Showing 66001 words to 69000 words out of 84782 words

Chapter 23 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10773

sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.
"Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai."
Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.
"Ina ziki je kuma?"
"Mami, kayan breakfast zan kawo miki."
Ta faWa taka kallonta, sai ta girgiza kanta.
"Barsu nagode, dawo ki zauna."
Umarnin dake cikin muryar ya kaWa hantar ta, taji wani abu yana ?o?arin Sallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna Win, hannunta na taSa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.
Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet Win nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun Wakin da cewar.
"Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?"
Sai da ta haWiye wani dun?ulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.
"A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba."
"Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.
Kan Tv's stand Win nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji.
"To matso ki kira su."
Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma.
Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu Waya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ?irjinta tun kafin ta fahimci abinda take faWa.
"Amina yi ha?uri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..."
"Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?"
A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Daga cikin wayar Amma tayi ?okarin gyara muryarta kaWan sannan tace.
"Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sau?i kar ki Waga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..."
Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta ri?e da wayar tasa hannu ta Sare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da Sata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.
Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ?awata mata tarin hanyoyin da kullum suke Sullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huWu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar Win, cikon da take fatan zai zama mataki na ?arshe da take da ya?inin zai kai ga nasararta.
"Barka da shigowa cikinmu Amina."
Kalamai biyar Win data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin Sare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.
***
Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ?arsa Hameeda da kuma Ru?ayya?
Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta?
Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?
Munaya and Ishaq, me kuke tunani?
Hajiya Kilishi...
Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buWe muku abubuwa da yawa game da ita...
Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam!
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA UKU.
~~~~~~~
There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.
- Unknown.
**
Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.
"TaSa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ?wa?walwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."
Tayi shiru bayan ta faWi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ?arar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.
"Ya akayi Awwalu?"
Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ?wa?walwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, ?irjinta dake Wagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaWai abinda zai sa ka san cewa idan ka taSa ta ba zata tafi ta faWi ba.
Wata?ila magana guda Waya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ?ara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda
"Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ?arshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.
Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."
Ta gyara zamanta kaWan sannan ta cigaba...
"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika Wauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ?ara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taSa samunsa ba ko zaki mutu sau Wari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a? wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.
Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaSi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ?arfina da kuma ikona nace ke kaWai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf Win da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na Wora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."
A yanzu Amina tayi ?o?arin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana.
Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.
"Bari in Wauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.
Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ?ananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata Sulle ga matsalolin sa, hakan yasa ?awayena dama mutanen unguwar a lokacin suka la?aba min sunan ?ar baiwa.
Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ?anuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ?aramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ?a?a tara, sauran biyun akwai mai goma sha Waya da kuma sha uku.
Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take ri?ewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daWi, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ?yar da rabo dai na samu na tafi.
A can na hadu da ?awayena biyu kuma ?anuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuWin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daWe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu.
Kowacce mace ta?i fita tare da ?a?anta kuma aka ?i a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ?a?anta sune suka fi samun arzi?i, musamman Innata da take ganin itace ?arama an riga an rainata ita da ?a?anta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuWi ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ?a?an ta su ke ?yallin mai?o a gidan.
Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ?wa?walwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ?wa?walwata wajen cimma manufata.
Almajirin da kakata ta ri?e Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaWa takardu... In ta?aice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuWi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban taSa bawa wani jikina ba sannan ban taSa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taSa biyowa ta kaina ba.
KuWin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ?anuwana duk suka dawo suka raja'a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe Sangaren Wakunan mu aka gina mana dan?arere da ya tsone idon sauran ?anuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu."
Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace.
"A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ?o?arin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri Waya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor.
Na kashe kuWi sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa.
Har da masinjan ofis Winsa da ma direbansa na haWa baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina.
Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ?ara yarda cewa sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina.
Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arzi?i ne kuma na ciri tuta a cikin ?anuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya.
Ban daWe ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ?arta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja Wanta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so haWawa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa.
Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karSi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi Wawainiyar da ?anuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa.
Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani Wan lokaci kaWan ba.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan."
Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba.
"Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ?ara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..."
Babu shiri Amina ta Wago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ?aruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama.
"?warai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ?afafunta, kin san dalili?"
Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba.
"Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen Waki na kawai nake Wagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi Sangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a Sangaren ?ashi, na bashi ma?uden kuWaWen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ?ashin mutum.
Kuma sai da na jira har bayan watanni huWu da rashin lafiyar zazzaSi ya kamata sannan na haWa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi.
Kuma bayan yayi mata allurar ?afafun nata sun lalace gabaWaya na bashi kuWi ya koma ?asar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka ha?ura don ko ?an sanda basu iya samo komai ba.
Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ?afafun har muka je India aka cire su gabaWaya, shekara guda da rabi na Wauka ina jinyarta, na hana kowa wannan Wawainiyar hatta ?a?anta da ?anuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taSa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ?ara min ?ima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ?a?an Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su? Munaya zasu zo su faWa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faWa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba.
Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne."
Muryarta tayi shiru a wannan lokacin,? wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba.
"Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na faWa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ?arasa babban burin da nake dashi a duniya.
A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login