Showing 39001 words to 42000 words out of 66006 words

Chapter 14 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

146

sai ya gudu, kuma sai a kama kanwarshi Ayita duka"

Tsaye yayi kawai yana kallon ikon Allah, wai dama haka Auren sweet sixteen Win yake.

Itafa bata damu da ya zauna ko kar ya zauna ba, ta kallonta takeyi

"To dear azo a taimaka min inci abinci"

"Uncle don Allah kaje Kaci nifa banson in tashi a wuceni"

Nidai nace "Sadeeq ka nunawa Yar banten uba cewa fa akwai banbanci tsakanin ku"

??????????

Cikin wani tafkeken mansion, Wanda Idan zan tsaya zayyana yadda yake to bazan samu damar cigaba da baku rahoto ba, a harabar gidan kuma Aadhil ne tsaye sai wata kyakkyawar babbar mace mara tsayi sosai Wadda ta dafa kafaWarshi, gefe kuma wata yar budurwa ce itama batada tsayi sosai.

"Ya Akhie wannan zuwa haka babu sanarwa kamar Wan gudun hijira?"

"Zaituna badai Rikici ba, keda zakiyi murnar ganina amma kin tsaya yin ?orafi"

"Nayi farinciki sosai mana , kawai dai naso ace ka faWa mana ne Saboda muyi maka welcome snacks"

"Shiru kowa yayi tunawa da sukayi cewa da yanzu su biyu ne zasu dawo ba Waya ba, sauri Aadhil yayi ya shige faloun tare da hayewa sama saboda yadda yaji hawaye na ?o?arin zubo mishi.

Ko cikin Wakin nashi ma haka yake tsaff a gyare, gefe kuma wani Wakin ne shima duka kayan zane ne a ciki, Kuma duka saman drawing board Win suma zanen Hafsat ne da dai wannan peach Win doguwar rigar.

"I'm on my way Noor" (haka yasa mata bawai don yasan ana ce mata hakan ba)

Nanma dai Saida yayi wanka ya chanza kaya Sannan ya fito falour.

"Mummyn Anya kuwa ba gidan Aunty Salma zan tafi nayi dinner ta achan ba?"

"Ai kunfi kusa ka'ida salma Win, a dawo Lafiya!" Mummy tace tana girgiza Kai

"Ya Akhie nima zani don Allah!" Cewar zaituna kamar zatayi kuka

"Oya taso muje mana" Aadhil yace yana yin hanyar fita daga faloun.


?????????

Still a dai dai wannan lokacin dai wata babbar mace ce wadda a ?alla zata iya kaiwa Shekara arba'in da Biyar zaune gaban wani boka Wan China tana faWa mishi Abinda ya Kawo ta



*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*18*

*MATAR RASHEED*


______"Zayt idan baki yimin shiru ba zansa, baba ya maida ke gida" cewar Aadhil yana jinjina kanshi alamar tabbatarwa

"Ya Akhie Allah da ace kaine ke tukin nan da tuni mun Kai, amma kabar baba driver sai riritamu yake a kan titi"
"Okay da alamu bakiji abinda nace ba kenan koh?" Aadhil ya kuma cewa yana mata wani irin kallo me cike da gargadi

Shiru zayt tayi domin tasan gamuwar su bata yin kyau, yau ma taci darajar dawowar shi kasar kenan shiyasa har ya barta ta biyoshi.

Ba'a Kara cikakkun minti goma ba baba yayi parking a bakin gate din gidan Aunty salma, da sauri zayt ta balle murfin motar tayi cikin gidan da gudu.

A hankali cikin nutsuwa Aadhil ya fito daga motar tare da karasawa gaban windon da baba driver yake "Sannu da kokari baba! Mungode, amma inaga kakoma gida yanzu saboda zamu Dade kada kayi ta jiran mu, idan yaso in mun Gama sai in kira kazo ka maidamu"

"To yallabai aini keda godiya, saika Kira din" reverse baba driver yayi tare da maida motar kan titi ya dauki hanya yana daga wa Aadhil hannu

A nutse Aadhil ya tura kofar dake jikin gate din gidan, aikuwa cikin rashin sa'a sukayi gware shida Aunty Salma, dafe goshi sukayi a tare inda ita kuma Aunty salma ta Kara da cewa "tsarabar tawa kenan mutan ketare? Ai gajiya nayi da jiran tsammani shine nace bari na biyo Sahu naga tun dazu zaituna ta shigo, gashi na kosa in ganka"

"Ashe dai kema kinyi kewata" cewar Aadhil yana murmushi me kamar dariya

"hmm kajika da neman zance! Nidai wuce muje ciki ka samu ka zauna ka huta"

