Showing 54001 words to 57000 words out of 66006 words

Chapter 19 - IZAYAR RAYUWA HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

141

zainab ne suka shigo Wakin mummyn cike da murnar ganin Hafsat da sukayi a falour, yanayin shigarsu ta nuna alamun daga wani waje suka dawo, Amma jin Abinda Ya faru sai kawai suka fashe da kuka suna cewa "Yanzu idan mu aka yiwa haka yaya sadeeq zaiji daWi? Fisbilillah Yar karamar yarinyar nan zai mayar bazawara?"

Sosai jikin Mummy ya ?ara mutuwa tana tunanin yadda zata tunkari gidansu Hafsat da wannan Wanyar maganar, amma koma yaya ne nauyin ya rigada ya hau wuyanta tunda dai yanzu Babu mahaifinsu.

???????????????????

*Aadhil*

Babu yadda beyiba akan Mummy ta barshi ya koma Maldives amma Abu ya?i, babu wanda ya goya mishi baya, ko Abba ma cewa yayi sai Nan da kwana goma Domin su kuma ganin yanayin jikin nashi, tunda babu Irin tambayar da ba'a yi mishi ba akan meye ya bashi tsoro amma yace shi sam babu komai, kawai dai yana zaune Cikin motar yaji jiri na dibanshi

Hakanan ya hakura da tafiyar har zuwa kwana goman da Abba ya bu?ata, Sai dai shi yasan zamanshi a garin zai ri?a tada mishi da sabon ciwon dayake ?o?arin ya warke ne, Sam ko dakinsa ma baya son shiga, ko wanka ma da yayi a Wakin Abba yayi ya shirya sannan ya dawo falour, illar da yayiwa kanshi shine duk inda yakeda muhimmanci agaresa to akwai wani Abu daya shafi Hafsat a gurin, kamar zanenta ko kuma wani Abu daya siya domin ta, ?an ya jiki kuma sai zarya suke, kowa da kalar Abinda zai riko idan zai zo.

Anan ne ?awayen zaituna Yan neman hanyar shiga suma suka zage damtse sai zuwa sukeyi, wasu harda mummynsu suke tawowa don cusa kai, haka basa zuwa hannu rabbana sai sun riko wani abun.

Shidai Aadhil babu Abinda yake iya ganewa, idan yaga Abin ma ya mishi yawa saiya rufe idonshi a Matsayin yana barci.

Mummy ko ta kasa zama, daga tayi wannan sai tayi wancan, duk wani Abu datasan Aadhil Win yanaso saida ta tanadar mishi.

?????????????????


*Hajiya bilki*

Yauma dai zaune take gaban boka Wan China ita da interpreter dinshi, magana bokan yakeyi shi kuma yana fassara mata
"Kamar yadda muka Sata kwanaki muna bincike akan wannan ahalin to taurari sun tabbatar mana da babu mutuwar ta Anan kusa, Amma akwai wata hanya guda Waya tak wadda itace makwafin mutuwar Tata tunda zata rabata da mijin kamar yadda mutuwa zata rabasu"

"Kace mishi ko wace hanya ce na yarda har dai Ni zan iya shiga gidan a Matsayin mata" cewar Hajiya bilki jikinta har rawa yake

Magana Wan Chinan yayi tare da bubbuga sandar dake hannunshi a saman buzun zakin dake gabanshi, take wasu manya manyan zannuwa jajaye guda uku suka Bayyana a wajen.

