Showing 51001 words to 54000 words out of 66006 words

Chapter 18 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

135

gaske ya rufe shi, sannan sam koda wasa beji koda Wigo Waya na haushin Sadeeq ba a ranshi, tunanin ta Yadda zai rayu babu ita yakeyi, ga dukkan jadawalinshi ya gama tsara komai ne akanta, amma saiga wu?ar ?addara ta tsinke komai tun kafin ma ya afku

_Masu tausayin Aadhil ina kuke ne_ kada fa Aadhil dinmu ya san?ame



*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*22*

*MATAR RASHEED*


_______Sai bayan kamar minti biyar Abba ya gama gaisawa da abokan nasa, tare da P.A Dinsa da Alhaji wadah suka karaso gurin motar
Sun danyi mamakin rashin ganin Aadhil a gurin, Cikin sauri P.A Win Abban ya buWe mishi gidan gaba gefen mai zaman banza Don ya shiga ya zauna Kafin Aadhil Win ya dawo daga inda yaje
Sai dai a maimakon ya matsa Abban ya shiga sai kawai ya shige cikin motar Yana rafka uban salati "Alhaji yana ciki fa, kamar ma a sume yake" cewar p.a yana janye Aadhil daga kwanciyar da yayi saman stearing

Cikin sauri Alhaji wadah ya buWe Waya gefen shima yana salati, kama Aadhil Win sukayi zuwa seat Win baya, sam baya ko motsi alamun ya daWe da suma, shi kuwa Abba yama kasa taSuka komai saboda gaba Waya zuciyarshi ta karye, gani yake a karo na biyu zai kuma rasa Aadhil bayan ko shekara Aakhil beyi da rasuwa ba

Sai Allah ya kyauta mutanen da suka Wan taru a gurin suke yi musu, tare da tambayar meya same shi,
Alhaji wadah ne kawai ya iya magana "wallahi kalau mukazo masallacin nan, shine ma ya kawo mu, sai kuma yanzu mukazo muka ganshi a haka" wani ne cikin mutanen yayi hanzarin miko Ruwan sanyi na roba da nufin a watsawa Aadhil Win kila a samu ya farfaWo Kafin su ?arasa Asibitin

Cikin Sa'a kuwa Allah ya taimaka P.A yana shafa mishi a fuska yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya, numfashinsa ya dawo Amma be buWe idanunsa ba

Shiga cikin motar sukayi duka inda P.A ya tu?a motar suka nufi asibiti Mafi kusa da masallacin, zaune Abba yake kawai, babu Abinda yake a Cikin zuciyarsa illah addu'a, tabbas yasan shi be isa ya hana Aadhil mutuwa ba muddin lokacinsa yayi, Amma yana rokon Allah akan yayi masa rangwame ga koma me zai faru
Koda suka isa Asibitin Alhaji wadah ne da P.A suka kuma fito dashi daga motar kafin aka Kawo gado likitocin suka shiga dashi, Emergency unit aka wuce dashi cikin sauri

Su kuma su Abba suka samu kujeru suka zauna a Hallway Win asibitin suna zaman jiran tsammani, kowa ya kasa cewa Wan uwansa komai in banda Alhaji wadah da yaketa tsaaki "Mutun fa sai Allah, jifa yadda muka tawo da Yaron nan gwanin sha'awa, kowa idan ya gansa zai tabbatar da cikar Lafiya a tare dashi, Amma ji cikin ?ankanin lokaci komai ya juye"

P.A ne kawai ya iya cewa "Wallahi kuwa! , Allah dai ya bashi lafiya"
Abba ko girgiza kai kawai yayi domin tsaff mutuwar Aakhil ce ta dawo mishi sabuwa, saboda shima kalau aka rabu dashi, mutuwar na zuwa kuma faf Waya ta faru ta ?are.


