Showing 12001 words to 15000 words out of 84782 words

Chapter 5 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10768

abincin 'Ci kar ka mutu, 1987.'"
Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai.
"Wai har yanzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu ma?udan kuWi Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam Win ake ta faman lissafi."
Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa.
"Aminu Allah ya shirye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi."
"To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ?araso ba tukunna."
Ya faWi hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cuWa kayan wankinta.
"Ke, idan kinyi ?unshin nan ma haka zaki cigaba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? KuWina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne."
"Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ?unshin ka kankare shi."
Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Maryam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar arzi?insa, Amma tace Aminu shi ya Wauki kaso mai yawa bayan addu'a wajen dawo dashi daidai.
A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya faWi duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe.
"Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin ya?in duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama."
Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, Aminu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa.
A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke,?Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya.
Sannan a ?arshe bayan sun shiga falo, wani film din indiyan da ake yi a tashar Bollywood ya Wan daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da maSallan rigar.
Falon ya Wauka da sautin wakar film Win da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata ganewa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam Win da suka cika da haushi fal! Haka take so... Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe.
Sai dai rayuwar bata taSa biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ?addara take kallo a kodayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen abokansa sannan Maryam da wata ?awarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita kaWai, kamar dama ?addarar ta zaSi wannan lokacin ne don ita kadai Win.
Amma ta kira ta zuwa Wakin Baba lokacin da take kokarin haWa kan kitchen Winsu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya Wan Waure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai.
Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe flask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta.
"Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga Wansu."
Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle kewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ?wa?walwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a buWe mata ?ofar shiga.
Shiru ya ratsa Waukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zu?ar numfashi, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya faWa ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta.
"Amina.."
Ta kuwa Wago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar Wakin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba.
"Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan mota kawai tasa aka Wauke ni aka kaini har ofishin mijin nata.
Acan na tarar dashi tare da ?aninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa Wansu, yace min Hajiya Kilishin ita da kanta ta ro?e shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al'amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu 'A'a' ba don bani da wata hujja ko dalilin da zai sa in faWi hakan..."
Ba fahimtar abinda yake faWa Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake cikin tashin hankalin karayar arzi?insa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-?iri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da take ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jikinta bi da bi ta kowanne Sangare.
"Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki al?awarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ?addara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi miki bayanin wannan ba don a ?ananun shekarunki kin gan kalolin ?addarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan Sangaren ?addarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban mi?a ki inda zaki wahala ba, don komai halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na.
Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wallahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yun?urin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda."
Yayi shiru a lokacin, Amina ta haWiye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, maganganun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kasa ganewa a fuskar tata Wazu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun!
Wani abu da ya ?ara rikita tunaninta a lokaci guda... Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan maganar zata dame ta?
Sai ta sunkuyar da kanta ?asa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da zancen rashin karatun tana jin ba wanda na zata iya daurewa ba don farin cikinsu.
"Baka ?arasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba."
Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta faWa, kuma a lokaci gudan Amina taji gabanta ya faWi, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya faWa, wani abu da wata?ila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau.
Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan ya kira sunanta.
"Amina..."
Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta Wago idanunta daga kan ?an yatsunta ta kalle shi, ?aguwar ya furta abinda zai faWa na haskawa tar a cikin idanunta.
"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taSin hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata wal?iya har da tsawa a cikin Wakin!
***
A wannan daren....
Wajen ?arfe tara saura a lokacin da wata mota ?irar kamfanin 'Elantra' ta shigo cikin layin, ?an yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar faWin layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko'ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ?yallin sabubtar motar haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da mai?o.
A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ?ofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa.
"Wancan ne gidan yallaSai, in dai gidan Alhaji Sulaiman Win daka kwatanta min ne to shine gidan."
Ma'aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ?ofar gidan shima.
"Nagode sosai kaji."
Saurayin ya washe baki.
"Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya."
Ya faWi hakan da tsantsar murna yana ?ara rike sababbin kudin da Ma'aruf Win ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sulaiman Win da yake nema, saurayin ne kaWai ya gane don haka ya ro?e shi yazo ya ?arasa dashi.
Saurayin ya rufe ?ofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai Wauki kiran ba.
Ya ?yale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta.
"Ma'aruf kana ina? Ina ka tafi?" Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa da kujerar motar sannan yayi murmushi.
"Kana magana kamar kana neman wani yaro Wan karami, sau dubu nawa a rayuwata na Wauki mota na fita da daddare Ishaq?"
Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici.
"Wai ka haukace ne gabadaya Ma'aruf? Yanzun nan fa muka dawo ?asar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ?arfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka Wauki mota ka fita a halin da kake ciki?"
Ya sanya Waya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office Win Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ?arasa gida, kuma zai iya rantsewa kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq Win shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar.
Don suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama ba?a wuluk da ita kamar kayan.
Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da mu?ullin motar Ishaq Win yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba'a dawo da ita ba tun ranar da al'amarin ya faru (lokacin da ya Wauko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.)
Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya buWe masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameera a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya taSa ratsawa da gidan ba lallai ne ta?i samunsa ba.
Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa Wan'uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman.
Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta.
"Waye Alhaji Sulaiman a ?anuwan Mami?"
Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace.
"Ko wanda yazo jiya? ?an'uwansu Hajiyar Mami ne, yana Wan zuwa dai ba sosai ba."
Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta.
"Da yazo jiyan me yayi?"
"Bai wani daWe ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office Win Daddy wai zasu yi magana."
Da jin haka ya tabbata shine wanda yake nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Kin san gidansa?"
"A'a, amma Mami tace a Gadon ?aya yake wai wajen layin transformer."
Ya gyada kansa.
"Kin san sunan ?a?an sa?"
"Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina."
Ya riga ya gama samun abinda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu.
"Ina Gadon ?aya."
Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar.
"Gadon ?aya? Wajen wa? Me zaka yi?"
"Ni da kai mun sani cewa abinda Daddy ke shirin ba ?aramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba."
"What?" ?arara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq Win, kuma Ma'aruf zai rantse ya shiga girgiza kansa lokacin da yake faWin.
"Kar kayi haka Ma'aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba..."
"Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu Waya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita kawai."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un... Ma'aruf me zaka yi?"
Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa.
"Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali."
"B, tsaya kaji..."
Dib. Ya katse kiran ya ma kashe wayar gabaWaya. Idonsa ya sake kallon ?ofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito.
Ya sake janyo hular rigar yana ?ara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo.
Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa.
"Bigboy ya sunanka?" Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya tambaya sanda yaron ya ?araso.
"Adam."
Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar Wari biyar daga aljihunsa yana mi?o nasa.
"Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo."
"Toh."
Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, idanunsa ko kaWan bama su ga kuWin da yake bashi ba.
Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma'aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ?ar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam Win yaja hannunta zuwa ciki.
A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa!
***
Me zai faru??
Me zai faru??
.
.
.
Me Ma'aruf zaiyi??
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA HUDU.
~~~~~
"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taSin hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata wal?iya har da tsawa a cikin Wakin! Kuma bayan wal?iyar ta Wauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa.
"Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..."
Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake Wago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ?araminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login