Suna shiga falon Aunty Salma tayi hanyar kitchen tana cewa "ka ko yi sa'ar zuwa wallahi, domin jiya mukayi shopping, duk abinda kakeso ka fade shi nasan akwaishi available"

Murmushi Aadhil yayi "Aunty salma dawo, Ai kinsan inda nafi auki, fara bani ita inyaso bayan mun gaisa sai kiyi min girkin" ya karashe maganar yana subale takalmin shi sau ciki kirar companyn milano.
Girgiza Kai kawai Aunty salma tayi tare da juyowa tana komawa dining area, fridge ta bude ta dauki maltina pack daya me guda shida a jiki.
Gaban Aadhil ta karasa ta ajiyeta a saman wani kyakkyawan center table "wallahi bansan sanda zaka chanza ba! Ace wai ka sauka a Nigeria amma ka rasa me zaka nema sai wata maltina, ga abinci nan kala-kala na gargajiya Dana zamani"

"Aunty salma bazaki gane ba, bawai bazan nemi abinci bane, zan nema! Amma nafiso yanzu kizo ki zauna mu fara gaisawa inyaso daga baya sai ki dafamin kayan dadi"

Hararar wasa ta jefe shi da ita "dadai bansan halinka na waskewa bane, nifa ina tunanin tunda nai aure baka taba cin wani abu a cikin gidan nan ba daya wuce maltina" A cikin ranta kuma Aakhil take tunawa, shi babu ruwanshi har kitchen yake shiga ya zuba abinda yakeso.

Murmushi shima yayi "to to to na tuba Aunty, ayi min afuwa, yanzu dai zauna ki Fara bani labarin abubuwan da suka faru sanda bana nan, idan kika Gama nima saina baki labarin Abinda ya faru acan"

Zama Aunty salma tayi a kujerar dake kallon ta Aadhil sai kuma ta Mike "bari na dafawa zaituna koda cous-cous ne tunda dai kai basai ansa ka a lissafi ba"

"Aunty salma Don Allah ki share wata zaituna a koshe take, ina take ma?" cewar Aadhil yana balle murfin maltina guda daya tare da kafata a bakinshi

"Tana dakin Aarhif nasan Suna can Suna hira da Mai rainon shi" cewar Aunty salma bayan ta koma ta zauna.
Cire gongonin yayi daga bakinshi bayan ya shanye, gongonin yasa a tsakiyar tafukanshi ya hada ya matse, take gongonin ya tabe ya koma dan karami, cikin dustbin din dake ajiye a bakin kofa ya jefashi.

"hali zanen dutse! Shiyasa bahaushe yace me hali be canza halinshi"

Dariya Aadhil yayi "Kai Aunty salma! Harma wata special Karin magana kike min?, bar wannan yanzu kije ki daukomin Aarhif inga ya kara wayau kuwa, duk da ina ganinshi ta whatsapp"

Itama Aunty salman dariya tayi tare da cewa " A to, ai gaskiya na fada, yanzu dai fara bani labarin Anjima zan dauko maka shi saboda kada ya tasamu da rigima" _*(AUNTY SALMA KANWAR MUMMYN SU AADHIL CE, KUMA A GIDANSU TA GIRMA SABODA TUN TANA YAR KARAMA AKA BA MUMMYN ITA, KUSAN SA'ANNI NE ITA DA AADHIL DA AAKHIL SHIYASA SUKA SABA DA JUNA SOSAI)*_
" " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " "

*SADEEQ*

Ganin bazai iya jurewa shirmen Hafsat ba yasa ya wuce dakin da yake a mazaunin nashi, hadawa kanshi ruwan wanka yayi ya shige bathroom, bayan ya fito daga wankan ya shirya cikin light blue din pyjamas masu taushi, anan ya janyo laptop dinshi Don duba ayyukan company Wanda be samu dubawa ba kwana biyu saboda hada hadar biki.
Anan ya tarar da sakonni da emails kala kala, yawanci na tayashi murnar biki ne, wasu daga ciki kuma na business dinshi ne.
Anan yayi ta dubawa yana basu amsa, daga baya kuma ya dubbuba files da documents, saida ya tabbatar yaci karfin aikin sannan ya Rufe laptop din yana yin hamma alamun ya Gama gajiya, koda ya duba agogo sai yaga karfe daya saura kwata 12:45am.
Da sauri ya sauka daga kan gadon don yaje ya duba Yaga ko ya Hafsat ta kwanta, abin mamaki koda ya fito falour sai ya ganta zaune ta kafawa TV ido, gabanta biji biji da ledojin chocolate.

Wani irin sassanyan numfashi ya sauke tare da folding din hannayenshi a kirjin shi sannan ya nufi gurinta "Noor Wai don Allah meke damun kine?, meyasa bakije kin kwanta ba?"

