Showing 30001 words to 33000 words out of 84782 words

Chapter 11 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10748

shima yana kallonta lokacin da da ya buWe baki yace.
"Ina so zan aure ki."
Ga mamakinsa sai kawai ta kalle shi na wasu sakanni ta cikin mudubin sannan ta ?yal?yale da dariya.
"Me kace?"
Ya haWiye wani abu mai zurfi a ma?ogwaronsa kafin ya saka hannayensa ya sake juyo da ita yana kallon fuskarsa.
"Wallahi da gaske nake, ina so zan aure ki Rukayya, ki bani dama ko a weekend Win nan zan turo iyayena, saboda na fahimci cewa I can't live without you. (Ba zan iya rayuwa ba sai da ke)"
A lokaci guda ta shiga girgiza kanta yayin da duk wannan rahar ke barin fuskarta, kamar tana karkade ta ne tare da girgizawar kan nata.
"Ba muyi wannan alkawarin ba Jawad, saboda haka don me yasa zaka yi tunaninsa, ofcourse kana burge ni saboda wasu abubuwa a gefe, amma bana sonka, na daWe ina gaya maka hakan, zuciyata ba taka bace."
Tana kallon yadda dukkan wani ?warin gwiwar da ya tashi dashi a safiyar ke zagwanyewa daga cikin idanunsa, tana kallon yadda yanayin dake cikin idanun nasa ke juyewa zuwa wani abu da ba zata iya fassara shi ba.
"Saboda me?" Yayi tambayar kamar iyakarta zata sa ta canja ra'ayinta.
"I'm sorry J, amma saboda gidan tsohon mijina zan koma kuma na riga na tsayar da zuciyata akan hakan, idan har ba zaka iya rayuwa ba sai da ni, to ni wata?ila munyi tarayya akan hakan,
don nima ba zan iya rayuwa babu Ma'aruf ba Jawad."
Bata san me yake tunani ba, bata san me yake lissafawa ba, kawai kallonta yake Wauke da wannan yanayin da, da ace lokacin da ta buWe ido daga bacci ne ta ganshi a hakan, zata rantse cewar ba shi bane.
Saboda haka tayi baya a hankali ta fita daga cikin hannayensa, kuma sai ?arar wayarta tazo a daidai wannan lokacin don haka ta isa wajen jakarta dake yashe daga can gefen gadon ta Wauko wayar, bata ko tsaya tantance lambar dake kiran ba, ta Wauka ta kara a kunnenta.
Kuma abin da muryar cikin wayar ta faWa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ?irjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faWo kasa ta tarwatse!
***
Ina Ma'aruf yake?
Kuna tunanin sa?on cikin wayar nan ya dangance shi?
Meye gaskiyar labarin Fatima?
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
Please go and read RAI DA ?ADDARA by LUBNA SUFYAN... that story is touching me.=?
?