A kalla sun Wauki sama da minti ishirin sannan likitan ya fito yana murmushi, mimmika musu hannu yayi suka gaisa sannan daga bisani yace "Don Allah ku kwantar da hankulan ku, ba wani abu bane me girma, saboda Binciken mu ya nuna mana jininshi ne yayi ?asa tare da ruwan jikinshi, shine jiri ya kamashi ya sume kuma hakan takan faru idan mutum yagani ko kuma yaji wani abin tsoro daya firgita shi"

"To doctor Yanzu ya jikin nashi?" Abinda Abba ya iya cewa kenan ya kuma maida bakinshi ya tsuke
"Ah jiki yayi kyau Alhamdulillah, Yanzu haka ma mun sa mishi ruwa ne saboda yadan samu ?arfi a jikinshi"

Murmushi Alh wadah yakeyi tare da cewa "Masha Allah! Masha Allah, Kenan ya farfaWo yanzu?"

"Eh ya farfaWo sai sai munyi mishi allurar Barci Saboda jikinsa ya Kuma samun hutu Kuma ?wa?walwarsa ta daidaita"

"Okay to Masha Allah, mungode likita" Kuma gaggaisawa sukayi sannan likitan ya wuce Bayan yace musu zasu iya le?awa su ganshi amma ba'a son hayaniya.

Kwance yake a saman gadon Asibitin a mi?e samSal kamar gawa, tsabar tsawon Aadhil Win gadon be isheshiba saida kafafunshi suka wuce tsayin gadon

Fuskarshi ta Kuma yin fayau har Wani Wan haske ya ?ara, hannun damansa ne sanye da drip Win, Bayan sun gama duba shine Abba yace bari ya fita daga waje saboda zai kira gida Wani yazo ya zauna da Aadhil Win Saboda su samu su koma office

_*AFTER 35MINUTES*_

Cikin hanzari da kiWima duka suka shigo asibitin, hankalinsu a matu?ar tashe

Hajjah (kakar Aadhil ta Wajen uwa) da Aunty salma da zaituna kuka suke yi wiwwi

Mummy ce da baba Tsoho (kakan Aadhil na wajen uwa) sai hameed da hamdan (kannen Abban Aadhil ne) sune kawai basa kuka Amma suma idonsu yayi jajir alamun tashin hankali

Suna shiga Wakin Aunty salma tayi kan Aadhil tana cewa "don Allah Aadhil kayi mana rai kada wani abu ya sameka!, Wallahi bazamu iya jurewa ba"

Itama zaituna gabanshi ta tsaya tana Wan girgiza shi "ku rabu dashi mana" hajjah tace Cikin murya me nuna karaya


"To umma mu zamu koma office saboda Akwai ba?i da zamuyi daga Lagos, sannan likita yace kada ayi hayaniya" cewar Abban Aadhil bayan ya mi?e, suma su Alh wadah sai suka bi bayanshi, yadda kowa yake Cikin tashin hankali yasa ko tunawa da wata gaisuwa basu yi ba

Baba Tsoho ne ya dakawa zaituna da Aunty salma tsawa "ke salma da zaituna kaniyarku, kuyiwa mutane shiru, koko ce muku akayi kukan da kukeyi ne zai iya hanashi mutuwa idan lokacinsa yayi! Da wannan sharar ?wallar da kuke da buta kuka dauka kuka yi alwala kukai Sallah raka'a biyu kukayi mishi addu'a ai dayafi, shikanshi Adalin _(yana nufin Aadhil)_ ai saiya fi son hakan akan ya farka ya ganku kuna risgar kuka

"Dadai yafi" cewar hajjah tana balla musu harara, ?ara cewa tayi "sufa gani sukeyi sun fimu sonshi"

"Hajjah bari naje gurin likitan naji Abinda Ya faru dukda dai yaya (Abban Aadhil) yace ba wani Abu bane mai tsauri" cewar hamdan yanayin hanyar barin Wakin, da sauri hajjah tace "to hamdan kace idan ma Akwai wani maganin ya kara mishi ko nawa ne Ni zan biya"

Murmushi hameed yayi yana bin baya hamdan Win da nufin suje gurin Doctor Win tare, shiru Wakin yayi bayan sun fita, ita Mummy dama tunda sukazo batace komai ba illah jan charbinta da taketa yi

