Showing 51001 words to 54000 words out of 84782 words

Chapter 18 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10766

na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi."
Faruk ya faWa yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace.
"Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka le?a motata ka gani wanki naje na karSo sannan na karbo Winki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski."
Faruq Win yana nazarin sumar kansa da banbancin ta kaWan ne da yadda ya ganta jiya, yace.
"A haka wannan gashin naka an aske shi?"
Ya girgiza kansa har yanzu bai kalle shi ba yace.
"A'a fixing nayi."
Sai kawai Faruq Win yayi dariya sannan ya juya kan tasa tab din dake blinking alamun shigowar wani sabon sa?on, suka cigaba da tattauna duk abinda ke gabansu har magariba ta tadda su anan, wanda kafin magaribar suka yi sa'ar ganowa cewa tabbas wannan kamfanin sun karbi kaya na ma?udan kuWaWen a hannunsu kuma dukkan receipt din kudin an saka adadin kudin daidai, har ma da alert din shigar kudin cikin bankin kamfanin, amma takardar da Faruk Win ya gano cewa an duba balance a wancan lokacin kuma kudin bai kai ba, ita ta daure musu tunani. Don basu san yadda za'ayi alert ya shigo da wani adadin kuWi ba alhali ba hakan aka turo ba.
Anan suka tsaya kasancewar magriba ta taho kusan kowa a Office din ya tashi tunda dama a ?a'ida ?arfe biyar ne lokacin tafiyar kowa.
A wajen Hamida ya daWe bayan yayi sallar magaribar, kuma wannan karon har nuna alamun cewa zata biyo shi tayi, ransa ya cika da farin ciki kafin ta ?arasa da cewar zata bishi ne ya kaita wajen Maminta, kuma Allah kadai ya san sau nawa ya zura hannunsa cikin gashinsa ya fito dashi kafin ya iso gida, don game da al'amarinta bashi da wata mafita ko kaWan, abu Waya ya sani shine ba zai taSa iya sake rabuwa da ita ba ko da me Ru?ayya da iyayenta zasu tunkare shi.
Ya tuno wayar da suka yi da Ahmad kanin Ru?ayyan a jiya, yaron bashi da hankali ya daWe da sanin hakan, tunda har sunyi magana da Ashraf ya gaya masa cewa zai neme su bai ga dalilin? da zai sa shi ya sake kiransa ba, kuma? yadda yake masa magana ma ji yayi idan akwai wani mataki da yafi na haukan, zai iya saka shi a wannan layin, don haka ?arara yayi masa gargaWin cewa zai iya sawa a kama shi idan har ya sake kiransa da wannan batun.
Ya riga ya sani cewa duk cikinsu babu wanda zai iya ja dashi don yana da da hujjar da zai kaisu ?asa ko a gaban waye za'a tsaya, bama wannan ba ya sani cewa babu inda Ru?ayyan zata je ta samo karfin halin da zata iya fuskantarsa a yanzu, tana yawo ne da nauyin waWannan kalaman Soyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taSa manta su ba.
Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa.
Kuma bayan ya Wauko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haWuwarsu ta Wanyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haWu.
Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a LamiWo Cresent ana musu gini iri Waya, bayani yake yiwa Ishaq Win cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma'aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ?arshen maganarsu.
"Dan Allah ka kula B."
Ya cije leSSensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba.
Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ?ar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ?amshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ?ara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa.
Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa Wakin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa.
"... Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuWi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu Wakin kwanansa na ?asa ne bai ko kai girman Wakin nan ba ka sani.
Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faWa wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma'aruf."
Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al'amari ne.
***
Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green Win da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da'a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da? Ma'aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ?ofar dakin daidai lokacin da robar vaseline Win dake hannunta ta subuce ta fadi.
Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta.
Ko kaWan bata ga wani yun?urin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go Win nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din.
Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai kawo wata gudunmawa kayan kitchen Win ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo.
Sauran Wakunan nan biyu ashe Waya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai Wayan ne aka tsara shi da wani irin nau'in furnitures masu tsananin kyau da Waukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum Wakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba'a tsara wannan don?ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling Win dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaWayansu.
Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin Wakin daga inda suka tsaya? a bakin kuma ?aton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye.
Ta fita Wakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table Win nan tray din dake dauke da? flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo Win ma bai taSa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo.
Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana Waki tana biya abinda zata ce masa taji ya buWe kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin.
Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba?
A cikin addu'o'in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace '... Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..'
To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me ?an uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace.
"Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ?a ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa Waya ne kuma kowa yana samun tallafawar Wan uwansa saboda ?aunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin."
Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faWarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta Sangarori da yawa.
Hajiya Kilish??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul'abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba.
Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma'aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za'a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar 'Uwa a rayuwar bahaushe' sai dai babu ?afafu, tana zaune kan Wheelchair Winta da Hisnul Muslim a hannunta.
Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara'arta da komai itama ta karSeta, tana ta zuba tarin addu'oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma'aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ?aranci a kalaman Hajiya Kilishi.
Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma'aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa.
Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ?arasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace.
"Barka da dare."
A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma'aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da.
"Kin yini lafiya?"
Haka yake tambayarta kullum,? don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuWa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ?ara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace.
"Wannan abincin..."
"Naka ne..."
Ta ?arasa da sauri tana Wago da kanta, idanunsu suka haWu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace.
"Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji."
Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ?arar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta Wauki plate din tana bude murfin flask Win farko.
?amshin abincin ya shiga hancin Ma'aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ?aramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ?arasa kan kapet Win gaban abincin ya zauna, ?amshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray Win shi kaWai ya raba tsakaninsu.
Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ?amshin daya baWe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar.
Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al'amari daya shuWe a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba.
"Thank you so much."
Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri.
"Ina zaki je?" Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba.
"Zanje in kawo ruwa ne."
Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya Waga mata kansa.
Ta isa kitchen din ta Wauko robar ruwa guda Waya da ba'a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haWa ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba.
Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ?arasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaWan dashi ta zauna sannan ta fara ?o?arin zuba lemon a kofi.
Ma'aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taSa gaya masa suna dawowa cikin kansa.
... Wannan ba irin ba irin Ru?ayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake bu?ata.
Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login