Interpreter ne ya kalli Hajiya bilki sannan yace mata "yace to angama amma zaki yarda da bukatarsa ta kwanciya dake daya nema satin daya gabata"

"Na amince ko yanzu ne har dai zai mini aikin"

Juyawa interpreter yayi ya faWawa bokan Abinda tace, sannan yayi shiru yana sauraron Abinda bokan yake cewa

"Hajiya yace to tunda kin amince nanda kwana uku zamuje muyi aikin, amma yace kitabbatar duk irin kwanciyar daya bukata zakiyi mai, sannan har zuwa kwana ukun Anan zaki zauna"

"Na amince, amma ina Neman Alfarma akan ya barni inje gida gurin yarinya ta sai in dawo anjima" Cewar Hajiya bilki tana ganin kamar harta gama shiga gidan ayau

"Yace an baki" cewar interpreter yana mikewa tare da Waukar jajayen zannuwan yana ajiye wa a saman wani kututturen ice dake ajiye jikin kusurwar faloun bokan

Cikin azama ta mi?e tana ajiye damin ?an dubu dubu a gaban bokan, hannu yasa ya dakatar da ita alamun baya bu?ata.
Jiki a subule ta dauka Sannan ta mi?e Tare da fita daga falourn, Anan harabar gidan taga interpreter, shima wasu kuWin ta mi?a mishi tare da yi mishi godiya sannan ta shiga motarta ta saita ta kan titi

??????????????????

*Gidansu Hafsat.....*

Abban hafsat ne zaune a two sitters sofa, gefenshi kuma umman Hafsat ce, A three sitters kuma kawu balarabe ne da kawu munzali suma zaune da jaka a tsakiyar su, a one sitter Win dake gefe kuma mummyn sadeeq ce zaune kanta a duke, mummyn husna da baaba indo kuma suna zaune a saman carpet Win dake tsakiyar falourn

Gyaran murya kawu balarabe yayi tare da cewa "To yanzu tunda an gama gaisawa bari mu gabatar da Abinda Ya kawomu gidan nan, duk da dai ba abu bane me daWi Amma ya zama dole mu sauke Abinda aka aza mana akai, sai dai kafin mu fara cewa komai zan fara ne da baku hakuri, kuma hakuri me sunan hakuri sannan muna bukatar yafiyar ku gaba Waya"
Gaban umman Hafsat ne ya bada daram, hakanan taji zuciyarta ta karye, take tsoro ya cikata, cikin yan mintoci taji zufa na zuba daga cikin gashinta zuwa saman wuyanta, abinda yasa babu wanda zai gani shine suturta kanta da tayi a cikin hijabi

Cigaba da magana kawu balarabe yayi inda ya fayyace musu komai gameda da Abinda Ya faru, sannan ya ?ara da cewa ga kuWin da sadeeq Win yace a bata mun taho dasu

"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un! Yanzu to kun samu shi Sadeeq Win, fatan dai ba wani ciwon bane gagarumi"

Sakin baki sukayi suna kallon Abban Hafsat Win, wato shi lafiyar Sadeeq Win cema ta dameshi ba aika aikar da yayi ba

Kawu munzali ne ya gaza hakuri yace "yanzu Alhaji ba aika aikar da Yaron nan yayi bace ta dameka! Kai ta lafiyar shi ma kake?"

Murmushin manya Abban Hafsat yayi tare da cewa "Iya zaman da nayi da Sadeeq nasan kyawawan dabi'un shi, kuma nasan Sadeeq bazai taSa sakin yarinyar dashi yace yanaso da kanshi ba tare da wata cikakkiyar hujja ko dalili ba"

Cigaba yayi da cewa "Yanzu dai kokari zakuyi ku samu ku shawo kanshi ya dawo, kunga idanma akwai Wani Abu da za'a yi sai ayi a lokacin"

Kowa mamaki ne ya cika shi na karamcin Abban Hafsat, ace mutum ya sakar maka Ya ba tare da wata cikakkiyar hujja ko dalili ba sannan ka tsaya kana nuna damuwa da kulawarka akanshi!

Ta Sangaren umman Hafsat kuma Hamdala takeyi da Allah ya taimaketa wata mu'amalar auratayyah bata shiga tsakaninsu ba, ta fahimci hakan ne sanda mummyn husna tace batada iddah.

