta fito"

Mikewa tayi "bari na kirata"
Dakin hafsat ta shiga da sallama, a kwance ta tarar dasu, baaba Indo naba hafsat labarai.

"Oh baaba nace miki ki dena biye mata tana damunki"
Murmushi baba Indo tayi "Nifa bata damuna daWi ma nakeji da take tambayata wasu abubuwan, Kuma ma ai karuwa muke yi da juna"

"To yanzu dai ki fito abban ki ya dawo tun dazu ku...." Ai bata bari ummanta ta ?arasa maganar ba tayi waje da gudu

Murmushi baaba Indo tayi "To kinga yarintar da nake faWa miki, wataran bazata yi ba, domin komai lokacine "

Gyara kwanciya baaba Indo tayi kafin a kira magrib. Ita kuma Umman tabi bayan hafsat

Hafsat na fita ta tarar da kaya jibge a gaban abban ta. Bata jira komai ba ta fara dagawa tana cewa "Abba kayan waye wannan?"

Murmushi yayi "Naki ne Yar Abba."
Murna ta fara yi tana Dada dagawa "Abba a ina ka siyosu?"

"Baban sagirne ya siyo muku keda ummanki, Nima kuma ya siyomin kala biyar."

Cigaba tayi da Wagawa tana dubawa "Allah sarki gaskia baban sagir yanada mutunci sosai"

Raba kayan akayi, inda umman hafsat ta samu atampopi hudu da dinkakku uku, ita kuma hafsat dinkakku biyar da atampopi biyu, sai takalma guda uku uku.
Hijabi ma haka, Acikin dinkakkun kayan umman hafsat ta Wauki guda daya tace hafsat ta kaiwa baaba Indo.
Fitowa baaba tayi tanata godiya, haWe da cewa "dama yau naso naje gida na kwaso kayayyaki na to amma saina bari sai gobe tunda na samu wanda zansa"

"Kada ki damu Allah ya kai mu goben lafiya" cewar umman hafsat

???????????????????

A kwana a tashi babu wuya, Har anyi wata daya da zuwan su Abuja, abin gwanin ban sha'awa
Gaba Waya sun murje sunyi kyau kamar ba suba, domin inba dama tuntuni kasan sunyi zaman kauye ba bazaka taba yarda ba. Saboda dama ko sanda suke a ?auyen Alhassan be barsu cikin wahala ba, domin sunasa kayansu me kyau kuma sunacin abincinsu masu gina jiki.

Matsala daya hafsat take samu, shine a makaranta ba'a son yi mata magana sai dai ayi ta kallonta.
Kuma ita bata sansu ba, sau?in ta daya shine idan da malami a ajin to zatayita masa tambayoyi.

Yauma da zumSure zumSure ta shigo gida, a tsakiyar faloun ta jefar da jakar ta ta faWa kan kujera.
"Lafiyar ki kuwa" Cewar umman hafsat tana tsare ta da ido "Umma nidai sam ?an makarantar nan basa ?aunata, ko kulani basa yi kuma benci nama Ni kaWai ce Babu Wanda yake hawa"

"A'a to meye? Dama ai dan kiyi karatu aka turaki ba don kiyi kawayeba"

Baaba dake zaune tana Sare gyadar miya tace "haba ke kuwa! Hafsatou zonan ki zauna kusa dani"

Tasowa hafsat tayi ta zauna a gefen baaba fuska duk a chukurkuWe.

"Kisan mene?"

"A'a baaba" Hafsat tace cikin zumuWi

"To nidai a ganina kamar tsoronki suke ji ,suna ganin idan sun miki magana kila ki wulakanta su"

"Baaba tsorona kuma?"

"Eh mana hafsatou, kinsan yadda Allah ya halicce ki ba lallai ko acikin mutum dari asamu Waya me kyan kiba kuma kinada kwarjini, shikesa suke kama kansu, Kinsan yawancin kyawawan mata akwaisu da wulakanci da izza, Yanzu dai abinda zance miki shine gobe idan kinje kiyiwa daya daga cikin yan ajinku magana da kanki zakizo ki bani labari "

"Oh baaba! kedai kina biyewa hafsatou, bakya gajiya da shirmenta"

"Yo ina zan gaji da ?awata!" cewar baaba tana Daria

"To ?awa ki tashi kije ki cire kayan makarantar kiyi wanka kici abinci." Cewar umman hafsat itama tana murmushi

Ita dai Hafsat haka ta yini tana mamakin maganganun Baaba Indo "wai itace me kyau! Duk da tasha jin ?an ajinsu na ?auye nace wa tafi duka ?an makarantar su kyau, shima sagir me kyau yake ce mata, amma da baaba Indo tace mata sai taji Abin yayi mata nauyi a zuciya, Amma Allah ya kaimu gobe zata gwada Abin da baaba Indo tace.

