Showing 60001 words to 63000 words out of 84782 words

Chapter 21 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10758

light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar.
Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake Wauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta sha?i wani numfashi mai nauyi a ?irjinta sannan ta rufe ?ofar falon a hankali.
***
"Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?"
Muryar Fatima ta faWa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurSa.
"Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima."
"Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai."
Saura kaWan murmushin da take yi ya suSuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gidan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar.
"Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?"
Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya Soyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su ha?a su binne, ko Maryam da take ?aruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata.
"Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne."
"Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?"
Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?'
"Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa."
"Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wata?ila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi."
"Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..."
"Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta.
"Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min."
Fatima ta girgiza kanta itama.
"A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake Sallo wani abu daban."
Ta haWiye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa.
"Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo."
Sai Fatiman tayi dariya tace.
"Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku."
Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina Wauke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan Wan screen Winta kafin hasken ya Wauke.
***
"Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. "
Ma'aruf ya faWa cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga Wakinsa.
"Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let's not make them wait." (Kar mu barsu su jira.)
Abinda aka faWa a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ?arfe uku daidai, Martha ta daWe da tafiya kuma shima bai daWe da tashi daga kan system Winsa ba.
Don bayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast Winta, ta dur?usa har ?asa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a kan carpet Win lokacin da ta dur?usa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ?an siraran ?afafun nan nata suka lan?washe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya haWe dana kasa kamar ta rufe su ne gabaWaya amma kuma tana cigaba da abinda take yi.
Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ru?ayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba'a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ru?ayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruwa.
Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za'a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu tare dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga Waki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba.
Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar tafiya dashi motar tun Wazu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke.
Ya Wora hannunsa akan ?ofar falon har ya buWe lokacin da yaji muryarta.
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
Idanunsa suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na ri?e da wani ba?in bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya ji?e yana tabbatar masa wanki tayi, Wankwalin da take yafe dashi tun safe ta Waura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama.
Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya suSuce a fuskarsa ba kafin ya Waga mata kai.
"Ameen ya Allah, nagode sosai."
Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ?ara fitowa.
"Insha Allah meeting Win zai tafi daidai."
Tana faWin haka ta shige hanyar Kitchen Win dake gefenta bokitin na bin bayanta.
***
Dab da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kunnensa yana gaishe shi.
"Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?"
"Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida."
"To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare."
"Insha Allah Baba gani nan."
Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta Waga kunnensa daidai lokacin da mai mashin Win ya taho da wani irin saurin da ba Aminun kaWai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ?arar injin mashin Win da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ?afafuwan sa.
Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin Win ya murde kan mashin Win ya mi?e titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa.
Wasu daga cikin mutanen suka bishi da jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki Waya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ?ofar gate Win gidan da ya fito, inda tun kafin ya karasa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin buWe masa gate Win ya shige.
A gaban wata ?atuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin Win sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration daga aljihunsa. Ya Wago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba.
"Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito." Ya faWa yana ?o?arin balle maSallin rigarsa na gaba.
Daga Waya Sangaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai armashi kafin tace.
"Kace min an gama kawai Awwalu."
"An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya."
Ta gyaWa kanta a hankali, tabbas haka ne, komai? daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya taSa kasawa umarninta ne?ko kuwa ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshi?i samun ?ancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu.
Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba'a banza zata buWe mata fuskarta ba, ba'a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai taSa samun waje a zuciyarta ba.... Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama na karshe, amma da an samu wani akasi ?ofar ta buWe kenan, duk wanda ya jiSanci Amina ya shigo cikin lissafinta.
Zata Waure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juyawa da yatsan hannunta.
"Ya batun Ma'aruf Win Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutumin nan mun tura shi lahira tukunna."
Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya Wauke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta haWiye wani abu a cikin ma?ogwaronta tana kallon tarin magungunan Ma'aruf Win da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL Win nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuWaWen sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse Waya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuWin kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor Win... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!"
***
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA BIYU.
Life is what happen to us when we are busy making other plans.
-Unknown.
**
Ranar lahadi ne da misalin ?arfe huWu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya.
"Wallahi sai ayi ba?i kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili."
Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa ?ar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta.
Munaya tana yanka carrots ta Wago ta kalle ta tace.
"Ki kara faWar abu guda Waya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba."
Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace.
"Ki ?yale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk Waya ne."
Samiran ta girgiza kanta.
"Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga Waki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faWan taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..."
Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faWin ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya.
Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taSa ciwon hannunta da bata daWe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru.
Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da Wan yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta Wanyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaWaya suka gaisa sau Waya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan.
Samirah ce dama kusan kullym zata leko Wan bsyami ko sa?onta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daWe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su.
"Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi."
Munayan ta faWa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta Wauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya Wanyi sanyi kafin ta ?arasa abinda zata yi tazo haWa lemon.
Fridge Win yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen Win take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da ?ofar kitchen din ta buWe Ma'aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana Wakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting Win.
"Kinyi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa."
Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daWi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan Waya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ?ara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf Win da ya bata wannan sa?on ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ?wa?walwa ba.
Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq Win da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin a?alla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ?arya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa.
?afarta ta ?arasa wajen Fridge Win ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi.
"Me yake faruwa anan?"
Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faWaWa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da wa?a.
"Yayaaaaa B...."
A ?an kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daWe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wata?ila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya.
Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faWa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke Wauke da fara'a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a Wazu na wani competition Win kamfanin Maggi da aka zaSe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop Winsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta...
Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waWannan mutanen?
Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a daWe ba taji an ?wankwasa kofar store Win dake buWe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta.
"Akwai ruwa anan?"
Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ?ofar store Win, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ?are tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta buWe na saman ta Wauko Waya, yana tsaye yana kallonta har ta ?araso ta mi?o masa, kuma ga mamakinta tana ?arasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba Waya ya jawo ta zuwa gabansa, ?afafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ?irjinta lokacin da yasa Wan yatsansa Waya ya taSa daidai wajen data yanke Wazu.
"Me ya faru?"
Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon.
Sai da ta haWiye yawu tana ?o?arin saita tunaninta kafin tace.
"Da wu?a na yanke."
"Me kika saka a wajen toh?"
Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login