Showing 27001 words to 30000 words out of 84782 words

Chapter 10 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10751

ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu."
Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin WiSan ruwa a buta suka yi soro.
"Amina dama wanda zaki aura da kika ce min Wanuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?"
Sai da gaban Amina ya faWi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron.
"Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?"
"Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ?anwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ?an gidan kuma da gaske bashi da hankali."
Sai ta girgiza kanta.
"Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaWaya."
Fatima ta girgiza kanta.
"Amina baki san me tace min bane..."
Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faWin.
"Mutane sun iya yaWa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..."
"Yana da wa sunansa Jamal?"
Fatiman ta katse ta, ba shiri ta Wago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ?ani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.
'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa Waya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...'
"Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.
"Me ta faWa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ?asusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba.
"Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal Win shekaru goma da suka wuce!"
****
"Kar ki Sata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ?wa?walwar da ake cewa ko shaiWan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?"
Muryar Hajiya Kilishi ta faWa cikin shirun Wakin yayin da wayarta ke kare a kunne. ?awarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.
"Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuWin da na zuba na neman tafiya a banza."
Wani murmushi ya suSuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani Sari na sirrin mafi yawan nasarorinta.
"Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata Worewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai Wore ba, har wani ?ato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?
Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana Waya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa Waya nake? juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ?anuwana da muke ciki Waya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buWe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?"
Tambaya ce, amma? Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya Saci amma har a cikin Sacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace.
"Yanzu a ina kuka tsaya?"
"Yace ita zai mayar can Egypt Win Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da ?a?a."
Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan.
"Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya Saci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaSin da yayi daidai ne, ya duba Wawainiyar yaranki ya taimake ki.
Sannan ki faWaWa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaSa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata Wawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu Wora."
"Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?"? Muryar Saratun ta tambaya Wauke da rauni da kuma wani irin tu?u?in dake cin ranta.
Sai ta sake wani guntun murmushin tana mi?ewa tsaye kafin tace.
"Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai Wore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki."
Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin Wacin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ?ancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa.
Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya Wauka ba. ?awayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buWewa cikinta su ga ainihin kalolin da take Wauke dashi bayan farar fatar ta.
Matsalar guda Waya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi ya?i da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma?sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa?yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuWin da suka fi ?arfin kayan nata.
Ta ja tsaki a hankali tana nufar ?ofar wardrobe Win ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata ba?ar ledar magani da kuma mu?ullin Sangaren? sannan ta nufi ?ofar Wakin ta buWe, ta buWe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ?aratowar bikin.
Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga Sangaren ?anuwan su Baffan na can ?auye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi.
Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuWi suka biya a dun?ule wa mutane daban-daban da zasu Wauki nauyin hakan.
Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ?anuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su Win da suka zo, ba abinda suke ma illa ?ara aikin, don in banda ci su da ?a?ansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta Waya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ?anuwanta take gani.
Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje.
Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta.
"Hajiya sannu da fitowa."
Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada.
"Yawwa, waWannan kayan fa? Ina za'a kai su?"
"Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin Win da za'a fara ne."
"Cincin kuma? Ina ita Samiran take?"
Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ?ar ?anwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari? da ya kusan kai kwata.
"Cincin Win me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?"
Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa Waukar buhun.
"Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya."
Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ?addararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course Win da take son yi a University shima Sangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.)
"Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je."
Ta faWa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ?warya ta fashe!
Sahla ta fito daga Wakinta a lokacin ri?e da labtop Win Munaya tana sake gyara gilasan idonta.
"Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ?are kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop Win wallahi ba zata sake siya mana ba."
"Kije Waki, na ajiye wasu canji akan mirror ku Wauka."
Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara Wayan nan.
Ta fita daga Sangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk Waukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma Sangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ?afa ne wanda Innan tace tana jin daWinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata.
Kuma bayan sun yi ?ar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa Sangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen Sangaren tana waya, sai gyara glasses Winta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaWai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ?o?arin da take dashi a Sangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) Win gidan.
Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ?asa, amma har yanzu ya?i barin zukata su huta, don ?aryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na? yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ?asa, don ta daWe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.
Ta zira mu?ullin hannunta ta buWe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama Sangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne Wazu? Babu abinda ?wa?walwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke Saci idan ta Waga labulen Wakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga Sangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaWai, me ya faru yanzu?
Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo ri?e da katon tray Win dake sha?e da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa.
Ta ajiye su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya.
"Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki daWe a waje."
"To Mami." Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta.
"Da gaske nake miki magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan."
Kuma duk da ta amsa Win sai da taga yadda ranta ya Wan Saci kafin ta fita. Dole ne ma ta ?ara dagewa wajen kokarin fara Sanbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ?arewa, wannan rayuwar ba dahir Winsu bace.
Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????lliyarta kafin wani abu ma na Wakin.