*Washe gari*
Koda hafsat taje makaranta ta kasa yiwa kowa magana, tsoro take kada su wulakantata.
Amma tasan baaba bazata bata shawara mara kyau ba
Bari tayi sai da malaminsu ya gama yi musu karatu ya fita, Sannan ta waiga bayan seat dinta , batayi indicating da wanda take maganaba tace "don Allah ku aramin biro nawa ya tsaya"

Har rige rige suke wajen daukowa, kusan mutum bakwai ne suka mi?o mata biron a tare.
Rasa wanda zata amsa tayi, gashi kuma kowa yana mata murmushi alamun ta amshi nashi.

*Mr Naph* wanda shine class Captain dinsu, shine ya taso yazo gefen ta "beautiful hafsatullah bari na raba faWa, kawai ki amshi nawa sai kowa ya maida nashi Koh"

Murmushi tayi "To Nagode" hade da amsar biron da mr naph ya miko mata.

Sauran ta kalla tace "duka Nagode bansan wanda zan amsa bane"

"Babu Komai" suka ce a tare.

Koda akayi break inda ta saba zama a cafeteria taje ta zauna, dama yawanci ita bata yin order komai sai vanilla flavoured ice cream ko chocolate, yau ma shi tayi order.
Ta fara sha kenan mr naph ya iso gurin, kujerar dake kallon tata ya ja ya zauna "Barka dai beautiful!"
"Barka" tace a takaice, tana dena shan ice cream din domin jinta tayi a takure.

"By the way nidai sunana Naphtali simon Kuma Ni Dan Asalin garin Bauchi ne amma anan Abuja ina zaune ne da kawuna.
I'm a Christian, but mu ba ranar Sunday muke zuwa church ba sai ranar Saturday.

Kallonshi kawai takeyi domin ita duk bata tambaye shi duka wannan al amari ba. Murmushi tayi "Allah sarki sannu"

"A'a ba haka zakice ba kema ya kamata ki faWa Min game dake, Koh?"

"To nidai sunana Hafsat Al-hassan kuma Ni yar asalin jahar Jigawa ce amma aiki ya dawo da mahaifina nan Abuja kuma as U can see ni musulma ce"

Murmushi yayi "fine! nice meeting you as classmate"

"Nice meeting you too" cewar hafsat

Fidya da A'isha ne suka zo wucewa ta gefen su "A'a hafsysy kina nan ashe" cewar fidya tana murmushi
" Eh tana nan" mr naph yace

Gefen hafsat suka samu suka zauna anata hira, ita dai hafsat duk a takure take jinta
A'isha ce tace "wai hafsysy meyasa da bakya yi mana magana?"

"Babu komai" cewar hafsat tana murmushi

"A'a kidai faWa mana gaskiya, ko don kinga kinada kyau ne koh?"
Cewar fidya tana kallon mr naph.

"A'a wallahi kawai dai rashin sabone"

A'isha ce ta kama hannun hafsat tana kallo "Amma ke ba yar asalin ?asar nan bace koh?"

"Anan kasar nake mana" cewar hafsat don ta fara ?osawa da maganar su.

"Ikon Allah! to amma dai keba bahaushiya bace koh?" Cewar Mr naph

"Eh! mama na shuwa Arab ce babana kuma kanuri (Yaren malam Musa kenan, Kasancewa hafsat batasan cewa mahaifinta dan tsuntuwa bane, saboda malam barau ya hana a fada mata hakan, yace a bar Malam Musa da inna kulu a matsayin kakanninta)

"Kai amma gaskiya kinada kyau, masha Allah! sai kace yar India ko yar Saudiyya!" Cewar fidya tana ?arewa fuskar hafsat kallo

Ita dai hafsat bata ce komai ba sai murmushin da take ta yi.

Koda aka tashi data koma gida babu labarin data keyi saina su fidya da Mr Naph.
Ita kuma baaba indo tana ta biye mata.

Washe gari ma haka akayi tun a class Saida ta samu seat mate, kowa saiyi mata magana yake yi, ita abinma har ya fara damunta.

Koda aka tashi yau drivern Hafsat baizo da wuriba,
A bakin gate Win school din ta tsaya tana Wan kalle kalle.

Wani matashi ne dogo kyakkyawa shima ya riko hannun wata yarinya, itama dalibar makarantar ce amma ita a primary section take duba da uniform Win dake jikinta.
Bai lura da hafsat ba saida suka kusa zuwa inda take, Binta yayi da kallo har suka wuce.
Ita hafsat ma batasan yana yiba Domin duka hankalinta na kan titi ta baza ido tana tunanin ta inda zata hango driver.

