Showing 33001 words to 36000 words out of 84782 words

Chapter 12 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10753

ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.
Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaWin cewa gidan zai dawo Sangaren da Baba Alhaji ya taSa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar.
Ya cije leSSensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faWa masa kwanakin baya.
"Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ?a?an masu kuWin da har layi zasu yi idan kace zaka zaSa."
Ya faWi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin Waurin auren ga kowa a Office Win kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk Win yayi wannan ?orafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arzi?i bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waWannan gidajen, misali aurensa da Ru?ayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci Waurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.
Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuWin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taSa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan.
"Ina kika baro masu yin cin-cin Win ne da kika biyo ni?"
Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita Win ta bata amsa ba ya mi?e tsaye, muryarsa da zurfi yace.
"Zanje in dawo."
Sai ta girgiza kanta..
"A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta Webo min ?an kayan kayan da zamu bu?ata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min."
Ya cije leSSensa kaWan yana bin maganganun nata kafin ya gyaWa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da Waukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.
Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na ri?e da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ?iyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ?iyasta yadda zuciyarta ke iya Waukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta.
Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ?aunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.
A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin Wakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ?ara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ?aiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?
Ta ?ara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda Wan ?aramin ?irjinta ke Wagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a Waya gefen ?wa?walwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi Wauke da tsananin damuwa da kuma ?aunar yarinyar dake nunawa ?arara.
Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai al?awari ne cewar ba zata taSa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaWai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haWa aurensa da yarinyar data san ba zata taSa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ?ara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.
Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suSuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf Win ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaSar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida...
GaSar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taSa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin Wakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suSuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ?aryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buWe don yaga sabon sa?on da zata aika masa a daren yau wanda zai ?ara ?aryata kalamansa fiye da cikin masaki.
Ta mi?e a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don Wakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taSa farinta.
Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buWe ta....
***
A cikin Wakin, da misalin ?arfe goma na safe, Ru??aya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ?ulli-?ulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.
"Wallahi Maamah Hanan ?awata ce ta haWa ni da ita, tace ta taSa yin aiki da wata ?aruwarta suna da ?o?ari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na Wauke ta a lokacin, kuma itama ta taSa fada min inda take amma na manta."
Kukanta ya ?aru lokacin da ta sake cewa.
"Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?"
Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ru?ayya na zaune a cikin ?aton falon gidan na ?asa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ?aramin mayafin rigar yayi da wayarta ke ri?e a hannu.
Idanunta na kallon Ru?ayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na Satan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ?asar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ru?ayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.
Saboda haka kai tsaye ta kira Ru?ayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ?araso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address Win gidansu ta karSo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.
Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ru?ayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haWin kan ?ar tata, ita kaWai ce mace kuma babba a cikin maza huWu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita.
Ta sani cewa tun daga lokacin da Ru?ayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta Wauki zuciyarta ta dan?a a hannun? Ma'aruf shikenan take zaune da ?irjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata ba?in ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ?wa?walwar ta tsaf ya goge wannan Ru?ayyan da take a baya, ?ar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ?a?an manya ake samun masu kwaikwayon ta.
Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, Waya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ?wararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf Win, amma wucewar sati guda Ru?ayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ?in Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.
Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ?ar tata, a lokacin ta mi?e tsaye tayi wani yun?uri da bai bawa Rukayyan zaSin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.
?arta Hamida bata taSa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karSe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ru?ayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ?awarta akan ala?arta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ?an kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.
Har ta buWe baki zata yi magana, Ahmad, ?anin Ru?ayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.
"Wai Maamah ki dawo ?asar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo."
Ya faWa yana ?arasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.
"Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu.
Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa.
"Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita."
"What? Ta yaya? Tun yaushe?"
"Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna."
Ransa a Sace yace.
"Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ?edara wai ita zata dinga kula da ?arta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?"
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
"Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?"
Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo ri?e da wayarsa a hannu yana faWin.
"Is it true yarinyar nan ta Sata? Umar just called me now wai ya ganki a waje Wazu kuna tambayar Hamida."
Hajiya Nafisa ta gyaWa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.
"?ansanda? Win dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba."
"Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?"
Tambayar tasa Ru?ayya sake fashewa da kuka.
Ahmad yace.
"Akwai wani abokin Ashraf da ya taSa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban Wauko wayata daga Waki ba, Ibrahim kira shi."
Ya kalle shi.
"Wa zan kira?"
"Ashraf Win zaka kira kace ya baka number B-man."
Wayar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta Wauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ?an sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.
Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir Wan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.
Gayawa zuciyarta take yi? cewa ba zata sake kuskuren rasa ?arta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaSin Ru?ayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karSi wannan ?addarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.
***
"Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi ri?o da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar al?iyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..."
Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ?aruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da Wimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ?a'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin Waurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu ba?oncin ?anuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.
"Bikin ?arki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan Waurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ?arki ta sunna bace kina tunanin zamu ?i halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?
Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waWanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ?arsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.
Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faWi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake Wauke da sauran labarin da bata ?arasa musu ba, sauran labarin da ko ?anuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar? ba, bata ce komai ba.
Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya Worar da saSanin cewa faWa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ?ofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saSani da ya shiga tsakaninta da mijinta.
"Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buWe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaSar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..."
Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take ta?ama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.
Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan Wumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wata?ila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.
Tana sanye da wani farin sa?i dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata Waurin ?irji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika dan?am don har ?an unguwa sun shishigo.
Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta Webo nata itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login