Showing 3001 words to 6000 words out of 84782 words

Chapter 2 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10745

sannan a lokaci guda ya fizge drip Win daga jikinsa ya mike zaune, jini ya shiga fitowa daga inda allurar ta fita amma bai ko bi ta kai ba ya kalli rigar dake jikinsa, rigar asibitin ce wadda ake bawa kowanne mara lafiya.
Ya shiga ?arewa Wakin kallo a hankali har zuwa kan drawer dake can gefe, a lokaci guda ?wa?walwarsa ta tuna masa da jakar da Ishaq ya ajiye a ciki jiya don haka ya mike tsaye, jiri ya so Waukarsa amma ya dage ya tsaya akan ?afafunsa sannan ya isa ga drawer.
Ya buWe ciki ya fito da wata ba?ar jaka ya shiga fito da kayan ciki, ?amshin turarensa na 'Dior Sauvage' shi ya tabbatar masa da cewar kayansa ne tun kafin ma ya gane su, kala biyu ne sai kuma wata ?atuwar rigar sanyi wadda ke zuwa har gwiwa, bai yi tunanin komai ba ya shiga canjawa zuwa kayan, sai da yazo Salle maSallan rigar saman sannan ya kula da jinin dake fita daga hannunsa.
Don haka ya saka rigar asibitin da ya cire ya goge sannan ya Wora daya rigar, ya kuma jawo rigar sanyin?ya dora akai, bai ko Wauke rigar asibitin dake kasa ba ya saita facing Cap Win da ya Wauko a ciki daidai fuskarsa sannan ya nufi hanyar kofar Wakin, ya san duka wayoyinsa basa nan kuma Ishaq bai bar tasa a gefen labtop Win ba don haka ya nufi ?ofar ya buWe, dogon korido ne a wajen mai dauke da kofofin Wakuna da kuma mutane dake ta wucewa ta cikinsa, ya tabbata babu ma'aikatan da suka san shi a cikin waWanda ke wucewa don haka kansa tsaye ya bi ta cikin mutanen dake tafiya ya saje, yana mai nufar hanyar waje.
Iskar dake kaWawa a wajen mai tsananin sanyi ta ratsa fuskarsa sanda ya fito daga asibitin gabaWaya, dare ne lokacin, ga fitulu a koina, na kan titi dana motoci, ga mutane birjik musamman na ?afa sai faman wucewa suke.
Haka ?ofar asibitin take a kullum, tun daga shekarun da ya fara zuwansa har yau. Sanyi ya shiga ratsa kunnuwan sa dake buWe sannan a lokaci guda yaji wata irin yunwa ta mamaye shi, sai kawai ya saka tafin hannayensa duka biyu ya gefen fuskarsa lokacin da idonsa ya sauka akan sunan wani kanti daga can tsallake, kantin da yake yawan yin siyayya duk lokacin da yazo kasar.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Baturen dake kan kantar ya faWa a lokacin da ya gama lissafa abubuwan daya Webo.
Ya kai hannunsa bayan aljihu kamar zai fito da wallet sai kuma ya dawo dashi, ya matso daidai jikin kantar yana kallon mutumin yace.
"You know me right?" (Ka san ni ko?)
Kallon da mutumin yake masa yasa ya cigaba da cewa.
"I used to come around, from that hospital...(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)"
Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da bata canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace.
"What I mean is my brother is coming to pick me from here... So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but I assure you he's going to pay when he arrive...."
(Abinda nake nufi shine Wan uwana zai zo yanzu ya dauke ni anan... so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo...)
Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin Wiba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Har ya ha?ura ya Wauke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye a bayansa yace.
"You're holding up the line, man! If you can't pay just leave."
(Malam kana ri?e mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.)
A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin da ya kusan kaishi har kasa, ya Wago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ?walla ?ara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba shiri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ?ara yana faWin.
"Someone should call the police!" (Wani ya kira ?an sanda!)
****
British Transport Police Station
No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom.
"Kun tabbata dukkan waWannan bayanan file Win gaskiya ne?"
?an sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma'aikacin asibiti a gefensa.
"Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba'a hayyacinsa yake ba."
?an sandan ya kalli ma'akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card Winsa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file Win.
"Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani ko sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba..."
"Ai da yake yallabai, mu? a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba."
Jin haka yasa ?an sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ?ulle tarin mutane a cikin wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai.
"Kai Wanuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?"
Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin harshen turanci shima yace.
"Yayi abubuwa da yawa yallaSai, waWanda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba..."
"Misali..." ?an sandan ya katse shi. "Misali zaka bani ba wani bayani ba."
Jin haka yasa Ishaq haWiye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da suke kallonsa daga cikin cell Win sannan ya gyara zamansa kaWan, muryarsa can kasa yace.
"Yallabai, a karo na ?arshe da ciwonsa ya tashi saura kaWan yayi kisan kai."
Idanun Wan sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gyaWa kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa.
"Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu ri?e shi har sai ya warke."
Dukkaninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani Wan sanda dake ?o?arin wucewa.
"Stone! bring the Black one out." (Stone! Fito da ba?in cikinsu.)
Stone Win baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi kaWai ne ba?i a cikin tarin turawan cell din, don haka ya zaro mu?ullai daga jikinsa ya nufi wajen.
