Showing 75001 words to 78000 words out of 84782 words

Chapter 26 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10764

sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa.
"Kamar ki Waya da Mamanki, na daWe ban ga masu kama haka irinku ba."
RuWani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta.
"Haka kowa yake cewa." Ta faWa a hankali.
"Haka kowa yake gani that's why."
Bata ce komai ya sake cewa.
"Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki."
Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suSuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake Wagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ?ara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba.
"Nagode sosai."
Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba.
A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta.
Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ?ankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daWe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya.
Tare da Ru?ayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation Winta akansa, ta daWe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daWi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaWai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa.
Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruWani, irin ruWanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ?amshin turarensa gabaWaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace.
"Kin manta baki Wauko basket Winki ba."
Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ?ara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaWan kafin tace.
"Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi."
Bayan ta faWi hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana.
"Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I'm really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear."
Dear, dear, dear....
Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka.
"Amina..."
Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta Wago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa.
"Ko zaki karSo mana maganin da za'a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga Waki na farko ne wajen Malam Ibrahim Win."
Malam Ibrahim Mijinyawa shine Wanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan nasa ba'a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ?auye ne dake gaba kadan mai suna KuWai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke Win dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su Win wani Waki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna.
A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani Wanuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba.
Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace.
"Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?"
"Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waWannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sau?i jibin."
Kalmar 'waWannan kayan' ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waWanne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi.
"Wallahi matar nan tana ?o?ari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi."
Taji Aminun ya sake faWa kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.
"Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada."
Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta dam?o mayafinta dake ?asa sannan ta haWiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri.
"Bari naje Amma."
Da haka ta tura ?ofar net Win Wakin ta fita, tana jin kamar tana Wauke da nauyin duniya ne bakiWaya a kafaWunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai Win ba.
Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu'ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe Waya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiWa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ?arfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin.
"Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taSa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?"
Lokacin da ta faWi hakan kallonta take da ?wallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa.
"Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba... Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta Soye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na za?ulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal."
Sautin muryar Amman ya fito da Wimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuWe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ?ulla zaren ?addarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar.
"Me suke yi miki Amina? Ki faWa min abinda yake ?asan wannan kyautatawar..."
Ba shiri leSSenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuWa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ?arta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya... Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da Woriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taSa jin kanta game da mijinta ba.
Nutsuwar da a cikinta ne idan za'a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ?aryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne... Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za'a buWewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ?wa?walwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci.
Zata gane cewa ba an halicci ?wa?walwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take ta?ama ba, zata san cewa Allah ya halicci ?wa?walwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi.
Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suSuce a fuskar Amman, ita ta sani ba'a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ?arta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai Wauke da irin ?wa?walwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ?wa?walwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal!
Idan kissa da dabara Kilishi ke ta?ama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma'aruf Win data zaSa dasu za'ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki Waya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi.
Don mutane ukun da ta ga ?arshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ?afarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ?wa?walwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan!
A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta.
"Daga yau kar na ?ara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taSa ganinsa a tawa ba...!"
WaWannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ?arta daga raunin da ta hau k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ?warin gwiwar cewa zata iya tunkarar ya?in dake gabanta saboda mahaifinta.
Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci ya?in ne saboda kyautatawar rayuwarta... a tafin hannunta zata Wora mata rayuwar gidanta sannan a Waya tafin, zata Wora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar...
'?an hakin da ka raina...!
***
Haseenah Guest Inn, Jigawa.
04:30pm
"Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma Ma'aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuWi kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi."
Muryar Ishaq ta faWa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma'aruf wanda ke tsaya a barandar wani ?ayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa Waya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota.
"Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ru?ayyan ita ta sani."
"Ka shirya faWuwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?"
Ya cije leSSensa kaWan.
"Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar."
Da haka suka yi sallama a wayar da wata?ila itace ta huWu tsakaninsu a yau kaWai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma'aikacin Guest inn Win ya ?araso inda yake.
"Yawwa yallaSai, gashi an kammala komai."
Cewar matashin yana mi?o masa wani mu?ulli.
"Nagode sosai."
Ya faWa da murmushi yana karbar mu?ullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi.
A wanna lokacin Hajiya Kilishi na Wakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ?o?arin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin.
Fuskarta Wauke da faffaWan murmushi ta Waga wayar tana fadin.
"Mai gaskiya na, kun taho ne?"
Ma'aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa.
"A'ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can."
A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan wal?iya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ?wa?walwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin Webo madarar da take yi tana jinsa.
Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma'aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne?
Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tu?in dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma'aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuWe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna Wagewa daga cikin tsarinta.
Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara Wagewa ba ko kaWan!
***
Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin??=??=??
To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faWi kasa wanwar??
Me kuke tunani game da Amma da kuma ?udirinta?=??
Kar ku manta kuma, zamu yi kwanan Jigawa....=?
?=??=??
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA BIYAR.
~~~~~~~
This could be the start of something new.
-High School Musical
"Ina zamu je?"
Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta mi?ewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar.
"Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba.
Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruWanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa.
"Nayi zaton gida zamu tafi."
Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saSanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure.
"Dare yayi kuna bana son tu?in dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna."
Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haWiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ?asa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta ro?e shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya Wauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma.
Amma duk da haka sai taji wani Sangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take Wauke dashi a Wazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ?ara buWe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaWaya ita bata hango su ba.
Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ?arfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ?ofar nasarar su.
"Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buWe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faWa akwai sauran ?urar da dole na san ta lulluSe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bun?asar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..."
Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ?ara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ?ara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a.
Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taSa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login