"Zaituna fita waje chan wajejen shagunan bakin titin nan ki amso mini martila (wai tana nufin Maltina) katan daya
Don nasan yana farkawa ita zai fara tambaya, hijabinta ta zazzage gefe da nufin ta ciro kuWin a cikin hular dake kanta, baba Tsoho ne yace "bari na bata kuWin kawai, basai kin ciro ba"

Gyata hijabin hajjah tayi tare da cewa"To Allah ya bada lada" amsar kuWin zaituna tayi ta fita daga dakin

Ba'a fi minti goma ba saiga su hamdan shida hameed sun dawo, hameed ri?e da carton Win madarar ruwa hamdan kuma da carton Win Maltina, suna shigowa zaituna ta shigo tare da mi?a wa baba Tsoho kudinshi tana cewa "gashi sunce kabarshi". Amsar kuWin baba Tsoho yayi yanata faman sa musu Albarka


Kafin yamma asibitin ya zama kamar gidan Barka, Wannan na shiga wannan na fita, koda Aadhil Win ya farka sosai Abin ya bashi mamaki, be taSa tunanin har Abin yakai haka ba!

Karfafa jikinshi yayi tareda yunkurin tashi zaune, da sauri hamdan ya ?arasa kusa dashi ya tallabe shi yana Wagoshi a hankali

Saida ya zaunar dashi da kyau sannan yace "big son ya jiki"

"Da sauki, waye duka ya tattaro ku nan?"

"Wallahi zaituna ce ta kiramu tana zunduma ihu" cewar hameed wanda karasowarshi kenan gurin

Harara Aadhil ya jefawa zaituna Wadda da tayi yunkurin zuwa gurin shi, ganin hararar daya jefeta da ita saita yiwa kanta full stop
Duka suka tashi suka ?arasa gaban Aadhil Win, kowa sai ya jiki yake mishi, Mummy ce kawai bata ?arasa ba saboda kunyar idanun iyayenta


"Babban Wa wai meye wannan Abin tsoron da ya dagula maka lissafi" hameed yace yana gyarawa Aadhil Win zaman rigar shi
Kafin Aadhil ya bashi amsa hamdan ya kuma cewa "mufa bamuji Labarin dawowarka ba sai dai ta ciwo, shiyasa bamu faWawa su iyaah (kakar Aadhil ta Wajen uba) ba Saboda kasanta da firgici saita ruWe gaba Waya

"Aiba wani ciwo bane fa, kuma dan zaituna ta taso kune" cewar Aadhil yana ?o?arin cire cannula Win dake manne a hannunshi "A'a Aadhil, pls kada ka cire mana, kabari ruwan ya kare mana, likita yace guda uku za'a sa maka kuma wannan ne na biyu" hamdan yace yana gyara zaman cannula Win saboda shima doctor ne

"Yauwa ku bashi wannan ya shanye" cewar hajjah tana mikawa hameed babban jug cike da madara da Maltina alamun guda bibbiyu ta juye

Kunshe dariya hameed yayi tare da cewa "To hajjah"

Koda Aadhil yaga uban kofin sai cewa yayi "haba hajjah, kema fa kinsan wannan ya mini yawa"

"To sha idan ka rage saina shanye ragowar" cewar hajjah tana komawa inda ta taso

Itadai Aunty salma Zaune take ta zubawa Aadhil ido, mamakin meye haka ya sashi ciwo farat Waya take, tasan Aadhil da cikakkiyar Lafiya, saiya kusa shekara beyi ciwoba

Mummy Ma tana inda take bata tashi ba illah dai yanzu fuskarta ta washe daga damuwa ta koma normal

zaituna kuwa sai satar kallon Aadhil Win take tanaso taje kusa dashi kuma tana tsoro

Ana haka likita ya dawo, kuma dubashi yayi sannan ya sanar dasu cewa sai yayi kwana biyu ko uku a asibitin saboda akwai wasu gwaje gwajen da suke so su ?arasa Yi mishi

