Showing 78001 words to 81000 words out of 84782 words

Chapter 27 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10762

ba, don haka ba zata taSa iya Worar da komai ba a wannan fannin.
Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buWe su tana ?o?arin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ?arfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take ta?ama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata Sullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan.
"Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ?wa?walwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ?ar?ashinta wanda kowanne da irin ?alubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buWe ?wa?walwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa.
Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yun?urin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ?a?ansu harma da duk wanda zai raSe su, sune wanda suka iya buWe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa.
Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar kar?ashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ?wa?walwar ki, ki karSi wannan girman sannan ki fuskanci naki ya?in Amina..."
A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ?arasowa ba. Ma'aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen.
Haseenah Guest Inn.
***
"Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?"
Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey.
"Next..."
Ya sake faWa bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar.
"Ka gaya min Net Patient Revenue din?"
"Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaWaya."
Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace.
"Operating Expenses din fa?"
Mutumin na ciki ya sake faWo masa wani adadi da ya shifa rubutawa.
"Sannan sir akwai Bad debts Win wancan..."
"Sai kuma Natural Expense Win?"
Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya Wanyi shiru kafin ya faWo wani adadi na makudan kudin da saida Ma'aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta.
"YallaSai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole..."
"Just tell me the total Sadiq." (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.)
Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki.
"Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report Win gaba Waya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that..."
"Ka gaya min total din kawai Sadiq."
Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ?okarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma'aruf Win ya sani idan za'a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza 'a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suSuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq Win ne a wajen.
"Wallahi yallabai..."
"Sadiq"
Ya katse shi, sautin muryarsa can ?asa amma kuma a kausashe.
"A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaWan na baku, I'm coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka Wiba ba ku ba, and just dare me and see.!"
Yana faWin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard Win dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ?o?arin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni'imal walkil? daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buWe bayan abinda zai iya kira a?alla minti talatin.
Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taSa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka ri?e hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya Wauko a ciro masa ita.
Daga yanayinta kawai?ya san ta saka ne don bata da wani zaSi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel Win yasa yazo ya karSi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar Wazu da safe.
Daga inda Amina take tsaye, cakuWa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ?ara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta Wauko ta Waura taga abin bai dace ba ta cire shi.
A ajiye ma zancen ?afafunta dake waje a gefe, tunda take bata taSa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba'a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haWewar da har a yanzu ta kasa samun sau?i duk kuwa da ?arfin halin da ta tattaro a ranta.
Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ?arasa jawo ?ofar toilet Win ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin Wakin. Wani abu ya zarce ma?ogwaron Ma'aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ?afafun nata ke tafiya.
Tare da Ru?ayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan komai banda kyawunta don ita Win kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daWe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake Waukan hoton ?afafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wata?ila ko bayan ransa ba zai manta ba.
Ta ?araso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani Wan ?aramin table da ma'aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni.
Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna.
"Wanne abincin zan zubo maka?"
Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ?o?arin buWe plates Win masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ?afafunsa suka tako ta kan carpet Win dake shimfide a wajen ya ?araso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin Wan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaWarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taSa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ru?ayya ya sani ne cewa da kaWan yafi ta.
Kuma wata?ila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta Wauko guda Waya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo, sai yanzu ya lura cewa akan farcen kafafun nata akwai kalar baki alamun lallen da bai gama fita ba, kuma yadda farcen ya rabu kala biyu fari da baki yasa shi kasa daina kallonsu.
Amina ta sunkuya kalli ?afafunta da yake kallo tana son ta nemo abinda ke wajen amma bata ga komai ba, yadda yake tsaye dab da ita kaWai ya isa yasa zuciyarta rabewa gida biyu, amma tunda bata rabe tun a lokacin data fahimci cewa yau zata kwana daya daki daya dashi ba, bata jin a yanzun ma zata yi. Ta sake haWiye wani abu karo na ba adadi a ma?ogwaronta tana son kore Wimbin tunanin dake kanta kafin ta sake yin magana.
"Zaka ci abincin?"
Muryarta ta fito ne kamar tana son tuna masa cewa ba'a kafarta fuskarta take ba, kuma hakan yayi aiki don a lokaci guda ya Wago da idonsa ya kalle ta.
"Naci abincinki, kin manta?"
