Showing 72001 words to 75000 words out of 84782 words

Chapter 25 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10757

share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon.
"Kin shirya a haka?"
Ya ?ara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace.
"Eh na shirya."
Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karSe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ?asan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta ri?e da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba'a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani.
Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace.
"Shi wannan ba'a rufe shi?"
Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ?afafunta amma ta haWiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace.
"Bana son wani yaga gashinki."
Bata Wago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita.
A hankali ta juya ta koma Waki, wani pink dankwali ta Wauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ?ara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake Waukan ?ar ?aramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches Win ko'ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito.
Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ?ofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth Win motarsa.
"Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu." Muryarsa ta faWa dab da bayanta.
Zuciyarta ta buga a ?irjinta, hannayenta suka fara rawa ri?e da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaWai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya Wauki waya yana cewa.
"Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ?aunar Allah ka tabbata kana nan..."
Sai kawai tayi ?arfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu.
Ta haWiye wani abu a ma?ogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buWe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a Waya ledar kuna wani ?aton food flask ne shi kadai mai faWi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buWe shi, kuma tun kafin ta gani ?amshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki.
Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan.
"Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na mi?o maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al'amarin da yafi ?arfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah."
Wani lokacin bawa yana yin addu'a ne akan gaSa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu'a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa.
Kuma rashin sani yana Waya daga cikin raunin Wan Adam!
***
Waye yake cikin wannan rashin sanin ne?
A cikin dukkan wannan hargitsin, me yake jiran mu a jigawa ne?=? ?
Wace mafita Amina zata samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda?
A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!=?0?
Ku shiryawa abinda ke faruwa daga Sangaren Ru?ayya.
Har da Jawad ma.=??
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA HUDU.
~~~~~~
I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul.
- Unknown.
***
Ru?ayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.
" ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..."
Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan Win kafin kai tsaye ta katse ta.
"Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?"
"Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?"
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan Win wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.
"?yale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf."
Ta fada ba tare da ta Wauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ?araso ta zauna a gefenta.
Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daWe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan Win ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ?arasa ta zauna ba tare da kallonta ba.
Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.
"Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faWa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki ?arki ki taho gida da ita.
Kwana Waya kawai a tsakani, zaki haWa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ?ullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haWu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.
Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ?ullin nan, wanda da anyi hakan Ru?ayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya."
Ta ?arashe zancen da wani faffaWan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.
"Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakar?arin mu ya huta haka kije can ki ?arata."
"Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saSani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai."
Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ru?ayya ta juya ga wayarta da ta shiga ?ara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya.
Ta mike a hankali ri?e da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurSar shayin kafin ta Wauki wayar ta kara ta a kunnenta.
"Barbie yau kika ce, 5pm."
Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi.
A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace.
"Ban manta ba J."
Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace.
"Then where did you decide?" (Ina kika zaba?)
Ta sake cije lebbenta na ?asa
"Where we first met." (Wajen da muka fara haWuwa.)
Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata Sangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haWuwar anan ya kamata ta kawo ?arshen ala?arsu gabaWaya, ko ya?i, ko ya so.
Kuma ?arfe biyar da ?an mintunan tayi mata a kofar Joint Win 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani Winkin mai kyau daga kasa kuma tayi buWewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ?an kaWan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ?amshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta.
Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haWuwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska.
Kafafunta suka ?arasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ?ara tuna mata da kammaninsa.
"Kina da cika al?awari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki."
Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna.
"Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingiWen da yake.
Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece Win hannunta sannan ta kalle shi sosai.
"Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana."
Ya gyada kansa yana kallonta.
"Zanyi duk abinda kika ce Barbie."
Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana.
"Jawad abubuwa sun cakuWe a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke ala?a ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe.
Kuma nayi ?o?arin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki."
Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba.
"Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haWu da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai.
Yadda kayi treating Wina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban Wauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taSa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad.
Zuciyata ta mutum Waya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad.
Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaWaya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuWi, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu ?anmata guda dubu da kallo Waya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka."
Ta ?arashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ?arshe Win sannan ya ?ifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito.
"Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?)
Ta haWiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.
"Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni."
Sai ya gyada kansa haWe da rufe idanunsa ya buWe kafin yace.
"Thank you." ( Nagode.)
Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai Win, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye.
"Nagode nima, sai wani lokacin."
Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaWawa da tafiyar da take yi yayin da ?wa?walwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro.
"Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka al?awari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!"
Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leSSen nasa lokacin da Ru?ayya tayi kwana ta fita daga wajen tana Sacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaWan kuwa ya Waga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zu?o haya?inta ya busa a iska sannan yace.
"Tayi biyu babu Haro, let the plan start!"
***
Jigawa,
11:05 Am.
"Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?"
Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ?o?arin zuba sukari a kofin tea Win data take hada masa.
Abinda ya faWa yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace.
"Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaWai ma zata iya kashe bakin ka."
"Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata ?ar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan."
Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska.
"Aminu wannan fa ba zancen wasa bane."
Ya Waga duka hannayensa sama.
"To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?"
Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta.
Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya Wauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ?an mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ?asa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman.
Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ?asa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiWar Aminun lokacin da zai fita.
"Guess what?" (Kin san me?)
Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su Wauko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuWi tsaya bata ko tuna da ita ba ta buWe kofar motar ta fita.
Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko.
"Naga yadda zaki koma idan kin ?ara girma."
Hakan yasa tayi saurin Wagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji ri?e da wayoyinsa, kuma a take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login