"Doctor naji sauki fa, Don Allah kada ka zaunar dani a Asibitin nan, inada Abubuwa da yawa a gabana" cewar Aadhil yana kissifa yadda zaiyita zama guri Waya, domin shi anashi a yau yaso ya bar ?asar basai zuwa gobe ba

"Calm down mana! Lafiya fa itace komai, ka kwantar da hankalinka kamar yaune Zamu gama komai"


Shiru Aadhil yayi don yasan babu me goyar mishi baya, komawa yayi ya kwanta tare da rufe ido saboda ciwon da yaji kanshi ya fara, tunanin Hafsat ne ya fara dawo mishi, ai babu shiri ya tashi ya zauna Saboda bayaso kirjinshi ya fashe, yayi mamaki ma da akace ?asa jininshi yayi ba sama ba, domin shi a nashi ya zata ma ciwon zuciya ya kamashi

*3days later........*


A dai bayaso Win saida yayi kwana uku a asibitin, shigar su gida kenan ya samu ya kwanta a three sitters sofa din faloun yana rufe idonshi, so yake yayi tunanin me zaiyi Anan gaba Amma ya kasa, jin tunanin shi yakeyi kamar ansa gum an dakatar dashi, ganin bazai iya ba sai kawai ya fara tasbihi a cikin zuciyarsa har barci ya kwashe shi


???????????????????

*KADARAR HAFSAT TA SOMA......*

Kwana daya kenan da tafiyar Sadeeq Cairo, Hafsat na gidan mummyn husna kamar yadda ta bu?ata
Duk bayan awa biyu sai sadeeq ya kira a waya ya faWa musu Abinda likita yace, yanzu haka ma waya suke shida Aunty salma inda yake ce mata yanzu zai shiga cikin gadon computer wadda za'a yi mishi general check up, sannan ya ?ara mata da cewa: koda Aadhil yazo Nemanshi tace mishi ya tafi kuma yayita kiran lambarsa bata shiga, sallama sukayi bayan tayi mishi fatan Allah yasa ya shiga kuma ya fito A sa'a

Dai dai lokacin Hafsat ta shigo ri?e da hannun husna suna dariya, kallon Hafsat Win mummyn husna tayi tana murmushi ganin Allah ya taimaketa kaninnata baiyi gaggawa ba, yanzu zata samu lokacin da zata yi mata gyara na musamman kafin ya dawo

Tunda sukayi wannan wayar Sadeeq be kuma kira ba, gashi ita ta kirashi Amma switch off, hakanan taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi kuma tsoro ya kamata matu?a

Da sauri ta Wauki wayar jin ?arar shigowar message, ganin number Sadeeq ce hannunta har rawa yake wajen budewa

Bata gama karantawa ba wayar ta subuce a hannunta ganin Abinda sakon ya kunsa, Allah ya taimaka wayar a saman carpet ta fadi da tuni ta fashe, bata Bata lokaci ba ta zari mayafinta tayo falour inda ta umarci su Hafsat da susa hijab su biyota, driver tasa ya buWe motar suka shiga baya duka suka zauna "kaini gidanmu" Abinda mummyn husna ta iya cewa kenan hankalin ta a Matukar tashe

Koda suka isa gidan haka ta fito kamar zata tashi sama tayi cikin faloun ummanta, " Mummy! Mummy!! Fito kiga da Abinda Sadeeq zai saka mana"

Chak Mummy ta tsaya zuciyarta fall cike da tsoron Abinda zai biyo baya a lafuzan mummyn husna, koda ta karaso kusa da ita bata ce mata komaiba illah wayarta data cirewa security ta mikawa mummyn Tata


*_Assalamu alaikum Ni Sadeeq na saki matata Hafsat saki Waya bawai donta yimin komai ba sai don ganin hakan shine adalcin da zan iya yi mata, don Allah kada kowa ya zargeta domin wallahi batada laifi daidai da kwayar zarrah, sannan kuma na bata kyautar million uku a cikin kudina dake account Win gurin yar uwata mummyn husna, Please inaso ku fahimceni, Nagode Sadeeq kaninki_*


Wata iriyar zufa ce ta fara zarya a gaban goshin Mummy, wannan wace iriyar ?addara ce kuma?, me Sadeeq yake nufi? Ko yayi hauka ne?