"Uncle! Wallahi film din nan ne yamini dadi shine nakeso a karasa sai inje in kwanta"
Kallon TVn yayi yaga tashar *""MBC 2""* Suna wani film *""THE BFG"" (Big Friendly Giant)*
"Amma Noor karfe daya fa! Pls ki tashi kije ki kwanta kefa kika cemin kunada Exam gobe, ko kin fasa zuwa Makarantar ne?"

Da sauri ta Mike daga kan kujerar tana cewa "No Uncle! Don Allah zanje, bari naje na kwanta" hanyar dakinta tayi cikin sauri me kamar gudu batare data tsaya taji me zai kuma ce mata ba, koda ta shiga direct bathroom ta shiga ta fara watsa ruwa sannan ta fito, a cikin kayan da aka jera mata a cikin wardrobe ta samu unisex din pyjamas milk colour tasa sannan tayi addu'oi tare da Jan mayafi ta kwanta.
Guri sadeeq ya samu ya zauna tare da dafe kanshi, tunani yake kusfa kusfa abubuwan da suke faruwa tun bayan biki, kuma Ada ba haka Hafsat din take ba, kawar da tunanin yayi daga ranshi Don kada ya karawa kanshi tension....

Saida ya leka ta ya tabbatar tayi barci sannan ya wuce nashi dakin shima ya kwanta Don baijin yau zaije dakinta.

" " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " "

*AADHIL*

A dai-dai wannan lokacin shima yana zaune rike da wayarshi yana kallon photon Hafsat Wanda aka dauketa da kayan makaranta, ya Dade yana kallon photon sannan ya fita daga gallery din, notification din sms ya gani a gefen wayar, koda ya shiga message din Aunty salma ya gani kamar haka

```yaro komai lokaci ne! Nima wata rana zan Rama, "adai juri zuwa rafi"```

Kyalkyalewa da dariya yayi tuna irin dramar da sukasha kafin tabarsu suka dawo gida, koda ya duba time din data turo message din sai yaga ashema wajen karfe goma ne sanda suke hanyar komawa gida

Reply yayi mata da

```Allah ya kaimu ranar da tulun zai fashe, kadafa ki manta nima fa na iya hausar nan```


Kashe wayar yayi ya ajiyeta a saman bedside table sannan ya shiga bathroom, shima dai wankan yayi ya samu pyjamas ya zira sannan yabi lafiyar gado.



Still a cikin Daren dai na kuma lekawa gurin matar da na gani a gurin boka dazu, zaune na sameta ita da wata matashiyar yarinya a falour sai kace ba dare ba, "mummy wallahi na tsani Hafsat din nan, ji nake kamar na tafi da wuka tsirara na Chaka mata"

"Kada ki damu komai ya kusa zuwa karshe, badai naje gurin boka Dan China ba! Ai kawai ki zuba ido, ubanta kanshi saina maidashi bawa na"

"yauwa mummy don Allah kada ki raga musu, tunda ta shiga makarantar mu kowa ya Dena kulani sai dai ita, kowa so yake ta Zama kawarshi, ga shegen kyau na jaraba kamar saida aka shawarceta kafin aka halicceta"

"diyana calm down mana! Nace miki babanta zan aure insa ya koresu sannan ya zama bawana"

"Yauwa mum sai yanzu naji zan iya yin barci" Cewar diyana tana mikewa don shiga bedroom ta kwanta


?????????????????????????????

Misalin 7:am na safe, Hafsat ce zaune ta hada tea tana kurba, jikinta sanye da Uniform din makaranta inda a daya gefen sadeeq ne zaune ya zuba mata ido yana kallon ta, shidai yasan yanason Hafsat bilhakki, hakan nema yayi tasiri a cikin zuciyarshi ya zamana baya ganin laifinta Sam.

Duk da gargadin da baffa yayi mishi jiya bayajin akwai abinda zai hanashi kaita makaranta muddin ba ita tace bata so ba ko ta fasa zuwa ba.

Shanye tea din tayi sannan ta Kalle shi "Uncle kai bazaka sha tea din bane"

"U'um nisai wajen twelve zan karya"

"Ah! To idan haka ne kawai ka jira na dawo saina hada maka wani abun koh?"

