Showing 15001 words to 18000 words out of 66006 words

Chapter 6 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

133

ba, shi yasa ma bata wani saba da kakar taba sosai ba, wato inna mairo (mamar ummanta)
Tun lokacin data Wauke ta yaye ta rika ciwo kamar zata mutu
Ba shiri aka dawo da ita gurin ummanta.


Abban hafsat ne yayi gyaran murya.

_"A tsawon watanni uku da nayi a Companyn nan ina aiki, Na tara dubu dari hudu da hamsin, ana biyana dubu dari da hamsin ne dama a duk wata"_ _To kinga ba wani abu nake kashewaba kuma baban sagir bai son barina haka, yana min ihsani sosai, Yanzu wannan kudin zan dauki dubu hamsin din kai inyi hidimar tsarabar makwabta, Dubu dari huWun kuma zan rabata biyu inba malam dari biyu yayi tsaraba da ita a Saudiyya, Ragowar dari biyun kuma zan bada a ginawa malam masallaci achan ?auyen idan mun sauka lafiya_

"Wani zuwan idan Allahu ya kaimu sai mu wuce har wajen inna kulu, amma wannan bazamu karasaba saboda ranar Lahadi zamu tawo da safe."

Farin ciki gurin umman hafsat ba'a magana, rasa irin godiyar da zatayimai ma ta rasa, tunda ta fara Godiya da addu'o'i saida ya dakatar da ita,

Itama hafsat taji dadi jin tafiyar koba komai zataga kawayenta na makaranta da wadanda aka Wan saba, dukda ba wani yawa gare su ba. Saboda ita dama bata fiya shiga shirgin da ba'a sata a ciki ba

Harda baaba indo aka shirya, driver yaje aka duba lafiyar motar sannan yaje gidan mai ya ciko tankin motar da fetur tunda tafiyar tasu da tsawo, domin akalla zasu ita Waukar tsawon awa goma sha daya suna tafiya.

Washe gari Misalin shida na safe suka dau hanya, Tafe ake hafsat na tambayar duk abinda ta gani, Allah yasa da baaba indo itace ta biye mata, tunda a kusa da juna suka zauna, umman hafsat kuma a ?arshe, Abban hafsat kuma yana gaba a mazaunin me zaman banza.


Gajiya hafsat tayi don kanta ta dena magana, tunani ta shiga yi tana tuna ranar da zasu zo Abuja a matsayin yan kauye, amma yanzu kalli yadda rayuwa ta koma, lallai Allah shine mai komai kuma me kowa, kuma yana nuna ikonsa akan kowa da komai kuma a lokacin da yaga dama.

Sagir ne ya fado mata da abubuwan da suka samu sanadinsa, take siraran hawaye suka fara zirarowa daga idanunta, ahankali ta rika tariyo abubuwan da suka faru tsakaninsu har zuwa ranar da akace mata ya mutu.

Hawayen ta goge sannan ta dubi zoben da yabata lokacin dazai koma Abuja, wanda har yanzu baiyi mata daidai ba Domin yasha faWuwa ma Allah ne dai yayi bazai bace ba.

Kallon zoben take tana Murmushi, baaba indo ce tace "hafsatu naga hawaye a fuskarki kuma kina Murmushi amma a hankali tayi maganar yadda ba kowa zai jiyo suba.

"Eh baaba, na tuna da sagir ne da dumbin alkhairan da muka samu ta dalilinsa!"
Dayake ta ba baaba indo labarin sagir din tun tuni,
"Allah Sarki hafsatou , ai kinyi rashin masoyi na hakika amma Babu komai, kuma Allah yasan dalilinshi nayin hakan, Sai dai kiyi tamai addu'a, domin itace abinda zaki iyamai ta amfane shi a yanzu"

"To baaba Nagode" sannan ta jingina da bayan kujerar da take zaune a kai.