*KU BIYONI A SANNU*

*#SAGIR*L'
*#SADEEQ*L'
*#ALHAJI MADU*'
*#GARBA SHOLI*
*#AADHIL (The true lover)*


```Pls share and comment``` =?O?
*IZAYAR RAYUWA*

*24*

*MATAR RASHEED*


________Jiki a sanyaye su kawu munzali suka tashi domin tafiya, Anan nefa Abban Hafsat ya kafe akan sai sun tafi da kudinsu, sosai suma suka dage da cewa saifa an amshi kuWi, tunda yaro da kanshi yace yaba yarinya.
Ganin bafa zasu hakura ba yasa Abban Hafsat Win ya amsa tare da rakasu bakin gate, duk wannan Abinda ake yi Hafsat tana dakinta ita da murja, sam Basu san Abinda ke faruwa ba sai ma hirar su da sukeyi

Baaba indo ce ta shigo Wakin a sanyaye "?awalli kije Abban ki yana kira"
"To" Hafsat tace tare da mikewa cikin hanzari ba tare data lura da yanayin baaba indo Win ba

Koda ta fita falourn ummanta ta gani zaune, sai Abbanta, babu su Mummy da mummyn husna da sauran ba?in da suka zo tare "Abba sun barni na kwana ne?"

"Noor sun barki har Abada! Inaso ki nutsu kuma ki saurari Abinda zan faWa miki da kyau, kome kikaga ya samu bawa to haka Allah ya ?addara mishi tun kafin ya halicce shi, don haka dole komai ya sameka ka amsheshi hannu biyu" sannan ne yayi mata bayanin Abinda Ya faru gaba Waya

"Abba to bayan zubar jinin wane ciwo ne ya kamashi?, Tabbas ninasan Uncle bayada Lafiya, saboda tun bayan biki kullum yana cikin damuwa, kuma idan na tambaye shi sai yace babu komai"
Sosai umman Hafsat taji zuciyarta tayi sanyi ganin Hafsat Win bata tada hankalin ta ba, shima wajen Abban Hafsat Win hakane Domin duka sunsha idan ta tubure sai Allah duba da Abinda ta ri?a yi Lokacin mutuwar sageer

"Babu komai Abba, in'sha Allah babu wata matsala Uncle mutumin kirki ne! Allah ya bashi lafiya"

"Ameen" sukace a tare, sannan umman Hafsat Win ta kuma cewa "kije ciki ki samu kiyi wanka, gobe Insha Allah za'a je a kwaso miki kayan ki na sawa duk da akwai wasu Anan ma sosai"

"To umma" cewar Hafsat tare da tashi tana yin hanyar Wakin ta
Kuka ta tarar da murja nayi wiwi "yanzu Abinda Uncle yayi ya kyauta kenan, da Abinda zai saka mana kenan! Koma meye ai saiya Bari ya dawo"

Dafa ta hafsat tayi "murja dena kuka, Abinda yayi shine adalci, daga yau karki ?ara ganin laifinsa domin nima bana gani" baki sake murja tabi hafsat da kallo
Jinjina kai Hafsat tayi tare da samun guri a gefen gadon ta tana zauna wa "baaba bazan boye miki ba, tunda akayi Auren nan nidai dai-dai da rana Waya ban taSa jin cewa ni matar Aure bace a cikin zuciyata, sam banason Auren, sai daga baya nagane ba son Uncle nakeyi ba kawai halayenshi masu kyau ne suke burgeni har yasa naji kamar sonshi nakeyi, don haka kuwa kinga mutum me kyawawan halaye irin Uncle be kamata ya zauna da wadda bata sonshi ba a Matsayin matarsa Wadda zata haifa mishi yara ba" a zancen Hafsat kawai baaba indo ta gane yarinta na damunta dukda itama taji sanda mummyn husna tace Hafsat Win batada iddah, to amma aiba kowa bane yasan da hakan.

Lau Hafsat ta saki jikinta tanata sabgoginta sai can da yamma ne mutumin garden ya fado mata arai aiko bata ?ara Sata lokaci ba tayi dakin ummanta, a zaune ta tarar da ita a saman dadduma ri?e da Qur'an a hannunta tana karantawa, zama tayi a gefe har saida ta ?arasa ayar data Wauka sannan ta kalli Hafsat

