Showing 57001 words to 60000 words out of 84782 words

Chapter 20 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10759

Sangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin Wakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya Wauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ?arar shuuuu kawai take fitarwa.
Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe Waya da rabi na dare, wani salatin ya sake suSucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka,?sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin Waure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ?ara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taSa irin wannan mafarkin a rayuwarta.
Taji ma?ogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin?mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan
ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa.
Makogwaronta ya ?ara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ?asa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga Wakin.
Kitchen zata je ta Wauko ruwa, wata?ila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ?ishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai.
Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen Win, ta buWe ?ofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable Win tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask Win abincin data dafa ne.
Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faWin kafaWunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ?ofar.
"Me ya faru? Me ya same ki?"
Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce ma?ogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta Waga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haWiye abinda ke bakinta kafin tace.
"Ba komai, ruwa zan Wauka."
Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge Win, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen Soye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida.
Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci.
Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case Win dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda a?alla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai.
Don haka dole a yanzu da ya Webo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya Wauko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse.
Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye.
"Wani abu ne ya same ki?"
Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buWe fridge Win,?kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda Wankwalin kanta yayi kala Waya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya.
"Mafarki kika yi?"
Amina bata san lokacin da ta Waga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan ba?ar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi.
Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya ri?o nata Waya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna.
"Kinyi addu'a?"
Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ?okarin yin ?aryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana ri?e da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ?asan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba...
"Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..."
Muryarsa mai zurfi ta sake faWa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haWiye yawu a ma?ogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa.
"Ayatul Kursiyu..."
Ta kai ?arshe lokacin da taji kamar almara, ?ar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi ri?e da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta.
"Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah."
Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi.
Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa!
***
?arfe bakwai na safe.
Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ?aunarsa da football (?wallon kafa) shi kaWai ne abu guda Waya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf Win da yake a baya ba, Ma'aruf Win da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace.
Son football Win ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium Win Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana Waya daga cikin members Win dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen.
Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa ta?i tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball Win sa daga booth Win motar ya shiga training Win da ya saba a compound Win gidan.
Kusan ?arfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ?ara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya Wauka, Martha ce.
"Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huWu na yamma."
Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leSSensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members Win nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office.
"Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka bu?ace su kafin a shiga meeting Win."
Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa.
"Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata ta?i tashi, amma bari na kira Ishaq sai a Wauko min tasa."
"Okay sir." Ta amsa muryarta a ?asa.
Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq Win da har yanzu bai dawo ba, bugu Waya biyu kuwa ya Waga.
"A ina ka ajiye mu?ullin motarka?"
"Me za'ayi?" Ishaq Win ya amsa daga cikin wayar.
"Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima."
"Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.)
"Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaWaya na manta da meeting Win ne."
Dariya Ishaq Win yayi daga ciki yace.
"Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu."
Ya girgiza kansa kafin yace.
"Baka da amfani."
Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani.
"YallaSai Barka da safiya."
"Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?"
"Ai kuwa Babu ranka ya daWe, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ?ankaba."
Sai kawai ya gyaWa kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun.
Da haka ya mayar da ball Win cikin booth Win motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ?amshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waWannan siraran ?afafun nata.
***
?arar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma'aruf bane, don a yanzu ?wa?walwarta ta haddace yanayin nasa b???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba.
Ta kashe gas Win da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma Waki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya Wauke ta, baccin da baiyi nisa ba ?arar wani abu ta tashe ta.
Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar Winta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows Win dake wajen sink yana ball, ta fahimci ?arar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ?irar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci.
Ta daWe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taSa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ?ara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya? ya zama gaskiya ba.
Komai zuwa yake saSanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan sa?on, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi.
Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faWa ganin kwanukan abincinta a gefensa... Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya ri?e hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ?onewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaWaya.
Da wannan tunanin ta kammala haWa abincin breakfast Win lokacin da ta tsinci bugun ?ofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani Winki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa Wankwalin V kawai ta yafa shi a haka.
Ta buWe ?ofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data Wora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da sa?o na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ?atuwar jaka irin ta aiki.
"Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Barka da safiya, sunana Martha, nice...)
"She's my sectary." (Sakatariyata ce.)
A lokaci guda muryar Ma'aruf ta faWa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ?amshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leSSensa.
Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaWan yana haWa ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaWunsa.
"You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman."
Sai da numfashin Amina ya katse a ?irjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta mi?o mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba.
"You came with everything right?" (Kinzo da komai ko?)
Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha Win wadda ta Waga kai.
"Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yallaSai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.)
Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ?o?arin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta.
"Kin tashi lafiya?"
Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ?afafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Barka da safiya."
Ya shafo gashinsa ta baya.
"Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?"
Ta san me yake nufi don haka ta Waga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa.
"Wannan sakatariyata ce sunanta?Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min."
Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta Waga kanta a hankali alamun ta fahimta.
"Zamu Wan yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?"
Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login