Ta yaya zata manta, da wannan busashshiyar doya da ?wan data soya tun safe yayi buWa baki, tea Win wajen kawai yasha ya cinye doyar gabaWaya, a lokacin tana waya dasu Amma, tana daga karshen Wakin kallon yadda yake buWe-bude a cikin labtop Winsa yana cin doyar, wani abu da ya kara nutsar da zuciyarta a cikin kirjinta tana jin dama abinda tayi yafi doyar kaWai, sannan kuma wani abu da ya fara buWewa kalaman Amma dake sa hannunta rawa kofa a zuciyarta.
Sai ta girgiza kanta a yanzu tana ?o?arin cigaba da kallonsa.
"Ai wannan ba zai isa ba, idan mutum yayi azumi gwara yaci abinci da yawa."
Ya gyaWa kansa shima yana kallonta.
"Na sani, amma raina ne ya fara Saci yanzu, bana jin zan iya cin abincin."
Kawai sai ta samu kanta da tambayar.
"Me ya faru?"
Kuma fitowar tambayar yasa taji kamar ta fara yin nisa da taraddadin dake zuciyarta.
Hannunsa Waya taga ya zura cikin gashin kansa kamar abinda zai faWa zai yi masa wahala kafin?wucewar sakan biyu yace.
"Ina da abubuwa da yawa a gabana, so mutane na using wannan opportunity Win suna cuta ta, Annual report din MMB- 6 aka aiko min yanzu, kuWin da suka ce sun kashe a shekarar nan Amina ko ni bani dasu yanzu."
Ba maganganun ne suka daki zuciyar Amina ba, sautin muryarsa ne yadda ya fito cike da wani rauni da idan za'ayi musu da Wimbin mutane zasu kwana suna rantsewa cewa ba daga muryar Ma'aruf wannan raunin yake ba,?ba shiri taji ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.
"Meye MMB-6?"
Wata?ila idan ta fara sani meye shi din zata fahimci abinda maganar tasa take nufi.
"Asibiti na ne da yake Abuja."
Sai ta sake gyaWa kanta tana jin kamar maganar tafi karfinta, amma kuma kai tsaye sai tace.
"Ance idan hankali ya Sata hankali ake sawa ya nemo shi, yanzu ko ranka ya Saci babu abinda zai canja, kamata yayi ka samu nutsuwa mai kyau, sai kayi amfani da hakan ka gano koma wane irin akasi ne aka samu."
Maganganun suka tafi har ?arshen zuciyar Ma'aruf, suna fito da irin kwanciyar hankalin da yake ji a duk lokacin da ya gayawa Mami damuwarsa kuma ta bashi Waya daga cikin shawarwarin ta, Amina bata sani bane amma itace mutum ta farko daya dangance shi bayan Ishaq da suka san da zancen asibitin nan.
Abu ne da ko Mamin bata sani ba, kuma shi yasa dama yake damuwa duk sanda aka samu matsala akansa don ya san babu wanda zai iya bashi shawara mai kyau akan hakan tunda ko Ishaq baya yiwa zancensa. Kuma haka kurum ya zaSi boyewa kowa sanin da zaman asibitin don so yake yi da gaske ya binne duk wata halayyarsa ta baya tare dasu kamar yadda yayi wa kansa al?awari.
Zama likita yana daya daga cikin burinsa na farko a duniya, don haka nacin da zuciyarsa ke masa shi yasa shi tsallakewa zuwa garin Abuja ya gina ?aton asibitin guda inda ya danka amanarsa a hannun wani likita mai suna Sadiq, shi yake jagorantar komai na asinitin don hatta tarin likitocin dake musu aiki shi yake biyansu, shekaru biyar kenan da kafa asibitin, kuma tun bayan shekaru biyun farko aka fara samun matsala a annual report din da suke bashi duk ?arshen shekara, ya zama kudin da suke cewa duna amfani dashi duk shekara ya fara fin karfin tunaninsa.
Sai gashi yanzu minti Waya kawai gaban Amina duk dauriyarsa ya kasa ri?e wannan sirrin ya fallasa mata komai, amma kuma da ta bashi sai tasa bai ji yayi nadamar sanar da itan ba, hasalima zuciyarsa gode masa ta dinga yi don a?alla abinda ta faWa Win ya sama mata wani sau?in.
