Showing 6001 words to 9000 words out of 84782 words

Chapter 3 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10767

ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa.
...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaWaya Ma'aruf!
***
Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ?aninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daWewa amma mahaifiyar su tana raye.
Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ?a?a goma sha Waya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ?alau.
Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, Wanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra.
Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faWa ko da na rana guda bai taSa haWa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaWai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su Win kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare.
Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karSe sshi bata ?ara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da Wa ke samu daga mahaifiyarsa.
Ita ta raine shi da ?arfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ?adda wasu daga cikin ?anuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daWin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaWai namiji babba a gidan.
?a?an Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raWin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka.
Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ?afafu bayan ta haifi ?arta ta ?arshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ?asashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo.
Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ?aton gida ne mai Wauke da bangare-bangare, akwai Sangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ?aton falo da Wakuna hudu kowanne da banWakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai Wauke da Wakuna biyu da falo da kuma wajen meeting Winsa inda yake ganin ba?i a gida.
Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen?Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ?aton falo, Waki Waya da kuma toilet, sai Sangaren ?an aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaWan ya koma, don haka wajen a ?ulle yake babu kowa.
Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma Wan'uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq Win da Hajiya Maimuna iyayensu Waya, asalin mahaifinsa Wan Kaduna ne kuma shi kaWai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daWe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya Wauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a.
Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin Wanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq Win Baffa ya Wauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya sha?uwa sosai a tsakaninsu duk da cewar Sangare daban-daban suka karanta. Ma'aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci Sangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro.
***
Washegari...
No. 58 Mafara Street, NNDC SharaWa Qauters.
.07:30 Pm.
Tun daga ?ofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaWaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa.
Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har Sangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ?aton falon Sangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaWayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ?amshin turarukansu ya haWe da ?amshin daddaWan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a can gaban Tv stand na Wakin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba.
Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an buWe kowannensu dake cike da kaya fal.
Lefen Babbar ?ar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ?anuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama Waya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biyu na ?a?an Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen? bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce.
Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ?aruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace.
"Hajiya su Ma'aruf sun iso, yanzu na tura Malam Sani (direba) ya Wauko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci Wazu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba."
"Toh Alhamdlilah, Mu?ullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ?awayenta abinci su ma."
Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama'ar gidan babu wanda bai san abinda Ma'aruf Win yayi ba da kuma cewar baya ?asar don labari baya taba Suya,?amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ?anuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba.
Daga nan Sangarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ?anmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su buWe nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ?an autan gidan kuma sa'annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology.
Har Hajiya Kilishin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma'aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ?anana.
Don haka ta amsa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ?anmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka daWe suna yi tunda wannan shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda.
"A'a ranar kunshi ne fa za'ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?"
Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar.
"Ranar kunshi fa shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za'ayi har style Waya."
Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa.
Hajiya Kilishi ta buWe kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din idonta tana kallon wayar Sameera dake hannunta inda take ?o?arin banbace tarin atamfofi da kuma lesukan da zasu yi ankon dasu.
A ?aton gadon Wakin gabaWayansu suke a baje dasu da tarin plate din snacks din da suke ci, sai wadanda basu sami waje bane suka zauna daga kan bedside drawers.
"Ni fa wallahi gani nake kamar wata Waya ba zai isa duk wannan shirye-shiryen ba."
Shukra ta faWa tana danna tata wayar.
"What?!" Salma ta mike daga kwance tana kallonta.
"... Ai Ya Shukra kar ma ki fara wannan zancen don wallahi Imran ba zai taSa yarda a ?ara mana ko sati Waya ba."
Salma ta faWa wanda hakan yasa dukkaninsu yin shewa a lokaci guda, don duk cikin amaren tafi kowa Wokin bikin, yayarta Safiyya ba ruwanta don ita dama ba mai magana bace tun farko, kuma wanda zata aura mai mata ne da ?a?an sa biyu duk da cewar ba wani manyan ta yayi ba. Shukra kuma dake kan matakin masters dinta a bayyane yake cewa hankalinta yafi tafiya ga Project work din da take kan gaSar yi fiye da bikin, duk kuwa da irin rawar kafar da? Suraj Win da zata aura ke yi shi, wanda dan wani abokin aikin Baffa ne.
Har Salma zata sake cewa wani abu Sameera dake gefenta ta daka mata duka, wani duka da idan zata yi Saram-Saramarta Mamin tazo wucewa suke yi mata shi, don haka a lokaci guda ta juyo ta kalli kofa inda Hajiya Kilishin ke tsaye tana kallonsu da murmushi.
"Mami ina wuni..."? Duka kawayensu na Wakin suka hada baki wajen gaishe ta don tun zuwansu basu ma ganta ba.
Da murmushin ta amsa musu sannan ta kira Sameera.