Cikin hanzari yasa yarinyar a cikin mota domin ya dawo gurin hafsat, amma cikin rashin Sa'a kafin ya ?arasa har hafsat ta shiga Mota sun nufi hanyar gida.

Dun?ule hannu yayi "damn it! naso muyi magana but never the less nasan zamu hadu wata rana"

Motar ya koma shima ya dauki hanyar gida.

*Readers ko akwai wanda zai iya cinkar waye wannan matashin?*
*Sadeeq? Alhaji madu? garba sholi ko Aadhil?*

*I'm tired*=?%?


*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*


*7*

*MATAR RASHEED*


__________Koda hafsat ta isa gida a gajiye take, kuma dayake tana _period_ sai takejin ta wani iri ko magana ma bata son yi sam.

Baaba indo ta lura da haka, kuma da yake dattijuwa ce mai Dattaku wadda tasan ya kamata sai ta kyale hafsat din bata wani shiga hurumin taba.

Misalin ?arfe biyar na yamma baaba indo ta shiga dakin hafsat din "jikalle ki fito kinyi ba?o, malamin da abbanki yace zai turo yaci gaba da koya miki karatu ne yazo tun dazu yana falour"

"To baba na gode" ta faWa a kasalance.
Tashi tayi ta samu hijab ta Wora a saman riga da skirt din dake jikinta ta kwashi littattafan addininta tayi haramar fita.

A harabar gidan ta sameshi zaune a saman farar kujera, matashine wanda bazai wuce shekara arba'in ba ko da Wan doriya kadan.

Bakine mai faWi kuma mai matsakaicin tsawo.
A ladabce ta gaisheshi bayan ta zauna a saman daddumar data Wauka a falour

"Alhamdulillah, komai lafiya"
bai ja gaisuwar tayi tsawoba kuma haka baya ko kallon ta.

Littattafan data ajiye a gefe ya duka ya dauki tauhid, ?an tambayoyi yayi mata duk ta bashi amsa dai-dai harda ?arin bayani.
Hakan ya nuna ta gama littafin.

Fiqhu ya dauka, itama haka tagama.

Sai da ya dauki littafi hudu duk ta gama ana biyar ne _*(tarbiyya)*_ tace shafi biyu ta karanta,

Anan ya kara mata a nutse saida ya tabbatar ta fahimta sannan yayi mata sallama ya tafi.
Bayan ya shaida mata cewa zai rika zuwa karfe biyar yana tafiya shida.
Wato karatun awa daya zasu rika yi.


Taji dadin karatun inda ta nemi kasalar da take damunta ta rasa.
Kitchen ta karasa anan ta tararda ummanta da baaba indo suna girki.

Sa musu hannu tayi anayi ana hira duk da yau babu wannan tambayar bin kwakwkwafin.

bayan sun gama ne suna ?o?arin fitowa daga kitchen Win abban hafsat yayi sallama, da sauri hafsat ta karasa ta amshi jakar hannushi da kuma shopping bags Win dake Waya hannun.

Bayan kowa ya kimtsa ne hafsat ta koma gurin Abbanta don amsar tsarabarta kamar yadda ta saba kullum.

Gefen babanta ta zauna "Abbana ni kaWai, yau me ka siyo min?"

Murmushi yayi "?ar Abba yau na siyo miki chocolate da ice cream, Baaba kuma da ummanki kaza na siyo musu"

"Ni dai Abba yau bana son kayan za?in nan zakar zaka Bani guda Waya"

Zaro ido yayi "hafsatou keda kike kamar shazumamu yau kuma kece ke cewa ba kya son Kayan za?i? Ahh lallai *_tatuwa_* an girma" yakan ce mata tatuwa ne duk sanda yake so ya tsokaneta.

"Dama kinga ranar juma'a zamu tafi malam madori yiwa malam sallama kinga sai a Daura muku aure ku tafi tare koh?"

Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, Hakan ya DaWa tabbatarwa Abban Lallai su hafsat anyi hankali, domin da ada ne yayi mata wannan tsokanar to ta ri?a murna kenan tana cewa "Ai malam yana sona kuma yana bani alawa, kanya harda galgale da magarya" Sabanin yanzu da tayi shiru tana Murmushi.

Ita dai umman hafsat tana jin su bata ce komai ba in banda Murmushin da tayi, sai dai ita tasan dalilin hafsat din na ?in yin maganar.

hafsat irin yaran nanne masu ?awazucin mahaifiya don ko tusa idan tayi sai ta fada mata.

Kuma bata taSa iya kwana a wani guri inba gidansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login