Sai kawai ya gyaWa kansa yace.
"Thank you."
Sannan ya zagayo ta gefen table Win yace.
"Me zaki zuba mana?"
Tambayar tasa ta juyowa itama tana jin nauyin abinda ya faWa, plates din ya shiga budewa gabadaya yana tara murafansu a hannusa Waya.
"Wanne kafi so a ciki?" Ta samu kanta da tambaya babu wani dalili.
Ya girgiza kansa shima.
"Ni zan ci ko meye kika zuba, favourite abinda nake so baya cikin wadannan."
Ya fada yana kokarin ajiye murafan a gefe, sannan kai tsaye ya shiga gaya mata irin abincin da yake so wanda kusan duka na gargajiya ne, sanda yace mata har da Wanwake sai da ta tsaya tana kallonsa, don ita a tunaninta mutane kamarsa basa Waukar abincin gargajiya da muhimmanci.
Ya tambaye ta abinda take so itama kuma sai ta samu kanta da ture komai a ranta ta shiga gaya masa, kuma da kowacce kalma data faWa tana ji kamar tana karkaWe ragowar taraddadin dake ranta ne.
"Ina son chocolate, sannan zan sha lemon zoSo a koina kuma a kodayaushe."
Ta fada lokacin da yake tambayarta abinda take so na kayan kwaWayi.
Ya gyada kansa.
"Naga alama, cox naga zoSo da yawa a fridge dinki."
Ta gyada kanta a hankali itama.
"Ina ga ba zan taSa iya dadewa babu shi ba a koina."
"Wow, I like the enthusiasm."(ina son kwarin gwiwar nan.)
Muryarsa ta gito da slamun cewa shima ya fara jin dadin sakewarta.
Sai tayi wani guntun murmushi da bata san daga ina ya fito ba tana kallon abinda take zubawa.
"Wane kalar chocolate kika fi so?" Da alama so yake hirar ta cigaba da yin nisa.
"Kowanne."
Wannan karon muryarta ta sake fitowa kamar silin gashin dake faWowa ?asa a hankali ba tare da ta dago ba.
"Chocolate bai dame ni ba amma I always enjoy Ferraro Rocher." (Ina jin dadin Ferraro Rocher.)
Bata taSa jin ko sunan ba, kuma sai Allah ya taimake ta kafin tayi tunanin abinda zata faWa, wayarsa dake can kan table Win daya baro ta ta shiga ?ara, don haka ya karbi plate din da gama zubawa ya tafi wajen, ya ajiye plate shi akan table din sannan ya kara wayar a kunnensa ya shiga magana da wani cikin Pidgin english, irin tsantsar Pidgin din da ita bata taba ji ba ma, amma kuma sai yayi mata dadi, yadda sautin muryarsa yake haWewa cikin accent Win da kana ji ka san ya fito ne daga Jinsin Hausa/Fulani.
'Matar ?an gayu.'
Haka Aminu yayi ta tsokanarta Wazu, kuma ita kanta duk da hargitsin yanayin da take ciki ta sani cewa kamar yadda Hajiya Kilishi ta faWa ne, idan banda kaddara ko zata mutu sau Wari ta dawo Ma'aruf yafi karfinta, don a yanzu da kowacce wucewar rana tana ?ara gane cewa yafi ?arfin hangen da take masa a lokacin da ta yarda da auren nan. Shi yasa ko a yanzu kawai ?wa?walwarta ta kasa auna mata adadin kuWin da ya kashe wajen kama Wakin nan don kwana Waya kawai.
Ta Webo farfesun kifi na ?arshe a cikin wani Wan bowl sannan ta juyo tana hango shi daga can inda ya zauna a jikin table din yana magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a ma?ogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ?addarar ba ba zata taba hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin daWawa a Hotel ba.
?afafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ?ar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture mata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya ri?o hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ?irjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau!
Ya sake ri?o hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dun?ule tafin kafarta akan sassanyan marbles din Wakin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata.
Ta buWe su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya dur?usar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ?asa tana cije gefen lebbenta.
"Wata magana nake son muyi Please..."
Yadda muuryarsa a fito a hankali da kuma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta.
"Zamu iya yi yanzu?"
Ya ?ara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskarta.
"Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login