?an sandan ya sake kallon file Win hannunsa a karo na ?arshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki.
Ma'aruf Mansour Bakori!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA BIYU.
~~~~
"Kowanne Wan adam yana da tarin ?alubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar 'Bipola disoder' nasu ?alubalen daban ne. Bipola disoder cutar ?wa?walwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ?arfinsa, yanayin tunaninsa har da Wabi'arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu,? zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai.
Cutar tana farawa ne daga lokacin ?uruciya, kuma duk da cewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ?aruwarta idan har ba'a bin ?aidojin magani daidai. Tana da matakai huWu kuma na ?arshen da ake kira da "Mania" shi yafi kowanne hatsari.
A matakin 'Mania' mara lafiya yana jin tsananin ?arfi da jin cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzu?a ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ?arancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ?wa?walwar su tana buWewa ta yadda za su yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine 'HypoMania'...."
Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ?aton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma'aikata ke wucewa wajen wasu gadaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen.
Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ?wa?walwar da ake dubawa a wannan Sangaren asibitin ne, masu jiran kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sau?in fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana Waya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ?iris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama yake faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije.
A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon Wan'uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa.
Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma'aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ?wa?walwar tasa, ya riga ya k?ure komai a Bipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma'aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba'ayi ba daga kowanne Sangare na iyaye da kuma ?anuwansa amma rashin tasa tallafawar ya haSSaka ciwon har sai da ya ?araso matakin ?arshe, 'Mania Stage'.
A baya bai fi ?an awanni ko kwana Waya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ?asar nan Ma'aruf ba'a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar dashi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu.
Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fitowarsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma'aruf ya shigo musu da gawar wani.
Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba ya zagaya ta Waya hanyar da wandanda ba ma'aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon.
"Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma'aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!"
Ya faWi hakan da harshen hausa daidai sanda ya bankaWa labulen da aka zagaye gadon. Dama abinda Ma'aruf Win yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya daWe a waje yana kaWa ?afa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ?orafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya Wago da idanunsa ya kalle shi.
"Kaima sani bana iya rike yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba."
Ishaq ya girgiza kansa.
"Ma'aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ?asar nan?"
Maimakon ya bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace.
"Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba."
"Kuma matsalar kenan, kai da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma'aruf! Mania!"
Ya faWi sunan mataki na karshe a cutar da Ma'aruf Win ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma'aruf Win ya juyo ya kalle shi, sannan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq Win zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da faWin.
"Shekara biyu da suka wuce a asibitin nan ko HypoMania test Winka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna Soye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma'aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya suma akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma'aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!" (Mahaifinsa.)
Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da Waukacin jama'ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ?wa?walwa ba Ma'aruf?
Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk Waukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ?wa?walwa ba? Waye bai san cewa kana da wannan nakasar ba Ma'aruf?"
Muryar Ishaq Wagawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake faWa din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma'aruf ke yi alamun cewa kowacce kalma tana bada ma'anar da yake son ya gane a ?wa?walwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba.
"Ka san me ya fitar dani Wazu? Ka san abinda yasa na bar Wakin har kaje ka aikata abinda kayi?..."
Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa.
"... Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma'aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gabaWaya Ma'aruf! Kana gab da rasa komai gabaWaya..."
"And so what idan na rasa?!"
Yadda Ma'aruf Win ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu?na kara lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin Sacin rai.
"Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?"
Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallonsa.
"Nasha gaya maka Ma'aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, ka?i ka yarda dani ne, amma Ma'aruf ya riga mutu, babu shi anan."
Ya ?arasa yana nuna ?irjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya buWe, wani bature ya le?o fuskarsa a murtu?e yace.
"What the in the world are you two talking abou..."
Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a Sace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda.
Shiru ya ratsa wucewar sakan Waya, biyu, uku... kafin Ishaq ya ?araso a hankali ya zauna a gefen sa.
"Kwana na nawa a asibitin nan?"
Ma'aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa.
"HuWu, you were unconscious for three days a Nigeria kafin mu taho."
A hankali ya haWiye yawu cikin ma?ogwaronsa sannan ya ?ara tambaya.
"Me Baffa yace?"
"Ransa ya Saci sosai, ransa ya Saci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yace da zarar ka dawo hayyacinka mu koma gida."
Yaji lokacin da ya zu?i numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa.
"Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma'aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, kowa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma'aruf, dan Allah ka taimaka ko don waWannan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah."
Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ?asan zuciyar Ma'aruf, kuma yana jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa.
Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kullum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma'aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma'aruf din da yake gabaWaya ya sani... Shi yasa fatansa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki.
Ya haWiye yawu a hankali cikin ma?ogwaron sa yana cigaba da kallonsa yace.
"Nayi mana booking flight, gobe zamu koma."
Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da 'Allah ya kaimu' ba.
Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya.
"Yaya kake ji?"
Ma'aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har a lokacin bai buWe idonsa ba yace.
"Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na."
Ba shiri wani guntun murmushi ya suSuce a fuskar Ishaq Win na tabbas Win da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma'aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa.
Ma'aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto Waya ne ke yawo a cikin kansa, hoton Wakin bincikensa, yana hasko tarin takardu da kuma hotunan da suke cikin Wakin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ?arshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru huWu ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho nan.
Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici... Don wannan Wauke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login