Showing 21001 words to 24000 words out of 84782 words

Chapter 8 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10749

ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake.
"Kin gayawa Malam ne?"
Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake kiransa, saboda haka ya girgiza kanta tace.
"Na san dai zai zo anjima."
"Kice yau Malam zai danWani ba?in cikin latecomer kenan."
Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya sannan yayi hanyar fita yana faWin.
"Idan wannan ?walamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ?alata nan na samo mata."
Bayan ta gama wake-wanken ta koma Wakinsu har a lokacin ?an islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ?asan kayanta ta sake Wauko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma'anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta.
Ma'aruf B.
Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sanshi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau Waya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta taSa ganinsa a rayuwarta kuma bata ?ara ba daga sannan.
Ranar Waurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassafe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ?anuwansa bayan Waurin auren, ita da Amman suna rakuSe daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ?an bikin mata da suka yanyame shi da tsokanar 'ango kasha ?amshi...' sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ?yalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala.
A wannan lokacin gani take kamar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara'a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ?ara lura dasu a gidan, sai wata mace guda Waya da tace Amma ta ara mata hijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta Webo tarin ?a?an da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen Wakunan masu aiki, inda anan ne suka Wan sake har Amma ma taga wata ?ar ajinsu ta sakandire a ?a?an dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan.
Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai iya kwatanta shi a duniyar nan.
Tsaya ma tukunna... Ina matar tasa take??
*****
"Baffa ya gaya maka komai ko?"
Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma'aruf Win dake zaune a gabanta, a cikin falon Sangarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen dining tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna 'Code Black'.
Sai da ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta.
"Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami."
Tayi murmushi tana kallonsa daWi na cika kowanne lungu da sa?o na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da al?ur'ani ko ya'yan da suka fito daga cikinta basa ?arasawa inda Ma'aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar Waya ce kawai... duk wani ado da zai ?awata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za'a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne.
"Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ?arshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A'a ba, shi yasa sai na bada tawa gudunmawar ta hanyar zaSo maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ru?ayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake bu?ata."
Wani murmushi yayi kaWan sannan yace.
"Na dade ina gaya miki kulawarki kaWai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess Wina a duniyar nan kuma."
Maganganun suka taSo wani abu a can ?asan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ?ar?ashin tafin ?afarta musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai? zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ?aramar ?walla a idanunta sannan tace.
"Yanzu dai ka san baza'a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za'a kai musu lefe dole sannan idan kana so ma zaka iya zuwa ka ganta."
Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata.
"Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a haWa dashi ba?"
"Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma'aruf, kaine damuwar mu a yanzu ba shi ba."
Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta.
"Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa."
Murmushin da ya sake yi ya sata jin wani Waci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma'aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ?aunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ?aramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba.
"Akwati nawa kake so a haWawa yarinyar?"
Kamar bai damu ba, hankalinsa kwance yace.
"Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan."
Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi tana janyo ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta mi?e tsaye tana karkaWe raunin daya baibayeta tun bayan data Wora idanunta akan Ma'aruf Win.
"Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?"
Wata ?ar ?aramar jakar daya shigo da ita a gefensa ya Wauko ya mi?a mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma'aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buWe jakar tana nazarin kayan ciki.
A lokacin Samirah ta shigo Wauke da lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta daWe da karSar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayyenta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a Sangaren Hajiya Maimuna akayi ba?i Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ?arya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan.
"Dan Allah Yaya ka bani kwangilar sati Waya in cicciko maka da waWannan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba."
Ta faWa tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma'aruf ya Wago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike ri?e da jakar magungunan tayi hanyar Waki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace.
"Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ?arfi nake nema nima yanzu."
Ta kuwa ?yal?yale da dariya daidai lokacin da Shukra (?anwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma'aruf Win yasa tayi murmushin dake ?arawa fuskarta kyau tana fadin 'Alhmdlilah" sannan ta juya da sauri don Webo takardun research Win da ta tara zai duba mata.
Don haka Ma'aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maimuna ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair Winta tana karatun azkar Win yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video Win wani tutorial daga labtop Win Munaya da suka aro.
Ya dur?usa har kasa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya taSa kallonta da wani abu.
"Yaya jikin naka?"? Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa.