"Noor ya akayi?" Murmushi Hafsat Win tayi
"Ummah rannan ne a cikin garden Win gidan su mummyn husna naga wani mutumi sak Abba, amma shi ba babba bane kamar Abba"

"Kamarwa yake? Kuma sosai yayi kama dashi? Sannan a ina yake?" Duka a tare umman ta jefeta da waWan nan tambayoyin

"Kamar dai Uncle Sadeeq yake sai dai yafishi girma da tsawo, kuma Wallahi kamarshi Waya da Abba sosai domin har Muryar su iri Waya"

Jinjina kai umman ta kuma yi tare da cewa "baki faWa min a inda yake ba"
"Gaskiya umma bansan a inda yake ba, iya garden Win na ganshi daga nan ban kuma ganinshi ba kuma ni ko sunanshi ban sani ba, dama Abinda yasa nace zan tambaye ki shine wai dama dagaske ne kowa yanada me kama da shi guda bakwai?"

"Noor nidai bansan sahihancin wannan maganar ba, nima tun ina karama nake jin ana yinta, amma nidai ban taSa ganiba idan ba Yan biyu aka haifa masu kama Waya ba"

"To Ummah yanzu a ina zan kuma ganin mutumin?"
Shiru umman Hafsat Win tayi domin ta Fara tunanin wani Abu daban "kada fa ace aljani hafsat Win ta gani, to ko shine ma ya aureta shiyasa ya kashe auren?, Tsoro ne taji ya Wan shigeta"

Kallon Hafsat Win tayi tare da cewa "gurin wa yazo a gidansu husnar?"
"Nidai ban sani ba! Kawai dai ganinshi nayi a cikin garden Win" tass dai Hafsat Win ta faWa mata Abinda Ya faru tsakaninta da Aadhil Win ba tare data boye komai ba
"Noor meyasa kika faWa mishi sunanki bayan baki sanshi ba?"

"Umma nidai haka kawai!" Hafsat tace tana kumbura baki
"Kin kyauta wa rayuwarki! Kinga idan aljani ne ma dakanki kin bashi lasisin shiga jikinki"

Shiru hafsat Win tayi ba tare data kuma cewa komai ba, tunani ta fara akan kilamfa aljanin ne, tunda itadai bataga wanda sukayi magana tare dashi ba.

Bayan Abban Hafsat ya dawo daga office ya ci abinci ya huta ne yace "ya kamata a kira baba (Malam barau) a faWa mishi"
Koda ya kira sai yaci Sa'a suna tare da kawu Shehu, a nutse Abban Hafsat yayi musu bayanin Abinda ya faru
Ai ba tare daya rufe bakinshi ba kawu Shehu ya fara surfa Ruwan bala'i da masifa "Lallai wannan yaron ya raina mu, Abinda zai saka mana dashi kenan? To aikuwa inanan zuwa Abuja'n kuma saina maka shi a kotu, kallon Malam barau yayi tare da cewa "ai baba harda kai, daga zuwanmu babu wani dogon bincike ka Wauki yarinya ka bashi sai kace wadda aka gaji da ita, to Yanzu ai ga irinta nan, fisbilillah yanzu wa gari ya waya?"

Duk wannan bakin na malam barau neman shi yayi ya rasa, gaba Waya abin yazo mishi a bazata, domin ko a mafarki be taSa hasashen haka daga yaronba a yadda ya ganshi, dama suna rumfa ne a zaune, babu shiri kawu Shehu ya tashi ya shiga cikin gidan tare da sanar da baaba mairo da Aunty Rafi'a

Suma sosai hankalinsu ya tashi, barinma Aunty Rafi'a, sosai Abin ya daketa, ita kuwa baaba mairo kuka ta ri?a yi wiwi wai sadi?u ya cucesu ya watsa musu ?asa a ido, haka dai suka kwana kamar gidan makoki

??????????????

*Aadhil.......*

