Showing 36001 words to 39000 words out of 84782 words

Chapter 13 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10769

tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ?ara karya zuciyarta suna saka kukanta ?aruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta taSa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ?arfi ya sake suSucewa a bakinta.
A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin sa?in, aka lulluSeta dashi har ?asa sannan kuma sauran ?anuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guWa. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ?an unguwa don haka abin ya birge kuma ya ?ayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi.
"Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan."
Fatima ta faWa da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai.
"To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ?arata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne."
Ummi ta faWa tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin Winkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu.
Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ?awayen su Ummin da kuma ?awayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faWa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ?arya ne basu yarda ba.
Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take ri?e da ?aramar ?ar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ?anuwan Amma, ?a?an Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ?a?an su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ?araso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan Waya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe Waurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ?a sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu.
Amina ta sani cewar ?anuwan mahaifinta suna da arzi?in da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi Win ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya mi?o masa ba.
Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ?ara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ?arfin gwiwarta na ?aruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta.
"Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi Wawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji Waya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ?afafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ?an fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ?auye.
Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki.
Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arzi?i ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai ro?o yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake bu?ata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba.
Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan."
Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ?ara ?alubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai Winki.
"Gobe zanje in karbo Winkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sar?ar nan mu ?ara yi musu tuni."
Fatiman ta faWa tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace.
"?azu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ?unshi ma."
"?unshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuWi zaki karSo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce."
Ummi ta faWa, kuma tana ?arashewa wata ?awarsu ma ta Wauka da faWin.
"Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa."
"To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki."
Momi ta faWa suna ?yal?yalewa da dariya, Amina kuwa ta haWiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline Win da take shafawa kullum shine dai, robar ko ?arewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne.
Don Allah ya sani idanunsa kaWai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ?warin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara Waukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere.
Tsoro take ji da gaske,
Tana ji kamar tana faWowa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta.
Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaSa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar!
***
Wasa farin girki!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.=?O?=?O?=?O?

BABI NA TAKWAS.
~~~~~
?imbin jama'ar dake yin tururuwa suna ?ara cika kowanne Sangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas Win da aka Waura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ?ara shigowa suna daWa adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ?ungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana Waukar hoto.
Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ?araso inda tasu tawagar ?anuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa.
"Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba."
"Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ?arfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan."
Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ?anuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace.
"Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba."
"Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi Win yana da hannun Waukarta."
Kawu Ibrahim ya girgiza kansa.
"Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi."
"Hankalin da bai kamata ace an ?untata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taSa faruwa ba."
Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ?o?arin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa Wauke da Wimbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana kuWin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu Wari cif!
A cikin ?wa?walwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taSa iya bada ?arsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ?wa?walwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ?in halartar wajen Waurin aurensa?
***
Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buWe gate Win juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ?ofar mazaunin direba ta buWe.
Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ?ofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ?asa. Security Win daya bude masa ?ofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin.
"YallaSai sannu da zuwa."
Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi.
"Ma'aruf yana ciki ko?"
"Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai"
Jin haka yasa Ishaq Win yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya Waga mata hannu yana zarcewa zuwa saman.
A hawa na farko can ?arashe ofishin Ma'aruf Win yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ?ofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf Win mai suna Martha ke fitowa ri?e da wasu files a hannunsa.
"Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala."
Martha ta fada da murmushin dake nuna masa da gaske take, kuma ya san lallai ba?in masu muhimmanci ne don babu ta yadda za'ayi ta tsaida shi idan ha haka ba.
Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ?arasa kofar ya buWe ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani Wan china, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma'aruf Win, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma'aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed Winkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shigar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba.
"Bismillah, ka shigo mana."
Ma'aruf Win ya faWa yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake gabansa yana ?arasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya mi?owa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa.
?aya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda, Ma'aruf Win ma ya mike yana mi?a musu hannu, Waya bayan Waya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu.
Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq Win suka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita.
"Wanne za'a kawo? Tea ko Coffee"
Muryar Ma'aruf Win tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi.
"Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba kenan."
"Na sani..." Ma'aruf ya faWa yana komawa kan kujerarsa.
"Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa."
Sai kawai ya girgiza kansa, yace.
"Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za'ayi ranar da za'a Waura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?"
"Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni."
Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace.
"Abinda kake yi ba daidai bane Ma'aruf, me yasa ko sau Waya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?"
"Me zai haifar?" Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba.
"Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin akwai abinda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra'ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa Waurawa?"
Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numfashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma'aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya faWa da farko gaskiya ne.
Su biyun sun sani cewar wannan auren ba ?aramin haWari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar Soyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su Win.
Ya haWiye wani abu a ?irjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma'aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba, bai taSa ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka haWa wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya Waukan ?arsa ya bawa mutum irin Ma'aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tura ?ar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa.
Sai kawai ya zaro wallet Winsa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma'aruf Win na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card Winsa ya nuno masa shi, kuma da ganin haka Ma'aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya Saci, don rana ta ?arshe da ya fito da ID card Winsa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya Wora aikinsa sama da ala?arsu? shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda ciwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa.
"Ban san me kake shiryawa ba Ma'aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake Soye min..."
"Jamal ya san yarinyar."
A lokaci guda muryar Ma'aruf Win ta katse shi yana kallonsa.
"Me kace?" Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar.
Ma'aruf ya gyara zamansa, ya ?ifta idanunsa yana kallon Ishaq Win sannan ya sake maimaitawa.
"Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wata?ila hakan zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!"
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office Win yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a buWe yace.
"Wai da gaske baka je Waurin auren ba?"
****
Kayan jikin Amina wani farin Lace ne wanda aka Winka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ?unshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi, Waurin Wankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yawa ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma.
Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba Waya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zuwa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har mai?o take saboda yadda take tas babu ko Wigon ?ananun ?urajen da ta saba fama dasu.
"Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!"
Wata Shukra Waya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login