BABI NA BAKWAI
~~~~~~~
"Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara."
Muryar Ma'aruf, ta faWa a cikin Wakin asibitin da misalin ?arfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon Wakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ?aramar yarinya ce kwance tana bacci.
Da hannunsa Waya ya shafo kansa sannan ya sake cewa.
"Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta."
Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa.
"Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba'a dauki shekarun da suka fi haka ba."
Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ?arshe, suka yi sallama bayan Ishaq Win ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja.
Ma'aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce... ?arsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita Win ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taSa zato ba.
Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ?o?arin daidaita al'amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din Satan ma?udan kuWaWen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ?arshen shekara da ake cirewa a duk ?arshen kowanne wata.
Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ?arshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karSi hakan a matsayin ?addara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa ta?i bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai... Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taSa bari a lissafa da wata tangarWa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin.
A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ?ananun ma'aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk Win yaje ya same shi har gida, sai ya ?i bashi haWin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk Win yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya Saci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani.
Amma shi kansa Faruk Win ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu?zai yi to tabbas zai yi Win, bai taSa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba.
Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address Win da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haWa da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema.
Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ?ara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa'a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa.
Wani saurayi da ba ko riga a jikinsa sai gajeren wando da kuma sar?a ya samu ya raka shi zuwa cikin gidan, kuma duk inda suka wuce juyowa ke an kallonsu da mamaki saboda manyan kayan dake jikinsa, nasa mamkin ya fara ne daga lokacin da suka shiga ciki inda yaga ashe gidan wani irin ?ato ne mai kuma tsawo, ga tarin ?ofofi birjiki daga kowanne gefe sannn da Wimbin mutanen da ya san zasu iya tashin unguwa guda, ?aton tsakar gidan ya cika taf da kaya da kuma igiyoyin shanya kota'ina, ga kwata layi-layi dake tashin wari kamar bola aka buWe, sannan hayaniya kamar zata fasa kunne.
Ba shiri ya haWiye yawu yana sake dam?e? mukullin motar dake hannunsa lokacin da idonsa ya fara arba da ti?a-ti?an mata sanye da ?ananan kaya suna ta harkokinsu tare da maza da kuma tulin yaran dake yawo koina, daga can gaba ya hango wasu suna faWa, mata biyu ne sai ihu-ihu da zage-zage suke cikin yarensu, yaga masu raba su basu da yawa kowa harkarsa kawai yake a wajen.
"Abeg no vex eh, this is Mr. Okafor's room." (Kar ka damu dasu kawai, ga Wakin Mr. Okfor Win nan.)
Saurayin nan ya katse shi lokacin da suka tsaya a kofar wani Waki mai Wauke da ragwajajjen ?ofar net. Sai kawai ya gyada kansa sannan cikin nasa kwantaccen turancin yace da saurayin ya fara shiga ya sanar musu zuwansa tukunna, kuma minti guda bayan tshin hayaniyar da ya jiyo a ciki sai saurayin ya fito yace zai iya shiga. Hannunsa ya zaro dubu guda a cikin aljihunsa ya mi?a masa, ai kuwa ya washe baki yana godiya gami da sake buWa masa ?ofor Wakin.
Da takalmansa ya shiga amma har a jikinsa yana?jin dattin da yake takawa akan ba?in carpet Win Wakin, kuma rashin iska da wari ko ?ansnin wani abinci ya hau kansa a take, amma yayi kokarin dannewa ta hanyar murmushi wa tarin al'ummar ciki dake ta Webe kaya don sama masa waje ana faWin.
"Welcome sir."
Shi kansa Mr. Okaforn jikinsa rawa yake yi na ganinsa balle kuma tarin ?a?an sa da kowannensu ya riga ya zube a ?asa, kuma cikin gurbataccen turncinsa Mr. okaforn ya shiga faWin.
"Ban san da kanka zaka zo ba yallabai, ai na cewa yallaSai Faruk ne ya bari sai na dawo aiki tukunna, matata ce ba lafiya muna ta faman jinyarta."
Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ?aryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen.
Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ?a?an da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaWai ya san duka ?a?an Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ?udirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaWaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ?i tayin ba.
Sai dai Wan adam baya taSa hango tazarar faruwar wasu al'amuran, don a lokacin da ya buWe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ?ar Mr. Okaforn ta fito daga wani Waki Waya tal dake manne da falon, hannunta Wauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ?o?arin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace.
"Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned." ( Baba zanje na kai musu ?arsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.)
"Mary!" Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta dur?ushe kamar ?anuwanta tana faWin.
"Welcome sir."
Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba.
A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau Waya ta buWe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karSeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daWe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga Wura mata drip mai haWe da ruwan magani.
Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan.
Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daWe da binne ta, yawan ?aunar yana sashi ganin irin ?o?arin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi ala?anta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita.
"...bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ?wa?walwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka."
Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne.
Don ranar da ya sha?e Ru?ayya bayan ya karSe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ?wa?walwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ?aiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ?wa?walwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karSe ta daga hannun Ru?ayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sau?i tukunna.
Kuma bayan hakan sai Ru?ayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace.
"Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaWan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ?o?arina wajen gyara maka rayuwar amma ka ?i barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda ba?uwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ?wa?walwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaSi dawowarka."
Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuWin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ru?ayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ?anwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo.
Yaji kansa yana Waurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ?anuwansa raSarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ?orafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba.
A lokacin ?ofar Wakin ta buWe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta ri?e da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?"
Muryar Mamin ta faWa, sai da ya taso ya mi?e sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ?o?arin ri?e hannun Hamidan da ya saki.
Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke Wamfare a fuskarta game dashi.
"Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, daWin abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaWowa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya."
Ro?on da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan.
A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta mi?o masa, kuma ganin ?o?arin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya karSa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar.
A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karSi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho Win a yanzu ba'a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ?anuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa.
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages Win dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen Win, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin.
Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login