Ba'a dau lokaci mai tsawo ba hafsat tayi barci duk da ba daWin zaman motar take ji ba saboda rashin sabo da tafiya me tsawo.

Itama umman hafsat din barci tayi, sai dai ita baaba indo daram take domin ta saba da irin wannan tafiyar.

Dai dai lokacin da suka zo zasu wuce ta gwargwaje Baaba Indo tace "Wana kaga inda nake sauka idan zani Zaria"

"Allah Sarki baba nasan sai kinji wani iri!"

Haka sukayi ta hira jefi jefi, Gidan mai driver ya shiga ya kara mai, shi kuma abban hafsat ya sauka ya dan sayi abinda zai siya.

Ruwa baaba Indo tasha sannan ta Wan mike kafa kafin su dawo.

Basu daWe ba suka dawo aka kuma Waukar hanya.
suna shiga Kano su hafsat suka farka daga barci, Abba Hafsat ne yasa driver ya tsaya don a samu Abinda zasuci kafin suci gaba da tafiya.
Restaurant suka samu Abban hafsat ya siyo musu abinci ya kawo musu, shida driver kuma suka ci achan,

Masallaci suka nema sukayi sallah, bayan sun dawo ne driver ya Wauki harami, sosai abban hafsat ya siya abubuwan da zai yi tsaraba da yawa a Kano din saboda sunfi sauki.

Sai misalin 5:39pm na yamma suka isa kauyen malam madori,
Murna a gurin malam barau da inna Mero ba'a magana, kamar su cinye su don farin cikin ganin yadda suka koma kamar basu ba.
Namma makwabta suka rika shigowa ana gaisawa tunda anyi zaman mutunci,

Kowa yazo bai fita saida Wan hasafi, dama Al hassan akwai kyauta balle yanzu daya samu abin hannunshi babu laifi.

Kwana sukayi da malam barau suna hira, Inda can ma wajen su hafsat din haka ne

Da gari ya waye kuma suka dan zazzaga inda sukeson zuwa.
Bayan sun dawo ne malam barau ya fara yiwa Al Hassan maganar hafsat, domin tunda suka sauka ya lura da girman da hafsat Win ta kara a cikin yan watannin dasuka bar kauyen.

"To ta samu mijine acan? idan bata samuba akwai mutum biyu da har yanzu suke min naci a kanta, kaga sai azabi daya aciki ace ya Turo"

Ai tuni Al Hassan yace "Aikuwa baba ta samu miji sai dai yace adan bashi lokaci kafin ya turo, dama da zancen nazo zan fada maka to sai kuma Allah yasa ka rigani yi"


Washe baki malam barau yayi "to to masha Allah kaga idan na dawo daga Saudiyya sai ayi bikin kenan Koh"

"Haka ne baba" cewar Alhassan Yana kauda maganar daci cigaba da hirarrakin su.

Washe gari da sassafe suka shirya don komawa Abuja,
Kamar kar a rabu haka sukeji, inda baaba Indo har sun saba da inna mairo (kakar hafsat)....

Haka dai aka rabu babu dad'i kowa yana kewa......

??????????


Tun bayan dawowarsu daga jigawa rayuwa taci gaba dayi musu sau?i, Allah yana ta ?ara buWewa abban hafsat kofofin alkhairi.

Ita kuma ta bangaren umman hafsat duk sun saba da makwabta saboda Yadda takeda mutunci da faram Faram da mutane


*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment```
*IZAYAR RAYUWA*

*8*

*MATAR RASHEED*



_______*_BAYAN WASU WATTANI_* Duk wani wanda ya san Alhassan saida ya ?aru dashi, domin duk bayan albashi saiya ware wasu kuWi daga ciki wanda zai kyautatawa al ummar musulmi da wanda zai yiwa yan uwa da makwabta hidima.