"Ina mu?ullin store dinsu Munaya? Yayanku sun dawo yanzu, kizo ki tayani mu debo abincinsu a saka a motarsu Hajiya Madina."
Da wani irin murmushi mai faWi Sameeran ta amsa, don Allah ya sani duk da kowanensu yayi waya dashi tun a jiya, da kuma hayaniyar gidan ta yau, suna cike da tunanin halin da Ma'aruf Win ke ciki, don abinda yayi wani abu ne da basu taSa gani ba tsawon rayuwarsu duk da sun san cewa kuwa yana da wannan cutar.
***
Mallam Aminu Kano International Airport?
08:30 PM.
"Wata nawa aka saka bikin yaran nan ne Malam Sani?"
Ishaq ya tambaya a lokacin da yake kokarin saka jakar kayansu cikin boot Win motar da Malam Sanin ya buWe.
"Wata Waya aka saka wallahi, ai gidan ma har yanzu yana nan a Winke, shi yasa Hajiya tace ba sai kunzo ba, kawai in wuce daku gida."
Ishaq ya gyaWa kansa yana rufe boot Win.
"Ai dama bamu da plan din zuwagidan nan yau, amma Lallai su Baffa sun shirya, har su uku ne fa a wata Waya kawai."
"To ai rufin asirin Allah ake ciki kullum kuma shi ke rufawar." Cewar Malam Sanin yana dariya.
Duk maganar da suke yi, Ma'aruf na zaune a cikin motar daga baya, wayarsa na ri?e a hannunsa haskenta na haska siririyar fuskarsa da a cikin ?an kwanakin ta ?ara ramewa, message ne kawai ke tururuwar shigowa da kuma tarin emails tunda ya kunna wayar har zuwa yanzu, ya lumshe idanunsa kawai sai kallonsu yake a lokaci guda kuma yana jin hirar su Ishaq Win daga waje.
Allah ya sani gabaWaya ya manta cewa shirye-shiryen bikin akeyi sai a jiya da Mamin ke tuna masa cewa yau ne za'a karbi lefen Shukra, kuma jin cewa gidan a cike yake yasa shima baiyi tunanin ya kamata su je Win ba, amma kuma ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa Waya ya share dukkan messages Win sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami.
Bugu Waya kuwa muryarta ta shiga kunnensa.
"Mai gaskiya na, kun taho?"
Ta kira shi da sunan data la?aba masa tun yarintarsa.
Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka buWe ?ofofin motar suka shigo.
"Eh Mami, Baffa yana gida kuwa?"
"A'a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wata?ila ma kuyi daidai dashi."
Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ?an kwanakin nan, sai dai kafin ya saurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa.
"To shikenan gamu nan insha Allahu..."
"... Akwai maganar da zamu yi Ma'aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben."
Sauran maganar Mamin ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi."
"Ma'aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka "
Yaji ta sake faWa lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani...
"Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a office Winsa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn Win sai mu koma."
Ba shiri Ma'aruf yaji wani abu ya zarce cikin ma?ogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau Waya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho.
Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq ya nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office Win Baffan, wani ?aton branch na kamfanin su inda iya ma'aikata ne kawai a wajen.
"Muhammad..."
Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office Win, bayan sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ?arya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma'aruf yaji ma?ogwaronsa ya bushe a lokaci guda, saboda Baffa baya taSa kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa.
Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika masa office din ta koina saboda kwarjini.
"Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka."
Ya san takardar shima, sun tura ta email Winsa sannan sunyi printing Winta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu.
"Sun ce a cikin shekaru biyu kawai ciwon ka ya kara haSSaka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru..."
Baffan ya faWi haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al'adar ta manya. ?arar sautin shigowar sa?o daga wayar dake aljihun Ma'aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigaba.
"Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma'aruf?"
Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya naWa shi a matsayin manajan kamfanin 'Bakori Enterprises' ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya.
"Baffa... Shekaru biyu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan."
Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa.
"Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma'aruf, kana ina?"
A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gabaWaya, kamar ya sake bin jirgi ya koma asibitin nan ya kwanta.
"Ka manta?"
Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba.
"... Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma'aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yarinya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin,? hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba."
Wani abu ya zarce a ma?ogwaron Ma'aruf, yaji wani Sangare na ?wa?walwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna Soyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ru?ayya har zuwa rabuwarsu ba yadda suke tunani bane sam.
"Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al'umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan karSa maka wani auren tare da na ?annenka."
Sai da aka shafe sakanni kafin maganar ta shiga cikin ?wa?walwar Ma'aruf, da wani irin ?arfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ?irjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya Wago idanu ya kalli mahaifin nasa.
Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce...
Lokacin daya sha?e wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ?arar sautin karkarin da take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login