Showing 45001 words to 48000 words out of 84782 words

Chapter 16 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10756

a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ?afafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi.
*
Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ?irjinta, yayin da take jin ?afafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ?arshe yayin da take cigaba kallonsa.
Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai Wan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ?ofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru.
Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi Win ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama?
Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faWawa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru.
"Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daWa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a ma?ogwaronta.
Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta Sace daga dakin.
Ya fitar da numfashin daga ?ofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba.
"Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaWai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..."
Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta.
Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake ri?e hannun kofar sannan ya furta mata.
"Sai da safe."
Ya rufe ?ofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa Waukarta gabaWaya.
**
Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haWe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar Wakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ?arshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi.
Ta rufe idanunta ta buWe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ?asa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al'amarin da ta kasa ganewa.
Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ?arshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaSi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi.
Ta mi?e zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ?wa?walwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ?ar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm Winta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ?ofar dakin ta tabbatar mu?ullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki.
Bayan ta idar da sallar ta daWe tana addu'ar neman gafara da kuma ?warin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito.
Ta dawo cikin Wakin dake ?ara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aay?in da take ji daya ne kawai na cewar ?an gidansu zasu zo, don haka da ?yar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata Waura Wankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta.
Ta kalli kanta a mudubin Wakin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman Wankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaWaya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin.
Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buWe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ?ofofin Wakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haWuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haWewa cikin kalar Wanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin.
Ta jinjina kai a hankali kafin ?afarta ta tafi zuwa daya korido Win anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ?urar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai Wan girma data buWa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a buWe ba.
Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan.
A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ?arasowa hanyar kitchen Win, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store Win amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ?ofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faWo daga wata sama mai nisa.
Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin Winkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana.
"Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din?
Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ?amshin turarensa, wani abu kamar ?amshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa.
"That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan waWannan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar."
Murza ?an yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faWin.
"Yaya baka ganta bane?"
Kuma kafin ?wa?walwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen Win hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour.
"Bata nan kitchen Win?"
Ta sake tambaya tana ?arasowa ciki fuskarta Wauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ?annensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen Win ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask Win can kusa da gas cooker.
Sai kawai tayi karfin halin Wauko wani jug a gefe sannan ta buWe ?ofar store Win ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ?irgen ya tashi daga su biyu ta tsira.
"Sannu da zuwa."
Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta.
"Ashe kina ciki, Barka da safiya."
Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta.
"Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?"
Ta faWa bayan ta janye daga jikinta, sai ta Waga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da.
"Lafiya kalau, nagode sosai."
A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faWi sakamakon haWa idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta.
Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buWe su akanta, kamar ma ?ifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen Win.
A kusa da kafafunta taji cikinta ya faWi gabaWayansa har ?asa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya Wauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ?o?arin tattara jikinta waje Waya kafin ta iya fahimtar me take cewa.
"Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?"
Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta Waga mata kai ba tace.
"Ina tashi nima naga na manta chager wayata."
"Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system Winta gabadaya ta manta kuma project Win masters take yi..."
Ta gyada kai tana ?o?arin murmushi sanda wata ta ?araso cikin kitchen Win itama, watakila itace zasu yi sa'anni Waya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a fito da Wan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi Waya da yayan nasu.
"Ashe kina nan matar Yaya..."
Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin.
"Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba."
A yanzu ?wa?walwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ?anuwansa.
"?an gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..."
Haka Aunty Ma'un ta raWa mata a kunne.
To me yasa ne komai yake faruwa saSanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane?
"Sunana Munaya.."
Ta kara faWa tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama.
"Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce."
Samirah ta faWa tana kallonta.
Sai kawai ta girgiza kanta.
"Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita."
"Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ?anuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ?wa?walwar su Waya da Yaya."
Munaya ta girgiza kanta tana murmushi.
"Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya."
Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su.
A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum Waya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ?asa kuma wasu ?an mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ?an aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke.
Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu.
"Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?"
Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ?an aikin nan tana gaya musu akwai wata ba?ar keda da badu shigo da ita ba.
"Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun.
Amina ta daga kai tana murmushi.
"Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma."
"Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din gidan nan."
"You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai."
Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu.
"Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena."
"Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi."
"What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?" Cewar Munaya.
Surayya ta koma kan kujera tana sake Waukar wayarta.
"Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za'a kira yayi aikinsa a gidan nan."
Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan data dauko a hannunta tana taya su da murmushi.
A lokacin Waya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace.
"Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin ba?i a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Dinner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da safe shi yasa na ri?o shi kar ta zube."
Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa.
"Kar ki wani damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci..."
Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta mi?e tana cewa...
"Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata."
Surayya ta mike kuma ga mamakin Amina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su.
Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din gudan da yasha wasu interlocks masu ?yalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba.
Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canjawa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu Wauki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar Wakin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi da abincin, ko da yake ba ita kaWai suka kawowa ba har dashi ta sani.
Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa... Ashe dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta...
Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa... Har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login