Malam barau ya dawo daga Saudiyya inda har sunje yi mishi sannu da dawowa, daga chanma suka wuce wurin inna kulu suka duba ya take, Anan suka haWu da zainabu tazo wanka gida, da yake ta haihu. (yarinyar malam Musa ta biyu)

Abu daya dake damun Alhassan a yanzu shine, matsa mishi da malam Barau yakeyi game da sai anyiwa hafsat aure.

A iya saninshi hafsat batada wanda take so sam, kuma a nashi bangaren baijin zai iya yiwa yarsa Waya tilo auren dole ba.

Shiyasama kwana biyu ya rage zuwa kauyen, amma malam barau saiya sa tanimu Walibinshi ya kira Alhassan din a waya yana yi mishi tuni akan maganar.

Kamar kullum dai, yauma yana zaune a office saiga kiran malam barau, a Wiririce ya dauka "Assalamu alaikum baba"

Tacan bangaren malam ya amsa da "wa'alaikumus salaam"

Bayan ?an gaishe gaishe malam barau yace "nakirane naji an turo zancen hafsatou kuwa? kasan kafin in tafi Saudiyya munyi dakai ina dawowa za'a gama komai ayi biki, to gashi kuma naga na tasamma wata biyu da dawowa amma zancen shiru"

"Eh baba matsalar ba daga gurinmu bane , domin na yiwa yaron magana to sai yace babu matsala zai turo amma akwai abinda yake so ya Wan karasa kafin ayi bikin"

"Alhassan inaga mafi a'ala kabar zancen Yaron nan, saboda naga abin nashi yanaso ya koma wasa bayan anan ga tarin masu neman aurenta sun hanani sukuni, ko zuwan nan da kuka yi bayan na dawo Saudiyya saida kusan mutum biyar suka sameni da maganar aurenta"
"Yanzu abinda za'a yi shine zan Wan kara bashi lokaci, idan ya turo to falillahil hamd idan kuma bai Turo ba to zan ba nanan garin dama duk wanda ya riga fitowa sai ayi dashi.."

"To baba babu komai insha Allah, Nagode agaida mama"
Ji yayi kanshi kamar zai fashe, wai meye abin takura!! yaga hafsat har yanzu bata cika 16 bama balle ace shekarunta sunyi yawa, gashi ya lura yanzu tana kan ganiyar son karatunta.

"Dole na nemo mafita"
abinda Alhassan yace kenan yaci gaba da aikinshi...

Yauma kamar kullum an tashi daga makaranta, tsaye take a bakin premises din makarantar tana so ta fito ta samu adaidaita,
Saboda tunda wata hudu ta cika driver ya daina musu aiki yace zai kawo musu kaninshi daga kauye, kuma har yanzu shiru be Kawo musu shi ba.

Wannan kyakykyawan matashin daya ganta kwanakine yauma rike da hannun yarinyar daya dauko....

Da sauri ya nufi inda yaga hafsat a tsaye amma yauma cikin rashin Sa'a yana zuwa gurin yaga babu ita ba alamunta sai dai adaidaita guda biyu da yaga sun wuce ta gabanshi

Tsakii yayi "mtsweews waini banida Sa'a ne? Tun ganin farko ban kuma ganin taba sai yau, yau dinma gashi ta Sace min"

Husna ce tace "Uncle menene naga ranka ya Saci?"
"Babu komai, banjin daWine amma karki damu"

"Uncle shikenan yau bazamu siyo ice cream dinba kenan?"

Cikin kosawa da surutun nata ga kuma abin dake damunsa yace "just keep quiet zan kaiki.."

Dariya tayi "yeyy thanks uncle" mota ya shiga itama ta shiga daya side din suka dau hanya.


Koda hafsat ta isa gida a falour ta tarar da ummanta, baaba indo da jikarta *Murja* datazo daga Kano , itama kusan sa'ar hafsat dince.