Wannan Yar karamar yarinyar zai mayar bazawara? Kodai wani abun yasha? Abubuwan daketa kai kawo a cikin zuciyarta kenan, ta rasa ma me zata furta

"Amma gaskiya Sadeeq be kyauta mana ba, koma meye ai sai ya bari ya dawo ?asar sannan ya aiwatar, amma ya za'a yi ya turo da saki ta waya fisbilillah? Bata gama magana ba wani sakon ya kuma shigowa, cikin sauri tasa hannu ta buWe

*_Nasan zakuji zafi kuma zakuce ban daukeku a komai ba, don Allah ku yafe min, sannan inaso kuje gidan su Hafsat ku sanar dasu sannan ku maida musu da yarinyar su, sannan nima kada a nemeni zan dawo zuwa Lokacin danake ganin shine daidai_*


"Tirkashi" Abinda Mummy ta iya cewa kenan tareda mikawa mummyn husna wayar, bayan itama ta gama karantawa ne tace

"To yanzu mu yake nufin muje mu kai yarinya kuma mu sanar da iyayenta cewa ya saketa!?"

"Kiramin shi maza" cewar Mummy cikin bacin rai

Saidai kash koda tayi dialling Win number sai akace *Switch off*

Wani irin tukuki Mummy keji a ranta kamar ta Wora hannu aka tayita zunduma ihu, meke damun Sadeeq? A ina zamu kuma samun irin Hafsat? Wannan abinda ya faru daidai yake da a dauki dutse a buga mata akanta ya tarwatse.


*Yan team sadeeq ina jiran sharhi* L'L' *Team Aadhil basaina ce komai ba* d'?d'?

*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*L'
*#ALHAJI MADU*
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*23*

*MATAR RASHEED*


______Ganin yadda hankalin mummyn nasu ya tashi sosai Sai mummyn husna ta zauna a gefen gadon Tare Da kama hannun mummyn tana zaunar da ita "Mummy Kada kisa Allah yayi fushi dashi, gaskiya nakeso na faWa miki game da duk Abinda na sani na Dalilin Zuwan Sadeeq Cairo, a Gaskiya bawai yaje Cairo bane Domin Kasuwanci, yajene domin Neman lafiyar shi Saboda tun kusan wata Shida da suka wuce ya Fara zubar jini ta hancinsa, Ni kaina be taSa faWa min ba sai a Cikin watan nan *Nan Dai mummyn husna taba mummynsu labarin komai data sani da ?arin cewa ita tace Sadeeq Win Kada ya faWa mata ganin lilita zashi Saboda kada hankalinta ya tashi"*

Sosai hankalin Mummy ya Kuma tashi a maimakon ya kwanta, yanzu damuwar ta zama biyu kenan! A Da ta laifin sakin Hafsat ce, yanzu kuma gata lafiyar shi
"Bakya ganin Dalilin cutar ya saketa?"

"Zai iya zama hakan Saboda a cikin sakon nashi yace _sakinta da yayi shine adalcin da zai iya yi mata,_ kuma kinga kenan akwai matsala"

"Amma memakon koma meye ya dawo gida ya faWa sai a duba idan za'a iya samun mafita a bashi Shawara, shine ya gwammace ya yanke wannan danyen hukuncin?, Ai kodai cutar mutuwa ce ta kama shi ya kamata ya dawo ya faWa mana"

"Kiyi hakuri Mummy, in'sha Allah komai Zai gyaru! Yanzu Abinda za'ayi su kawu balarabe zaki kira shida kawu munzali saimuje tare su rakamu, gara aje gidan su Hafsat a yau Win, yadda ko sakon ma idan aka duba za'a gane yau ya turo, kinga kada ayi jinkirin sanar da iyayenta kuma wani Abu yazo ya faru daga baya"

"To ya zanyi! Amma nidai Sadeeq beyi mini adalci ba sam"

Su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login