"Lafiya ?alau Hajiya, naji sauki ai."
"Allah ya ?ara sauki. Kaje wajen Inna ne?"
Ya girgiza kansa.
"Yanzu zan shiga idan na fita."
Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ?asa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ?irar jikinsa mai tsari, wani abu dake Waya daga cikin abinda ke ?ara masa kwarjini a idon mutane.
A lokacin ne kuna maganar ?ar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta.
'Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma'aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba...'
Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana? haWiye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ?wa?walwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke taauresa jiya da daddare, sai dai har ta buWe baki zata yi masa magana kawai taga ya mi?e tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake Wago wani abu a zuciyarta da ta daWe tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ?ofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba.
A falon Inna Danejo Ma'aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kwana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ?afafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ?ullin kayanta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu.
Tarin messages Win da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen Winsa, sai ya zura hannunsa Waya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko Wayar.
A ciki ya lalubo nambar Faruk, aboki Wayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki.
"Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma'aruf."
Faruk din ya faWi hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office Win ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya taSa sabawa dashi don haka ba shiri ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa.
"Account number Daniel zaka turo min."
"Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi."
Ya cije leSSensa a hankali yana hango fuskar Daniel Win a idanunsa, sanda ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ?arewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau Waya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ruWani har ya fita daga hayyacinsa.
Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya fito dashi har waje Wimbin jama'ar Office Win na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot Win motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma...
Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya dur?ushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel Win har gabansa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba...
"Just send it Umar..." (Kawai ka turo min...)
Ya faWa yana katse tunaninsa kuma bai ?arasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnensa daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ?o?arin ture abinda ke ?o?arin tasowa daga ?asan zuciyarsa.
Ya cillar da ita gefen Wayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danejo ta idar daga sallarta.
"Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la'asar?"
Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ?al! da farin cikin ganinsa lafiya ?alau, don a cikin addu'inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata a cikin addointa banda fatan nema masa sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?uki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace.
"Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku."
Murmushi yayi a hankali sannan ya buWe idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe.
"Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ?amshinta."
Maimakon ta bashi amsa sai tace.
"Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana ratsa ka Muhammadu?"
Ba shiri murmushinsa ya karu.
"Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna... Ki tashi ki Wauko min furar dan Allah."
Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana faWin idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai daWi, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan.
A haka har Ishaq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma'aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya gaya mata ba, sai faWan kuma ya koma kan Ishaq shi kaWai, tana yi tana zayyano masa jikokin ?anuwanta na ?auye, kowacce ta faWo Ishaq sai ya gyada kai yace "Kuma da alamun tana da hankali."
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko kaWan babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne? auren ba zai yiwu ba.
A hankali ya sake rufe idanunsa yana tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ?arshen lissafinsa, amma a yanzu... yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ?wace masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi kaWai ne abu guda a duniyar nan da baya taSa haWawa da kowa, Wakin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai buWe shi ba don haka a yadda ya tafi ya barshi yake hango shi... Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel.
"... Kaga Rabi ma ?ar wajen BaWWejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau..."
Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka a ?irjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya buWe idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cikinsa, shekaru goma cikin wannan Wakin.
Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na Wakin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci guda Ishaq Win ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya.
"Ga Halima ma ?ar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau..."
Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace.
"Akwai abubuwa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan... Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina..."
Kuma a lokaci guda ?wa?walwar Ma'aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen...
Abubuwan da nake son daidaitawa a cikin gidan nan... Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan...
Tabbas! Ya akayi bai taSa tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ?wa?walwarsa bata taSa hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake Sullewa ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunkuWo da ?arfi.
"B, Yaushe zaka fita?"
Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye.
"Yanzu." Ya bashi amsa idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi kaWai yake hangowa.
Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ?okarin tsaida dashi amma bai tsaya Win ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo.
A harabar gidan ya gano

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login