Gefe ta ajiye jakarta "sannunku da gida"

"Yauwa sannu da dawowa ?awalli" cewar baaba Indo

Da sauri murja ta mike tayi kitchen, dawowa tayi dauke da warmer da ruwa tana Murmushi
"Yaufa mutuminki akayi"

Cikin sauri hafsat ta mike ta amshi warmer din ta buWe, dambun shinkafa ne wanda yaji zogale da gyada ga man ?uli sai kamshi yake yi.

Murmushi tayi "umma keda baaba kuka yi koh?

Harararta umma tayi "ai sai yanzu kika ganni koh?"

"A'a wallahi a gajiya nake ne shi yasa"

Zama tayi ta fara cin dambu tana cire hijab dinta.

Koda ta gama har murja ta haWa mata ruwan wanka.


Bayan ta kimtsa ne ta fito falour sanye da ba?ar doguwar riga tayi rolling din gyalen sai mini purse data ri?e silver colour takalminta ma silver colour plat.

"Murja je ki shirya kizo ki rakani Companyn su Abba."

"To" Murja tace tayi Waki da gudu.

Bayan kamar minti biyar ta fito sanye da doguwar rigar atampa da gyale ba?i.

Dakin ummanta ta shiga "umma zamu tafi"
"To hafsat Allah ya kiyaye hanya, don Allah ki kula kinga dai yanzu babu driver, ki samu adaidaita ta kaiku har bakin Companyn in zaku dawo ma haka"

"To umma insha Allah zamu kiyaye"

"To saikun dawo, Allah ya tsare"

A tsakar gida suka tarar da baaba indo tana shan iska.

"baba mun tafi office Win Abba" hafsat tace tana murmushi

"To ?awalli Allah ya kiyaye hanya idan kinga goro ki siyomin ko gauta"

"To baba zamu siyo miki insha Allah" cewar hafsat tana gyara rolling din kanta
Ita ko murja ta ?osa a fita, domin tanason yawo sosai, gashi kuma hafsat ba gwanar yawo bace, don bata wuce sahad stores ko chicken republic sai office Win Abba idan yace tazo ta amshi sa?o.

Shi Abban yanayin haka ne ko Allah zai haWata da mijin aure a hanya duba da yadda malam barau ya dame shi da zancen aurenta.

Suna fita daga gidan suka samu adaidaita, shiga sukayi bayan ta faWa mishi inda zasu..

Cikin yan mintoci kadan suka isa companyn su Abba, dayake dama babu nisa sosai, sallamar mai adaidaitar tayi suka nufi cikin Companyn.

Kamar kullum yauma duk wanda ta gani saita gaisheshi a mutunce, masu zuba mata ido nayi, masu jin haushin kyanta suma sunayi ..

Office din Abba suka shiga da sallama.

Alhaji sulaiman suka gani zaune suna hira da Abban nata.

"A'a ?ata yauma an kawo mana ziyara kenan?"

Du?ar dakai tayi sannan ta gaisheshi, Ita dai hakanan takejin nauyin mutumin, hakanan sai ya sayi abu yaba Abba wai yakai mata, haka itama inya ganta dubu goma ko biyar ke rabasu.

Cewa yayi "Ai kuwa dai yau sai kinje gidana kingaida mamanki da husna, dama baki taba zuwaba, kuma Nasan ma baki san husnar Bama, kuma makarantar ku daya da ita, sai dai ita tana primary section ne"

Kafin tayi magana Abbanta yace "Babu komai, kawai su bika tunda kaima gidan zaka inyaso idan suka dawo sai su amshi sa?on..."

Bin bayanshi su hafsat sukayi har cikin mota..

Gidane babba na alfarma sosai, murja kuwa ta baza Ido sai kallon gidan take, koda yake dama babu gidan banza a asokoro

Fita sukayi bayan yayi parking a harabar gidan inda ya musu jagora har cikin babban parlour gidan, inda yace su zauna, shikuma ya shiga ciki don kiran hajiyar.