Yau kwana uku Kenan da dawowarsa daga asibiti, sosai yaji kw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arin jikinshi domin Mummy bata wasa saita tasashi yaci abinci yasha magani, sai dai ta Waya Sangaren zuciyarshi Hafsat ce A makale, ya rasa yadda zaiyi ya yakice ta

"Yaya Aadhil Mummy tace nace maka wai anjima ka shirya Uncle hameed Zai zo ya rakaka asibiti a kuma duba jikin naka" cewar zaituna Cikin Wari Wari, domin kwana biyu faWa suke yi ita da Aadhil Win saboda gayyar Yan matan da take jibgo mishi

"To" kawai yace mata ba tare daya motsa koda yatsan shi ba,

Yafi minti goma a gurin sannan ya tashi ya shiga ciki, a kasalance yayi wankan ya shirya cikin shiny Black Cashmere, sosai yadin ya amshi farar fatarshi, be tsaya saka hula ba ya taje gashin shi kawai bayan ya shafa musu mayuka kala kala,
Ba?in Palms ya zira sannan yayo falourn yana zira cuff links dinshi yana sauka daga stairs a hankali, tun kafin ya gama sauka yaji muryar Uncle hameed Win suna gaisawa da Mummy alamun zuwanshi kenan

Da murmushi hameed ya tare shi yana tsokanar shi, "big son ciwon nan ma sai naga kamar kyau ya ?ara maka, kaga yadda kayi wani fresh ne kamar Ango!"
Harara Aadhil ya watsa mishi tare da cewa "Na kusa mutuwa kana cemini wai nayi kyau"

Ita dai Mummy binsu tayi da ido, tana ayyana ranar da zataga Aadhil Win a Matsayin ango Irin farincikin da zata tsinci kanta a ciki

Fita sukayi zuwa parking lot, inda hameed Win ne zai tu?a motar saboda Abban Aadhil Win ya faWa mishi kada ya bar Aadhil Win ya tu?a tunda har yanzu jikin nashi da saura

BuWe musu gate me Gadi yayi suka mi?i hanya,

A hankali yake tukin suna hira kaWan kaWan, inda sosai Aadhil Win ya ware kamar ba shine mara lafiyar ba


????????????????


Umman Hafsat ce zaune a falour, alamun shigarta ta nuna fita zatayi saboda harda Yar madaidaiciyar jaka a hannunta, kuma sanye take da yalwataccen hijab a jikinta

"Noor wai bazaki fito bane? Lokaci fa yana ?urewa, ko so kike mu rasa ganin likitan?"

Da gudu Hafsat ta fito tana yin rolling Win galen ba?ar abayar dake sanye a jikinta, "Ummah kiyi hakuri, wallahi murja ce ta tasani wai saita Yi min kwalliya, da kyar ta yarda nasa powder da kwalli da wetlips, da wai so take na zauna ta maidani kamar aljana
Murmushi kawai umman tayi ganin Hafsat Win tayi tsaff da ita, "to muje" cewar umman tana kallon takalmin kafar Hafsat Win da yaketa walwali, irin me stones Win nan ne gasu farare

Koda suka fita drivern da Abban Hafsat Win ya turo musu yana zaune yana jiransu, saboda dashi Abban ne zai kaisu to sai aka kirasu taron gaggawa a office,

Bayan sun shiga motar sun gaisa ne, drivern ya tada motar a hankali ya miki titi, ana tafe Hafsat tana ta yiwa umman hira, sai dai hafsat Win ta lura kamar umman bata jin dadin jikinta sosai, saboda sai yatsina fuska takeyi
"Ummah jikin ne?" Cewar hafsat Cikin nuna kulawa

"Amai nakeji, kuma kinga banci komai ba" cewar umman Hafsat Win tana kara yatsina fuska

"Ayyah sannu Ummah, ai naga ma mun kusa ?arasawa asibitin" cewar hafsat tana rungumo umman jikinta


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login