"Okay as you wish, yanzu dai tashi muje na kaiki, and Pls kada ki bari husna ta ganki"

"To Uncle, aida wuya ma idan zamu hadu saboda su ba wannan satin zasu fara jarabawa ba"

"Okay to hakan ma yayi, 11 za'a tasheku ko?"
"Eh Uncle" cewar Hafsat tana gyara zaman jakar bayanta
dai dai lokacin sun isa inda motar take, bude mata side din me zaman banza yayi, saida ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya koma side din driver

A hankali yake tukin shi saboda da sauran lokaci kafin ayi assembly, shidai bece mata komai ba Itama kuma bata ce mishi ba, saida ya isa bakin makarantar sannan yace, "Ayi jarabawa me kyau! Duk da dai *_The big friendly giant_* be bari anyi karatu ba"
Dariya Hafsat tayi tare da rufe fuska "uncle ai na iya subject din da za'a yi mana yau sosai"

"Okay to idan kika dawo gida anjima saiki koya min, yanzu kiyi sauri an kusa fara assembly"
Hannu yasa a cikin drawer motar inda ya zaro sabuwar waya tare da yan dubu dubu sababbi kamar na jiya yana Mika mata
"wayar a silent take, idan kun fito saiki kirani nazo na daukeki"

"To Uncle nagode" bata tsaya cemai yabar kudin ba saboda tasan ba bari zaiyi ba ta amsa duka tasa a jaka inda kuma ta bude kofa ta fita tana daga mishi Hannu

Saida ta shige ciki sannan ya kauda kanshi tare da sauke ajiyar zuciya, igniting din motar yayi ya dauki hanyar gida


*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*19*

*MATAR RASHEED*


_______Misalin karfe takwas Aadhil ya sauko daga sama zuwa dining area, direct gefen Abba ya karasa ya tsuguna don gaisheshi, kafin Aadhil din yace komai Abba yace "good naji dadin ganin ka haka, that means yanzu Ka amshi kaddara kenan" (yana nufin ya hakura da mutuwar Aakhil kenan, duba da kwanakin baya duk yabi ya rame yayi baki)

Murmushi Aadhil yayi "Abba dama tun tuni na amsa, saboda duk musulmi ya kamata ya yarda cewa _KULLUNAFSIN ZA'IKATUL MAUT_ kawai dai a lokacin na kasa jurewa ne, saina rika ganin kamar zai dawo ko kuma wata rana zan ganshi kusa dani"

"Aadhil kenan! Ai Aakhil tafiya ta tafi, sai dai Allah yabamu hakurin rashi sannan yabamu ikon aikata daidai kafin muma lokacinmu yayi" cewar Abba yana murmushi don ya danne damuwar dayaji ta taso mishi

Mikewa Aadhil yayi ya samu guri ya zauna, saida ya gaisa da Abba tukuna ya gaida mum wadda dama zuwanta kenan gurin, gaisheshi zaituna tayi sannan Abba ya kara tambayar Aadhil "komai dai normal koh?"

"Abba komai normal kawai dai nazo na duba kune sai kuma wani dan aiki da zanyi, amma beda wani yawa"

"To masha Allah! Allah ya taimaka yayi jagora kuma ya kiyake ka daga dukkan sharri"

"Ameen Ameen Abhie nagode" Cewar Aadhil fuskarshi a washe alamun yaji dadin Addu'o'in da Abba yayi mishi

Sai sannan mummy tace "me zakaci zaituna ta zuba maka"

"Mummy Bazanci komai yanzu ba sai anjima insha Allah, Yanzu nadai fitone mu gaisa da Abba kafin ya fita, Anjima kadan ma zan koma sama ne saboda na yi muku order tun jiya kuma har yanzu banji feed back ba"

Atare mummy da Abba sukace "Aadhil baka gajiya da hidima, Allah ya kara budi" Itama zaituna sai murmushi take sanin cewa itama zata kwashi tata ganimar

Cigaba da tattaunawa sukayi kafin Abba ya fita office

?????????????


Achan gidansu iyayen hafsat kuwa yan biki kowa ya hada kaya don tafiya Gida, a babban falour kuma malam barau ne da kawu Shehu suketa fafatawa kamar yadda suka saba "Allah nifa ba yau zan tafi ba, nace ku tafi zan biyoku daga baya" cewar kawu shehu yana murtuke fuska domin ya fara gajiya da abinda Malam barau yake yi mishi

"Nidai na fada maka bazan barka a garin nan ba, kafata kafarka! So kake daga komawa ta a turomin da sakon mutuwar Auren maidaddawa".

"Au baba dama abinda kake zargi na dashi kenan, yanzu baba har lalacewata takai na kashewa yata aure?"

"Bawai ina nufin hakan bane a fili, kawai dai ina zargi ne saboda na lura kamar Bakason Auren"

"To nidai baba Ka taimaka ka cire haka daga ranka, wallahi banida niyyar haka! Nida nake burin zuwa wata shekarar ma a kiramu suna"

Washe baki malam barau yayi tare da cewa "ah to dan albarka! Lallai da gaske kake,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login