Da fara'arta ta fito "sannunku sannunku! hafsat yau kece a gidanmu? Ikon Allah!! rannan ma naje gidanku sannan kina makaranta baki dawoba"

Kayan ciye ciye ta kwaso musu dasu drinks ta ajiye a saman table din dake gabansu "Bismillah kuci mana"

Ita dai hafsat tun bayan data gaisheta ta dukar da kai tana wasa da yatsun hannunta "mutanen nan suna bata mamaki Sosai domin basu haWa komi dasuba amma sun dauke su kamar yan uwa,

Ita ko murja ta bude baki tanata kwasar Gara, ta kalli nan ta kalli can, dama ita batada bakunta ko kaWan

Ruwa kawai hafsat ta iya sha, domin hakanan taji duk ta kosa su bar gidan.

dagowa Hafsat tayi "Mummy ina husna?"

"Aff rabon za'a yi daga dawowarta daga makaranta ta tasa uncle dinta *Sadeeq* wai saiya Kaita park ta sha ice cream, Gashima basu dade sosai da fita ba, amma kila su dawo kunanan"

Mummyn cema take ta Jan hafsat din da hira har ta Wan saki jikinta, murja kuwa tuni ta zama yar gida sai kalle kallen ta takeyi tana hira da mummy.

Husna ce ta shigo da gudu "mummy mummy yau uncle harda ?ar baby ya siyomin "

Dariya Mummyn tayi "Lallai kam gaskiya uncle ya kyauta"

"husna zo mu gaisa" cewar hafsat tana miko mata hannu
Sai sannan husna ta waigo tana kallon hafsat cike da mamaki

"Mummy wannance antyn dana baki labari rannan ta siyan min ice cream da nawa ya fadi a makaranta"

"Don Allah! to an gode hafsat ashema kinsan kanwar taki, mun gode sosai da kulawa"

Murmushi kawai hafsat tayi, batare data ce komai ba.

Dai dai nan sadeeq ya shigo cikin faloun sanye da wani tattausan farin yadi, hannunshi daure da bakin agogon fata kirar companin Armani sai bakar Hula Dake kyalli a saman gararren ba?in gashin kanshi, tuni iskar dakin ta chanza zuwa turaren Dake jikinshi, ko inda su hafsat suke be kallaba yayi haryar stairs cikin hanzari.

Murja ko ta baza Ido da hanci tana kallonshi batare data tuna cewa ana gaisuwa ba, Hafsat cema tayi Karfin hali cewa "Ina yini?"

"Lafiya" yace a takaice ba tare daya kalli koda inda take ba

Mummyn husna bataji daWin abinda sadeeq yayiba, duk da tasanshi dama shi baya sabga da mata, yanzuma sai fama ake yi dashi yayi aure amma ya?i wai bega wadda zai iya auraba.

"Sadeeq! hafsat ce fah yarinyar manager din companynka"
Darajar sunan Manager da mummy ta kira tace yar shice shi yasa ya dago ya kalleta

HaWa ido sukayi, A tare zuciyar su ta buga damm!! kamar saukar aradu.

Da sauri hafsat ta dauke idonta daga kallonshi.
Shi kuwa Wiriricewa yayi ya kasa gaba ya kasa baya.

*Yarinyar da kullum saiyayi mafarkinta, yarinyar da tunanin ta ya hana shi sakat, yau itace a gaban shi tana gaisheshi yana Sata rai tsabar rashin sani lallai da yayi wa kanshi.*

Baya ya dawo ya zauna a kujerar dake kallon tasu hafsat, Mamaki abin yaba mummy amma sai ta basar.

"Hafsat amma makarantarku daya da husna koh?" Muryar sadeeq ce ta cika falon da tambaya

"Eh makarantar mu daya, amma ban sani ba sai yau"

"Ikon Allah, nikuma wani zubin ina ganin ki idan naje daukota"
Murmushi hafsat tayi tace "Allah sarki" domin ita tsoron shine taji ya kama ta.

Mummy ta kalla "mummy zamu tafi Abba na jiranmu zamu amshi sako a gurinshi"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login