Sai dai kafin ta ?arasa Win wayar hannunta tayi ?ara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta faWa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ?irjinta? sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faWi kasa ta tarwatse!
***
Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen Wakin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana ?ara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba.
"J dan Allah mana.."
Muryarta ta fito a can kasan numfashinta.
Jawad Win dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ?al da kuma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita.
"Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?"
Bata bude idanunta ba tace.
"And what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?)
"Eight tana dab da ?arasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki."
Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa.
"Sai yaushe zaka dawo?"
"Sai nayi kwanakin da kika yi Paris."
Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ?ara shiga cikin gashinta.
"Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne."
Ya gyada kansa a hankali.
"Na sani Barbie, na san ni zan haukace..."
Sai kuma yayi shiru yana kallon kyawawan idanunta yayin da itama tayi shirun tana sauraren yadda sautin numfashinsa ke fitowa akan fuskarta.
"You never know what I went through da bakya nan Rukayya, zan iya tsayawa a gaban ko waye in faWa miki ke daban ce."
Ta lumshe idanuwan nata tana murmushi, tana da tarin hujjojin da zata yarda cewar dukkan maganganun Jawad akanta gaskiya ne, yana ?aunarta ne da gaske, sai dai maganganun basa taba ?arasawa har cikin zuciyarta don bata so ya tsallake huruminsa, tafi so ya tsaya a iya matsayin da tsananin kulawarsa gare ta da kuma matsayinsa na Wan gidan minister da mahaifiyarta ke kwaWayi yasa ta bashi kawai. Amma akwai wajajen da duk yadda ta kai ga jin sa a zuciyarsa bai isa ya tsallaka ba, Ma'aruf ne kadai mai wannan ikon akanta.
Ta tuna da text Win da ta tura masa a jiya ta nambar da aka tabbatar mata tasa ce, wani text layi guda kawai da ta tattara dukkan fatanta a cikinsa tana fatan ya zama silar niyya da kuma ?udirin da ta gama tsarawa a cikin kanta har ma tayi masa ado da ?arin wasu kyawawan abubuwan da zuciyar tata ke so.
'M'aruf, Hameeda ta tambaye ka...'
Kuma sai bayan da ta tura ne sannan bangaren ?wa?walwar tata mai hankali ya shiga jero mata kuskure tare da wautar ta, yana gaya mata kamar ba haka ne daidai ba, yana hasko mata tarin yarjejeniyar data yarda da ita a cikin doguwar takardar nan, lokacin da ta yarda tasa hannu akan komai yayin da zuciyarta ke cike da Wokin rayuwa mai kyau a gaba kamar yadda mahaifiyarta tace, yana gaya mata cewa saboda ta sami saSanin tunaninta hakan baya nufin cewa ta shirya fuskantar duk waWannan sharaWan?
"Jibi zan dawo, ki gaya min zan ?ara samunki dan Allah."
Muryar Jawad ta jawo ta daga tunanin yayin da yake ?o?arin ?ara matsowa. Sai kawai tayi murmushi sannan a lokaci guda ta shammace shi, ta ture shi ta mi?e tsaye tana dariya, yayi ?o?arin kamo ta amma ta kauce saboda haka shi ya faWa kan gadon inda ta taso.
"Zo."
Ya faWa daga kwancen yana kallonta, ta matse kafaWarta Waya.
"Zanje in shirya ne kar kayi missing flight dinka."
"Wani abu zan gaya miki."
Ta ?ara matse kafaWarta.
"Ka barshi sai na fito."
Da haka ta shige banWakin tana murmushi yayin da Jawad ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu yana jin wani abu kamar taraddadi akan abinda ke shirin faruwa.
Allah ya sani da gaske yana sonta, irin son da bai san adadinsa ba kuma bai san lokacin da ya shige shi ba, abinda ya sani kawai shine a matan da yayi mu'amala dasu a rayuwarsa Rukayya daban ce, komai nata daban ne ta yadda tun daga lokacin da ya santa, sanda suka haWu a airport zuciyarsa ke bin ta kamar ra?umi da akala. Shi yasa a yanzu da iyayensa ke damunsa da maganar aure ya ture duk wani kokwanton zuciyarsa ya tsayar da abu guda, don ya tabbata idan yayi saSanin hakan zai zama kamar an bar baya ba zani ne.
Saboda haka a lokacin da ta fito take tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sai ya ture komai ya jawo ?warin gwiwarsa ya isa kusa da ita ya tsaya daga bayanta. Ta ?ifta masa idonta Waya tana murmushi ta cikin mudubin kafin ya kira sunanta.
"Ru?ayya.."
Sai ta juyo ta kalle shi amma yasa hannayensa ya komar da ita gabaWaya, tana kallonsa ta cikin mudubin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login